← Book details Bintu Diyar Bayice Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 16

Sashe 6

Bintu Diyar Bayice Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sarkin Fabarusa ya yiwa Sarkin S’ayrasa bankwana, ya d’au hanya tare da tawagar sa. Haka d’aya bayan d’aya taro ya shiga watsewa. Tawagar shugaban k’asa ma tuni su ka d’auki hanya dan tadda su Aisar.

Sarkin Sa’ayrasa na komawa turakar sa Jakadiya ta zo ma sa da buk’atar iyalan sa na ganawa da shi. Ganin magariba ta gabato ya ce su maza su iso gare shi kada ya rasa sallah.

Hajja Kilishi, Inna Salti, Gimbiya Binta da kuma Gimbiya K’amariyya ne zaune gaban sarki, sai kuma Jakadiya da Bintu can gefe nesa da su. Jikin Bintu har karkarwa yake, fatan ta Allah ya sa Sarki ya duba lamarin ta hanya warware auren masifar da aka d’aura mata.
Ya na mai kallan Gimbiya K’amariyya ya ce

‘’ke mu ke sauraro’’

Maimakon ta bashi amsa sai ta kai kallan ta ga Inna Salti, cikin idanun ta ta na mata magiyar ta taimaka ta shedawa sarki. Inna Salti da ta gane halin da K’amariyyar ke ciki ta ce

‘’Allah shi ja da ran Takawa, batun amren da aka d’aura ne, wanda aka d’aura amren da shi, shi ke neman amren Kamariyya’’

‘’dama akwai wanda ya zo ya same mu da batun amren d’iyar mu? Ba mu san da wanga Magana ba’’

Fad’in Sarki Sule. Inna Salti na mai kame kame ta ce

‘’eh dama ba su zo din ba, kasancewar da akwai rashin jituwa tsakanin Masarautar ta Fabarusa da ta mu, hakan shi ya kawo jinkiri Allah ya taimaki Takawa’’

Sarki Sule na mai gyad’a kai cikin nuna 6acin rai ya ce

‘’ki nufin d’iyar mu ta na sauraran wani ba tare da sanin mu ba?’’

‘’ta yi kuskure, ayi mata afuwa’’

Cewar Hajja Kilishi, da ita kad'ai ke iya bawa Sarki hakuri idan ya na cikin yanayin 6acin rai. Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Sarki Sule ya ce

‘’a shedawa wanda d’iyar mu ta ke saurara a bayan idon mu, ya zo nan da kwana biyu dal mu na so mu gana da shi’’

‘’shi ne Yarimar da aka d’aurawa amre da d’iyar bayi Allah ya huci zuciyar babban bijimi’’

Cewar Inna Salti a hankali kamar wacce ke tsoran maganar. Sarki na duban Gimbiya K’amariyya ya dad’a tambayar

‘’ku na nufin Badde na Fabarusa?’’

‘’Badde kuwa Allah ya k’ara ma ka lafiya’’

Ga mamakin su sai gani su ka yi Sarki ya murmusa, kafin ya k’ara da

"shin kin san ita d’iyar bayi a matsayinwa aka d’aura mata Badde?’’

Inna Salti wacce ta fara dana sanin furta maganar ta ce

" a matsayin Binta, Allah ja da ran ka’’

‘’wacece Binta?’’

Tambayar Sarkin Sule da ya sa kowani mahalukin da ke wajan sai da ya sha jinin jikin shi. Da kyar Inna Salti ta yi k’arfin halin furta

‘’d'iyar babban bijimi ce’’

Cike da 6acin rai ya ce

‘’ita Kamariyya da aka amrer da d’iyar bayi a matsayin kaunar ta, kuma ta zo mana da zancen alakarta da wanda aka d'aura din, ya ta ke so mu yi ma ta?’’

Shiru babu wanda ya iya furta komai. Idanun sa bisa silin yace

‘’an bar mu muna jira, ke mu ke sauraro K’amariyya!’’

Murya na rawa ta ce

‘’dama tin da haka abin ya kasance, na ke so a warware matsalar ta hanyar raba amren …….’’

‘’yashasheshshen zance!’’

Sarki Sule ya katse ta ta hanyar daka mata tsawa, tuni jikin K’amariyya da Binta ya hau k’yarma tsabagen firgici, kowa sai da ya sha jinin jikin sa, Jakadiya ta durkusa ta na fad’in

‘’tuba mu ke ran Babban biji ya dad’a, Allah huci zuciyar Babban Biji, lafiya salamun’’

Sarki kuwa be gushe b ya cigaba

‘’mun biye mu ku mun bi san zuciya mun aikata ha’inci, hakik’a Sarki Abdulrahman ya kasanse mai zurfin tunani, mu kuma mun kasance daga cikin ma’abota san zuciya, fatan mu shi ne gyara wanga kuskure da mu ka aikata bisa san zuciya ba tare da 6ata dangantakar arziki da mu ka kulla a wanga rana ta yau ba’’

Kallan sa ya mayar ga Bintu, kana ya ce

‘’ina Kilishi?’’

‘’ran Takawa ya jima, gani kusa gaban ka’’

Cewar Hajja Kilishi.

‘’wagga d’iya ta arziki (yayi nuni ga Bintu) ta ma na abun da jinin mu basu ma na ba, sanadiyar ta yunwa ta kau a masarautar mu, idan ba mu maishe ta d’iya ba, ko shakka babu mu na daga cikin wanada ake kira butulu, wagga d’iya d’iyar mu ce, ni Sule na kira wagga d’iya da d’iya a gare mu, maza a shirya d’iyar arziki, idan an wayi gari ta bi tawagar masarautar Fabarusa dan kuwa jinkirin makwannin biyun ka iya zama barazana a gare mu, da zafi zafi akan bugi karfe…mun gama Magana’’

Ya na dasa aya ya tashi cike da Sarauta yayi shigewar shi daga ciki, ya na jiyo koken Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta amma ya mu su kunne uwar shegu duk da kuwa har ran sa ya ke jin abun.

Ita kan ta Bintu jin gobe gobe za a wuce da ita hankalin ta ya dad'a tashi, ta ma kasa motsawa daga in da ta ke, ta nemi kuka ta rasa.

Gimbiya K’amariyya kuwa wacce har shid’ewa ta ke tsabagen kuka da ya ci karfin ta, tuni ta sake fad’uwa sumammiya a karo na biyu. Nan waje ya sake kaurewa da salatin su Hajja Kilishi da Jakadiya. Dan kok’ari har da Bintu cikin kawo d’oki ta hanyar ciro mayafin ta, ta shiga yiwa Gimbiya K’amariyya fifita, yayin da Inna Salti ke yayyafa mata ruwa.

Wani k’akk’arfar ajiyar zuciya ta saki, alamar ta farfad’o, amma idanun ta lumshe ta kasa bud’e su, hawaye ke gudana bisa kuncin ta. Sai fa a sannan Gimbiya Binta ta ankare da Bintu da ke sunkuye bisa kan Didin na ta, sai fifita ta ke ma ta, ai kuwa ta daddage ji kake tas! Ta sauke yatsun ta biyar bisa kuncin Bintu sai da ta ga wuta a idanun ta. Hannun ta biyu bisa kuncin ta ta ke duban Gimbiya Binta, hakan ne ya dad’a k'ular da ita, ta sake d’aga hannu da niyar kai mata wani marin caraf Inna Salti ta ruke hannun ta, ta na mai fad’in

‘’kul kar ki kuskura ki sake! Kin san kuwa matar Yeriman Fabarusa ki ka d’aga hannu ki mara? Ina hankalin ki ya tafi?’’

Jin haka Gimbiya Binta kamar ta yi hauka, fad’i ta ke

‘’d’iyar bayi na mara, d’iyar bayi wacce na saba takawa ita na mara, babu wata matar Yariman Fabarusa da ta wuce Didi, duk makirci da munahunci wanga wulak’antacciyar Baiwa arudu ya k’are bisa kan ta! Ku ma mu zuba ni da ke ina mai tabbatar mi ki alkiyamar ki ta zo dan kuwa da ki tafi zuwa Fabarusa a gurbin Didi gwamma ki je ki kashe kan ki, dan kuwa masifa da balak’I ya na nan an tanadar mi ki, kuma shi za ki riska, sai dai uwar ki ta haifi wani…..’’

Ta juya fuuuu ta fice gudun kar Bintu ta ga hawayen ta, dan kuwa su ke sauka d’aya bayan d’aya tsabagen bakin ciki da takaici. Hajja Kilishi shi ce ta ja Bintu zuwa turakar ta dan neman yanda za a yi idanun Bintu da ya kumbura da shatin yatsun Gimbiya Binta ya baje, bayan Inna Salti ta bata baki bisa ga lamarin Gimbiya Binta da kuma mata alk’awarin irin haka ba mai sake faruwa ba ne. Nan su ka bar Inna Salti ta na rarrashin Gimbiya K’amariyya, domin kuwa bakin alk’alami ya bushe tuni.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[8/16, 4:34 PM] ‪+234 803 583 5431‬: ®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

5⃣

Da daddare bayan an idda sallar isha’i, Yarima Jafar da Yarima Barde zaune a falo sun yi jigum kamar wanda aka yiwa mutuwa, Khalil na daga d’aka ya na waya da matar sa.

Babban falo ne mai d'auke da k'ayataccun kujeru na sarauta, masauki ne da dama a ka tanada na musammam domin saukar bak'i na alfarma irin su Barde.

Tun da su ka isa ga masauki Barde ke zaune nan falon, sallah kad'ai ke iya sawa ya motsa. Shigar sa na d'aurin aure ke jikin sa, sai dai ya cire babbar riga da rawani, sumar kan sa kwance lub lub bisa kan sa.

'Daya daga cikin dogarawa da ke ciran kofa ne ya shigo ya zube gaban Yerima Barde, kana ya ce

‘’ran Yarima ya dad’e, Gimbiya K’amariyar d’iyar Mai martaba Sarki Sule na S’ayrasa ce me neman iso gare ka’’

Jin sunan K’amariyya tuni kafad’a Barde ta tasa, yayinda jijiyoyin wuyar sa su ka bayyana. Amma ya kasa furta komai. Yarima Jafar ne ya ce

‘’ka iso da ita gare shi’’

Dogari na mai fad’in

‘’an gama ran Yarima Ja’afar ya dad’e’’

Ya tashi da sauri ya fice. Yarima Ja’afar ma tashi yayi, ya d’an dafa kafad’ar Yarima Barde sa’annan ya shige ciki. Shigar sa ke da wuya Dogari ya shigo biye da shi Gimbiya K’amariyya ce. Sai da ya kawo ta gaban Yarima Barde sannan ya juya ya koma waje in da bayan Gimbiya K’amariyya ke tsumayin ta.

Tin shigowar ta ya kafa mata ido, har ta iso gare shi sanye cikin atamfa koriya wanda ta rufe da farar alkyabba ta alfarma. Duk tashin hankalin da ta ke ciki da kuma wanda Yarima Barde ke ciki be hana shi ganin kyauwun Gimbiya K’amariyya ba. Ga wani k’amshi mai saka kwanciyar hankali da ya kasa gane kan sa ke tashi daga jikin ta sa’in da ta zaune gaban shi. Yayi kok’ak’arin sanya kwayan idanun sa cikin na ta, amma hakan ya gagara kasancewar ta yi k’asa da na ta idanun.

‘’K’mariyya…..’’

Ta ji murya mai d’auke da tarin kwarjini ta daki kunnan ta, wanda tun da aka d’aura masa aure da Bintu, kwakkwarar kalma d’aya be fito daga bakin sa ba sai a yanzu da ya ga K’amariyya zaune gaban sa.

‘’K’amariyya’’
Chapter 6 · 0% Book details