← Book details Ba Jinina Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 10

Sashe 8

Ba Jinina Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawaye hawaye fa take gani a idanunsa Baffa ne yake mata kuka da rok'on ta haifa masa 'ya'ya yana nufin ita ke zubar masa da yara idan tasamu ciki.

Itama fashewa tayi da kuka mai k'arfin gaske zuciyar ta yana wani irin suya take kalaman anty shamsiyya suka shiga dawo mata akaro na hud'u data sake rasa cikin dayakai kimanin watanni biyar wanda har sunfara saka rai da shi tunda yafi sauran ukun jimawa.

"Amina nifa nafara zargin kishiyarki akan wannan b'arin dakike yi ajere ajere duk dana san cewa komi dayake faruwa daga Allah ne kuma dama can Allah ya hukunta wannan cikin da suka lalace bamasu taka k'asa bane amma akwai sula kuma Koda ba haka bama idan kin zauna kinyi tunani taya ita bata haihuba zata bar wata tazo da daga baya ta cika gidan aikinsan dole zatayi wani abun akai duk wannan soyayyar da kulawar datake baki duk na banzane ga uban bautar dake da take a siyansace tunda kikazo gidannan baki gaba baki baya kullum ak'are ya kud'in guzuri inzaki farka ki gane ki farka sannan maganar gaskiya Amina ta inda zaki gane cewa magana na gaskiya ne idan kin sake samun wani cikin ko Baffan kada ki sake ki fad'awa sai dai su ganshi tunda na lura ke ba mai girman ciki bane irin girman cikin bane irin cikin Umma ne dake wanda inda anganshi to bazai k'ara sati guda ba zai fito duniya dan haka duk irin wahalar da zakici ki daure ki cije ki raini abinki dan tun mahaifarki tana iya d'aukan ciki zata zo ta gaza kema azo ana samun wata matsalar kinga kunyi duro kenan burinta ya ciki ke babu ita kinga anyi one one kenan daman abinda take so kenan.

Ganin tayi tsaye ga hawaye na tafaman shatatowa daga idanunta yasa ya kamo hannayenta ya zaunar da ita asaman cinyar ta yana cigaba da hawayen tare da rok'on ta daure ta daina Yi Masa ganganci idan tasamu ciki, ganin cewa ko me zata ce ba fahimta zaiba yasa ta tsuke bakinta amma ranta banda suya babu abinda yake mata.

_________________________

Wannan karon Saida tayi wajen wata hud'u kafin Allah yabata wani cikin mai d'an Karen laulayi dan haka kamar yadda 'yar uwarta ta bata shawara ta rik'a daurewa tana shanyewa dan tanaso ta tabbatar da abinda ta fad'a mata akan wannan kareemar matar ma kula da ita da damuwa da al'a muranta

Hakan kuwa akayi duk yadda taso ganewa bata bata damar hakan ba haka ta rik'a daurewa tana nuna babu komai duk da kuwa irin bak'ar azabar datake sha wajen cimaka da kuma rashin son wani k'amshin haka ta dinga daurewa har zuwa lokacin da cikin shiga wata bakwai bai fitoba amma komai nata ya k'aru domin Amina macece mai matuk'ar kyau da diri gata fara tas babu ta inda ta baro mahaifiyar ta bafulatanar asali mazauna wani daji.

Bayan wata guda lokacin cikin ya shiga wata na bakwai Kuma cikin kariya da k'udura na Allahu S W T A daga Baffa har Sailuba babu wanda Allah yasa ya gane cewa Amina tana da ciki, yayin da Baffa yadamu sosai har yana cewa kodai wani abun tayi dan karta haihu dashi?

Tun bayan da cikin ya shiga wata na biyar ta daina duk wani laulayi sai dai dan banzan kwad'ayi kasancewar Koda yaushe itace a kicin tana bauta da aiyukan gidan hakan yasa duk abinda ranta yake so shi take dafawa taci son ranta kayan kwalam kuwa Baffa baya rabo da kawo musu dake ita Sailuba tafi ganewa ta narki abinci aci kaji da su kifi duk wannan abubuwan basu dameta ba haka Amina zatayi taci ta kuma bawa duk mai rabo dan itama mutum ce mai yawan kyauta kamar Baffa, sannan kuma duk wani irin kyau da shek'i data k'ara hakan baisa Sailuba ta ganeba kasancewar dama can ita d'in Mai kyaun ce, Baffa ne kad'ai ya kula da hakan saidai bai tankaba domin ya lura da ita a y'an kwanakin wani bin sai tayi ta k'unci irin dai abubuwan da ba a raba mai tsohon cikin dashi.

Ranan wata laraba Amina ta tashi da matsanan cin ciwon mara cikin dare Allah yasa Baffa ad'akin ta yake ganin irin murk'ususun wahalar datake yasa yayi tunanin ko wani cikin tasamu zai fita dan haka yadda take kuka tana fad'in ya taimaka mata haka shima yake rok'on dan Allah karta bari wannan karon ma yayi asaran cikin dakyar ta iya bud'an baki tace"dan Allah ka taimakamin Baffa ba bari bane wannan karon haihuwa zanyi d'a zan haifa Baffa da sam bai gane abinda take cewaba ya fita da gudu zuwa d'akin Sailuba dagashi sai gajeran wando ko riga babu ajikinsa haka ya fice yatasota tasha mamakin ganin yadda Amina take murk'ususun ciwo wani b'oyayyen murmushi ta saki tana fad'in aranta magani yabi jiki Kennan, ita ta taimakawa Baffa yasa kaya yasunkuci Amina da gudu yayi waje sam kasancewar sa na likita bai kamata ace har irin haka yafaru a gidansa ba matarsa da suke kwana su tashi tare har tasamu ciki ya kai tamakin haihuwa duk bai saniba, amma idan mukayi duba da cewa Allah shine me yadda yaso Kuma asanda yaso sai muga hakan ba abin mamaki bane.

Labarin yafara sauyawa ne daga lokacin dayagama dubata ya tabbatar da abinda ya gani bai k'ara tabbatarwa sai da yayi mata scainin, tashin hankali yatad'a a rud'e domin ganin dan mutum muraran yana neman hanyar isowa wannan duniya mai cike da abin al'abi da mamaki.

Kasa control d'in kansa yayi yafashe da wani k'arkarfan kukan dayasa Sailuba danno kai cikin d'akin da mugun gudu zuciyar ta kamar takarda tsabar haske tasani wannan kukan na Baffa yana nufin wannan karon ma sunyi messing babynsu saidai kuma abinda tagani ba k'aramin kad'uwa tayiba domin har lokacin bai kashe na'urar ba ga babyn nan wanda basu gane wane jinsi bane na ta wutsulniya sosai ta daskare a jikin k'ofa zuciyar ta yana wani irin masifaffen bugu.

Wani irin juyi Amina tayi gami da sakin wani k'arkarfan nishi da gudu Baffa yatarota dan saura kad'an ta fad'o daga gadon tarotan yayi daidai da sallamar babyn izuwa duniya wadda ta fad'o ita da mahaifar gaba d'aya rasa yadda zaiyi yayi sai kawai ya zube gwaiwoyinsa ak'asa yayi sujjada shukuriyya kafin yayi saurin Kiran ma aikata suka shigo dakayan karbar haihuwa shi ya gyara matarsa da 'yarsu takafin ya rungumeta ajikinsa yana tofe ta da addu o I kala kala.

Wani abin mamaki tun kafin Baffa ya sanarwa kowa haihuwa Muhammad yafara sanarwa haihuwar Wanda a yanzun yake shekara ta uku amatakin karatuntasa Wanda yakeyi Kuma zab'in Baffansa yayin da ak'asan ransa Kuma yasha alwashin bayan ya gama zaije yayi na soja wanda shine zab'i da ra'ayinsa amma yanzun kam zab'in mahaifinsa yabi yake Wanda ya zabar masa.

Hakanan ya tsinci kansa da wani irin farin cikin kasancewar ganin Baffansa cikin tsantsar farin ciki, haka ma Inna ana fad'a mata haihuwar da kanta ta taso abinda bata tab'a yiba wato kwana agidan Baffa wannan karon cewa tayi ita zata kula da maijegon da'yarta wannan karramawa ta Inna ya k'ara mata kima da mutunci a wajen iyayen Amina.

Ranan suna kuwa Saida Muhammad ya yabaro makaranta yazo suna yasha fad'a wajen Baffa domin a lokacin suna shirin jarrabawane, a lokacin murmushi yayi yace kasa daurewa ne.

Tunda yai arba da kyakykyawar yarinyar yaji ta masifar shiga ransa shikenan Kuma ya tare a d'akin domin kullum ya fito daga b'anga rensa yana d'akin Ammey kamar yadda itama Baffa yasashi fad'a mata har zuwa sanda yakoma makaranta dakewar MARAYAM kamar yadda taci sunanta wanda take Ammey tace sunan mahaifiyar malam ne hakan kuwa yayiwa malam dad'i kulawa ta musamman yake bawa yarinyar kullum sai ankai Masa ita ya tofeta da addu o in tsari

Sailuba kuwa

Takuce maman islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
BA JINANA BACE
2021

NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 12

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, yayin da Sailuba sukayi amanna da malaman tsubbu wani lokacin suyi sara kan gab'a wani lokacin kuma sai b'ata lokaci da nesan ta kai da mahalicci.

Wata rana Sailuba takaima k'awarta haj. Zakiyya ziyara anan ne take cewa "k'awata ni kuwa me zai hana ki karb'i Maryam?"

Wani d'an iskan kallo ta watsa mata tace "amma k'awata basiranki ya gude ne ko?kirasa yar da zakice na karb'a na raina da hannayena masu albarka"

"Hum k'awata kenan inbaki saniba ki sani rainon wannan yar shine zai baki duk wani abu da kike nema kuma ta hakane zaki cimma burinki akanta sannan zokiji" tajawo tayi mata rad'a, bushewa sukayi da dariya suka tafa sun jima suna kulle kullensu kafin su sallami juna.

Haka Maryam taci gabada samun kulawa daga ta ko wane fanni kamar yadda Nanne ta buk'ata haka dole Ammey ta cire kunya take kula da yarinyar ta domin ta kula abokiyar zamanta ba irin wannan matan bane da suke son jan d'an wani jikinsu.

Sai dai abinda yai masifar d'aga hankalin Amina shine sanda Maryam ta isa yaye kawai tace ita Maryam takeso abata tunda ita an tabbatar da bazata k'ara haihuwa ba, ita kuma Amina yanzune ma ta soma Kuma babu wanda yasan iyaka ci sai Allah dan Allah ya rok'ar mata ita ta temaka tayi mata wannan sadaukarwar.

Wani irin masifaffen tashin hankali ne yakawowa ziciyarta farmaki take tafashe da wani fitinannen kuka mai mugun k'arfi wanda yasa duk suka maida hankalinsu kanta yayin da Baffa yake dubanta da masifar mamaki Sailuba kuwa wani b'oyayyen murmushi take saki azahiri Kuma hawayene yake ta rige rigen fitowa daga idanunta ta bala in kalar tausayi ta taso ta durk'usa agabanta tareda rik'o hannayenta tana wani irin kuka mai cin rai tace.

"Dan girman Allah badan halina ba dan soyayyar da kikewa annabinmu muhammadur rasulillah (S A W) ki taimaka kiyimin wannan sadaukarwar na miki alk'awarin Maryam bazata tab'a sanin zafin cewa bata tareda mahaifiyar taba zan rik'eta da gaskiya da Amana zan kula da ita fiye da yadda bakiyi tunaniba kiyimin wannan temakon 'yar uwata" ta k'arashe tareda zubowar wasu hawayen Mai uban yawa.
Chapter 8 · 0% Book details