← Book details Ba Jinina Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 10

Sashe 5

Ba Jinina Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffa yana d'aya daga cikin d'aliban makarantar haka kuma bashi uban dayafi malam babba kaf unguwar domin shine mutumin da baya duba girma ko matsayinka zai fad'a maka gaskiya kai tsaye komin d'acin ta kuwa, haka duk sanda Baffa yake gari bashi da wajen hiran yamma sai wajen malam babba haka nan cikin hikima yake dad'a yiwa duk Wanda suke tare nasiha da hak'uri da zaman lafiya da kowa tare da rok'awa duk Wanda ka gani ba akan daidai ba shiriya bawai ka rik'a zaginsa ko la antarsa ba domin hakan ayace wata rana sai ya faru akan ka ko akan d'anka.

Cikin matasan da alh. Baffa ya bawa aiki akwai 'ya'yan malam Babba guda biyu Kamalu da kuma Usman yana matuk'ar jin dad'in aiki dasu saboda ingantaciyyar tarbiyyar da suka samu daga mahaifin su.

Oh na manta ban muku bayaniba tun lokacin Baffa yana k'auyen su yana da aminiya gsai d'aya Hassan Wanda suka kasance tamkar uwa uba d'aya koman su tare sukeyi hatta wajen kwana ma idan ya sun kwana agidan su Baffa to gobe agidan su Hassan zasu kwana Wanda har hakan yaja wa iyayen su kusanci suka zamo kamar 'yan uwa na jini.

Sai da aka shafe shekara guda Inna bata kumayiwa Baffa maganar k'arin aure ba saboda danne tan da akayi da k'arfin asiri sai lokaci guda yaje garin Wanda alokacin ma rabon data sanyashi idanunta ma an d'ebi wata kusan biyu mutumin da duk k'arshen sati sai yaje ya ganada mahaifiyar ta ya kai mata abubuwan bak'ata yanzu kuwa sai gimbiya Sailuba tabada umarni wannan kenan

Taku maman islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASA

MAMAN ISLAM

Page 7

Bayan sun gaisa da tare da tambayar juna bayan rabuwa yabata uzuirin cewa baya zama ne shiya sa ta d'an jima bata ganshiba da mamaki ta rik'a kallon sa domin bata tab'a ganin uzurin daya hanashi gaida itaba Sai a wannan lokacin sai dai ta alak'anta hakan ne akan maganar auren data dameshi da ita hakan yasa tace "Allah ya kyauta"

Gyara zaman ta tayi tace "Baffa kamar dai yadda na takura maka na matsa maka har hakan yasa kake ganin kamar na matsa maka dayawa to Baffa inaso kasani 'ya'ya suna k'arawa mutum martaba da kima idon al'umma kuma 'ya'ya rahama ne sannan ni'emane da ba kowa Allah yake yiwad,,,irin wannan baiwar ba, kai yanzun ba abin alfaharinka bane ace yau ga sanyin idaniyar kaba kana dubansu kanajin dadi? to inaao ka saurareni da kyau yau muna biyar ga wata dan haka na baka daga nan zuwa k'arshen wata kafito da mata ka aura ko kuma ni na zab'a maka kamar yadda nayi maka na Sailuba"

Shiru yayi yana sharce gumin dayake tsiyayar masa har saida Inna ta kula da halin dayake ciki amma sai tai kamar bata ganiba gyara zaman sa yayi yace "dan Allah Inna ki d'an k'aramin lokaci zanyi yadda kike so amma Inna taya zan fara fad'awa sailuba wannan labarin?"

Sosai inna ta hasala abatunsa ta lura saboda bayason bacin ran Sailuba ne baya so dan haka ta had'e rai tace "au saboda b'acin ran Sailuba ne kai baka son barin baya to wllh kaji na rantse muddun ka bari k'arshen watannan yazo baka nemo matar aure ba ni zan nema maka ance maka ita Sailuban haihiwar take sone da tana so ai bazata rik'ka to she mahaifa tana d'inketa ba ko ance maka bansan halin da kuke ciki bane to ita aminan nata da tad'auki amanar zuciya da rayuwanta ta damk'awa sune suke kewayowa suna kawomin labarin komai dan haka ni na gama magana idan kuma ka isa kai d'ane ka k'etare magana ta kagani duk duniya babu wanda yakaini son Sailuba domin ita d'in 'yatace halak malak kuma JININA CE sannan rainona ce sai dai a irin tarbiyyan da nabata babu wanda take amfani dashi sai na banzayen aminanta da suke d'orata a keken b'era har nagaji da fad'a mata gaskiya ta nuna bata buk'ata Allah yasani na sauke hak'k'in ta da yake kaina nabata kula da tarbiyyan da ko uwar data haifetane iyaka kenan dan haka na fita hak'k'inta sannan inayi mata fatan shiriya"

Tunda yake baitab'a ganin fushin mahaifiyar tasaba sai wannan karon domin daga shi har Sailuba lallabasu Inna take amma yau kam yaga tsantsar b'acin ranta dan haka ya rik'a lallab'ata har zuwa sanda yabaro garin.

Sai dai babban tashin hankalin sa yadda zai fuskanci gimbiyar tasa da wannan batun yasan cewa ba abune mai sauk'iba ya tunkareta da wannan babban al'amarin, koda yadawo gida haka abin yay ta damun sa arai har gimbiyar tasa tay ta tambayarsa damuwarsa yace babu.

Sau tari idan abubuwa suka sha masa kai yakan nemi shawarar malam Babba wannan karon ma yazo wajen malam d'in kamar ko yaushe neman shawara tare da baran addu a kamar yadda yasaba abin Allah kuma masu Karin magana sukace kaddara ta riga fata anan suka had'u da Amina d'iyar malam wacce tunda yake Allah bai tab'a sawa sun had'uba sai ranar dan dama ba wani sanin yaran malam d'in mata yayiba domin basu cika fitaba sai da babban dalili kuma bayan haka ma dole bazai san Amina domin ko acikin gidan ma abune mai wahalar gaske kayi katarin ganin ta atsakar gida domin koda yaushe tana d'aka.

Tunda yay arba da Amina ya nemi nutsuwar sa yarasa bai tab'a katarin had'uwa da abinda lokaci guda yai tsalle ya shige zuciya lokaci guda ba sai Amina, itace tayi masa kamun dashi da kansa ya kasa daurewa har saida ya furtawa malam Babba hakan, take batare da wani jinkiriba yace ya bashi Amina halak malak yaje ya sanar da mahaifiyarsa kuma insha Allahu k'arshen watan da muke ciki za ad'aura auren haka nan Allah yasanyawa malam Babba k'aunar baffa saboda Baffa mutum ne dayasan darajar manya haka nan ya iya mu'a mala da duk wanda suke tare daahi.

Cikin tsantsar farin cikin daya kasa b'oyuwa ya k'arasa gidansa fuskar nan d'auke da annuri haka ya dinga abubuwa har dai Sailuba ta kasa daurewa ta tambayeshi yace mata babu komai kawai dai yajishine fresh shiyasa yake farin ciki.

Bata k'ara tsinkewa da lamarin ba sai washegari dataga yana shiri ta tambaye shi inda zashi yabata amsa da wajen Inna take taji 'yan hanjinta sun kad'a tace "naga yau dukafa kwananka biyu da dawowa shine zaka kuma komawa?"

Dakatawa yayi da fesa turaren da yake ya dubeta yace "yanzu dai kina so kice dan na dawo daga gaida uwata shekaran jiyaifi ne kenan dan na koma yau?"

"Ba lafi bane amma gaskiya bazaka koma yauba ina laifin ka bari zuwa koda k'arshen watane amma daga dawowa sai ka wani kwashi jiki kace yau zaka koma nidai gaskiya ban amince ba"

Ta k'arishe da irin yaudararrun kalaman da malamain su yace su d'an rik'a had'awa dasu dan ba ko dayaushe ne aiki yake amfaniba wani lokacin sai an had'a da kissa.

Wani banzan kallo ya watsa mata kafin yace "to uwata ai tunda kin isa sai ki hanani zuwa tunda naga alama kin kai har kin wuce wuyanki yayi kauri" mts yaja dogon tsaki ya juya batare da ya kalli inda takeba ya fice.

Sau tari wasu abubuwan dayake mata sai yaga kamar cikin tsoronta yake ga wani d'an banzan Shankar ta dayake wanda indai zata bashi umarni sai ya bi.

Ita kanta Inna tasha mamakin maganar dayaje mata dashi ba k'aramin farin ciki tayi da irin da ya nemoba dan ita kanta ganau ce akan irin tarbiyyan Yaran malam Babba dan haka batare da b'ata lokaci ba ta tashi 'kaninta d'aya da k'anin Baban Baffa suje suka kai dukiyar aure da kayan nagani ina so har da nasakun rana.

Babu yadda malam baiba akan su barshi ai shima Baffa d'ansa ne suka k'iya cikin mutuntawa suka baro gidan malam Babba suna ta yaba karamcin sa.

Sanda Sailuba tayi ido biyu da kawun ta dana Baffa saida tasha jinin jikinta domin tasan cewa banza baya tab'a kai zomo rafi.

Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 8

Haka nan dai ta yi musu sannu ta kawo musu ruwa da abinci kasan cewar dare yakawo kai domin tsakanin garinsu da nan akwai d'an nisa hakan yasaka dole suka kwana dan ason ransu so sukayi subi motar 'yan kasuwa.

Duk naci da son jin kwakwaf na Sailuba babu abinda ta fahimta dan babu wanda ya tanka mata har zuwa wayewar gari da suka shirya Baffa ya kuma maida shi har gida anan ne Inna take masa maganar dawo da Muhammad d'an amininsa dayake rik'o tunda shima Hassan shikenan d'an nasa k'wara d'aya kamar rai tundaga haihuwarsa da matar ta rasu bai k'ara haihuwa ba duk kasancewar shima alokacin matansa uku kuma uwar Muhammad itace amarya kuma da ita Allah ya bashi haihuwa wanda shima Innan ce ta raineshi da madara bayan ya isa yaye kuma k'iri k'iri Babba ya d'auke shi ya hana uban shi wanda saboda kara baiko kara waiwayar Baffa akan maganar ba dama matansa ba wani son sa sukeba sun masifar tsanarsa saboda tarin dukiyar da Allah ya horewa Hassan gashi duk cikinsu babu wacce ta haihu hakan yasaka ko k'aunar ganinsa basayi tun yana zuwa gidan idan Baffa ya kawoshi hutu har dai ya gane ba a buk'atar sa shikenan idan yazo sai dai yasamu Abbansa akasuwa suyi wuninsu anan susha hiransu.
Chapter 5 · 0% Book details