← Book details Ba Jinina Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 10

Sashe 6

Ba Jinina Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsanar da Sailuba tayiwa Muhammad kuwa ta ninninka wacce matan babansa sukayi masa domin acewar ta akansa shi kad'ai Baffa ya tare baya kula kowa baya ganin kowa indai yana tare da Muhammad wanda bata da damar musguna masa dan akan yaron tayi imanin zai iya sakinta ga ubansa malamin k'auye injita koda tabi tak'asa babu nasara dan haka ta koma ci masa mutunci da wulak'anci iri iri ga d'an karen gori wannan ne yasamo asalin tsanar da Muhammad yaiwa Umma kamar yadda Baffa yasashi dole yake kiranta dan da farko Sailubanta yake kiranta dan Muhammed tayayyen mutum ne kaifi d'aya kuma mara tsoro sannan baida shakka duk abinda yayi India yasan shine kana tambaya zai ce shi ya aikata wannan abun sai dai kome zai faru ya faru ganin kima da darajar Baffan shine yasa har yake kiran sailuba da umma.

Ak'alla Muhammad yakai shekaru sha biyar a hannun Baffa tun baifi shekaru hud'aba ya d'aukko shi yanzun haka yana shirye shiryen turashi waje karatune dan atsarinsa yafison shima d'ansa yazamo likita kamar shi.

Bayan tafiyar Muhammad da sati biyu aka d'aura auren Baffa da Amina auren da yai mutuk'ar girgiza rayuwar Sailuba domin koda wasa bata tab'a kawowa Baffa aure nan kusa ba domin malaminta ya tabbatar mata da cewar an kawar da tunanin Baffa akan wata maganar aure kujifa wani shirme.

Lokacin da falonsu yake karb'ar bak'uncin 'yan garinsu, ita kuma sannan tafice a matuk'ar gigice zuwa gidan k'awa aminiya kuma babbar mai bata shawara haj. Zakiyya.

A haukace ta shiga gidan lokacin mijimta yana durk'ushe yana mata matsar k'afafu yayin datake hakimce asaman kujera tana faman shan k'amshi yayin da shi kuma bawan Allahn yake tasharb'ar gumi abin dai gwanin tausayi kamardai yadda ta sharad'anta masa duk sanda wata k'awa ko 'Yar uwa tata suka zo kuma hakan yazamar masa dole ko ya shiga tashin hankali da masifar ta.

Yau kam baisamu amsa daga haj. Sailuba ba domin a hargitse take dan tundaga bakin k'ofa take kiran "nashiga uku na lalace shikenan k'arshene yazo, yau ni Sailuba naga takaina" yayin da hawaye suke rige rigen zubo mata daga wannan ya fito wani zai tunkud'oshi.

"Lafiya k'awata naganki haka saikace wacce aka aikowa cewa iyayenta sun mace rana d'aya irin wannan tashin hankali haka?"

"Ai wallahi gwanda ace iyayena ne suka mace rana d'aya wannan tozarci da wulak'ancin da Baffa yayimin, baffa tozartani ya nunawa duniya ni ba komai bace Baffa yagama da rayuwata k'awata" tafad'a tareda rushewa da wani shegen kuka wanda yasake d'aga hankalin haj. Zakiyya tai k'uri tana binta da kallo kafin daga bisani ta sauke ajiyan zuciya tace

"Wai duk mai yai zafi kike irin wannan maganganun k'awata?" Majina ta fyace sannan tace "Baffa k'awata shine" ta rik'a maimaitawa babu k'k'kautawa,

"Naji shine, me yayi miki mai zafi haka?" ta katse da tambayarta "waini Baffa zaiwa kishiya?"

"Hmmm shine me?k'awata yanzun ke akan wannan kike d'aga hankakalinki indan wannan ne ai basai kin d'aga hankalinki abanzaba yau d'innan ma Baffa yana iya dawowa yace miki anfasa"

"Daga baya kenan k'awata aure kuma saidai wani amma wannan yafi mintuna talatin da d'auruwa"

A firgice haj. Zakiyya take kallon k'awar tata "aure Kuma? Aurefa kikace shi Baffan neyayi mana wanna cin mutuncin lallai yatarowa kansa dala ba gammo dan wallahi sai yayi nadamar abinda ya aikata manata Kinga yanzun dare yayi babu damar mufita amma gobe da asbah zaki fito mu kama hanya dole ne mu ladaftar da Baffa amma kafinnan zokiji" ta fad'a tare da rad'a mata wani abu a kunne duk da cewa abinda tace ya d'an sanyaya mata rai amma hakan baisa ta saki rantaba domin bak'aramin shammatar ta Baffa yayi ba amma tayi alk'awarin saita shayar dashi ruwan mamaki saita sa yayi nadamar abinda ya aikata mata wallahi

_________________________

Duk da cewa ranta ajagule yake hakan bai hanata yima kawunna nan nata sauka ta musamman ba kuma Saida tayi k'orafin auren da akayi batare da ansanar da ita ba Suma sun amsa laifinsu sai dai sunbata uzurin cewa basa sone su d'aga mata hankali wai idan abin yazo lokaci guda zai wuce ba kamar afad'a mata tunda wuriba abin yayi ta damunta.

Maman islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥

2021
NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 9

Haka dai ta daure tayi musu karb'a ta musamman har zuwa lokacin da suka wuce, cikin k'awayenta babu wanda yasan da maganar auren sai haj. Zakiyya dan haka da itakad'ai suka zauna har zuwa bayan sallahr magriba sanda 'yan kawo amarya suka fara shigowa.

Haj. Zakiyya ce ta rik'a tausarta da k'yar tasamu ta hak'ura dan da cewa tayi wallahi saitayi musu hauka sai sun ganecewa mijin mahaukaciya 'yarsu ta aura haj. Zakiyya tace "haba k'awata waishin duk abinda na fad'a miki tun muna gidana baki d'aukaba? na sani da ciwo amma idan kika daure zakiyi dariya harda shewa kinga yanzu idan kikayi wani abu to duk abinda yasamu 'yarsu to kaitsaye zasuce kece dan zaki aikata amma idan kika bi yadda na fad'a miki zakiga yadda zasuga kima da darajanki"

Da k'yar haj. Zakiyya tasamu ta lallab'a haj. Sailuba a wannan gab'ar har ta hak'ura ta karb'i bakin amarya yadda ya kamata har suka tafi suna yabon kirkinta ganin yadda ta karb'i amarya cikin farin ciki da walwala, tare da ita aka raka amarya har d'akinta suka tafi suna godiya

Bayan ta tafiyar sune haj. Zakiyya ta dubeta tasaki shu'umin murmushi tace ba'a faraba k'awata sharar fage ake kafin wasan ya fara"

"Allah ko k'awata?"
"Ai ke d'ince bakya ganewa baki da aiki sai fushi Kuma babu inda wannan zai kaiki sai na dama"

"Abinne ya masifar d'amin hankali k'awata amma yanzun ya zanyi?"

"Shi nake son ai ki nutsu ki fahimta domin abune da zakiji dad'insa kuma zai amfaneki batare da kowa ya fahimtaba, Kinga yanzu angon yana hanya abinda nakeso dake goben ya kasance kin gama musu duk wani aiki har abin kari kafin ki fito, kidai fito da wuri kinsan wajan yana da nisa sosai"
"Angama amine zanyi yadda kikeso insha Allah"

_________________________

Ranar dai ango ya gwangwaje agwancinsa shi da amaryar sa Amina yayin da Sailuba ya yadda taga rana haka taga dare batako runtsaba tsabar masifaffen kishin dayake cin ranta.

Koda gari ya waye tun bayan da ta idar da sallar asuba bata komaba ta zauna ta had'a musu had'ad'd'an break wanda rabon data girka irinsa har ta manta tsab ta gyare gidan tsab aranta take cewa duk wani abu da zanyi agidannan na bankwana ne domin nima lokacin hutawana yazo.

Sanda Baffa suka fito daga d'akinsa shida Amina tuni Sailuba sunyi nisa a hanyarsu ta zuwa wajen shahararren malamain da yai k'aurin suna aciki da wajen garin wanda ake kira da kowa naka.

Sosai yaji dad'in yadda ta gyare ko ina tayi musu girki duk da cewa yaji babu dad'in fitar ta arana irin tayau daya kamata ace ta tsaya ta Kula da komai na gidan kodan bak'in dayasan cewa bazasu rasayi ba aranar irin ta yau d'in.

Bayan gama cin abincinsu babu dad'ewa kuwa saiga yayar Amina wacce takasance ita kad'aice 'yar uwarta mace dan duka yaran malam Babba mata biyune kawai sai maza guda goma Sha uku yayin da ad'akin su Amina ita kad'aice mace sai kuma d'aya d'akin nanma guda d'ayar ce shamsiyya.

Matan malam suna da matuk'ar had'in Kai yadda zai wahala a yaransu ma kaban bance na wannan da na wannan.

Yini su anty shamsiyya sukayi kamar yadda Amina take kiranta tare da bata shawarwari da buga mata misali akan gidansu da kuma nuna mata yadda umman ta take bin nanne mahaifiyar shamsiyya sau da k'afa duk da kasancewar Nanne wacce ainihin sunanta Zahra u irin matan nanne masu fad'an tsiya, hakan bai hanata jin dad'in zama da Mariya ba (Umma) domin ita mutunce mai mugun hak'uri dan zan iya cewa duk wani hali na Amina da shiru shirunta a wajenta ta gadosu, tun bayan da aka kawota gidan malam Babba ta kama yaran nanne ta runguma tamkar nata dake tana da matuk'ar ilimi haka take dad'a fahimtar dasu duk wani abu daya gagaresu a makaranta hakan ba k'aramin dad'i yayiwa malam da Nanne ba gaba d'aya tasakarwa Mariya ragamar yaran hatta kayansu d'akinta suka koma sannan itace ta aurar da Shamsiyya yayin da tunda aka haifi Amina Allah ya jarabce ta da masifar k'aunar yarinyar wacce tun tana k'aramar ta take da wannan hak'urin abin har tsoro yake bawa Nanne takan cewa malam kodai yarinyar bata da lafiyane.murmushi yakeyi mata a duk lokacin datayi masa irin wannan tambayar yace "Zahra'u kenan ai kowane bawa da kikegani yana da kalarsa ita wannan kalar ta kenan hak'urinta har ya zarta na uwar ta"

Baki Nanne takan tab'e tace "sam ni wallahi hakan bamin dad'iba wani hak'urin idan yayi yawa a cutane" shima dariyar yake mata baya k'ara tankawa.

Sosai shamsiyya ta d'an bata kad'an daga tarihin gidansu da irin ribar da Umman take ci na irin tsantsar hak'urin da Allah ya hore mata

Basu bar gidanba sai bayan sallar la'asar kuma har lokacin haj. Sailuba bata dawoba.

_________________________
Tunda haj. Zakiyya tafara jan sailuba wajen malami bata tab'a kaita waje mai wahala da ban tsoron wajen ba dan haka ta matuk'ar wahala tun kafin ma su kai wajen domin tafiyar k'afa ce wacce koda tayi rayuwar k'auye bata tab'a, sai dai abinda ya matuk'ar k'ayatar da ita shine yadda suna zuwa malamain ya hau zayyano mata dukan abinda ya kawosu, sannan shi da kanshi yafara dace"kinyi babban kuskure da har kika k'i yarda ki haihu da mijinki Kuma d'an uwanki Baffa domin dakin haihu dashi shine samun nasarar rayuwarki ni bana fad'awa mutum abinda zai kasance karya dan haka nake tabbatar miki da cewa ita wannan mata zata haihu itace uwar 'ya'yansa sai dai kuma ke kin riga kingama da rayuwarki domin keda haihuwa har abada kin gama lalata mahaifarki da k'wayoyin hana d'aukar ciki shekara goma shabiyar ba kwana goma sha biyar bane babu ke babu haihu amma zaki mulki mijinki da kishiyarki yadda ranki yake so.
Chapter 6 · 0% Book details