← Book details Ashraf Love Story Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 8

Sashe 3

Ashraf Love Story Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Harabar jirgin tacika sosai harsaida Akasoma fidda wasu waje Sannan jirgin yasauka, mutane keta fitowa Cikin jirgin Amma shuru ba champion, masu d'aukar photo kuwa Y'an jarida Ankasa Antsare kowa sai k'yalla idanuwa Yake domin Ganin champion, saida kowa yagama fitowa Cikin jirgin Kafin wasu manyan escort d'insa biyu sufito d'aya rik'e da jibgegiyar rigarsa tasanyi wato jacket d'aya kuwa Akwatine maikyau yajanyo fitowa Sukayi katsaya saida yak'ara kusan 10 minute's sannna yafito tindaga Kan K'afarsa nakebi da kallo harzuwa samansa masha Allah Kawai nake Fad'i domin yahad'u Kyau iya Kyau tamkar shine yazab'awa kansa halitta, farine sol fatarsa tamkar jariri gashin kansa Bak'i sid'ik yasha gyara sai k'yalli Yake idanuwansa d'auke da zarazaran eyelashes Bak'i bakinsa k'arami lip's d'insa Pink gefen fuskarsa yak'awatu da saje gashin gemo Dana baki kad'an idanuwansa sanye Cikin farin glass, sanye yake da suits Green color lights k'afafunsa sanye da takalmi cover shoe's kalan maroon, Kai fad'ar kyawon wannnan gayen B'ata lokaci ne Kawai ku haske yanayinsa dama kyawonsa tacikin Idanuwanku Nabaku damar wannnan...
Fitowa yasomayi Ahankali cikin rangaji da Isa gamida da k'asaita kallo d'aya zakamasa kasan hutu naira tana Magana tindaga jikinsa zuwa kayansa, bayansa kuwa wasu escort d'in duka sake fitowa d'aya d'auke da kofin gold Wanda yaci A wasanda yabuga A Canada sai shek'i kofin Yake, d'ayan kuwa d'auke da laptop da wata Y'ar k'aramar jaka yarato, yana fara fitowa Mutane sukahau shewa da tafi da Ihun gwarzantashi sai champion Allah yak'ara lafiya, Allah Yabarmuna Mai gwarzonmu kowa da Abunda Yake Fad'i photona kuwa yashasu tamkar Sabon jinjirin wata, d'aga musu Hannu Kawai yake fuskar d'auke da Murmushi, Yana Ida saukowa mutane suka k'ara matsowa indayake dataimakon escort d'insa da Sauran security d'in wurin yashiga Mota dak'yar suka Sami Damar Fita Amma duk da Hakan cikin mutane suke, Samari duk sunfito ko wanne sanye da Riga da hula ja da fari kalan dai ta ball d'insa irin Wanda Yake sawa Shida Y'an tim d'insa jikin rigar Anrubuta CHAMPION 1,
"Abokina waikana ganin ikon Allah kuwa? Mutane kamar da Aljanu Kuma sai k'ara yawa suke Kamar yau Suka Fara saninka, Gaskiya ka godewa Allah irin Wad'annan Masoyan haka,"
Kamar bazaiyi magana cikin Isa da izzarsa Yace"Nima ina mamakin yarda natara Masoya Haka a 9jar Bayanni bama mazauni 9jar bane Saidai kawai suga wasana amma bawanda yatab'a ganina a zahiri inaga wannnan yasa Nasamu irin wannnan tarbar haka Amma ba Abunda zance Saidai Alhmdllh Allah shine Abun godiya"
"Wallahi kuwa Uncle gaba d'aya garinnan ya d'auka zuwa Unguwanni dayawa ko Ina kaduba murnar dawowarka Ake, kanada Masoya nikaina Uncle nayi wani Aboki Mai masifar k'aunarka Sanda yagane ni jininkane zokaga murna Yana Rok'ona Kota hotone na nunamasa Kai, yanzu da dashi zamuzo Saidai Kash taronnan yasa yab'acemun nayita kirashi Kuma basamu ba, idan kahuta zankawoshi kaganshi, Uncle Yanada.....,"
"Ohh khamis parrot Sarkin magana, kozaka iyabarina nahuta naji da iya wannnan hayaniyar tawaje,"?
Dariya khamis da Omar sukayi, Sarai sunsan halin AShRAF bayason hayaniya, Omar shine Babban Abokinsa Abotarsu hartamaidasu Y'an uwanjuna, Saidai shi Omar likitane Yanada sauk'i sosai bakamar Ashraf fa,
Saida suka iso bakin gate Suka Shiga sannan Samarin Suka wuce, kowa yana yaba kyawo da mutuncin ASHRAF, Koda sukayi parking yajima Saida yagama Jan Ajinsa sannan yafito, direct inda momynsa yanufa Suka rungume juna cikin k'auna da d'auki domin Yanzu Shekara 5 kenan baizo 9jar ba, Sam bayajin dad'in zaman k'asar kamar Ana zare lafiyarsa yakeji musamman lokacin shiyasa yayi tafiyarsa, k'asaitaccen palourn nasu suka yada zango fira tab'ark'e kuwa sai murnar ganin yayansu da d'ansu suke Shikuwa k'arfin hali kawai Yake Domin duk yagaji ga hayaniya kawai Yana daurewane ganin soyayya da d'auki gun Iyayensa da Y'an Uwansa, Saidai duk wannan d'aukin bako Alamar Small mom tanacan tana k'unci jidda kuwa tini tazo itada mijinta domin tajima da Aure, Kuma Sam batabi halin Uwartaba shiyasa suke Shiri Sosai da ASHRAF dama Mommy da Zuciya d'aya take zaune dasu,
Abinci sukafaraci dukansu sai A Lokacin small Mom tashigo tana kame kame Wai Aiki ya rik'eta Shidai ko kallonta baiyiba Dan yasan Sarai basonshi takeba, wani gefenma yana ragamata ne Saboda mutuncin jidda domin tana bala'in bashi girma duk Abunda zatayi saitayi Shawara dashi hakan Yasa Shima yakeji da ita yake iya fad'amata damuwarsa,
Mik'ewa yayi tareda dafe Kansa Yana Shirin fad'uwa da sauri Omar yarik'e Yana Fad'in"kagaji haba, muje kahuta Kan kasomemuna Anan, kusan mutumin Ajeboter's ne bayason wahala,"
Dariya sukayi dukansu banda small Mom data d'an tabe Baki Kawai,
"Eh kuje Kam yahuta daga baya Ayi firar aiyayi k'ok'ari ko yanzu," Cewar Daddy
"Khamis waiya banga Abokinka ba gashi kuma Son yadawo,"?
"Wallahi Mommy bansani ba Ad'azu munatare sai yace zaije yadawo kuma bansake Sanin Yarda yayiba Ninama d'auka yab'atane saboda Yawan mutane amma gashi haryanzu wayarshi kashe,"
"To tinda ya iso lafiya kuma kaganshi saikaje kaduba kagani ko lafiya, mutanen nada kirki gashi Haris Yana k'aunarka Dama Uncle d'inka,"
"Hakane Mommy Bari naje yanzu, sainadawo,"
"Yawwa to kagaida Iyayennasa,"
"To mommy"
Chapter 3 · 0% Book details