← Book details Akan Social Media Part 1 Complete Local reading mode
READING PART 2 OF 5

Sashe 2

Akan Social Media Part 1 Complete · about 7 min read

```Salma```
Kusan karfe bakwai na safe ta kammala had'a masu breakfast d'insu, indomie ta dafa masu, akasa ta dire farantin sukayi basmallah suka fara cin abuncin, suna fira irinta masoya wasa da daria.

```Rashida```

Bayan ta kammala karyawa ta shirya tsaf cikin uniform d'inta ta kama hanyar zuwa makarantar islamiyya kasancewar bana ta kammala secondary. Kasancewar dga gidansu zuwa makarantar akuy yar tazara.
Ta kusa isa a mkrnta taji ana yimata horn, juyawan da zatai ta hangi wani santalelen saurayi a cikin mota, batasan sanda tai wata irin murmushi ba
Saurayin saukowa yay dga motan
"Yan mata sannu ko"?
Fuska ta d'an gimtsie
"Yauw, sannu"
"Plz idan bazaki damuba ni sunana abdulmaleek, amma ana kirana da abdul, zanso ki bani lokacinki, dan wallahi kin burgeni kuma ni bada wasa nazo ba da maganar aure nake tafie"

Kallonshi tai tare da k'arewa motarshi kallo
"Tohm yxn dea kaga makaranta zan tafie"
"Ba damuwa, mss...??
"Rashida"
"Yauwa rashida, plzz ki bani number d'inki zuwa idan kin dawo sea muyi magana ko"?
Fadamashi lambarta tayi shi kuwa ya d'au katuwar wayarshi fara tas ya fara rubutawa akai, bayan ya kammala yay saving ya danna kira.
Vibration wayanta dake cikin jaka ya farayi
"Yauwa ta shigo"
Juyawa yay zuwa motanshi ya shiga
"Zuwa karfe 1 zan kiraki nasan kin zama available, ki kula da kanki rash, I love u"
Wucewa yay abunshi yayinda rashida tai tsaye tana jin kamar mafarki takeyi.
"Yeeeeh! Abun kamar a novel wallahi, mai kyau mai kud'i yana son yar talakawah, yeeeee! Burina ya cika. Zan wataya inyi walkiya kan daula.
Anya kuwa rashida rayuwar novel d'aya take data zahiri kuwah? Inji kausar. Zamu gani dea.

```®Kausar Luv💞```
[1/6, 6:21 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸
(YANAR GIZO)```

*Page 31 to 40*

```Rashida```

Karfe d'aya na rana, kira ya shigo a wayan rashida, murmushi tayi, ta d'auka tare da karawa a kunne
"Assalamu alaikum"
Abdul yay sallama
"Amin alaika salam, gskya kam kana da cika alkawari"

D'an murmushi yay
"Gskyne amma kinsan abubuwa suna zuwa haka ai, yxn dea kimin misalin gidanku idan na tashi zuwa karfe 7 na dare zanzo in shaa Allah"
Fari da ido tai kaman wanda ke ganinta ta fara yimasa bayani
"Well! Nagane sea kinganni"
Haka sukai sallama rashida dake zaune ta fitah wajen tsakar gidansu
"Innah!!!"
"Ke lapiya kike kwala min kira haka"?
Ajiyan zuciya ta sauke
"Inna kinsan na ta6a karanta maki labarin littafin martaba ta na ummi aisha ko"?
Kai ta d'aga tare dayimata wani irin kallo
"To inna abun kamar haka, yau na had'u da wani handsome, zuwa darema yace yana nan zuwa, shiyasa kiga inna na dage na iya abunci kala2 saboda tsaro"
Murmushi innah tayi tare da cewa
"Allah ya kyauta"

```Fadila```
Bayan tayi wanka tayi sallah ta d'an kishiengid'a kanta akan gefen kujerah.
Ji tai gabad'aya batajin dad'in jikinta, wayanta ta d'auka kaman zatai kirah, sai kuma ta koma ta ajiye, bayan kmr minti 2 haka ta k'ara d'auka ta danna kiran number d'in adnan. Video call.
Murmushi yay
"Kyakyawa ykk? U miss me"?
Kai ta d'aga masa
"Yes! Adnan plz mai yasa bazaka fitah rayuwana ba"?

Ido ya kanne mata
"Ni adnan in rabu dake fadila kema kinsan abune wanda ba xai taba yuwu ba, just relax ki cigaba da kulamin da kanki kinji"

Hawaye suka zuba mata a fuska
"Adnan kasan cewa zamu mutu kuma zamu koma ga mahallicin mu, abunda muka aikata dashi Allah zai mana hisabi, mai yasa bazamu deana ba"

Tsuke bakinshi yay
"To dga yau kada ki kara kirana a waya, zan goge number d'inki a cikin wayana in koma gogeki a cikin zuciyata da kuma rayuwata"

Jin kalamanshi da fadila tai yasata cikin tashin hankli, stammering ta fara yi, kapin ta bud'e baki ta bashi amsa ya kashe wayan tare dayin tsaki.
Ido tabi wayan dashi da idanunta da suka chanza kala, take ta maida kiran nashi, har sau 3 kiran na shiga yana tsunkewa bai d'auka ba. Jikinta ya hau rawa gabad'aya ta fita hayyacinta, idanunta suka chnza kala saboda kukan data soma tana fad'in
"Plzz adnan pick d call, plzzzzzzzz"

Sea a karo na hud'u adnan ya d'aukie wayan
"U see! Baxaki iya rayuwa badani ba my one, am in need of u, kina jina? Come on cire min hijab d'in nan, kinji"?

Kallonshi tai, saboda maganar adnan kamar ta zama maganar iyayenta bazata iya kaucewa duk abunda yakeso ba.
Kamar yanda yace haka ta aikata
"Yauwa my one, kinsan fa ina sonki, fuskanki mai kyau, gaki chocolate colour, hancinki har kusan baki, ga manya ido, ga...
Bai karasa ba taji sallama, da sauri ta katsie wayan ta maida dubanta ga matar dake cikin d'akin
"Mother"!
Ta furta a sanyaye
"Nice fadila ba wata ba, mai yake faruwa ne haka"? Naga kamar kinyi kuka?
Murmushi tai
"Laa! Mother banyi kuka ba, ynxn dea zaunah, bara in kawo maki abunci"
Tashi tai ta wuce kitchen ta zuba mata abunci a plate ta hadu mata da drinks ta dawo ta kawomatah ta ajiye, mother na saman kujera ita kuma fadila tana kasa.

```Salma```
Sallaman zaid da tajine yasata waigawa tare da sakin murmushi a fuskarta
"Yaana barka da dawowa"
"Yauwa matata, wlh nagaji sosai, bara inyi wanka in fitoh"
"OK"
Tashi bilal yay ya shiga toilet ya watsou ruwa ya fitoh ya chnza kayah zuwa d'an 3quarter black da farin riga karama ya feso turare ya dawo zuwa ga salma
"Yaa bilal baxaka ci abunci bane"?
Murmushi yay
"Kinga wallahi dga office dana tashi sea na biya gidan hajiya shine fa ta bani towu naci"
Murmushi salma tai
"To shikenan sea mu barshi muci da dare ko"?
"Haka za'ayi matata kizo gareni"
Matsawa tai kusa dashi ta zaunah a kasa, bilal ya d'ora kanshi akan cinyarta yana wasa da hannunta
"Ki bani labari"
Wayarta ta d'auko
"Kaga bara in karanta maka wannan"
"Emhum ina jinki"
"Yauwa! Wato wannan labarin ynxn akai mana posting d'inshi a group, wea wani mutum ne yanada mata, a kullum idan xata fitah sea tayi kwalliya ta kure adaka iya iko, ta bad'e jikinta da turare, to mijin yayi2 ta deana takie bari, kawea watarana suna tare da abokinshi sea ta wuce, abokin yace
"Waiyh gskya kamshin turaren nan yayi"
Mijin ya juya yace
"Ubanwa yace ka kallie matata"?
Sea shi abokin nashi yace
"Wai dama matarka ce"?
Mijin yace
"A'a dan ubanka uwarka ce"
Mijin tashi yay ya wuce gidah
"Ke dan wanda y haifeki nagaji na sakeki"
Matar sea ta fashe da kuka tana rokonsa arziki akan ya mayar da itah
Fafur mijin yaki hakuri.
To wea idan kaine ya zakayi"?
Daria bilal yay
"To ai shine dea2 amma shima ya kamata yayi hkuri ya kara bata dama"
"Hkne yaana, amma itama ai bata kyauta ba, bai kyautu ba matar aure zata fita ta rika saka turare har wani namijin da ba nata ba yanajin kamshin turaren ta ba, haramun ne"
"Sannan kamshin turare yana jawo sha'awah, dga sha'awa kuwa sai a afkawa zina, hakika yayana wasu matan auren suna keta haddin aure. Wasu a zahiri wasu kuma a social media"

Hannunta bila ya kara kamawa
"Data why nake alfahari dake, duk da kina amfani da yanar gizo baki chnza minba, kinada lokacina, kina kula da hakkina na aure, kigafa abokina yanada mata amma wlh yace idan ta kama wayar hannunta tofa baya gabanta batada lokacinshi, sea dea kawea chatting, kuma ko kad'an wayanta baya zuwa hannunshi"

Murmushi salma tai
"Allah ya kyauta dea, zan cigaba da baka labarin"

Haka dea salma ta cigaba da baiwa bilal labarai a cikin whtsapp d'inta yana faman daria, wasu kuma labaran su maidau topic of discussion. Har shi da kanshi yake kar6an wayan yana karantawa ya shiga whtsapp d'inta yayi duk yanda yakeso abunshi, hankalin salma zaune zuciyarta kwance.
Saboda bata bar yanar gizo ta lalata mata rayuwa ba, kowanne abu yanada nashi amfani yana kuma da rashin amfani.
Mujeh zuwa dea akan yanar gizo.

*****
Karfe 7pm abdul ya dira a kopar gidansu rashida yakirata a waya ya sanar da ita cewar yana kopa.
Dama ta shirya tsaf abunta turare ta kara fesawa, ta kamo hanya cikin takun k'asaita ta fitoh wajen.
Kallonta abudul yayi ya bud'a baki yace...

```®Kausar Luv💞```
[1/6, 6:22 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸
(YANAR GIZO)```

*Page 41 to 50*

"Rashida kamar ynda na fada'maki ni aurenki nake son yi, kuma kapin inzo nan sea da nai bincike a kanki, saboda haka bana son a 6ata lokaci idan dai har kina sona"
D'an murmushi tai wanda ya kara mata kyau. Rashida kenan, fara kyakyawar yarinya mai matsakaicin tsaye, ga tsabar shigar rai.
"To yayi ba damuwa, zan fad'awa innah. Kasan cewa Allah yayiwa babana rasuwa"

"Hakane rash, Allah ya jikanshi da rahama ynxn dea...
Jin ana sallama ne yasa Abdul dakatawa
"Yes! Malama lapiyah"?
Bawan Allah sani ne rike da leda a hannunshi
"Rashida gunki nazo"
D'an murmushin yaki ta saki
"Abeg malam tafi ka bani guri wallahi bana son haka"
Ko kad'an sani bai nuna alamun damuwa a taredashi ba, juyawa yay abunshi yayinda abudl ke mamakin rashidah, gata dea mai ilimin addini amma tana wulakanta bayin Allah, kodayake ai baisan mai ya had'asu ba.

Sun d'an jima suna fira kapin nan sukai sallama.
Chapter 2 · 0% Book details