← Book details Abar So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 19

Sashe 11

Abar So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh Abba , amma inada wani urgent emergency wanda gobe karfe 10 nasafe zai iso, insha Allah idan nadawo zanje mugana da ita yarinyar" Amin yafada

"Toh dan Albarka,yadda kake shirin faranta min rai haka Allah zai faranta maka naka " Abba yafada cikeda jindadi

"Ameen Abbana" yafada yana murmushi sakamakon tinawa dayayi da moment dinshi da ABARN SOnshi dazu

"Jeka" inji Abba

"Toh Abbana" yafada tareda ficewa zuwa part dinshi

    Abangaren Nadhira tana shiga tanufi wajen Dadynsu lokacin kuma idonshi biyu da alama mah yunwa yakeji batareda bata lokaci bah ta debi juice din a cup sannan tafara bashi shikuwa karba yakeyi sosai kuma alamu sun nuna yana jin dadinshi sosai. Tana gamawa takimtsa shi sannan tashiga watsa ruwa tareda dauro alwala, tana idar da sallah da sallah tasa kayan baccinta kafin tafara tinani  abinda yawakana tsakaninta da Kursum

"Zakisan dani kikeyi" tafada tareda da lumshe ido. Sallaman datajine yasata gyara hulan net din kanta sannan ta amsa shikuma yashigo wani irin bugawa kirjin tayi cos batayi zaton zata ganshi bah

"Who are you?" Shine tambayar daya mata, abazata tambayar tazo mata

"Na rokeki da sunan Allah da  karkimin karya kuma akwai abubuwan da nayi noticing gameda ke shiyasa nake son sanin more about you" Abba yafada mata

"Bazaniya baka amsa dakaina bah amma ina iya baka address din wanda zata iya baka kyakyawan labarina " tafada mai cikin sanyin murya

"Okay if that's fine with you" Abba yafada

"Tnx for understanding" tafada sannan tadauko paper tarubuta mai address dinsu then tamika mai

"Gud night baby" yafada da murmushi a face dinshi

"Good night Abba" itama tafada tana miyar mai da martanin murmushin.

       Bangaren Kursum kuwa tana hawa upstairs direct room nata tawuce , travelling bag dinta tadauko tadinga zuba kayayyakin ta aciki

"Wlhy yarinyan nan tadebo ruwan dafa kanta , harni zata mara , harni takecewa zata auramin miji if am not mistaken  kwacemin miji fah take nufi, this can't be Amin must leave this house first thing tomorrow morning , i won't bear to loose my love to another woman wait mah is she a woman?no she's a girl" haka tadinga magana itakadai kaman wanda maganin ta yakare(loh....hhhh).

      Tana gama parking din kayanta tafice zuwa part din Amin, ko kwankwasa kofa bata yi bah takutsa ciki , hangoshi tayi asaman bed yana danna laptop yana ganinta amma yayi biris kaman babu abinda ya gani kuma sarai tasan yaganta zama tayi awajen dressing mirror  tana kallon swollen face nata wanda haryanxu shatin hannun yarinyar bai bace bah, tsakin dataja neh yasashi kallonta

"Kai yarinya nan badai zafin hannu bah, mtsww shegiyar yarinya kawai dangin mayu wlhy sai tayi dana sanin marina, kazama mah daita,  Love you need to see that small insect wlhy yarinyan bata da sense wai kai zata aura wai saita sace zuciyar ka hhh, stupid slot kawai cos daga ganinta mah zakasan da yi PHD a karuwaci tana magana tana rolling din ido" kallonta yakeyi ko kiftawa baiyi cos wlhy maganan ta mah zainuna yadda takejin haushin yarinyan,   shafa kanshi yayi sannan yace.........

Comment,
Vote &
Share
💋💋wurarh💋💋

💝💝💝💝💝💝  
                       *ABAR SO*
                                    💝💝💝💝💝💝

*WRITTEN by: NAFISAT  MA'ARUF  SHEHU*
                      *💋💋wurarh💋💋*

*Wattpad:Nafisatma'arufshehu*

🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

               🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Page 79-80

.....Ga Wanda tafiki nan ta iso,sanye take cikin wata doguwar rigan kanti amma da kadan yawuce gwiwa dakuma hula colourn kayan,cos yawancin kayayyakin ta basu cika tsayi bah,gaishe da mumy tayi hade da durkusawa har kasa as usual while mumy ta amsa da fara'a cos yarinyar na burgeta

"Kanin mu yanaga tarike kaman kayo mata sata"tafada mai cikeda son gano abinda ke dariya

"Gwanda dakika Zo Matar yaya cos Allah yagani bazan iya dukar Matar yayana bah,kuma gaskiya bazan iya zaginta bah"yafada hade da shafa Kai

"Gaskiya kayo tunani mai kyau ,and ke Anty Kursum wannan dakika rike haka kinsan kanin mijinki neh Kuma yakamata kidinga girmamashi "tafada

"Ke fah nalura kinada shishigi,tukunna mah yaushe nadawo Antynki?yaushe Abdulkadir yadawo kanin mijinki?yaushe Amin yadawo mijinki?,toh wlhy ki kiyaye ni,karkiga jiya kin mareni banrama bah wlhy bashi Kika dauka Kuma ni ba'acin bashina batareda an biya bah"tafada tana zazzare eyes

"Wai ni bashin miye naci miki neh?kodai marinki danayi miki jiya?hala kinmanta ke Kika fara mareni nah rannan?toh bari in fada miki an eye for an eye,blood for blood and life for life,ma'ana shi kuwa shine  ni Nadhira bana yafiya duk abinda akamin bana mantawa  cos there's a blood of vengeance running in my veins,ba'a shiga sabga ta akwana lafiya"tafada looking so serious hade da Jan kujerar dining,while itakuwa Kursum tafara tsorata da lamarin Nadhira cos taga yarinyar hayakin kanta yafi Wanda yake nata kan,cikin sanyin jiki tahaura sama. Mumy mah taji dadin yadda Nadhira ke magana Kuma alamun yarinyar yanuna cewan there's something burning in her ,itama haurawa tayi Sai yasauran daga Nadhira Sai Abdul  Wanda ahalin yanxu sun fara cin abinci.

    Can ba da dadewa bah saiga Kursum tasauko da traveling bag a hannunta,tana hango su taja tsaki

"Allah yaraka taki gona"Nadhira tafada hade da siping din tea,dariya Abdul yayi tareda fadin

"Wlhy matar yaya bakida  dama"itama dariyar tayi while Kursum takara sauri  acikin tafiya ta

"Mutum dai yafadi nikuma nasha dariya"tafada yadda Kursum din zataji........

       "Matar yaya!!"Abdul yakirata cikin serious tune bayan sun kammala cin abinci,dagowa tayi  tareda kura mishi ido

"Hmm... Daman so nake kinema min budurwa,kinga Sai tsufa nakeyi,inkina da kawa saiki hada mu in yaso Sai asa ranar aurena da Dana yayana rana daya "yafada tareda Sosa Kai

"Amma fah ka kawo point ashe kwakwalwar ka naja"tafada cikin sigar tsokana

"Waye zaki bani?"yatambaye ta

"Zan baka tsalelliyar budurwa wacce itama kwakwalwar ta yana jah,amma fah sorry to say tafika Jah,kuma sunan ta Hasana idan kun daidai ta toh Falillahilhmd,amma fah saika yi dagaske cos Zuma ce,ita Zuma Kuma Saida  Wuta" tafada mai

"Kai amma nagode sosai,amma inbazaki damu bah ina son in miki tambaya"yafada mata

"Am all hears"tafada

"Wani school kikayi attending?"yatambaye ta

"Nayi NTIC na Abuja"ta bashi amsa,sanda yakaremata kallo kafin yakara fadin

"Amma scholarship board neh suka dauki nauyinki koh?".... Yafada while itakuma tayi dariya

"Dadynmu neh ya samu"tabashi amsa

"Yasaku Kuma?keda waye?ya jera mata tambaya

"Eh mana ai bani kadai bane nida twin sis dinna neh"

"Wow kardai itace Hasana? Amma Kuma intake?"yatambaye ta cikeda zumudi

"Ba ita bace wannan din kawata ce,ita sis dinna tarasu last year"tafada looking so sad

"Sai gobe"tayi adding cos bazata so yaga tears dinta bah cos she believes that babbar rashin hankali shine kabari nakusa dakai yasan wickness dinka

"But bamu gama bah"yafada mata cos bayason discussion dinsu yayi ending this way,juyowan datayi neh yasashi yin Shirin daga maganan dayake son yakara fadi ,ga eyes nata yayi mugun ja,kuma daman haka take in tahana kanta kuka lokacin da take da bukatan yin hakan,jah idon sukeyi daganan kuma tafara Head migraine dinta.

     Barin wajen tayi hade da komawa side dinsu,tana shiga kuwa ciwon Kai yamata sallama ,fadawa tayi toilet don watsa ruwa ,tana gama wa tafito sannan tasa short nickern ta na mata da vest ,ga gashin kanta ajike cos tasawa kan ruwa ko zataji  saukin ciwon amma ina!!!!.

Dakyar takarasa kan bed ga gashin yamannu mata,jitayi she can't hold it anymore daman Kuma in tana ciwon kan kama mata akeyi Sai amata Addua,dakyar tajanyo wayanta sannan tabugawa Hasana Kira ,bugu biyu yayi aka sauke

"Sai yanxu aka gama fushi damu?"Hasana tafada cos tinda tadawo bata kirasu bah amma tamawa Antyn text amma Kuma idan Antyn takira bata dauka

"Kina gida neh?"ta tambayeta cikin dauriya don bayason Hasana tasani

"Eh... Amma yanaji voice dinki haka ko dai Baki jin dadi neh"tafada cikeda damuwa

"Not at all,lafiyata lau kawai dai ina son kizo neh"tafada wa Hasanan

"InshaAllah zaki hannu In the next 20 minutes"

"Pls kiyi sauri"

"OK"sannan takatse Kiran while ita Nadhira tagyara kwanciyarta

"Allah kabani lafiya"tafada hawaye na gangaro mata(it's said that in mutum baida lfy,yayi Addua cos Adduan majinyaci nasaurin karbuwa,bawai mutum yace am sick,need your prayers bah)

    Sallama Hasana tamawa Umminta tafito har zata shiga tafada wa antyn,kawai saita bari sanadiyar ganin wani Lexus Jeep Parke akofar gidan cos ita atunaninta big dadynsu neh.

Adaidaita ta tsara sannan suka wuce GRA,tana sauka ta gaishe da Baba maigadi  sannan tamai bayanin wajen Wanda tazo gani batareda bata lokaci bah yafada mata inda zatashiga.......

Fitowanshi kenan dinshi kenan zaije wajen car park cos yake yazaga gari ,itakuwa ta taho tana cire phone nata daga side bag nata domin shaidawa Nadhira ta iso,gware taji tayi da mutum har sanda wayarta yafadi kadai

"Buuu....wlhy saika biyani phone dina ,taab saikace baka gani,kana tafiya kaman Wanda yasha abu,karma kafara bani hakuri cos saika siyamin wani, sabon phone neh fah ko sati banyi da fara amfani dashi bah,kaii banma bukatan wani, nawa nakeso"tafada cikeda masifa(daman Kuma hasynah akwai masifa🤣🤣..lol) galala yayi yana kallonta cos babu karya tamai Dari bisa Dari amma da itace

"Gaskiya kinma raina nih kidubi tsabaragen eyes dina kice nina bugeki , karki manta fah kece bakya kallon gabanki"yafada mata while eyes nata nayawo ajikinta

"Kaikuma dakake kallon gabanka miyesa baka kauce bah?nikam duk wannan maganan ba problem dina bane problem dina shine phone dinda kafada"tafada tana mainuna phone dinda ke hannunshi

"Alhmdllh tinda fashewan kadan ne,saikije kiyi manage kafin natambaye matar yayana duk hukuncinda tayanke shi za'ayi"yafada tareda Mika mata phone dinta

"No gaskiya ban yadda bah,daman Zan Kira besty na ne yanxu Kuma gaskiya bazan iya amfani da wannan bah"tafada haryanzu bata karba bah

"Toh ganawa ki kirata dashi "yafada yana mai mika mata nashi wayan

"What kana nufin da wannan abin xanyi waya"tafada tana mai nuna Samsung Galaxy S6 din hannunshi sannan tacigaba

"Inama kace muje wajen matar yayan naka tayanke whatsoever hukuncinda xatayanke tinda nalura maybe ita judge ce "yafada tana mai murguda mai Baki

"Muje"yafada tareda yin gaba cos idan yacigaba da tsayuwa da ita baisan miye zai faru bah. Suna Isa bakin kofa yadan bude sannan yace tayi sallama....

"mushiga kawai"yafada mata suna shiga suka hangota ta akan bed bed

"Matar yaya yadai? yafada while ita Hasana tayi wajen bed din cos daga ganin yana yin ta zaka San something is wrong

"Babynmu!!!"tafada dakarfi SAKAMAKOn........

Vote,
Comment&
Share

💋💋wurarh💋💋

💝💝💝💝💝💝  
                       *ABAR SO*
                                    💝💝💝💝💝💝

*WRITTEN by: NAFISAT  MA'ARUF  SHEHU*
                      *💋💋wurarh💋💋*
Chapter 11 · 0% Book details