← Book details A Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 80

Sashe 57

A Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'ah.....yaron namu ya iso kenan......maraba" Ta fada tana sauya reaction na fuskarta cikin qasa da second biyar tare da takowa cikin falon a hankali. Akaikaice yake dubanta da wani irin kallo,sam baisan fuskarsa ba......bai kuma tuna ko yaya a inda ya santa ba,ta yaya ita din akayi tasan wayeshi?,yaya akayi tasan daga tafiya ya dawo?.

"Bana jin zaka iya shaidani.....shi ya sanya banyi mamakin musaddiq daya kasa ganeni ba.....ga yayansa ma ya gaza shaidani?" Ta fadi tana sakin fara'ar da bata kai ga qarasawa ainihin zuciyarta ba,yayin da kwarjininsa ke barazanar hanata samun abun fadi. Still dai baice komai ba yana ci gaba da dubanta. Ko dis baiji matar tayi masa ba,bai hangi dattako ko kamala da sukayi daidai da shekarunta ba a tattare da ita,sai kawai ya dauke kallonsa daga kanta don baiga amfanin maida hankali tare da son qoqarij fahimtar abinda ya tabbatar daga qarshe bame amfani bane,amma ina suka fita har na tsahon awannin ita da maamah din?. Tambayar data maqale masa kenan,bashi kuma da amsa.

Qafarsa kawai ya miqa ya zira takalmansa ya miqe

"Lokacin sallah ya kusa,zanyi salla na dawo" Ya fadi yana juyawa a nutse yana fita a falon.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 57
_________________________
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy

Assalamualaikum

Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule??
Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen??
To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen.
Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki.
Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina.
Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode

https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
____________________________

"Yaa huda.....yaa huda?" Muryar haneefa ta ratsa kunnuwanta dai dai sanda take kwance qudundune cikin bargonta. Kusan idan bawai dare ne yayi ba hakan ba dabi'arta bace,amma a yanzun yana neman ya zame mata dabi'ar da sabreen ta fara karantar hakan.

Batakai ga ce mata komai ba,don ba abinda ta gani behind kwanciya din da take yawan yi,sai ta barshi kawai a zuwan yanayi ne da yakan sauyawa kowanne dan adam. A yanzu ma gaba daya hankalinta yana kan ayshatu.....ciwonta gaba yake qara yi,ga mika'il a gefe,ga mashkur shima daya sanya wuta da yawa a kanta. Ya'aqoub ne kawai me dan sauqi saboda bai cika zafafawa ba. Dukkansu batason kowa ya subuce mata a daidai wannan lokacin da shirinta ke qara zurfi a kansu,kuma tafi hangen samun nasara da wuri akan mika'il da mashkur,don shi ya'aqoub a yanzu tunaninsa yafi karkata kan yadda zai shawo hankalinta ta aminta ta aureshi,abinda kuma bataga ranar yiwuwarsa ba. Wai mema zata tsinta ne a auren?,bayan tana ganin yadda su mazan suke?,tana ganin kuma yadda matan ke komawa?,ko hanyan aure yanzu mutum yayi mata ai bai qaunarta ballantana ace mata tayi. Duka tsari da halayyar mazan baiyi mata ba ballantana ta cusa kanta a sabgarsu da nufin zama tsakaninta da waninsu zama na din din din?.

Miqewa tayi a dole tana duban haneefa,sai haneefa din ta miqo mata takarda tana cewa

"Wani ne wai a waje yace a baki...." Da sauri ta fiddo mata idanunta waje sanda muryar sabreen wadda ke amsa waya take dosowa cikin dakin. Yadda suka daga kai suka kalleta duka su biyun ya sanyata janye wayar daga kunnenta tana kallonsu

"Lafiya?" Tayi tambayar tana sauya yanayin fuskarta. Wani faduwa gabanta yayi,cikin tsoro tsoro ta girgiza kanta tana qaqalo murmushi tace

"Ba komai.....ina kwance haneefa ta tsoratani,na dauka wani abune da naji tanata tashina". Idanu ta sake zuba mata na daqiqu sannan ta amsata tana zama gefan nata gadon

" Ko bata tsorataki ba dama ai yaci ace kin tashi,an kusa kiran sallah.....uniform dinku nadra ta wanke tunda kin koyi laziness......kije kiyi alwala ki dawo ki kwashe abincin tukunya a flask a wanke sauran abinda ya rage".

"Tom" Ta fadi tana matse takardar a tsakiyar hannunta tare da tunanin yadda zata miqe da takardar ba tare data lura da ita ba,to amma kuma ci gaba da zama dinma tunanin mafita tamkar tana bata damar dora ayar tambaya ne a kanta.

Aljihun skirt dinta ta tuna dashi,cikin dabara ta cusa a ciki,sannan ta zame ta sauko tana gyara inda ta kwanta din,ta daura dankwali saman doguwar sumarta ta juya tana fita a dakin. Dauke idonta tayi daga kan tab dinta ta bita da kallo. Haka kawai ta gagara samun nutsuwa kwanaki biyun nan,duk motsinsu a kan idanunta yake,kuma da gaske tana ganin dan sirkawar wani abu kadan tattare da huda din.

Bandaki kawai ta wuce kai tsaye tana fata da zumudin budewa taga meye a takardar?.

Sai data samu guri cikin toilet din ta zauna sannan ta ciro takardar ta kuma warwareta.

Kaman yadda ta zata shi dinne,sunansa kawai data gani sai bugun zuciyarta ya qaru da kaso hamsin cikin dari.

Yau kwanaki uku kenan,ya rakota daga hanyar makaranta har dab da gidansu kamar yadda ya saba a kowacce rana......tun tana gocewa har ya fara zame mata sabo ba tare da sanin nadra ko haneefa ba wadda yanxun aka banbanta musu lokutan tashi qarfi da yaji ba tare da kowa yasan dalili ba. Ya zame mata kamar abokin rakiya a yanzun.....tun tana dari dari da tsoro har hakan ya fara gushewa daga zuciyarta.

A ranar alhamis tayi matuqar mamaki yadda ya tsaya suna tsaka da tafiya,ya kuma kafeta da idanu

"Lafiya kake?" Ta tambayeshi da mamaki

"Ke kyakkyawa ce" Ya fadi yana jin wutar sha'awarta na ruruwa a ransa tamkar yadda ya dinga jin ta 'yar uwarta. Yana jin kamar ya dauketa a yanzun ya wuce da ita ya aikata abinda ya tanadi aikatawa,saidai kuma bazaiyi haka ba,yanason komai ya kasance a daidai sanda zatafi jin ciwo da radadin da zai iya zama ajalinta,ya kuma tarwatsa farincikin da take musu tattali. Yanason idan ya tashi ya tarwatsata tarwatsewar da ba zata taba dawowa ta gyaru ba ballantans ta koma yadda take.

Idanu ta waro tana dubansa,yadda yake yawan kambata da kurantata ya sanya kusan kullum sai ta kalli madubi......kusan kullum sai ta kalli kanta da kanta taga wannan kyan da yake magana a kai......wannan budurwar da yake yawan kiranta dashi. Tun bata ganin abinda yake fada din har ta fara ganin,amma tana ganin kaman bata ca canci kowacce rayuwa ba a yanzun......karatu shine yafi da cewa dasu kamar yadda yaa sabreen ke gaya musu

"Ina sonki huda.......ina tsananin qaunarki tun daga ranar dana fara ganinki.......zuciyata tana miki wani mahaukacin so da bansan iya adadinsa ba......wallahi inaji a zuciyata tamkar zanyi hauka saboda ke huda......ki soni don Allah......ko baki sona ni zan koya miki yadda zaki soni din". Kalaman da suka tsoratata suka kuma razanata kenan. Kalaman kuma da Naseer din ya shiryasu ne kawai don ya soma wasa da tunaninta da qwaqwalwarta,plan na biyu kenan daga cikin tsarikansa.

Baya taja tana girgiza kai,tana jin tsoro yana shigarta. Wacce irin soyayya a shekarunta?,duka duka nawa take?,koda yaa sabreen bataga ta kawo kowa tace shi zata aura ba,bataga wani yazo qofar gidan da sunan zance wajenta ba.....koda abinda ake maganarshi a kanta da nasu idanun basu taba ganinta cikin motar wani ko tsaye da wani ba har zuwa yanzun da take tsaye a gabansa. Ko rakota da yakeyi kullum kwanan duniya a tsorace take......wani lokaci zuciyarta tana raya mata idan sukayi kacibus da yaa sabreen fa?,sai kuma zaqin bakinsa da daddadar hirarsa ta yaudare tunaninta da kunnuwanta.

Tayi mugun tsoratar data dinga ja da baya da baya tana girgiza kai. Yana tsaye ya kafeta da idanu,abun yana masa sugar sosai. Irin hakan yafi buqata don ta haka ne sabreen din zata fuskanci girman nasa aikin. Ya samu sabon ruhi sabon gangar jiki da baisan komai ba game da rayuwa......zai hurewa zuciyar kunne,sannan ya mori gangar jikin yadda yaso ya kuma watsar da ita tamkar wani yasashen abu maras amfani. Yana tsaye harta gudu a layin ta bacewa ganinsa,sai ya bushe da dariya.

Hakan da tayi ya tabbatar masa qwaila ce,ya kuma bashi tabbacin baa taba gaya mata kalmar so ba sai a kansa

"Allah sarki......gashi baki fara da jin kalmar ba a sa'a......anyway......ko mene ya faru dake 'yar uwarki ce taja miki" Ya fada yana juyawa don barin layin ya qarasa inda yaransa ke cikin mota suna jiransa.

Hannunta har rawa yake sanda take warware takardar. Tsakanin alhamis jumaa asabar da kuma yau lahadi ba wasu mintuna biyar kyawawa da suka wuce ba tare da tunanin abinda ya faru tsakaninsu ya dawo kanta ba. Duk juyin da zatayi sai kalamansa sun dawo mata,kallonsa murmushinsa da kambamawarsa. Fuskarta kam ta kalleta yafi sau adadi tana sake duba kyawun surarta da yake yawan jaddadawa. A yadda take gani ba mace me kyan yaa sabreen dinsu......ashe itama to tana da kyau dinne da gaske?,ko kuma yana fada ne kawai?.

*_Hello me kyau,fadin azabtuwar da idanuna da zuciyata sukayi saboda rashin tozali dake ba abu bane me sauqi......ina fata zaki daure a gobe ki barni naga wannan kyawawan idanun da zuciyata ta mutu a kansu.....idan ba haka ba.....zan iya rasa numfashina_*

Da sauri ta duqunqune takardar ta kuma jefa a toilet ta bita da flushing zuciyarta na bugawa sosai. Tsoro zumudi fargaba da mamaki dukka suka hade mata har ta rasa wanne tunani ma zatayi.

Bugun qofar bandakin da akayi ana jiranta ya sake rudata,sai kawai taja qofar ta bude ta fito ba tare da tayi komai ba,taja burki bakin famfo ta daura alwala tayo dakin nasu.

Gaba daya tunaninta ya karkata ga saqon,har ta mance da batun kwashe abinci tayi zaune saman kujera tana bitar saqon da ya riga ya rubuta kansa da kansa a kwanyarta. Fitowar sabreen din ya sanyata tunawa,ta miqe da hanzari ta nufi kitchen.
Chapter 57 · 0% Book details