← Book details A Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 80

Sashe 36

A Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Anni......fargaba kiranta yake sanyamin,anni banason ganinta tana kirana.....anni bana buqatar mu'amala da ita......nafiso taci gaba da nisantarmu anni kaman yadda tayi a baya......bama buqatarta......duk sanda zan ganta anni sai naji wani abu a kanta.....inama zaku fahimci laifi mafi girma data aikata mana wanda yafi tafiya ta barmu girma muni ciwo da kuma girman zunubi?" Wadannan sune abinda so samu ya kamata ya cewa annin,amma kuma bakinsa ya gaza furta hakan,sai shi kadai daketa jujjuya maganganun cikin zuciyarsa. Ya rasa waye zai zayyanawa su,ANNI dince,to amma bayaso yabar mata wani abu da zaya yi mata tsaye a zuciyarta ko kuma a rayuwarta. Damuwa itace abu na qarshe da yayi alqawarin tarewa anni shigarta,kamar yadda ta sanya duk wani qarfin iko na jiki dana aljihunta ta tare ma rayuwarsu kasancewa da wanzuwa cikin damuwa har kawo bigiren da suke kai haka a yanzu. Wannan tunanin ya sanya ya zabi bawa anni amsa ta hanyar cewa

"Ba komai".

" Ban tsammaci haka daga gareka ba Muhammadu,kanaso abbanku yaji ba dadi a ransa shima kamar yadda naji?" Ta fadi cikin tausa murya tamkar tana magana da qaramin yaro.

"Ko kadan anni.....kema da muka sanya kikaji ba dadin yanzu haka kiyi haquri ki yafe mana......za'aci gaba da kokawa da zuciya,kuma zaa gyara in sha Allah". Murmushi ta saki tausayinsu yana narka mata zuciya. Lallai duk dan da baiyi sa'a da dacen uwa ba abun tausayi ne shi.

"Bakuyimin laifi ba muhammad.....illa dai lahirarku da kuma fagen rayuwarku da nakeson na sake share muku ita tas". Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa ta karaya......inama ana canjen uwa?.......inama ace anni ita ta haifesu kamar yadda ta haifi Sadiq da farouq?.

" In sha Allah anni bazai sake faruwa ba"

"To Allah ya yiwa rayuwarku albarka,ya tsaremin ku daga dukkan sharrin me sharri"

"Kinyi addu'a me kyau anni" Ya furta qasan ransa,don sai yaji kaman ta nemawa kanta tsari ne daga dukkan wani matakin da maama keson kutsawa dashi cikin rayuwarsu.

Ya jima yana juya wayar a hannunsa,tunani da dama suna kutsawa kwanyarsa. Sai yaji gaba daya madarar da duka breakfast din da aka kawo din ya fita a ransa,don haka ya maida mug din ya ajiye,ya miqe ya jawo bedside drawer ya zari dukka abinda yake da buqata ya taka a hankali yana fita a dakin jiki da zuciyarsa duka babu walwala da karsashi.

Sannu a hankali motar dake dauke dashi zuwa companyn ke tafiya busa qa'idoji da dokokin qasar,yayin da shi kuma yake kwance jingine sosai da back seat din na motar. Wayarsa ya sake cirowa cikin rashin walwala ya budeta,bangaren kira ya shiga yana duba adadin miscals na wayar nashi. Miscall dinta shine na qarshe a jerin kiraye kirayen daya rasa cikin wayarsa. Ya bude numbers din yana kalla tamkar me qoqarin haddace numbers din. Tsahon wasu sakanni sai ya dauke duban nasa ya mayar ga titi da yake ita hangowa tarwai ta glass. Haka kawai yake jin bayason kiran,gaba daya bashi da wani hope ko marmari akan dukka wani abu da ya shafeta,ta kashe komai ta kuma qonashi murqus tun a shekarun baya da suka shude,ME YAYI SAURA?. Amsar da kullum take biyowa baya shine BABU.

Da wani dan qaramin hanzari ya danne zuciyar tasa ya danna maballin kira,kiran kuwa ya tafi direct kai tsaye,wanda cikin qasa da sakan goma kiran ya isa ga wayartata.

Duk da jerin dinner abincin daren da me hidima da ita keta faman jere mata a gabanta amma ba wani abu daya daya burgeta ya ko ya bata sha'awa. Sai yanzu ta fahimci dawowa DUNIYARsu da kuma shiga DAULARSU ba shine kadai iya abinda take buqata ba. Ba shine kadai iya abinda ruhinta da zuciyarta suke da muradi ba. Lallai tana buqatar wani abu da yafi wannan muhimmanci a tattare da ita.

Ta juya a hankali tana duban zuwaira data cika plate da pepper chicken tana ci hankali kwance. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana kallonta

"Zuwaira....."

"Asama'u" Zuwairan ta amsa mata da bakinta daya cika da zallar tsokar kazar gwamnati(broiler).

"Me yake faruwa dani ne?......wa kaman ba nice ma'u ba?,kamar ba nice asama'u ba?,koda karin maganar nan da hausawa keyi ne yakeson tabbata a kaina?,lokaci shekaru da zamani suna son maidani wata lusara?......indai hakan ta kasance bazan taba yafewa kaina ba......bana ma fata hakan ta kasance,dole yarana su dawo qarqashin iko na kamar kowacce uwa.....dole su kasance qarqashin shimfidaddun dokokina.....suyi abinda nakeso na sakasu....su kuma bar abinda na hanasu......suso wanda nakeso.....suqi wanda bana so.....su kyautatawa wanda naso su rabu da wanda bana so.........dole na rabasu da aminatu.......dole Alhaji hamza ya zame musu babban abokin gabar da babu irinsa......zuwaira.....wannan karon burina da muradina me girma ne.....inaji kuma ina ganin kamar girman buqatata a wannan karon ya shallakewa aikin MADUGU.....Ina buqatar wanda yafi madugu zafi.....ina buqatar aiki da zafi zafinsa" Idanun zuwaira suna kanta har ta kammala,sai zuwairan ta nisa ta ajiye plate din naman hannunta ba don ya isheta ba,sai don gano damarmarki masu girma da yawa a gabanta.....da wata siririyar qofa da take hangota da fadin gaske daga can ciki.

"Akwai BAHAGO bayan madugu din......bani da kokwanto ko tantama a kansa.....tun ba yau ba......tun kina kogi na miki sha'awar zuwa wajensa amma kika qi bada hankali.....na tabbatar inda kin aminta da hakan da yanzu ba wannan matsalar a gabanki.....da tuntuni kin jima da tsallake wannan babin.....saidai kina da buqatar kudade..... Kudade masu kauri.....kaman yadda aikinsa yake da zafi haka yake da karbar kudi,saidai ribar da zaki samu yafi abinda duka zai amsa daga gareki".

Zamanta ta gyara sosai tana duban zuwaira. Ta sani ita din gaba take da zuwaira ta fannin abubuwa masu tarin yawa.....zuwaira bata isa ta hada kanta da ita ba indai ta wannan bangarenne......amma kuma komai qasqancin bawa akwai ta inda yake iya wuce maka

"Tunanin da ya fara zuwa kaina kenan.....abun nan yana min ciwo.....kamar ni zuwaira?" Ta fadi tana nuna qirjinta da yatsanta

"D'ana......mamallakin jadda diamondchore resources amma bazan iya kallon mutum nayi masa kyautar million biyu zuwa sama ba?,zaman me nakeyi a duniya zuwaira?" Ta qarashe fada da wani irin zafi da take jin ya ishe mata har qasan zuciyarta

"Komai ya qare idan kinbi a sannu.......idanma baki da wannan jumurin zirga zirgar ai kina dani,driver kawai zaki yiwa umarni......fu'ad kuwa danki ne.....muddin kuma yana neman albarka.....dole ya biki" Ta fadi tana tallafar farantin namanta da nufin ci gaba da kaiwa cikinta. Daidai Lokacin kiran ya iske wayar dake yashe a gefe guda.

Tare suka kalli wayar,sai zuwaira da tafi kusa da ita ta miqa hannu ta jawota tana dubawa. Baki ta tabe sannan ta furta

"Tabdijan" Ta matsa gaba tana ajewa maahmah a gabanta

"Qarshen sakaci......qarshen toxarci......tabbacin akalar duka yaranki suna hannun aminatu.....tabbacin steering dinsu yana damqe a hannunta kenan......sai yadda taga dama zata juyashi......an bada umarni kuma ya karba da gaggawa gashi ya zartar" Maganganun zuwaira kamar saukar ruwan dalma tsakiyar tsokar zuciyarta take jinsu. Tamkar tana yiwa ciwonta fami ne,sai ta gaza cewa komai,ta ja wayar tana daga kiran ta sakashi a hands free ta ajiye saman cinyarta

"Assalamu alaikum" Nutsatstsiyar muryarsan me nuna zallar kwarjini da nutsuwar mamallakinta ta bayyana tana karade falon

"Amen......sai yanzu kaga damar kirana bayan da aminatu ta baka umarni ko?" Tayi maganar cikin tsananin daci da bacin ran dake damfare a zuciyarta.

Idanuwansa ya lumshe kana ya budesu duka Lokaci guda. A duk sanda yaji sautin muryarta abubuwa da dama take tunasar dashi wadanda suka jima da shudewa. Yana jin kamar tana bankada babi babi na wata rayuwarsu ta baya da a yanzu yaketa kokawar binneta tana sake boqarewa gami da son bayyana kanta.

"Am sorry" Ya tattara kalmar da qyar yana gaya mata.

Shuru ne ya wanzu a tsakaninsu,kowa da abinda zuciyarsa ke raya masa,kowa kuma yana qoqarin controlling kansa ya fuskanci dan uwansa

"Barka da dare.....kin yini lafiya?"

"Da ban wuni lafiya ba zaka ganni fu'ad?,ko kana jiran labarin baqincikinka kai da Musaddiq ya kwantar dani ya kasheni?"

"Ya salam" Ya furta a hankali har kalmar ta shiga kunnuwanta da kyau,abinda yada karya lagonta kenan tayi shuru bata sake cewa komai ba. Shurun da tayi ya bashi damar sake cewa

"Am really sorry.....naso kiranki to amma kuma ban samu zama ba......" Qaramin tsaki taja me sauti,ita sam a yanzun ma ba wannan bane a gabanta,kiransa ko akasinsa......hanyoyin biyan buqatarta sune abinda take da muradin riska

"Ba wani matsala ko?,ba abinda kike da buqata?" Yayi mata tambayar data zama lazeem a kansa a duk sa'ilin da zaya kirata ta waya ko zaiyi tattaki zuwa inda take

"Akwai matsala......kuma ina da buqatun da zasu zama tamkar abun kunya a tattare da kai ace uwa ta mutum irinka sunfi qarfinta" Murmushi yaso qwace masa,duk da koda a gabansa kake ba zata fahimci hakan ba.

Ya riga ya fara harbo layin da ta soma hawa,don haka furucinta bai dagi hankalinsa ba ko kadan. Ya bata dukkan wani jin dadi ta fannin sutura.....muhalli abun hawa lafiya,abinci da abun shan da kaf gidan daga ita har masu aiki a qarqashinta babu wanda ke ta'ammali da wani ruwan sha idan ba ruwan gora ba. Ya bata kulawar da babu yadda za'a girka abinci cikin gidan ba tare da nama ko kifi ba. Ba irin nau'in nama ko kifin da babu shi cikin gidan muddin musulunci ya halasta cinsa.....hakanan babu nau'in cima da babu ita a gidan muddin halas ce cikin addininsa.....kamar yadda abun sha ba nau'in da babu.......ana kuma sake shiga da wani duk qarshen kowanne wata ba tare da damuwa da cewa akwaisu bila'adadin ba bash kuma qare ba

"Maahma?......wanne abu ne yafi qarfinki?" Ya tambayeta murya a tausashe yana son ya kaita muhallin da yayi imani can takeson zuwa

"Kudi fu'ad.......a matsayina na mahaifiyarka......bani da wani abu da zai shiga tsakanina da kai sai dubu dari a wata?" Ta furta tana jin ciwon abun sosai cikin zuciyarta.
*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 37
Chapter 36 · 0% Book details