← Book details Ummakatiti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 4

Sashe 3

Ummakatiti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaka na kawo miyar suka fara cin abincin a tsanake kamar basu bane suka gama cecekuce yanzu ba.

Kaka da MANGA da cokali suke ci ita kuwa mai capacity ɗin tamu hannu ta duma a cewar ta" cin abinci da hannu yafi albarka."

Su na gama cin abincin suka yi alwalla suka gabatar da sallar magriba suka baje nan tsakar gida suka fara fira kamar yadda ya kasance masu al'ada dan kullum magriba na yi zasu shimfiɗa tabarma ƙatuwa su na yin Sallah zasu zauna fira isha'i na yi su tashi su yi su dasa wata firar daga nan har lokacin kwanciya bacci ya yi.

Idan lokacin sanyi ne shi ne zasu shige ɗaki ,idan kuma lokacin zafi ne shimfiɗa suke yi su yi kwanciyar su anan waje har asuba ta yi.

Su na cikin firar ne Kaka ta sako ma UMMAKATITI zancen ɗazu tun daga zuwan Hinde har shawarar da suka yi fa Aminiyarta sai da ta rattaba mata labarin Sannan ta ƙare da ce mata ita mi ye shawarar ta.

Nan UMMAKATITI ta lailayo wani ashar ta ɗurka ma Hinde akan abun da ta ce a kan ta.

Follow me on Instagram: Meenart Wurma....

Tiktok: meenartwurmah....

Facebook:oum ummeeytah....

Telegram: Meenart Wurma....

Snapchat: Meenart Wurma....

....✍️

🙎‍♀️🙎‍♀️ UMMAKATITI🙎‍♀️🙎‍♀️
(SHORT STORY)

Na Aminatu Mansur Dikko
(Meenart Wurma)

Sadaukarwa

Na sadaukar da littafin nan ga masoya na Hafsat (Aneesart Wurma)
Da Hafsat (Nasreen)
Da Ummukulthum (Ummitah)

Ina roƙon Allah ya tsaremin ku aduk in da kuke, ya yi ma rayuwar ku albarka.

PAID BOOK NAIRA 200

Payment via this account number 0017446862 jaiz bank Aminatu Mansur Dikko
Or
7071524017 opay Aminatu Mansur Dikko
Or
Recharge card via this number 07071524017
A tura shedar biya ta numbar.

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

**EPISODE FOUR**

Nan UMMAKATITI ta lailayo wani ashar ta ɗurka ma Hinde akan abun da ta ce a kan ta sannan ta ce" yo Kaka wallahi na rantse da Allah Hinde ta bani da Ni cikin garin nan, munahika ashe ta na nan ta na samun idanu da wata shegiyar ƙafarta kamar mariƙin lema."

" Haba Yaya...."

"In kika ƙarasa na rantse da Allah sai na baje ki ƴal bura'uba kawai, ke wallahi kamar ma na lura dake ba ki ƙaunata Yarinyar nan kamar yadda nake son ki."

"Wallahi Yaya ba haka bane kin san duk duniya bani da wacce nake so sama dake saboda irin mugun son da kike min kema, Ni abun da nake so ɗaya ne dan Allah ki daina zage-zagen nan da neman rigima kawai." Ta na magana ta na ƙara marairaicewa dan UMMAKATITI ta ɗauki maganar da gaskiya.

Abun da MANGA ba ta sani ba shi ne tun lokacin da ta ce ma UMMAKATITI Yaya zance ya lalace dan tuni ta shiga tunanin abun da za ta yi ma MANGA dan ta huce takaicin Yayar nan da take ce mata.

Dan ba ta ƙaunar sunan ko kaɗan kuma ta yi-ta yi MANGA ta daina ce mata haka amma ta ƙi ta bari.

Duk lokacin da ta yunƙuro dan ta ɗauki mataki a kan MANGA sai ta kasa saboda mugun son da take mata.

Jin UMMAKATITI ta yi shiru ba ta ce komai ba ya sa MANGA ƙara cewa"Yaya wai ban ji kin ce komai ba......."

Take ta zuƙe maganar da ta ɗebo lokacin da ta ɗago kai ta kalli UMMAKATITI jin shirun ya yi yawa, aiko ta yi arba da wata munafukar harara da UMMAKATITI ke ta aika mata da ita ba tare da ta sani ba.

Hakan ya sa ta tuno ɓaranɓaramar da ta yi na cewa Yaya, ai ba shiri ta miƙe tsaye daga zaunan da take tare da kama kunnenta sannan ta ce"Dan Allah ki yi haƙuri wallahi na kasa daina kiranki da Yaya."

Ta na ƙara marairaicewa hada ɗan matso wasu guntattakin hawaye duk dan ta haƙura.

Aiko plane ɗinta ya yi aiki dan UMMAKATITI duk duniya ba abun da ta fi ƙi irin ta ga hawayen MANGARTA, duk laifin da ta yi mata sai ta haƙura, In ko wani ne ya sa ta kuka to ya kuka da kansa, dan ba makawa sai ta sa shi mafiyin sa.

Sai a lokacin kaka ta buɗi baki da duk ta cika da goro ta ce"nikam MANGA ban san wane kalar kunnen ƙashi ke gare ki ba, ache kullum magana ɗaya ake dake, tunda ta ce ba ta son kina ce mata Yayar nan ba sai ki bari ba."

"Haba Kaka mai makon ki ba ta haƙuri a'a kuma sai ki ƙara zugata."

"Yo to MANGA ai abun naki ne da ban haushi wallahi." Ta na magana ta na gantsarar goronta ta na ci.

"Hmmmn Kaka ki barni da wannan yarinyar dai, wallahi duk ranar da kika kai ni ƙarshe sai na maki mugun duka cikin gidan nan in ga wanda zai kwace ki wallahi." Ta faɗa ta na ƙwafa alamun dai za ta gane kuranta idan ta danƙeta.

"A'a a'a wallahi in dai Ni ce ba zan wani kwace ta ba ,tun da ita kunnen ƙashi ke gare ta."

Nan dai suka ci gaba da cecekuce har suka manta da zancen Hinde.

Sai kusan ɗaya da rabi sannan suka wuce ɗaki suka kwanta.

Asuba na yi UMMAKATITI ita ce farkon tashi a gidan, sannan ta tashi MANGA sai da suka gyara gidan tass sannan suka tashi Kaka dan ta yi sallah lokaci ya yi.

Bayan sun gama gabatar da sallar asuba suka yi wanka suka yi shirin tafiya school, dan bayan rasuwar Mahaifinsu Mamarsu da ƙyar ta samu UMMAKATITI ta koma makaranta, shi ma sai da ta yi mata alƙawarin da ta yi junior weac za ta yi mata aure sannan ta haƙura ta koma (dan duk duniya babu abun da UMMAKATITI take so yanzu wanda ya wuce a yi mata aure) dan ta na ƙaunar ta ji an ce wannan gidan UMMAKATITI ne, kuma ta na son ta ga ta haihu dan ta na da son yara sosai.

Sun gama shiryawa ta kwashi kayan sana'arta dan ba ta wasa da harkar kuɗi sannan suka yi gaba.

Su na hanyar tafiya Makaranta suka haɗu da ɗan Hinde shi ma zai tafi Makaranta, sai a lokacin ta tuno da munafurcin da ta yi mata.

Aiko ta kama Yaron ta yi ma sa dukan tsiya da ƙyar MANGA ta amshe sa, ita kuma ta na cewa"ka ce ma Uwarka ta fita harkata in ba haka ba wannan somin taɓi ne na yi maka, dan na rantse da Allah sai na sata asara da yawa, tun da ta ce Ni tsararta ce." Ta yi ƙwafa sannan ta yi gaba abun ta, ta bar MANGA da lallashin Yaron.

Ko da suka je Makaranta UMMAKATITI ba ta bar Yara wanda tafi aji ba da sa'anninta har ma da wanda suka fita aji, kowa shakkar ta yake ji dan ba ƙaramar masifaffiya ba ce ba, ga ta da ƙarfin bala'i.

Malamai ma ba ta bar su haka nan ba, dan duk wanda ya yi gigin taɓa ta sai ta rama ta hanyoyi da dama,

Amma duk da haka Malamansu su na son ta, saboda ƙoƙarinta dan ta sha ciwo masu gasa wadda suke yi da Maƙwabtan ƙauyikansu.

Yanzu haka UMMAKATITI ta na js2 MANGA kuma ta na js1, saboda jinkirin shekara ɗaya da UMMAKATITI ta yi ba ta yi joining secondary School ɗinta ba ya sa tafi MANGA da aji ɗaya.

Sun dawo Makaranta UMMAKATITI take ba ma Kaka labarin dukan da ta yi ma Lawali ɗan gidan Hinde.

Nan Kaka ta ce"Ai kin yi daidai ƴar Albarka, gwara da kika gwada mata ke jininace ba wai ba."

Haka suka yi ta tattauna zancen, ita dai MANGA ta na gefe ta na jin su dan ta na iya da ta yi Magana su yi mata cha, shi ya sa ta yi shiru ta na sauraransu.

Yau ta kama juma'a ana tasowa daga Masallaci ƴan ta'adda suka yi ma garinsu UMMAKATITI dirar bazata.

Haƙiƙa sun yi ɓanna sosai dan har sun kashe Mai Garin garin da wasu mutane daga cikin Al'ummar garin, sun raunata wasu daga ciki sosai.

Cikin waɗanda aka kashe hada Mijin Laure Aminiyar Kaka, shi ya sa su UMMAKATITI suke cikin tashin hankali su ma.

Kowa ka kalla a cikin garin ya na cikin tashin hankali akan abun da ya faru da su.

In da suka ɗan samu kwanciyar hankali har suka gudanar da Jana'izar wanda suka rasu washe gari Asabar shi ne turo masu sojoji da aka yi daga headquarter ta sojoji.

Hakan shi ne ya ɗan ba su ƙwarin guiwa da har su ma waɗanda suka raunata aka kwashe su aka miƙa hospital.....

Follow me on Instagram: Meenart Wurma....

Tiktok: meenartwurmah....

Facebook:oum ummeeytah....

Telegram: Meenart Wurma....

Snapchat: Meenart Wurma....

....✍️

🙎‍♀️🙎‍♀️ UMMAKATITI🙎‍♀️🙎‍♀️
(SHORT STORY)

Na Aminatu Mansur Dikko
(Meenart Wurma)

Sadaukarwa

Na sadaukar da littafin nan ga masoya na Hafsat (Aneesart Wurma)
Da Hafsat (Nasreen)
Da Ummukulthum (Ummitah)

Ina roƙon Allah ya tsaremin ku aduk in da kuke, ya yi ma rayuwar ku albarka.

PAID BOOK NAIRA 200

Payment via this account number 0017446862 jaiz bank Aminatu Mansur Dikko
Or
7071524017 opay Aminatu Mansur Dikko
Or
Recharge card via this number 07071524017
A tura shedar biya ta numbar.

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

**EPISODE FIVE**

**AIRFORCE BASE OF JAJI**

"Hey Soldiers never ace Terrorist su zo har cikin garin da muke a zaune su yi ta'addancin da suka ga dama, kuma mu naɗe hannu mu kwanta ba tare da mun ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki a kai ba." Wani Marshal na Sojojin Airforce dake tsaye gaban Hall yake magana cikin ɓacin rai cikin meeting room ɗin da suke meeting a kan abun ya faru a cikin garin Jaji.

Can wani daga cikinsu ya yi magana ya na ƙoƙarin kwantar wa da Ogansu hankali ya ce" Sorry Sir In Sha Allah za mu yi ƙoƙari mu kuma Jajirce wurin ganin hakan bai ƙara faruwa ba."
Chapter 3 · 0% Book details