Sashe 1
Ummakatiti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🙎♀️🙎♀️ UMMAKATITI🙎♀️🙎♀️
(SHORT STORY)
Na Aminatu Mansur Dikko
(Meenart Wurma)
*Sadaukarwa*
Na sadaukar da littafin nan ga masoya na Hafsat (Aneesart Wurma)
Da Hafsat(Nasreen)
Da Ummukulthum(Ummitah)
Ina roƙon Allah ya tsaremin ku aduk in da kuke, ya yi ma rayuwar ku albarka.
PAID BOOK NAIRA 200
Payment via this account number 0017446862 jaiz bank Aminatu Mansur Dikko
Or
7071524017 opay Aminatu Mansur Dikko
Or
Recharge card via this number 07071524017
A tura shedar biya ta numbar.
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💪✍️(J.W.A)
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️
**EPISODE ONE**
*SHIMFIƊA*
Suna na Ummukulthum Ibrahim amma an fi sanina da UMMAKATITI, Ni haifaffiyar garin Jaji ce dake tsakanin garin Zaria da Kaduna, Mu biyu Mahaifanmu suka haifa Ni da ƙanwata Hafsat ana ce ma ta MANGA.
Daga mu Allah bai ƙara ba su haihuwa ba har Allah ya yi ma Mahaifinmu rasuwa.
Ibrahim Musa shi ne asalin sunan Mahaifinmu tun ya na yaro Allah ya yi ma Mahaifinsa rasuwa,
Mahaifiyarsa kuma sunan ta Ummukulthum bayan rasuwar Mahaifinsa ba ta koma garinsu ba saboda ba ta da kowa a yanzu, asalinta ƴar garin kankia ce dake jahar Katsina a wani hari da ƴan bindiga suka kai garin suka kashe duk wani dangi na ta.
Hakan ya sa bayan rasuwar Mijinta ta zauna a nan Jaji ta ci gaba da kula da ɗanta har ya kai munzalin aure in da ta kawo ma sa ƴar Aminiyarta Laure me suna Hassatu ta ce ita zai aura, bai yi ma ta musu ba ya yadda suka daidai ta kansu ba wani ɓata lokaci aka sha biki.
Sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙa ba Kakarmu ganin har Hassatu ta yi shekara biyu a gidan Ibrahim ba ta taɓa ko ɓatan wata ba ya sa ta tashi hankalinta akan lallai-lallai sai Ibrahim ya ƙara aure.
Bai yi ma ta musu ba dan dama faɗuwa ce ta zo daidai da zama tun da daman ya na da wacce yake so wato Mahaifiyarmu Maryam.
Ita kuwa Kaka ba wani dogon bincike ta amince aka shiga shirye-shiryen biki.
Ba ɓata lokaci aka sha biki in da aka kai Amarya gidanta anan cikin gidansu Ibrahim ɗin ga ɗakinta ga na abokiyar zamanta wato Hassatu.
In da Allah ya taimaki Ibrahim da Mahaifiyarsa duka Matansa su na da ladabi da biyayya ga haƙuri don haka sai suka haɗa kansu suka zauna lafiya.
Su na nan su na zamansu lafiya sai ga ciki ya bayyana a jikin Maryam, haƙiƙa sun yi murna mara misaltuwa kuma sun yi godiya ga Allah buwayi gagara misali.
Hassatu ba ƙaramin ƙoƙari ta yi ba wurin danne abun dake cikin zuciyarta na ciwon rashin haihuwa , haka ta zage ta rinƙa kula da Maryam da abun da ke cikinta.
Hakan kuwa ba ƙaramin ƙima da daraja ya ƙara ma ta ba a wurin Ibrahim da Mahaifiyarsa har ma da Maryam ɗin.
Haka suka ci gaba da kula da cikin dake jikin Maryam da ma ita kanta har lokacin haihuwarsa ya yi in da ta haifi ɗiya mace, ranar suna yarinya ta ci sunan Mahaifiyar Babanta wato Ummukulthum mutanen gari su na ce ma ta UMMAKATITI.
Bayan haihuwar UMMAKATITI da wata ukku sai ga ciki ya bayyana a jikin Hassatu ita ma, faɗin murnar da suka yi ɓata baki ne saboda abu ne da suka ri ga suka fidda rai da samun sa.
Nan ita ma Maryam ta zage damtse wurin nuna ma Hassatu kulawa fiye da wacce ta ba ta lokacin da take da na ta cikin a cewar ta dole ta rama ma kura aniyarta.
Haƙiƙa ita ma ta samu kulawa sosai har ta shiga watan Haihuwarta, In da suke zaune suna jiran Allah ya kawo ranar haihuwa tare da addu'a tuƙuru da fatan sauka lafiya.
Dan tunda Hassatu ta shiga watan Haihuwarta idan su na fira da Maryam sai ta rinƙa ce ma ta"Dan Allah Maman Umma ki kula da abun da zan haifa kuma ki yi ma sa tarbiyya mai kyau, kar ki so shi da yawa har ki kasa ba sa tarbiyyar da ta dace, saboda ke ce Mahaifiyarsa wadda za ta kula da shi." Da ire-iren waɗannan kalamai su take yi ma ta duk lokacin da suka keɓe su na fira.
Idan ta ce ma ta haka ita kuma Maryam sai ta ce ma ta" Dan Allah ki daina sa damuwa a ranki in Sha Allah za ki haihu lafiya kuma ke za ki kula da abun da kika haifa da kanki har ki yi ma sa tarbiyyar da ta dace da shi."
Idan ta ce ma ta haka sai dai ta yi murmushi kawai tabar maganar.
Ranar wata Alhamis tun asuba Hassatu ta tashi da naƙuda sai gumurzu take har dare haihuwa shiru sai uban ciwo kamar za ta haihu sai kuma ta lafa.
Ganin haka da Ibrahim ya yi ya sa asuba na ketowa ya yi sauri ya fita dan ya samo mota akai ta asibiti tun da abun ya ƙiya.
Bayan ya fita da ƙyar ya samo mota suka garzayo dan zuwa su nufi asibiti da ita sai dai kuma kana naka Allah ya na na sa kuma na sa shi ne gaskiya.
Shigar sa gida kenan ya ji kuka na tashi nan da nan hankalinsa ya tashi kar dai abun da yake tunani ne ya faru.
Aiko dai ya na shiga gidan ya ji wannan mummunan labari na rasuwar Hassatu tare da abun da ke cikinta.
Sun yi kuka sun yi baƙin cikin rasa Salihar mace irin Hassatu da abun da ke cikinta amma ba yadda suka iya haka suka dangana suka ci gaba da bin su da addu'a.
Bayan shekara ɗaya Maryam ta ƙara haihuwar ɗiya mace in da aka sa ma ta sunan Marigayiya Hassatu wato Hafsat su na ce ma ta MANGA.
Daga nan kuma sai haihuwar ta tsaya ma Maryam cakk.
Ganin haka ya sa Kaka ta ɗauki son duniya ta ɗaura mana Ni da ƙanwata MANGA, ba ta bari kwata-kwata a ɓata mana rai ko mu nemi wani abu mu rasa hakan ya sa muka tashi a sangarce.
Dan ma Mahaifanmu su na matuƙar ƙoƙari wurin ganin sun ba mu tarbiyya mai kyau da nuna mana mahimmancin abubuwa da dama.
Ba dan haka ba da sai mun fi haka sangarcewa.
A haka muke ci gaba da rayuwarmu cikin farinciki da ƙaunar juna a tsakaninmu.
Babanmu ya sa mu a makarantar je ka ka dawo ta primary Ni da ƙanwata duk da bana son makaranta amma haka nake zuwa badan raina ya na so ba.
Saɓanin ƙanwata ita ta na son makaranta sosai amma a haka kuma na fi ta ƙoƙari.
Lokuta da dama idan na nuna Ni ba za ni makaranta ba aka tirsasa Ni akan sai na je sai na gudu ɗakin Kakata wadda daman acan muke kwana na ɓoye.
Sai ta yi ta faɗa akan cewa a barni ai makarantar ba dole ba ce na je ta muhammadiyya kawai ai ita ce ta tafiya lahira ba waccen ba.
Da wannan Nake fakewa in yi zamana gida ko in tafi gidansu ƙawata Lubabatu muna ce ma ta Luba sai dai ƙanwata ta tafi makarantar ita kaɗai.
Dan jin yadda rayuwar su UMMAKATITI zata kasance ku ci gaba da bibiyar ƴar mutan wurma ta kafafen sada zumunta ngd.
Fallow me on Instagram:
Meenart wurma....
Tiktok: meenartwurmah....
Facebook:oum ummeeytah....
Telegram: meenart wurma....
Snapchat: meenart wurma....
....✍️

A tura shedar biya ta numbar

**EPISODE TWO**
Ina da shekaru goma a duniya na gama primary school ɗina, Babanmu ya yi-ya yi in ci gaba da makarantar secondary Amma na ƙeƙashe idona na ce"Ni wallahi ba me sani In ci gaba da Wannan makarantar Ni aure nake so dan haka shi za'a ma ni."
Da ya ji na ce haka shi maganar ma dariya ta ba shi dan shi a ganin sa duka nawa nake da har zance aure nake so, bayan ko a cikin ƙawayena ba wacce aka yi ma aure ballantana na ce wata na gani an mawa nima nake so.
Dan haka sai ya share zancen nawa ya ci gaba da cuku-cukun nema min makarantar gaba da primary.
Ban tashi raina kaina ba sai da ya kawo min kayan makaranta da littattafai sannan, aiko nan na tada bori akan ni fa har yanzu ina akan bakana na aure nake so.
Jin haka da Kaka ta yi ya sa ta ce" to ai shi ke nan sai a ƙyale ni tun da na ce bani so." Allah Sarki Babana ba yadda ya iya haka ya haƙura ya bar Ni da maganar karatun, amma kusan kullum sai ya min nasiha mai ratsa jiki.
Ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba ranar wata juma'a da asuba muna kwance a ɗakin Kaka, Mama ta zo ɗakin ta na tada mu ta na cewa "mu zo Babanmu ba lafiya." haka mu ka tashi hankali a tashe mu ka nufi ɗakinta dan acen yake.
Muna zuwa ya kamo hannuna jikinsa na ƙyarma bakinsa na ɓari ya ce min"Ummana dan Allah ke ce Babba ko bayan ba raina ki kula da Mamata da Mahaifiyarku da ƙanwarki kar ki bari su yi maraicin rashi na, kuma dan Allah ku kula da mutuncinku kar ku bari wani abun duniya ya ruɗe ku har ku zubda mutuncinku, ku kula da ibada da bin dokokin Allah, na yafe ma ku duniya da lahira Allah ya yi ma ku albarka ya zaɓa ma ku mazaje nagari." Ya na gama faɗar haka ya fara wani jijjiga ga shi ya na so ya yi magana amma ba hali.