Sashe 2
Ummakatiti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin haka ya sa su Mama suka fara biya ma sa kalmar shahada har Allah ya sa ya maimaita daga nan rai ya yi halinsa.
Faɗin irin tashin hankalin da muka shiga ɓata baki ne haƙiƙa mun yi rashin Mahaifi mai son mu da gaskiya wanda a kullum yake nuna mana bin Allah shi ne gaba akan komai na rayuwar duniya.
Nan Kaka ta rushe da kuka ta na faɗin "shi ke nan Ibrahim kai ma ka tafi ka barni yanzu ba Ni da kowa innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, amma ba komai na yafe ma ka Ibrahim duniya da lahira Allah ya ƙarbi bakuncinka."
Kafin ka ce me gidanmu ya cika da jama'a ana ta ba mu haƙuri, muna ji muna gani aka yi ma sa sutura aka kai sa gidansa na gaskiya.
Bayan sadakar arba'in Mahaifin Mamanmu ya ce ta dawo gida ta ida takabarta, anan ta ce za ta tafi da mu Kaka ta so ta ƙi amincewa amma haka ta haƙura muka bi Mahaifiyarmu gidansu.
A haka ma kusan kullum mu na gidan Kaka domin mu ma mun ri ga mun saba da ita, kuma mun fi jin daɗin zaman wurinta saboda ba kwaɓa ba ƙyara.
Mahaifiyarmu ta gama takabarta da wata ukku Allah ya fiddo ma ta Miji farko ta ce ita ba za ta yi wani aure ba amma Mahaifinta ya ce ba ta isa ba dole ta yi aure tun da ba wuce yin sa ta yi ba.
Haka ta haƙura za ta yi auren wani mai garin ƙauye ne dake kusa da garinmu za ta aura, Matarsa ce ita ma ta rasu shi ne zai yi aure, ya na da yara ukku shi ma duka mata, biyu ya aurar da su ɗaya ce kaɗai ta rage zata zauna wurin Mama, kusan sa'anni muke da ita hakan ya sa ya ce ya amince ta tafo da mu.
Amma kaka na jin haka ta yi tsalle ta dire ta ce "wallahi ba mai tafin ma ta da Jikoki agolanci dan haka a maido mu wurinta, dama ba da son ranta ta bada mu ba."
Haka kuwa a ka yi ba yadda Mama ta iya ta tattara mu muka koma hannun Kaka da zama,
ita kuma ta yi aurenta a wani gari dake kusa da mu.
A lokacin ina da shekaru goma sha biyu a duniya ita kuma MANGA shekaru Goma daidai muka koma hannun Kaka da zama.
Komawarmu hannun Kaka da zama ya sa duk muka manta da nasihohin da Mahaifanmu suka rinƙa yi ma na, saboda sabon shafin tattali da kulawa da so ta ɓude ta na nuna mana, a cewar ta ba ta da wasu da suka wuce mu a duniyar nan.
A cikin ƙanƙanin lokaci muka ƙara sangarcewa saboda ba abun da muka nema muka rasa kuma ba wanda ya isa ya taɓa mu ya zauna lafiya.
Ina mugun son ƙanwata MANGA fiye da yadda nake son kaina, zan iya yin komai domin ta.
WANNAN KENAN KAƊAN DAGA CIKIN TARIHIN RAYUWARMU NI DA ƘANWATA, YANZU ZA MU SHIGA LABARIN KAI TSAYE.
Fallow me on Instagram:
Meenart wurma....
Tiktok: meenartwurmah....
Facebook:oum ummeeytah....
Telegram: meenart wurma....
Snapchat: meenart wurma....
....✍️
🙎♀️🙎♀️ UMMAKATITI🙎♀️🙎♀️
(SHORT STORY)
Na Aminatu Mansur Dikko
(Meenart Wurma)
Sadaukarwa
Na sadaukar da littafin nan ga masoya na Hafsat (Aneesart Wurma)
Da Hafsat (Nasreen)
Da Ummukulthum (Ummitah)
Ina roƙon Allah ya tsaremin ku aduk in da kuke, ya yi ma rayuwar ku albarka.
PAID BOOK NAIRA 200
Payment via this account number 0017446862 jaiz bank Aminatu Mansur Dikko
Or
7071524017 opay Aminatu Mansur Dikko
Or
Recharge card via this number 07071524017
A tura shedar biya ta numbar.
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
**EPISODE THREE**
"Na rantse da Allah yau sai naga abun da ya ture wa buzu naɗi a cikin garinnan, yara marayu za'a bi duk a takura masu saboda anga ba uwarsu a gari ubansu kuma ba ya raye to bada ni za'ayi wannan iskancin ba wallahi." Kaka ta haƙiƙance ta na masifa, yayin da suke tattaunawa ita da Aminiyarta Laure.
"Ai maganar gaskiya kar ki wani yadda, danni da Ni ce ke wallahi wurin hukuma zan kai zancen nan dan a shiga tsanin jikokina da wasu daga cikin mutanan garin nan." Iya Laure ta ƙarashe zancan da son ƙara kunno ƙawarta dan su ɗauki mummunan mataki.
"To ai Laure ko yanzu ba haƙura na yi ba saboda abun ya yi yawa wallahi dan haka bari wani ɗan kutumar uba ya ƙara zuwa min da maganar yaran nan ya ga yadda zamu ƙare wallahi."
Nan suka zauna sun kai awa biyu su na ta bambamin masifa akan abun da bai kai ya kawo ba.
Duk wannan masifar da suke yi fa akan wata makwabciyarsu mai suna Hinde ce da ta zo har gida ta samu Kaka bayan sun gaisa a mutunce ta ce mata" Kaka dan Allah daman abun da ya sa na zo wurin ki akan abun da UMMAKATITI take yi a cikin garinnan ne, ace kamar UMMAKATITI duka shekararta sha ukku fa amma ta hana yaran mutane saƙat a cikin garin nan, ba ka isa ka aiki Yaro ba in dai ta haɗu da shi ko dai ta duke sa ko ta lalata abun aiken."
Ta numfasa ta ci gaba da cewa"shi ya sa na zo dan In faɗa maki dan Allah ki ja mata kunne akan ta daina abun da take yi kar wata rana ta jawo wanda ya fi ƙarfinta a samu matsala." Ta na kaiwa nan ta ɗaga kai ta kalli Kaka jin tun da ta fara magana ba ta ce komai ba, aiko ta ga Kaka ta hangame baki ta na ta zabga mata harara sai huci take.
"To sannu Sarkin munafikan duk duniya wa'azi kika zo ki min ko kuwa kina so ki nuna jikokina ba su da tarbiyya iyye! Nace iyye!!."
Tuni Hinde ta shiga taitayinta ganin Kaka ta miƙe tsaye ta na nunnunata da hannu kamar zata mare ta,
Hakan ya sa ita ma ta miƙe ta ce" A'a Kaka wallahi ba haka nake nufi ba kawai na faɗa maki dan a gyara ne."
"To na ji kuma ki fita a harkar jikokina, na san ba kowa ma kike magana a kanta ba sai takwarata UMMAKATITI tun da naga duk mutanan garin nan ita kaɗai ku ka sa ma idanu."
"Kuma da kike cewa kar ta jawo wanda ya fi ta to ko ta jawo ina ruwanki nace ina ruwanki." Nan Kaka ta rufe ta da masifa kamar zata hauta da duka.
Hinde na ganin haka ta tashi ta ƙwamishi ɗan silifas ɗinta da duk ya siɗe ta yi gaba.
Ko bayan fitarta Kaka ba ta yi shiru ba ta ci gaba da mita har Aminiyarta ta shigo ta isketa a haka take tambayar ta mi ya faru ta kora mata zancen shi ne suka ci gaba da mitar a tare.
Har wurin shidda na yamma sannan Laure ta ce "kin ga Umma bari na tashi na tafi yanzu Malam zai neme Ni don basa ruwan alwalla ga magriba ta ƙarato."
" To shi ke nan Laure sai gobe in nayi shawara da UMMAKATITI kin ji yadda muka ƙare."
Nan suka tafi zaure su na bitar zancen, kusan mintinan su goma a zauren sannan ta tafi.
Ta na tafiya kuwa sai ga su UMMAKATITI sun dawo daga makarantar allo.
Wanda UMMAKATITI badan komai take zuwa ba sai dan saida ɗan tamatsitsin da take tare da daɗi biyu(kwalbebe).
"Yawwa ƴan albarka kun dawo ko?."
"Ey Kaka mun dawo sannu da gida." In ji MANGA cikin ladabi take maganar.
Ita kuwa gogar tamu wato UMMAKATITI tuni ta baje saman tabarma ta fara ƙirga kuɗin cinikin da ta yi na kayan sana'arta a makaranta.
Kaka na magana da MANGA amma hankalinta ya na a kan Ƴar lelenta dan haka ta ce mata" Ƴar lele an dawo daga makarantar ne?."
UMMAKATITI ko ɗaga ido ta kalli in da Kaka take ba ta yi ba saboda gabaɗaya hankalinta na akan ƴan canjinta da yau ta yi ciniki sosai.
Sai da ta gama ƙirga kuɗinta chass ta ga sun cika Sannan ta ɗago ta kalli Kaka ta ce "Kaka ya gida? ya gari? Ni wallahi yunwa nake ji, ina abincina." Ta na magana ta na shafa ciki alamun cikin dai sai kukan yunwa yake yi.
"Bari na ɗauko maki abincin, ai abun da kike so ne na dafa wato shinkafa da miya hada nama na sa a ciki."
"Yawwa Kakus kai gaskiya ina mugun yin ki dan haka duk ranar da na yi kuɗi za ki ji daɗi aradun Allah." Ta faɗa ta na washe baki alamun ta ji banza ta samu.
Ƙasa-ƙasa MANGA ta ce"tabɗi ke ɗin ce za'a ci kuɗinki wai sai dai wata ba dai ke ba wallahi."
"Ke MANGA mi kike cewa na ji kamar kina gunguni."
" A'a Yaya Umma ni ba abun da nake cewa wallahi."
"Ke wai dan uwarki bana ce ki daina cemin Yaya ɗin nan ba kamar wata Babba, duka nawa nike shekarata sha ukku fa da har za ki wani rinƙa cemin wata Yaya." UMMAKATITI ta faɗa ta na dungure ma MANGA kai.
Daidai nan Kaka ta iso da kular abinci ta sako ta saman plate da cokali guda ukku.
Ta ce "ke MANGA Wallahi kin cika jan faɗa, shin tunda ta ce ba ta son kina ce mata Yayar nan ba sai ki bari ba, ko ana dole ne?."
"Kaka Malaminmu ne fa ya ce idan mutum ya girme ka ba'a faɗin sunansa kai tsaye, shi ya sa nake ce mata Yaya."
"To wallahi kika ƙara cemin Yaya sai na ci kutumar ubanku ke da Malamin dan mi nace dan mi ko ana dole ne?."
Ta na ida faɗa ta jawo plate ta fara zuba farar shinkafa ta na siɗe baki tun kafin ta ga miyar ballantana ta fara cin abincin.
(Dan UMMAKATITI ba ta wasa da cikinta ga kwaɗayin tsiya).
"Ki yi haƙuri bazan ƙara ba In Sha Allah."
"Da dai ya fi maki wallahi Ni kawai ki rinƙa cemin UMMAKATITI na nafi jin daɗin sunan wallahi."