← Book details Tsutsar Nama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 22

Sashe 8

Tsutsar Nama Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_

......“Madam bafa taci abincin nan ba, ko buɗe plate ɗin ma batai ba kuma tayi barci.” Janny ta faɗa cikin nuna damuwa.
     Ƙaramar dariya Hajiya ta sauke tana wani lumshe idanu, sai kuma ta buɗesu akan Janny cike da salon irin na wayayyun mata da suka gogu da sanin duniya. “Barta yunwar ai ba ƴar  gidansu bace, dan kanta ma zata ɗauka taci”.
      Dariya tayi itama Jannyn da jinjina kanta. “Hakane Madam. Amma yarinyar yana da ƙyau fa sosai, ina ka samo shi haka? Ko dashi zamuje Lagos ne?”.
         “Tsintacciyar mage ce, dan haka ma na dawo da tafiyarmu gobe kafin ta canja shawara. Saboda na kula babbar kaddarace wannan, kwalliya da sutura kawai take buƙata”.
      Sosai Janny ta washe haƙwara, dan duk hausar da Hajiya tai tsaff ta gane kasancewar taji hausa sosai. Hajiya ma murmushin taketa faman yi, dan ita kanta tasan zata ƙaru da yarinyar sosai...

      ★Washe gari kamar yanda Hajiya ta faɗa suka tashi da shirin wucewa Lagos, harda Samraah nan dako sunanta basu sani ba har yanzu. Tunda suka tambayeta sau ɗaya tayi shiru basu sake tambayar ba. Tun jiyan kuma tana ɗaki kwance sai dai akai mata abinci a ɗakko kwano.. Janny ce mai ƙoƙarin kai-kawon, Hajiya dai nata bada umarni kawai, bakuma ta sake neman ganin Samraah ba tun shigowarsu gidan sai a yanzu da suka kwana suka yini dan tafiyar yamma zasuyi.
     Ita dai Samraah bata san ina zasu je ba. Koda ta tambayi Hajiya kuma sai cewa tai ta jira zata gani. Badai tace ita ƴar Kano bace, zata bata mamaki ne. Al'amarin kamar asiri Samraah ta gagara cewa da Hajiya komai. Hasalima jinta take jikinta duk ya gama mutuwa ga bakinta ya mata nauyi. Sannan bata jin zata iya tsallake umarnin Hajiya sam koda cewa tai ta shiga wuta ta ƙone ko ruwan teku.

       Tunda suka fito Janny taga Samraah na faman laɓe-laɓe a bayanta, Idanu Hajiya ta zuba musu kawai. Sosai ƙyawun yarinyar ya ɗauki hankalinta, sai taga tama ɗara yanda Jannyn keta kurantawa tun jiya. Baki ta buɗe zatai magana Samraah tai saurin faɗin, “Ina yini” cikin risinawa. Murmushi Hajiya ta ɗan yi tare da ɗauke kai, sai kuma ta sake maidawa ga Janny. “Wai nikam ashe amarya na kawo gidan nan ban sani ba. Irin wannan ɓoyo haka”.
      Dariya Janny takeyi sosai itama idonta akan Samraah dake ta faman sinne kanta, da alama dai itama taji kunya, tunda koba komai ya kamata ta fito ta gaida Hajiyar da safe amma taƙi yin hakan. Duk sun fahimci taji kunyar ne suma, dan haka Hajiya ta kamo hanunta tana murmushi. “Daughter ai ko gaisuwa a fito muyi tunda dai naga baki son musan sunanki. Da alama dai yana da tsadar gaske, ko sai mun saya ne?”.
         Karan farko na ɗago dara-daran idanuna masu shegen haske na sauke akan Hajiyar ina mai girgiza kaina da sauri, idanuna cike da ƙwalla alamar ina gab da shirin sakin kuka, dan haka kawai naji wani irin tsoro da shakkar matar ya shigeni mai tsananin gaske..
   “A'a da alama dai ɗiyar tawa shagwaɓaɓɓiya ce, to mun haƙura tunda dai ba'a son mu sani. Mu sai mu saka miki namu sunan ai kawai kinga an huta canki canka ko”. Hajiya ta sake faɗa cike da salo tana murza hannuna a hankali.
    Janny dai dariya take, yayinda ni kuma na duƙar da kai kawai, sai dai abinda Hajiyar ke min a hannu sam bana so, amma tsoron janye hannuna nakeyi..
“Baby zata shiga gaba koni Hajiya?”. Janny ta faɗa dai-dai muna isowa gaban hamshaƙiyar motar Hajiya data sha wanki take ta ƙyalli. Kallon Janny Hajiya tayi, yayinda ni kuma na ɗan ɓata fuska, a raina ina ayyana (baby kamar wata ƴar tsanar wasan yara) a fili kam sai na girgiza kaina a hankali na ce, “Sunana *_Samraah_*”. 
      A kusan tare Hajiya da Janny suka kalleni, Hajiya ta saki murmushi, Janny ta ce, “Woow nice name dear. Dole ki mana yanga irin wannan golden name haka”. Ta ƙare maganar tana ɗan rungumoni. Jikina na ɗan jaye daga nata batare dana sake cewa komai ba. Hakan yasa Hajiya ɗan harararta akaikaice alamar ta sakeni. Jayewa Janny tai tana faɗin, “I'm sorry maa”. Bata tanka mata ba ta kama hannuna muka shiga baya, dan tuni driver ya buɗe mana. Gaba Janny ta shiga, daga haka driver ya harba mota zuwa gate. Mun ɗan tsaya a bakin gate Hajiya tai magana da maigadinta, tare da bashi kuɗi masu yawa da suka bani mamaki. Shiko sai faman godiya yake bakinsa a washe har motar tai nisa da gate ɗin bai bar ɗaga mana hannu ba....
Chapter 8 · 0% Book details