← Book details Tsutsar Nama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 22

Sashe 20

Tsutsar Nama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_

https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG

https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

______________

......Sosai hirarmu da Bahijja ya tsaya min ƙyam a rai da zuciya. Duk yanda nake yaƙin son turesa hakan ya gagara. Gashi tun ranar ban sake ganin makirin ba. Hakama cikin gidan ban sake shiga ba. Bahijja dai ta sanar min Babansa da matar babansa sun dawo daga tafiya, hakama ƙanin baban nasa da iyalinsa sun dawo suma dai. Sannan yau gaba ɗaya sunyi busy wai ana aiki ne acan sashin saboda bikin birthday da za'ayi wai na mahaifiyar tasa. Ni al'amarin ma sai na ɗaukesa hauka. Yo inba hauka ba, koma nace sunfi ita mai ciwon haukan zama mahaukata mara lafiya dake buƙatar addu'a ce wai za'ama wani shegen birthday party. Kai yawudanci ma baiyi ba. Ko kuwa dukiyar tasu ce ke neman zauta musu ƙwaƙwale ma oho musu. Sosai takaici ya kumeni, ji nake kamar na buɗe ido na gansa a gabana. Wlhy da ko zai tsireni sai na faɗa masa gaskiya sai dai ya mutu shiya sani. Ina nan kwance ina ƙullawa da kwancewa wajen ƙarfe biyu su Mama balki suka fara dawowa. Hayaniyarsu tasa na fito falo nima. Sannu na shiga musu, wasu su amsa wasu su shareni batare dana san mina musu ba. Mama Balki ce ta dubeni da murmushi, cikin kulawa ta ce, “Ai kema daga gobe za'a fara miki sannun. Dan Aunty Mama tace zaki fara aikinki. Kinga sai ki shirya idan mun gama zamu wuce dake tare wajenta kamar yanda ta bada umarni”.
       Sosai naji wani irin abu mai nauyi ya soki zuciyata. Na dai danne da ƙyar ina murmushin yaƙe. Da girmamawa na amsa mata da “To mama nagode”. Daga haka ban sake cewa komai ba saboda baƙin ciki. Ni kuma haka rayuwata zata ƙare. Wahalar gidan Abba. Rabani da masoyina, auramin azzalumin mutum irin wannan mutumin da bai san komai ba a rayuwa sai kansa. Daga ƙarshe ma maimakon na shigo gidansu matsayin matar aure a ƴar aiki nazo. Nasan shine ya tsara hakan, kuma zan tabbatar masa ya tsara ramin muguntar da shine zai afka ciki daga ƙarshe. Dani yake magana Samraah Abdul-wahab gwarzo.....

       _Hummm Sam-G tamu. Koda yake aunty kike tunda matar Yayanmu ta🥱🥱🚴_

      ❤️ Kamar yanda Mama Balki ta umarceni wanka nayi nima. A'i da yanzu ta ɗan fara kulani itama ta kawo min doguwar riga ta farin Material da suma naga sun saka a jikinsu inji Mama Balki. Nayi mamakin kayan, dan sababbine ƙal kuma daga gani ba ƙanana bane ba. Haka dai na shirya ina zancen zuci. Ganin yanda Bahijja ta tsaya tana kallona ya sani mata alamar lafiya? Da idanu. Murmushi tayi da sauke ajiyar zuciya. “Wlhy Kandala baki ganki ba. Sam bakiyi kala da masu aiki ba. Kayan nan sun sake fiddo da ainahinki na ƙyaƙyƙyawar mace wayayya. Dan ALLAH idan bazaki damu ba ki sanar min labarinki. ALLAH sai nake ji a raina ko sunanki ba gaskiya kika sanar mana ba”.
      Idanu na ɗan waro mata kamar zanyi magana sai kuma na fasa nayi murmushi kawai. Dan babu abinda na ɗauki zancen nata sai shirme. A girme zan iya girmar Bahijja, amma yanayin inda take rayuwa da kuma halitta ta na mutum mai jiki yasa a ido zaka iya cewa sa'anni ne mu. Riƙoni tayi zata sake yin magana Afrah ta shigo. A wulaƙance tace, “Malamai ku Mama ke jira kuka wani zo nan kuka haɗe kawuna dan munafunc....”
      Ta gagara ƙarasawa saboda saukar idanunta a kaina. Ɗauke kaina nayi tamkar banga kallon da take min ba. naja ƙaramin mayafin Bahijja na yafa nai ficewata na barsu..
         “Kan uba Bahijja kinga kuwa abinda na gani tattare da yarinyar nan?”. Afrah ta faɗa cikin jimami da shiga ruɗani. Ƴar dariyar shaƙiyanci Bahijja tayi. “Yo mi kika gani?”.
      “Bahijja anya ba ƴar leƙen asiri bace ba. Sam yarinyar nan batai kama da wadda ta fito a cikin wahala ba. Musamman kwana biyun nan da tayi a gidan nan jikinta ya sake murjewa sai ainahinta ya fito. Duk da muma yawancinmu badaga ƙauye aka kawomu ba rashin gata ne da neman rufin asiri amma yarinyar nan fa ta fita daban a cikinmu wlhy.”
      Cikin son basar da zancen Bahijja ta ce, “Babu wani leƙen asiri. Itama dai neman rufin asirin ne ya kawota. Acikin ƴaƴan talakawan ma ai akwai ƙyawawa da yawa irinta har ma da wanda suka fita. Kin san dama irinsu gatan ne kawai babu, amma da sun samu kulawa sai ki gansu tarr da su”.
     Badan Afrah ta gamsu da bayanin Bahijja ba tai shiru. Dan Bahijjar na gama bata amsa ta nufi hanyar fita itama. Kai kawai Afrah ke jinjinawa da sake tabbatar ma kanta dole ne ta sakama yarinyar nan ido a gidan nan, dan sai ta san ko ita wacece....
Chapter 20 · 0% Book details