← Book details Tsutsar Nama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 22

Sashe 21

Tsutsar Nama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Koda na fito falon ma gaba ɗayansu suka zubomin ido. Hatta da Mama Balki naga alamar shock a tattare da ita. Tuni na ƙara gyara yanayina, dan na fahimci fa nima sai na yarda na ari wata rayuwa kafin na cimma burina akan mutumin nan dama zaman gidan nan. Sam bana fatan zama a cikinsa na dogon lokaci. Amma ina da burin son sanin sirrin cikinsa da mutumin nan keta faman ɓoyema duniya. Hakan kuma bazai taɓa ya kasance ba sai na zauna a matsayin da kowa ke kallona a yanzu na ƴar aiki. Ta wani gefen kuma begen ganin mahaifiyarsa da tausayinta na tsungulin min rai da zuciya. Sai dai ban san ta ina zan kama ba har yanzu. Gaishesu nayi kawai na koma gefe kaina a ƙasa...
      “Tab ɗi lallai akwai rigima a gidan nan. A banga laifin Hajiya Azizat ba. Anya kuwa babu alamar tambaya anan gurin?”. Aunty Falilah ce tai maganar cikin nuna baƙin cikinta muraran a kaina. Dama na fahimci ita da sauran ƙawayenta su Aunty Kubrah basa ƙaunata sam. Kafin wani ya sake magana Mama Balki tace muje. Dole kowa ya haɗiye abinda ke a ransa muka fice. Cikin raɗa Bahijja dake ta gefena ta ce, “Kiyi haƙuri karki damu da su. Su dama su Aunty ƴan neman fitina ne, sam basa riƙe girmansu a cikinmu saboda suna gadarar yaran Mammah ne a gidan. Itace mai juya akalar kowa a gidan kuma hatta da mai gidan kansa da matarsa”.
      Murmushi kawai nayi batare da nace komai ba. Dan ta gefena su Afrah ne idan har nayi magana zasu jini. Sosai an sake ƙawata gidan. Tako ina ka kalla kasan za'ayi shagali ne. A maimakon cikin gidan yau garden muka nufa. Bamma san sanda na furta “Masha ALLAH” ba a zahiri. Dan tsayawa muku misalin haɗuwa da tsaruwar da garden ɗin nan yayi ma ɓata lokaci ne. Sai dai abin mamaki bamu tsaya anan ba. Ta wata ƙofa da ganyen flower ya baibaye muka sake ratsawa sai gamu a wani killataccen waje da yafi wancan ƙatoton da muka ratso, wani irin shiryayyen adon furanni da koriyar ciyawa akai masa tako ina masu ƙamshi. Ga ƙaton swimming pool da ruwansa ke wani kalar ƙyalli da walwali tamkar ba normal ruwa ba. Ƙasa-ƙasa Bahijja dake kusa da ni ta furta, “Wannan sashen garden ɗin babu mai shigowa cikinsa sai a irin wannan ranar. Sau ɗaya a shekara kenan kawai”.
      Da mamaki nace mata, “Saboda mi?”.
      “Saboda bana kowa da kowa bane. Bakiga an zagayesa da waya ba. Uncle boss kaɗai ke shigowa cikinsa, dan tanan shine jikin part ɗinsa”. Ta ƙare maganar da ɗan nuna min wata hanya da aka ƙawata da koriyar ciyawa tamkar a irin lambun mafarkin gaibu ɗin nan. Na jima ina kallon ƙofar abubuwa masu yawa namin kai-kawo. Sai dai bance komai ba face ɗan kalle-kallen garden ɗin da nake yi. Komai a tsare a tsaftace. ga Docorretion ɗin da akai masa ya bala'in sake ƙawatashi. Hannuna da mama tazo ta kama ya sani kallonta firgigit, murmushi tamun da faɗin, “Zo muje ke anan zaki zauna har sai an buƙaci ganinki”.
       “Mama saboda mi?.
    “Saboda Aunty Mama bata bada umarni na shigo da ke har nan ba”.
Komai ban sake iya cewa ba har taja hannuna muka fito a wajen. A ƙaton garden ɗin na farko muka dawo. Ta kaini can wani ɗan lungu ta ce, “Zauna anan. Kar kije ko ina dan ALLAH dan akoda yaushe zan iya zuwa kiranki”.
    Kaina kawai na jinjina mata. Dan koda bata roƙeni ba ma bazan tashin ba. Nakai zaman mintuna talatin a wajen dukan tunanina naga Yaya Musaddiq. Yau wani irin kwaɗayin son jin muryarsa nake shi da Hafizzullah. Tamkar wadda hankalinta ke dawowa jikinta a wajen nake jin ƙarfin zuciyata da komaina dake neman ƙwacemin a kwanakin nan na fara dawowa. Sai kawai naji harshena ya ɗauki ambaton sunayen ALLAH. A jere na ringa sauke ajiyar zuciya kai kace a barci na farka. Ratsa kunnenna da sautin muryar malam tayi yana karanto addu'a ya sani lumshe idanuna a hankali. Ji nake hatta da jinin jikina yamutsawa yake yi har a cikin farautana har malam ya kammala. Ajiyar zuciya na sake saukewa a karo na babu adadi, dai-dai nan sai ga Mama Balki ta dawo kirana.
       Nasha mamakin ganin wajen yanzu dan cike. Dan komai da alama an tsarashi ne hatta da mutanen dake a wajen. Ɗan bin kowa da kallo nake ƙasa-ƙasa nima har muka isa inda su Bahijja ke tsaye jere. Dai-dai nan mc ke shelanta fitowar mai gayya mai aiki tare da tabbatar da shi a madadin  mai birthday ɗin. Tsitt wajen yayi kowa ya sake maida hankalinsa ga hanyar da Bahijja ta nunamin ta sashensa. Duk da yanda zuciyata ke tafasa na kasa ɗauke idanuna daga kallon wajen nima. Ƙanjamammiyar baturiyar nan mai shegen iyayi da yaje da ita wajen taron buɗe companynsa ce ta fara fitowa sanye cikin doguwar riga milk da wasu shegun dogayen takalmanta. Siririn tsaki na saki tare da ɗauke kaina a wajen gaba ɗaya.
       “Woow masha ALLAHU”. Da Bahijja dake a gefena ta faɗa ya sakani ɗagowa na kalleta. Ganin yanda ta saki baki da hanci da idanu tana kallo ya bani mamaki, kaina kawai na girgiza zan ɗauke caraf ta kamo hannuna. ”Dan ALLAH ki kalla ado ya namijin ɗawusu Aunty Kandala. Wlhy Uncle Boss na kasheni da salonsa, komai ya saka a jikinsa sai kiga kamar danshi dama akayi kayan, wani lokacin sai nakeji kamar na ciza uwawuna”.
      Takaicin shirmenta ya sakani dalla mata harara. Nai ƙoƙarin fisge hannuna amma ta sake damƙeshi. Haushi ya sakani kallonta, amma sai naga ma ita hankalinta sam baya a kaina. Takaici ya sani girgiza kai kawai nakai dubana ga abinda take zuzutawar batare da nasan dalili ba nima..........✍️

      _Bayin ALLAH kuyi haƙuri dani Please. Wlhy biki gareni na ƙanwata asabar ɗin nan. Jiya kuma rasuwa akai mana data bugeni sosai. Amma in sha ALLAHU komai ya kusa dai-dai da amarya taje ɗakinta zaku cigaba da ganina yanda ya kamata. Kuyi hakuri da asha ruwan tsuntsayen nan nawa na yanzu🙏_

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_

......Akan takalman ƙafarsa na fara sauke idanuna, yanda suke sheƙi da ɗaukar idon mai kallo ya isa tabbatar maka almubazzaracin da akai da kuɗi wajen sayensu. Coffee brown suit ne a jikinsa, sai rigar ciki milk color. Kamar kullum botiran farko a buɗe har ana iya hango jikinsa kaɗan. Luf-luff gashin kumatunsa ke kwance a saman fuskarsa tamkar masu barci, sai wani irin sheƙi suke suma. Hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa ɗayan riƙe da wayar dake manne a kunnensa yana wani motsa ƙananun pinkish lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima tilas. Kamar kullum kunnensa ɗaya manne da ɗan kunne, daga tacan saman kansa zane da kitso ƙwara biyu zane ata gefe da gefe, tsakkiya wiving kusan biyar, cikkune dan haka ɗaure yake a tsakkiya ƙarshen kitson kuma gashin a warware ba'a kitseba dan haka ya sakesa kawai a baya yana lilo. Wani irin takaici da haushi ya sakani kallon fuskarsa duk da nasan tabbas yayi ƙyau. Karaf kuwa idanuna a cikin nasa. Bamma san lokacin dana balla masa harara da murguɗa nawa bakin ba. A mamakina sai kawai naga ya lumshe nasa idanun tare da buɗesu a lokaci guda yana cije gefen lips ɗinsa ya ɗauke kansa. nima ɗauke nawan nayi kamar zan fasa kuka, ji nake tamkar naje gareshi yanzu na zazzage masa abinda ke a raina. Amma dai na dake, sai harara dana sake jefama jelar PA ɗinsa dana fahimci tunda idonsa ya sauka a kaina yay suman tsaye. Niko na ɗauke kaina tamkar ban san da zamansa a wajen ba. Tunda nasan dai duk abinda mugun ogansa ya ƙulla tare da shine makirin shima.
Chapter 21 · 0% Book details