← Book details Tsutsar Nama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 22

Sashe 4

Tsutsar Nama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       _Ni kaina Bilyn ku zuciyar tawa bugawa take. ALLAH yasa dai ba rasa Mansoor mukai ba😭😭🙆._

*_ABUJA_*

       ★Sosai na birkicema likitan nan akan nifa sai nasan a inda nake. Hankalinsa ya tashi, dan ya tabbatar min in har ban kwantar da nawa hankalin ba aikinsu zai iya komawa baya. Ganin fa ba saurarensa zanyi ba ya sanar min in a Abuja ne cikin MAASH HOSPITAL.
      “Abuja?!”.
    Kansa ya jinjina min da sauri. “Yes, yes. You were brought from our branch in Kano. Once you have finished receiving the medicine, you will return. Please calm down”
    Rasama mi zance masa nayi, sai kawai nayi shiru ina kallon PA da suka shigo kusan tare. Shi doctor ya zata na fahimcesa ne, dan haka ya sauke ajiyar zuciya da cigaba da kwantar min da hankali. Ko kulashi ban sake yi ba. Har ya gama ɓaɓatunsa ya fita. Ɗauke idanu nai da ga kan PA ina mai cije lips ɗina da ƙarfi. Na fahimci waɗan nan mutanen so suke sai mun kai matakin ƙarshe da su. So suke sai na bijire ma maganar Yaya Musaddiq da Mansoor. So suke sai na musu fallasar da zata ruguza dukkan tanadinsu. Kamar PA ya fahimci mi nake ayyanawa a raina. Takowa yay ya ƙaraso gaban gadon ya ajiye ledar hannunsa. Kafin ya ciro wayarsa a aljihu yay ƴan danne-danne batare da yace komai ba ya ajiye min saman table da akai crossing a tsakiyar gadon da magunguna a kai da dama sune Nurse zata bani na birkice musu. Harara na ɗago zan watsa masa sai idanuna suka sauka akan fuskar wayar. Tamkar waccan ranar yanzun ma tar-tar nake ganinsa. Yanda ya kafeni da shegun idanunsa kaifafa kalar na maguna ya sakani sake ɗaure fuska tare da ƙarasa antayawa PA ɗin nasa hararar da nayi niyya. Sai dai ashe shi harma ya fice ya barni da wayar. Wani irin takaici ne ya sake ruƙunƙumeni. Dan haka na rumtse idanuna da ƙarfi ina jin matuƙar zafi a raina. Kafin na buɗesu gaba ɗaya a fusace kan wayar. Shiko shiru yay kawai yana kallona da kaifafan idanunsa da nake jin tasiri su har a cikin jinina. Duk da yanda nake jin tasirinsu ban janye nawa dake masa kallon tsana da takaici ba. Cikin kaushin harshe da disashiyar muryata ta marasa lafiya na furta, “Kai ko akwai zuciya a ƙirjinka?”.
        Shiru babu alamar zai tanka min, sai ma janye idanunsa da yay a wani kalar slowly ya maida kan laptop dake gabansa. Dan alamu ya nuna kamar a study table yake zaune. Cikin sake jin wani sabon baƙin cikin na kai hannu saman kaina dake sara min. Fahimtar bazai amsa min ba ya sani cigaba da faɗin, “Anya kai Musulmi ne?”.
      Cak ya tsaya daga barin abinda yake yi, dan haka ya ɗago muna kallon juna cikin ido, idanunsa sun wani kaɗa blue ɗin gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama siririya like mage sak. Zamansa ya gyara na ƙasaita da isa da ke tabbatar da shi matsayin ingarman namiji, ga wani irin shegen kwarjini da nake ji ya mamaye ɗakin har kamar na matsu kai kace a gabana yake mayen. Ganin haka ya sakani cigaba da maganata batare da na damu da duk abubuwan dake tattare da shi ɗin ba.
       “Idan har kai musulmi ne bana jin kasan HARAMCI da HALLACIN dake cikin dokokin addinin musulunci. Idan kuma har da zuciya a ƙirjinka tabbas bata masu IMANI bace. Ina mai baka shawara kada kai wasa da wuta a tafin hannunka, dan wutar da UBANGIJI zai ladabtar da ma'abota bijirewa ta ninka wadda ake girka maka shinkafa a duniya kaci sau dubu bisa dubu. Idan baka sani bane zan faɗa maka a yanzu ni ɗin MATAR WANI CE. igiyoyin AURE ne a kaina ba igiyoyin ɗaure dabba a turken turka ba. Kaji tausayin kanka, da gujema saɓama UBANGIJI ka maidani inda ka ɗakkoni gidan aurena hannun MIJINA da IYAYENA.”
          “Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN kuma fa?”. Ya faɗa cikin wata iriyar muryar dakiya da gizago mai tsarga zuciya. Dan yanda sautin amon muryar tasa da kaifinta ya tasirantar da furucin nasa a tsakkiyar kaina kaɗan ya rage zuciyata bata ɓullo ta bakina ta fito ba. Amma duk da hakan sai ga tari mai ƙarfi ya sarƙe min numfashi. Gaf-gaf jikina dake a cikin yanayin rashin ƙarfi ya fara rawa. Bamma san lokacin da bakina ba ya furta “MIJI?!”. Sai kuma kaina yay wani irin masifar sarawa da ban taɓa ji ko tsinkayen irinsa ba. Ga nauyi da idanuna sukamin har inajin jijiyarsu na ja kamar za'a fincike min su. In dai har wannan ake kira hawan jini to tabbas ya sameni kuwa a yanzun nan. Dan ƙirjina kansa yay wani irin nauyi. A karo na biyu hankalina ya sake neman barina. Nai yaƙin maidosa jikina tare da ɗagowa ina kallonsa domin son tabbatarwa. Amma a maimakon amsa ma da nake buƙata garesa hankalinsa kwance yake cigaba da aikin gabansa. Wani irin kallo nake masa mai kama da firgici, yayinda shima ya zuba min nasa cat eyes ɗin cikin yanayin i don't care tamkar zai cinyeni da su.
Cike da salon izza da ƙasaita ya wani sake tsuke fuska da yamutseta sannan ya furta, “Har yanzu kina da sauran dama. Domin guri bai ƙure miki ba na komawa inda kika fito. Ki bama yarona video ko fadar inda yake a ɗakko gobe ki koma garinku. Saɓanin hakan cigaba da dawwama ƙarƙashin mulkin mallakar Maashhhh. Ke baki mori rayuwar taki ba. Ba kuma ki iya yin komai akan abinda kike tunanin iyawa ba”.........✍️

Yayanmu Barka da salla, ban sani ba ko a duniyarku kunyi azumin kuma🥱👩🏻‍🦯.

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_

.......Wani irin sake sarawa kaina yayi, dole na kai hannu na sake dafesa tare da saurin dafe ƙarfen gadon dan ji nake zan zube ƙasa, hasalima sam bana fahimtar maganganunsa a yanzu. Sai kalamansa ne na farko ke faman maimaita kansu a cikin kaina cikin matuƙar amsa kuwwar data zarce ƙarfin muryar daya sanar min su. (Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN fa?) Kalamansa suka shiga min amsa kuwwa a cikin kunne tamkar wadda akema shelarsu. Gaba ɗaya ma brain ɗina ta toshe, sai nake jin kamar na kasa fahimta ko fassara su a bigiren daya dace. (Kai ina wannan gangan ne) wani gefe na zuciyata ya ambata. (Samraah dawo cikin hankalinki mana) sashen zuciyar tawa dai ya sake maimaitawa. Hannuna dake a saman kaina na sauke tare da kaisa saman kumatuna na ɗan bubbuga, dan nafi tunanin mafarkine kawai. (Kai amma wannn mummunan mafarki da muni yake) na sake faɗa ina bubbuga fuskar sosai da ƙarfin gaske kozan farka. Zafin daya ratsata ya sakani rumtse idanun da ƙarfi. A masifar jigace da ƙoƙarin haɗiye hawayena na ce, “Wai kai minene alaƙarka da ni ne? Mi kaje ka ƙulla? Miye matsalarka dani?”.
       Idanunsa ya ɗauke da ga kaina gaba ɗaya. Sai kuma ya ɗan taɓe baki alamar yanzun ma bazai tanka min ba. Rainin wayonsa ya gama zuwa min ko ina. Dan haka na fisgi ɗan ƙarfen dake cikin tasar asibiti a gefena na ɗago ina kaisa saman cikina cikin soyewar ido data zuciya. “Dana zauna da kai a matsayin miji gara na kashe kaina na san ban mori komai a rayuwata ba.”
       Idanunsa dake min wani kallon ƙasa-ƙasa ya sake ja luuu kamar zai rufesu gaba ɗaya. Sai kuma ya buɗesu warr cikin yanayin i don't care manners ya furta, “So! Ai ba hanaki zan ba. Abinda kawai nake buƙata kafin ki mutum ki bani video”.
      Wani irin sakartaccen kallon tsana da takaici nake masa. Na cije lips ɗina da masifar ƙarfi. “Har abada kuwa buƙatar taka bazata biya ba. Dan wannan videon bazai taɓa zuwa hannunka ba har gaban abada.”
     “Ashe kuwa ko kin mutu gawarki zata cigaba da zama a gareni. Ahalinki kuma zasu cigaba da amsar hukuncin laifinki”.
          “Idan kuma kai na kashe fa?”. Na faɗa ina jefar da ƙarfen cike da tsantsar fusata da tafi ta ɗazun. Idanunsa ya ɗan zuba min, sai kuma cikin nuna rashin damuwa ya janyesu yana wani shegen annamimin murmushi daya ƙona min rai.
      “Oh are you threatening me? Ai game dani ba wasan yara bane ba. Har yanzu bamu fara wasan ba, balle ki tunanin samun game over. Zan iya baki damar kwanaki domin shiryawa. Ba kince kinfi ƙarfin laɓewa bayan wani domin faɗan sunƙuru ba. To gana gaba-da-gaba nan kin samun bissmillah. Matsoraciya kawai. Kwana uku kacal har kin fara banbance tsakanin aya da tsakkuwa”.
      Bamma san lokacin da wani irin ƙarfin zuciya yazo min ba. Cikin tsantsagwaron ɗaukar alwashi da tsawa na ce, “Har abada nafi ƙarfin yin laushi a hannun matsoraci irin ka. Dan ni har yanzu banga MAZANTAKA ba anan tunda sai da ka laɓe a bayan aure yanzun ma. Kasaka a ranka daga yau ni Samraah bint Abdul-wahab Gwarzo, sai na sakaka lissafin lissafa kwanakin rugujewarka daga yau har zuwa ranar dana ɗeba maka da zan kuma koma ga masoyina. Ni nan sai na sakaka gudu, gudu irin wanda babu wajen zuwa a tsakkiyar sahara mai tsananin zafi rana da ƙarancin ruwa. Wlhy sai kasan ka ɗakko KARA DA KIYASHI. zakuma kasan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na ture wayar ƙasa batare da na jira jin abinda zaice ba. Sai ma wani irin izza da ƙarfin iko da naji yana ratsa gaɓɓaina, duk da sara min da kaina yake tamkar zai rabe biyu. Sai kuma hawaye sharr suka shiga kwaranyomin masu zafin gaske....

       (🥱🥱tofa irin wannan alwashi haka Sam-G).

         💦💞💦💞💦💞
Chapter 4 · 0% Book details