← Book details Almajirai Ma Yaya Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
CHAPTER 6 OF 6

Part 40

Almajirai Ma Yaya Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 27 min read

Tsaye Sajan Gali yake agaban Alhaji Bashir, bayan sun gama gaisawa Alhaji yace kaga kira daga sama ko? Gali yace wallahi kuwa, ai kullum cikin zuba ido nake ina jiran kiranka.
Kasan idan mutum ya rasa aikinyi sede yayi ta 'yan bugege, kawai dazu ina zaune sega kiranka. Alhaji yace wallahi wannan sakaran megadin nawa ne ya kara bata mani rai, kasan halin Mabaratan banzan nan, basuda aikinyi se damun mutane.
Wai mutane bazasu tashi sunemi nakansu ba kawai kana zaune se kaga katon Allah yashigo yana kware murya yana maka bara. Wallahi da ina da iko se na sa an kame duka Mabaratan garin nan.
Dariya Gali yayi yace wallahi Alhaji kana da gaskiya, lokacin ina aiki bana shiri da Mabarata, nifa ban dauka marar arziki shine Mabaraci ba, kawai masu matattar zuciya sune Mabarata.
Hatta da karamin Almajiri idan zuciyarshi bata mutu ba yasan yaje yarika neman aiki base yayi bara ba. Amma ai Bara akwai cin rai. Alhaji yace ai shiyasa naji dadin samunka. Wannan katuwar gorar taka bana so ka saurara ma kowa.
Mutum ko kofar gidan nan yazo kaci mani Ubansa. Gali yace aini nayi mamaki da kace mani wai Mabarata suna shigo maka gida, shi megadin a ina yake zaune? Alhaji yace kullum yana daki se kace boka.
Idan ka ganshi a waje to baya wuce kofar dakinshi, yanda kasan shine megidan, sam bayason yarika zama awaje se kace Dan wani, idan yanajin kunyar aganshi yana aikin gadi meyasa yafara, nasan wannan shine dalilin da yasa baya son zama awaje.
Gali yace Alhaji ka sani ko akwai surikinshi a unguwarnan? Tsaki Alhaji yaja yace shi yasani, nide inaso kayi mani aikin da ko dabba marar hankali bata isa ta shafi gefen gidana ba bare mutum me rai.
Ko Almajiri bance ka raga mashi ba, tunda yasan yazo yayi bara ze iya daukar kowane hukunci, gara muruka sa masu jin zafin abinda muke masu hakan zesa suyi zuciya suje su nemi nakansu. Gali yace Alhaji baka da matsala inde nine.
Ina so a kafa mani rumfa a gefen gate din nan, domin gadi nazo banga dalilin da zesa nashiga daga ciki ba, dama kamata yayi ace idan zakuyi wannan dakin kurikayin kofa biyu.
Daya awaje, dayar aciki saboda idan kuna kiran mutum base kun fito waje ba ze iyaji ta kofar ciki, kofar wajen kuma kaga se mutum yarika shiga ta ciki kawai, amma dama an dauki mutum gadi a sakashi cikin gate sannan abashi daki hada kofar rufewa ai dole yayi abinda yakeso.
Matanku da 'ya'yanku suna shawagi a harabar gida megadi kuma yana gefe yana kalle makasu, kilama kai kana can kana nema shikuma yana ciki yana kalle maka mata da yara, kowace irin shiga sukayi yana nan yana zuba masu ido.
Komin tsufan mutum Alhaji kada ka yarda dashi inde a fannin iyalanka ne. Masu gadi su zauna awaje shine magana bawai su shiga cikin gida ba, domin bazasu rika ganin abinda yake waje ba.
Jinjina kai Alhaji yayi yace hakika Sajan ka fadi gaskiya, tunanina be taba hango mani haka ba, amma acikin bayaninka na fahimci komai, amfanin tarayya da wanda yayi ilimi kenan.
Kasan akwai banbanci tsakanin wanda yayi boko da masu ilimin zaure, domin nasan Malan Abu iliminshi na zaure ne. Bakomai ba rumfa za'ayi maka ba, kamar yanda ka bada shawarar ayi kofa biyu hakan za'ayi.
Gobe zan kira masu yimani aiki suzo a fasa maka kofa ta waje, bandakin ma za'a fasa maka kofar ta waje, nagode sosai da wannan karin hasken naka. Malan Abu ina biyanshi dubu ashirin awata.
Amma kai zan baka dubu talatin saboda kai kana da ilimin boko kana da diploma koba komai kafi Malan Abu me ilimin zaure. Dariya suka sa Gali yace nagode kai Alhaji bakada dama. Alhaji yace ka zauna bara akawo maka abinci.
Zama Gali yayi yana gyara hula yace anzo wajen, Allah nagode maka daka bani wannan aikin, tunda Allah yasa an ganoni da takardun bogi an koreni daga aiki yanzu Allah yakara bani wani, dubu talatin sekace me aikin gwamnati? Wai me diploma, nida ko primary ban gama ba.
Abinci me kyau, lallai idan mutum ya iya dadin baki babu abinda baze samu ba, lallai Alhaji kashigo hannu, dama na gama sanin labarinka, inde zugace da dadin baki kazo wajen. Ina zaune awaje ko cikin gida duk daya ne, hakan ma zanfi sakewa da masu talla na dan latsa yara ta kofar waje babu sa idon yaranka.
Allah sarki abokaina ko sun dawo suzo su sha labari me dadi? Kai nasan Goga zeyi farin ciki dajin wannan labarin, ina tsoron fada masu korata daga aiki kada suyi mani dariya segashi kuma na samu wanda yafishi tsoka, gyara zama yayi yana fadin tunda kudi sun samu anjima na sa kudi na taboshi.
**** *****
Fiddausi ce ta fito dauke da wasu kwanuka tana zuwa Nazeeru yana wanke wanke ta watsa mashi tana fadin wai kai dan ubanka wane irin yaro ne me kwakwalwar kifi? Kai kullum se an nuna maka yanda zakayi aiki.
Dukar da kai Nazeeru yayi yana rike kafa saboda wani kofi daya bugar mashi kafa yaji zafi sosai saboda na glass ne, ganin yayi shiru bece komai ba yasa taji haushi. Bokitin ruwan dauraya ta dauka.
Ba bata lokaci ta juye mashi ruwan ajiki, wani irin ihu Nazeeru ya saki a rude ya mike tsaye, dede lokacin Ashiru yashigo gidan saboda yayi mantuwa shine ya dawo dauka.
Farida ma da sauri tafito jin ihun Nazeeru, shiko Nazeeru tunda yayi wannan ihun be kara motsi ba yana tsaye duk ya kafe, da sauri Ashiru yayi kanshi ganin halin da yake ciki, saurin kamashi yayi yana jijjigashi.
Farida ma kanshi tayi tana kiran sunanshi, Fiddausi kuwa tsoro ne yafara kamata ganin halin da Nazeeru yashiga, matsawa tayi wajen kofar dakinta kamar me shirin zubawa da gudu.
Ganin numfashin Nazeeru yaki dawowa yasa Ashiru yayi saurin daukarshi ya nufi gidan Baba Kamal dashi saboda yaganshi a kofar gida daze shigo. Yana zuwa yashiga zaure yana kwala sallama da karfi.
Da sauri Baba Kamal yafito jin muryar Ashiru da karfi, yana zuwa Ashiru yace ba lafiya temaka mana kada dan mutane ya mutu, wallahi Fiddausi ce ta watsa mashi ruwan wanke wanke.
Karbarshi Baba Kamal yayi yana fadin bismilla kashigo, haka suka shiga Farida tana binsu abaya se kuka takeyi. An dauki lokaci kafin numfashin Nazeeru ya dawo, duk wani temako Baba Kamal ya bashi harseda numfashinsa ya dedeta.
Koda ya tashi a frigice ya farka yana kwalama Mamarshi kira, saurin kan kame Baba Kamal yayi yasa kuka yana fadin zata kasheni dan Allah kiyi hakuri. Kara rikeshi Baba Kamal yayi yana tofa mashi addu'a.
Baba Kamal yace Farida wai me yake faruwa? Daga ganin yanda Nazeeru ya tsorata da Fiddausi akwai wani abu da takeyi mashi. Dukar da kai Farida tayi tana goge kwallar data zubo mata. Ashiru yace kiyi magana mana.
Nan Farida ta fada masu irin abubuwan da Fiddausi takeyima Nazeeru idan ranar girkinta ne. Idanuwan Baba Kamal sosai suka kada saboda bacin rai. A fusace Ashiru ya nufi hanyar fita. Saurin kamoshi Baba Kamal yayi.
Tashi tsaye yayi yana fadin haba Ashiru, idan rai ya baci ai ba'a saurin tunkarar wanda yayi laifi alokacin, yanzu idan kaje kasan irin abinda shedan ze kulla maka? Kayi hakuri, Fiddausi de matarka ce.
Zaka iya canza Nazeeru domin baka hada komai dashi ba, ita kuwa koba komai kuna da diya da ita, sannan kunyi zaman shekaru da ita, haka kawai saboda Almajiri wanda nine silar kawoshi gidanka bazanso ace kun samu matsala ba.
Nazeeru de nine na kawoshi, kuma dalilin da yasa ban ajeshi agida na ba saboda muna da me aiki, ganin muna makwaftaka da kai yasa nayi tunanin kaishi gidanka tunda kana da bukatarshi.
Amma tunda har zamanshi agidanka ze jawo matsala gara ayi hakuri, dama haka zaman mata biyu ya gada, matukar ba'a samu hadin kai ba to dole asamu matsala ta wajen masu aiki.
Ina me rokonka da Allah kada kace zaka dauki wani mataki marar kyau, kasan halin mata base na fada maka ba domin ka rigani zama dasu, hakuri zakayi kuma ka nuna mata kuskurenta.
Na tabbata itama yanzu hankalinta yana can atashe, idan Nazeeru ne yake cutarta zata gani, idan kuma itace take cutarshi wallahi Allah baze barta ba, domin Nazeeru maraya ne gaba da baya.
Ajiyar zuciya Ashiru yayi yace shikenan nagode, kuma kamar yanda ka fada tabbas Allah ze saka mashi, domin duk wanda ya cuci maraya Allah baze barshi ba. Hannu yasa aljihu yaciro dubu biyu ya mikama Baba Kamal yace duk da wata be kare ba, ga dari biyunshi nan ta wata.
Sauran kuma abashi nagode da irin aikin da kayi mani, tabbas Nazeeru ka cika dan halak, ba kowane Almajiri bane ze samu irin damar daka samu amma arika mashi wanna cin mutuncin kuma ko so daya baka taba fadama Kamal ba.
Allah yayi maka albarka, ya temakeka aduk inda kake, Allah ya baka sa'a idan kasamu wani aikin. Kamal ina fatan babu wata matsala ajikinshi ko? Baba Kamal yace e to, ayanzu bazan iya cewa komai ba.
Zan barshi anan yaci abinci yasha magani seya kwanta zuwa anjima muga yanda jikinshi zeyi, yau ma sede kayi hakuri da zuwa makaranta duk da kun kusa fara C.A test, nasan zaka fahimci komai nasan kana maida hankali.
Hannu Ashiru yabashi yana me kara yimashi godiya yace zuwa anjima idan ya farka seka fada mani yanda jikin nashi yake, nima mantuwa nayi nadawo rabon nazo na iske wannan tashin hankalin ne.
Farida cike da damuwa tace Nazeeru Allah yakara sauki, nikam zanyi bakin cikin tafiyarka, duk cikin yaran da suke mana aiki bamu taba samun yaron kirki irinka ba, sam baya da hadama Nazeeru, abinda aka bashi shi kadai yake dauka.
Baya shiga inda ba'a ce yashiga ba, gashi da aiki tsakaninshi da Allah, gaskiya zanyi kewarka, duk da ka kasance yaro karami amma kana da halin manya. Allah yabaka lafiya kuma ya temaki rayuwarka.
Juyawa tayi ta fita tana kuka, saboda tsakaninta da Allah tana son Nazeeru, tana matukar tausayinshi. Baba Kamal yace ma Matarshi bara na kaishi wancan dakin, hado mashi tea ki dauko mashi dankali idan yaci seya sha magani.
Sallamar Anas sukaji dan yaje gidansu Farida tace mashi yana nan, ya jira a makaranta bega Nazeeru yadawo ba hakan yasa ya biyoshi. Baba Kamal ne ya amsa yana fadin Anas kaga abokinka shiru ko? Shigo ka ganshi nan bejin dadi.
Bayan Anas ya gaishesu ya tsugunna yana fadin Nazeeru meya sameka? Baba Kamal yace bawani ciwo bane me zafi, tashi kuje can dakin kuci abinci. Nazeeru cire kayan na samo maka wasu seka sanya a shanya wadan nan.
Anas yace ai ga kayan makarantarshi nan ma na taho mashi dasu. Baba Kamal yace yauwa bashi yasa dama ina tunanin kayan da zasuyi mashi acikin nawa. Bayan yacire kayan yasaka na makaranta.
Matar Baba Kamal ce ta kawo masu abinci ta dauki kayanshi ta wanke mashi ta shanya mashi. Rawar sanyi kawai Nazeeru yakeyi da kyar yaci abinci, Anas se lallashinshi yakeyi.
Anas yace wai Nazeeru waya jika ka? Cikin kuka Nazeeru ya fadama Anas abinda Fiddausi tayi mashi, Anas yace ai dama wannan matar bata da tausayi, kuma se Allah ya saka maka, itama seta samu wanda zeyi mata abinda tayi maka.
Cikin kuka Nazeeru yace ai dama kullum nayi sallah senace Allah ya saka mani duk abinda takeyi mani, kuma Malaminmu yace duk wanda kayimashi aiki be biyaka ba ranar lahira acikin ladarshi Allah ze biyaka.
Kuma wallahi bazan kara aikin wanke wanke ba. Anas yace kawai kazo ka koma wajen aikina, idan kuma baka sonshi akwai wani me gyaran motoci akusa da wajen aikinmu naga kafin Sani yatafi ganin gida awajenshi yake aiki.
Kuma kullum yake biyan mutum, idan kanaso anjima zanyi mashi magana, amma fa akwai wahala aikin shiyasa nace banaso nafison aikin ruwa. Nazeeru yace nide inaso, bazan kara shiga gidan mutane ba.
Kaga idan ya biyani se murika cin abincinmu kawai. Anas yace shikenan zanje nayi mashi magana. Bayan sun gama cin abincin Baba Kamal yabashi magani, yana gama sha ya kwanta suka rufeshi da zani, nan take bacci ya daukeshi.
Baba Kamal yace Anas zaka zauna yatashi ko tunda yau alhamis babu karatu? Anas yace akwai inda zanje, amma zan dawo kafin yatashi. Baba Kamal yace shikenan anshi wannan karike ko.
Godiya yayi mashi yatafi. Baba Kamal yace ma matarshi idan yatashi ki kara bashi abinci zanje shago kome kenan zan kiraki. Tace to seka dawo Allah ya bada sa'a, yace amin.
****** *******
Zaune su Goga suke akasan bishiyar kofar gidan su Hajara suna shan rake, Ado ne da sauran abokanshi sukazo wajensu Goga. Ilu yace kaga yaron Goga, daga ina kuke? Ado yace wallahi daga cikin tasha muke shine muka yo nan.
Goga yace zonan dan Ubanka, nasan tunda kace mun daga tasha kuke wani abun kuka saido ko? Dariya Ado yayi yana shafa kai yace wallahi Goga Shattima ne yanzu yake mana samu sosai.
Ka ganshi de karami dashi amma akwai fasaha, shigowarshi cikinmu yana kawo mana kaya sosai, inde yashiga gida Bara baya fitowa haka nan. Kallon Shattima Goga yayi yana fadin zonan yaro.
Kanshi ya shafa yana fadin lallai yaro kashigo da kafar dama, kaida yawon bara ana wulakantaka har abada, domin zakayi mana rana sosai, kuma daga yau ka zama Autan Goga.
Duk wanda ya tabaka kazo ka fada mani, kai daga yau ma tare zamu rika yawo, wannan karatun idan ka biye mashi bazaka samu komai ba, kuma zaka kare a Bara. Kana so narika tafiya da kai ko? Kai Shattima ya daga.
Ilu yace lallai Yaro kashigo Almajiranci a sa'a. Ado yace ai da tare suke da su Anas da wannan sabon zuwan, sun maidashi kamar wani kaninsu ganin zasu kwareshi yasa yadawo ckinmu.
Rannan ma wata sabuwar waya ya dauko mana a wancan gidan, dama inajin haushin matar wata rana naje Bara bakaga yanda tayita zagina ba ta koreni, naso ace kana nan wallahi dana fada maka.
Amma nima na rama akan diyarta, shine da Shattima yashiga gidan yadauko wayarta nace muje mu saida wallahi matar masifa gareta, wai ta tsani Almajirai.
Garbati yace lallai kuwa zamu koya mata hankali, tunda Allah yasa muka taso cikin Almajiranci ai duk wanda ya zagemu se mun koya mashi hankali. Shattima tashi kaje kayi Bara agidan.
Ilu je kajiyo mana me zatace. Tashi Ilu yayi yana fadin idan ta zageshi Allah sena barar da ita. Goga yace haba, me kakeci haka? Kawai kajiyo mana kalar zagin da zatayi mashi zamu sama mata lokacinta.
Mijinta ai dan kasuwa ne. Tashi sukayi shida Shattima, yana zuwa yashiga zauren gidan ya fara kware baki da karfi yana bara. Hajara tana zaune ita da kawarta suna fira muryar Shattima ta cika masu kunne.
A fusace Hajara tafito tana zuwa Shattima ya fito aguje dan ya tsorata daya ganta, kara labewa Ilu yayi agefen gidan, tana fitowa tafara dura mashi zagi tana fadin abun naku ma iskanci ne, kawai mutane suna hutawa zakazo karika damunsu.
Kuma nafito shine zaka ruga da gudu saboda ka maidani mahaukaciya, shegu asararru masu matattar zuciya, wallahi idan ka kara zuwa Bara gidan nan sena zaneka. Biyota kawarta tayi tana fadin haba Hajara.
Kina matar aure kifito kofar gida kina daga murya kina zagin Almajiri, yanzu wancan yaron meye abun zagi ajikinshi? Kada kimanta suma fa ba laifinsu bane, laifin Iyayensu ne da suka kawo su Almajiranci.
Shifa kawai Bara yazo, idan bazaki bashi komai ba kiyi shiru ki kyaleshi mana ai ze gaji yabari, amma ke baki bashi ba, kuma kinzo kina zaginshi, gashi kina karama kanki zunubi amatsayinki na matar aure kin fito waje kina daga muryarki.
Janta ciki tayi tana mata nasiha. Hajara tace ke dande unguwarku ta 'yan gayuce kuna cikin gida me gate shiyasa kike fadin haka, yanzu ko baccin safe mutum yakeyi inde gidanshi abude yake haka suke shigowa surika damun mutum.
Kuma idan na kulle gidan idan Fadila ta dawo makaranta setayi ta bugawa ko kuma idan nayi baki wani lokacin banajin zuwansu, shikenan kuma saboda nabar gidan abude se Almajirai surika damuna.
Idan sukaga inayi masu haka zasu dena zuwa, kwanaki da nayima wasu haka har yanzu basu kara zuwa ba. Murmushi kawar tayi tace shikenan tunda kince haka, amma shi Almajiri ba'ayi mashi haka, domin ba dukansu sukeda halin kirki ba.
Wasu zasu iya yimaka wani mugun abun. Hajara tace wallahi dana kai yaro wajen 'yan sanda. Kinga mubar wannan maganar bara na dauko maki kayan da nake fada maki.
Dariya Goga yayi yana fadin kabarta kawai Ilu, mu da muke anan ma munajiyo sautin abinda take fada, zata gane kurenta, karamin yaroma ban barshi ba inaga babba, zamu sa mata lokaci. Wayarshi ce tayi kara.
Yana daukowa yace shegen kaya, ina shigowa garin nan nasamu labarin korarka daga aiki ai, bayan ya dauki wayar yace shegen kaya, Sajan Gali ashe kuna nan, na dauka se manyan mutane kuke nema? Dariya Gali yayi yace Goga ashe kadawo garin.
Dama cewa nayi bara na gwada wayarka ko zata shiga. Goga yace tun shigowata garin nan nasamu labarin korarka ai, ina cewa anjima nazo nayi maka jaje. Gali yace kaide bari, ana gano takardun bogi gareni akayi waje dani.
Allah ma yasoni mutum daya ne ya kamani wallahi da senayi yari, cikin rufin asiri ya sallameni babu wanda nayima sallama na tafi, mutane sun dauka tsautsayi ne ya hauni. Amma yanzu kana ina? Goga yace ina makaranta mana, ai bamu fara fita aiki ba.
Gali yace shikenan anjima da dare zanzo akwai labari, wallahi nasamu abun arziki. Goga yace shegen kaya, shikenan sekazo. Yana kashe wayar Garbati yace Gali manya, ko wace Uwar ya kara samowa kuma? Goga yace kasanshi da shige shige, idan yazo zamuji komai.
Kutashi mutafi cikin gari, Ado kuje kawai zamu tafi da Auta, Ado yace shikenan, ai yau babu karatu, Ilu yace ko akwai ma baze je ba, gara ya ginu da sana'a me kwari, kude da kukeson karatun kuje kuyi tayi.
Ado yace wallahi nima bana son wani karatu kawai mutafi. Goga yace kai taho, ku kuma kutafi yawon ku. Kama hannun Shattima yayi yana fadin Auta mutafi, ke kuma kijira zuwanmu.
****** ******
Se wajen 12 Nazeeru yatashi, cikin ikon Allah zazzabi be kamashi ba, Zarah matar Baba Kamal ta zuba mashi ruwan zafi ta bashi sabulu tace yashiga bandakin tsakar gida yayi wanka, bayan yagama tabashi,mai ya shafa yasa kayanshi da suka bushe.
Waya tayima Baba Kamal yace gashinan zuwa, dama ta gama abincin rana zuba mashi tayi tace yaci seya kara shan magani. Farida ce tashigo dauke da robar Nazeeru cike da abinci, duk da ba itace da girki ba da Fiddausi ta gama ta bata robar tace ta zuba mashi ta kai mashi.
Babu bata lokaci Fiddausi ta cika mashi robar, dan tun dazu hankalinta yaki kwanciya dan batasan wane hali yake ciki ba, gashi Ashiru daya shiga gidan kayanshi kawai ya dauka ya fice bece mata komai ba, kuma tanajin kunyar tambayar Farida.
Zarah tace Farida sannu da zuwa, tace yauwa ashe ma yatashi? Tace wallahi yanzu yatashi abinci ma zeci. Farida tace sannu Nazeeru, yace yauwa. Bayan yagama cin abincin Zarah ta bashi maganin yakara sha.
Baba Kamal ne yayi sallama yashigo yana fadin Nazeeru katashi ko? Meyake damunka yanzu? Nazeeru yace banajin komai zantafi wajen Anas. Murmushi Baba Kamal yayi yace Nazeeru na Anas.
Anan cinyeka zamuyi kenan? Dukar da kai yayi kwalla tacika mashi ido yace nide kawai makaranta nakeson zuwa, Zarah tace amma ai zaka dawo nan karika mani aiki ko? Nazeeru yace bazan kara aiki ba nide.
Baba Kamal yace shikenan ya isa, dena kuka zakaje wajen Anas,amma zaka rika zuwa shagona ko? Nazeeru yace E, Baba Kamal yace shikenan dauko mashi kayanshi mutafi idan na kaishi sena dawo.
Zarah tace to Nazeeru amma karika zagayomu kaji? Nazeeru yace ai kuna da kirki ke da Maman Zainab kuma idan nayi sallah zan rika maku addu'a amma banda Umman Samira ita muguwa ce. Baba Kamal yace tashi mutafi bazata kara ganinka ba bare ta kara dukan ka.
Suna fita suka hadu da Anas, murmushi Baba Kamal yayi yace dama makarantar zamuje, ga abokinka yaji sauki. Anas yace sannu Nazeeru, yace yauwa. Baba Kamal yace ga dubu biyunka da Ashiru ya baka seka saka a asusu.
Nazeeru yace ka aje mani idan bamu da kudi zamuzo murika amsa idan natafi dasu za'a sace mana. Baba Kamal yace toshikenan, kome kukeso kurika zuwa shagona kunji? Sukace to.
Anas yace ai nayima wannan mutumin magana yace anjima da la'asar muje tare. Baba Kamal yace wanene? Anas yace me gyaran mota ne, Nazeeru yace can zerika zuwa. Baba Kamal yace amma seka taso daga makaranta ko? Anas yace ai dama na fada mashi yana zuwa makaranta yace bakomai.
Baba Kamal yace zaka iya aikin ko Nazeeru? Yace zan iya ni bazan kara shiga gidan mutane ba. Murmushi Baba Kamal yayi yace Nazeeru kana da zuciya me kyau, Iyayenka sun gina ka bisa turba me kyau.
Allah beyi zasuga girmanka ba, bazasuci gajiyar baiwarka ba. Allah ya kareka daga sharrin makiya, ya kuma taimake ka amin. Kaima Anas yanda kake son Nazeeru Allah ya kara hada kanku. Sukace amin.
Dari 2 yabasu yace ze koma gida, godiya sukayi mashi suka tafi, Anas ya amshi robar Nazeeru ya tayashi dauka. Baba Kamal ya dade atsaye yana kallonsu kafin yatafi.
Tun daga wannan ranar Nazeeru yafara aiki awajen me gyaran mota, yana tasowa makaranta wajen karfe 12:35 yake cire kaya yatafi wajen aiki, da yake kusa yake da wajen aikin su Anas, karfe daya suke fita su sayi abinci suci sannan su koma aiki.
Biyu saura suke tafiya makarantar allo, ana fitowa kuma sukayi sallah suke komawa. Yanayin aikinka yanayin biyan da za'ayi maka. Kasancewar Nazeeru yana da natsuwa yasa cikin lokaci kankani ya fahimci yanda ake aikin.
Duk abinda yaga Ogansu yanayi baya yin shiru, zuwa yake yarika kallo yana kuma tambayarshi yanda akeyi, cikin lokaci kan kani Nazeeru yashiga zuciyar Ogansu, musamman da yaga bashida ha'inci kuma yana da maida hankali.
Gashi duk cikin kana nan yaran shikadai ne yake zuwa makarantar boko, da lokacin sallah yayi Nazeeru yake tafiya matsallaci koda kuwa ba lokacin sallarsu bace, danshi yanda ya sani da ankira sallah agidansu suke tafiya masallaci da Babanshi, shiyasa ko karfe 1 yana sallar azahar.
Wadannan halaye na Nazeeru yasa Ogansu me suna Habibu wanda yakasance musulmi amma ba bahaushe bane, sede ya dade a Daura idan yana maka hausa bazakace ba garin aka haifeshi ba, yana da gaskiya da rikon amana hakan yasa mutane da yawa suke kawo mashi gyaran mota.
Yayi kudi sosai da gyaran mota, kuma yana da manyan yara duk da haka idan aka kawo gyara babba shine yakeyi da kanshi, koda yaranshi ne sukayi seyazo yaduba sannan. Ganin gaskiyar Nazeeru yasa yaji yana sonshi.
Ko aiki aka bama Nazeeru a makaranta idan beje wajen Baba Kamal ba Oga Habibu yake tambaya, wannan dalilin ne yasa suka kara shakuwa, gashi dama yanzu Nazeeru yadena zuwa Bara, cikin kudin da ake bashi suke cin abinci shida Anas,
sauran kuma su saka asusu.
Dama tuni sun dauke asusun sun kaima Baba Kamal gudun kada asace masu. Haka Nazeeru suka fara yin test amakaranta, kuma sosai yake kokari.
Shattima kuwa ya zama dan gatan Goga, domin Shattima Allah yabashi sa'a, inde yashiga gida da wuya yafito hakanan batare da yasamo wani abu ba, ko da shagon mutum yaje kafin ka ankara yadauke maka wani abun, gashide karami amma yasan takan sata.
Hakan yasa Goga da Yaranshi suke kara sonshi. Lokacin da sukaje ma Gali ziyara a gidan da yake gadi Shattima yaja da baya, Goga yace Auta meya faru? Shattima yace wannan gidan dukan mutane sukeyi, mun taba zuwa bara nida Nazeeru megidan yace zesa adauremu.
Dariya Goga yayi yace wato haryanzu Alhaji be dena halinshi ba kenan, zomuje babu abinda zasuyi maka. Suna zuwa Gali yana zaune asaman kujerarshi a kofar dakinshi da aka fasa daga waje, gefenshi kuma babbar kula ce ta abinci.
Dariya yayi yana fadin kaga manyan yaran Malan. Goga yace shegen kaya, wato kana nan anyi maka rumfa kanacin me dadi ka barmu a rana. Gali yace kaide bari, kalli wuyana harya fara cikowa.
Gaskiya masu gadi sunajin dadinsu, na tausayama Malan Abu da aka koreshi daga gidan nan. Gaskiya Alhaji yan wulakanci son rai. Goga yace yanzu Auta yake fada mani rashin mutuncin da yayi masu.
Ashe haryanzu mutumin nan yana nan da halinshi? Na dade ina jin labarinshi ashe be canza ba? Gali yace sema abinda yayi gaba, waya fada maka masu kudi kuma masu hali irin na Alhaji suna canza hali? Ai suna tsufa halinsu yana kara karuwa.
Ai Alhaji beda mutunci, irinmu sune sukejin dadin zama dashi. Garbati yace ai nayi mamaki dakace wai dubu talatin yace zerika baka. Gali yace nine fa, kasanni da shegen dadin baki, sede akwai matarshi da wata shegiyar diyarshi marar kunya.
Sam basa ganin talaka da gashi, idan diyar zata fita batasan tayi horn so daya ba, idan banje na bude da wuri ba nashiga ukku da masifa, kuma sam uwarta bata tsawatar mata. Kanwarta Nafisa ita kadaice me hankali.
Kullum idan zataje makaranta seta gaisheni, idan ta dawo ma se tace mani sannu da aiki Malan, na rasa waya fada mata sunana Malan, kodan ta saba da Malan Abu ne? Ilu yace ai masu tarbiya basu iya kiran sunan babba.
Goga yace aiko zan......... karar horn sukaji, da sauri Gali yatashi yana fadin yanzu haka itace zata fita. Rikeshi Goga yayi yana fadin dan tsaya naga kalar rashin mutuncinta. Gali yace saboda ba kai zatayimawa ba ko.
Dan Allah sakarni. Goga yace Allah bazan sakeka ba seta fito. Kausar seda tayi horn so 3, cike da bacin rai tafito ta karamar kofa, tana fitowa Goga yasaki Gali, tana zuwa tace haba Gali, wannan wane irin rashin mutunci ne ka zo ka tara kattin banza kuna mana hauka a kofar gida.
So kake nazo na bude gate din da kaina? Meye amfaninka agidan nan, kasan kuwa saboda shirmen Malan Abu yasa aka koreshi, kai kuma ka samu an taimaka maka an daukeka shine zaka fara yima mutane shirme.
Wallahi idan bakayi hankali ba zansa Abba ya canza ka. Tsaki taja ta juya tana fadin dalla wuce kaje ka bude mani gate, dama haka kuke talakawan nan, da kun samu waje shikenan kunfi kowa iskanci.
Duka Gali ya kaima Goga yana fadin kaga kaja mani fadan da ba'a taba yimani ba, wucewa yayi yaje ya bude mata gate. Murmushi Goga yayi yana shafar fuska yabita da kallo har tayi nisa.
Girgiza kai yayi yana fadin kattin banza ko? Hmmm, Gali zamu wuce seka jini. Gali yace shegen kaya, tunda naga kana wannan murmushin akwai wani abu aranka. Goga yace bakomai, Ilu muje kawai.
Gali yace kuzo kuci abinci mana, Goga yace barshi sauri mukeyi banaso wani yagammu tare da kai ne, hannun Shattima yakama suka tafi yana fadin zan kiraka. Gali yace lallai Kausar kindebo ruwan dafa kanki, kin tabo Goga sede ince Allah ya kyauta.
****** *****
Tsaye su Barira suke suna jiran Balki ta fito daga gidan da taje yima Hajiyar gidan sallama saboda Barira tace ya kamata su canza unguwa saboda duk mutanan wajen sun ganosu yanzu ba sosai suke samun bara ba.
Ko Auta yaje Bara baya samowa sosai. Larai tace Balki yau ta dade kila wani aikin Hajiya ta sata, Barira tace ai nasan kila zata yimata babbar kyauta. Larai tace aikinsan Balkita akwai farin jini.
Mukam Bara ta biyamu, a unguwarnan mun tara abun arziki sosai, kinga tunda angama ganemu gara mu canza waje, semuyi fatan samun sa'a. Bakisan wani abu ba, jiya da dare seda muka hau sama da Baban Balki.
Ko zuwa yayi wani ya zugoshi akan fitar da mukeyi nida Balki Bara, jiya bayan mun dawo ya hauni da fada wai ya fara gajiya da wannan yawon Barar da mukeyi, idan zan zauna na fara sana'a acikin gida in zauna dan yagaji da fitar da mukeyi.
Kinsanni bana barin seta kwana, nan na bude mashi wuta, na rasa ina yasamu bakin yimani wannan maganar, Dan Ladi da kome zanyi baya iya hanani amma wai shine jiya yake fada mani nadena zuwa yawon Bara.
Yamanta ranar da Bara takeyi mashi, koba komai idan na dafa abincin da na shanya ya bushe ai ina bashi, kuma duk cikin kayan da muke samowa a wajen Barar ne. Dayaga de nafi karfinshi shine yace wai idan zantafi nadena daukar mashi diya.
Nace be isa ba, daga karshe yace wai wajen Uwarshi ze maida ta, nace haka kawai nida shan wahalar haihuwa akaima wata tsohuwa can ta karu da baiwar diyata da farin jininta.
Sosai fa muka hau sama, nace wallahi babu wanda ya isa ya rabani da Balki, daga karshe wani abokinshi yazo ya rabamu, shine yace kome ya faru da mu babu ruwanshi, kuma daga yanzu ba ruwanshi da Balki nizan rika mata komai.
Ni kuma nace tunda haka yace sede ya bani takarda ta zanfi jin dadin fita nasan bani da nauyin komai akaina, nan fa abokinshi yafara bani hakuri shima na zageshi tass, saboda duk wani munafunci shine yake koya mashi.
Daga karshe yace inje ya sakeni saki daya, nace aikin banza ai daya karasa dayan, saboda saura shikadai yarage mana, zeyi magana abokinshi yajashi suka fita, kuma nace idan na koma yau zan bar mashi gidanshi kuma bazan bashi Balki ba.
Shi kuma yace idan natafi da ita sede in nema mata wani Uban, nace nayarda. Tagumi Barira tayi tana kallonta, ajiyar zuciya tayi tace amma gaskiya Larai kinyi ganganci, taya zaki raba Balki da Ubanta? Yanzu idan lokacin aurenta yazo me zakice ma manemanta? Gaskiya kinyi kuskure.
Saboda yawon Bara ki kashe aurenki kuma ki raba diyarki da Ubanta? Duk fa girman Uwa bata kai Uba ba, domin dashi kowa yake takama, baki taba jin anyima marar Uwa gori ba sede ayima marar Uba gori.
Larai tace haba Barira, nafa san halin kayana, nan da wani lokaci ze sauko, wancan karon daya sakeni ya mukayi dashi, bayan kwana biyu yafara zuwa wajena, kibarshi yanzu ma dakanshi ze dawo, saukin abun ma ina da gidan zama.
Barira tace yanzu kinfi so atafi ahaka? Kada kimanta itama fa Balki diyace kamar kowa, saboda Bara zaki maidata marar Uba? Larai tace ina me tabbatar maki Balki setayi sanadiyar arzikinmu nida Ubanta.
Kina ganin duk gidan da zataje Bara seta samo abun arziki, wallahi wata rana se yayi kuka da idonshi idan yaga Balki ta bashi dukiya acikin kudin data tara na Bara, ke daga yau ma asusu zan bude mata.
Zata tara abun arziki wanda zan aurar da ita tamkar diyar wani babba. Shima kuma ze sauko ai. Barira tace to Allah ya kyauta, nide kinga da Babansu Auta ya hanani zuwa da Yayarshi banyi mashi gardama ba.
Yanzu gashi duk bayan kwana biyu tana zuwa tana gaisheni, kinga da yake Auta namiji ne ai be hanani fitowa dashi ba, kila shima saboda yana ganin Balki ta fara girma shiyasa ya hana, ada da tana karama ai be hana ba ko.
Larai tace kede kawai dan mijinki yafi karfinki ne, kema kuma ai kina cin albarkacin Balki. Barira tace haka ne kam, to Allah ya rufa mana asiri. Larai tace Barira duba can ki gani, wancan gidan ashe mutanan ciki sun tare.
Barira tace kode bakone, ai naga an dade da gama gidan kuma bana ganin alamun mutane aciki. Larai tace ga megidan can kina ganin yana bude gate zeshiga. Kai Auta zo yi sauri kafin ya rufe kofar kaje ko kudi ka samo mana ai mun kara na mashin.
Barira tace anya akwai mata agida can kuwa, kina ga kome gadi babu shine yake budewa da kanshi, Larai tace kede kibarshi yaje idan yayi mashi kuka kinsan maza da tausayi yana iya bashi kudima.
Barira tace to, Auta yisauri kaje, idan kaje kace Mamarka bata da lafiya gata nan akwance kuma yunwa kakeji kaji? Auta yace to, roba ya dauka ya nufi wani gida me kyau. Larai tace ai semu zauna mujirasu kinga jiran Balki ze jawo mana wani samun.
Auta yana zuwa yaga karamar kofar dazata isheshi ya wuce, shiga ciki yayi yafara fadin Almajira yana Bara, mutumin daya fito daga mota yayi saurin juyowa jin karamar murya tana magana ita ba mace ba kuma ba
namiji ba.
Seda yadan tsorata ganin yaron da yake tsaye abakin gate, dakewa yayi yace kai yaro kaidawa kazo nan? Auta yace Mama bata da lafiya kuma yunwa nakeji. Murmushi mutumin yayi yana shafa fuska yace kacemun kune yaran Mabaratan nan da suke turowa.
Hula yacire yana shafar sanko, shiru yayi yana dan tunani, kara washe baki yayi yace zo ka anshi sadaka, juyawa yayi ya dauko wani abu a motarshi, Auta yana zuwa mutumin ya dora mashi wani jan kyalle a kanshi.
Saurin runtse ido Auta yayi jin kamar an dora mashi wani abu akai, seda abun ya dade akanshi sannan yacire, wata alawa ya dauko ya bare yana fadin zakasha alawa? Daga kai Auta yayi.
Abaki yasa mashi yana fadin tauna ka hadiye in baka kudi ka kaima Mamarka bakowa gidan babu abinci. Bayan ya shanye yace yauwa dan karamin yaro, dubu daya yaciro sabuwa yace amsa ka kaima Mamanka taje asibiti.
Maza kaje kada tajiraka, amsa Auta yayi ya tafi yana me kara juyowa yana kallon mutumin. Wata irin dariya mutumin yasa yana fadin gaskiya yau nazo garinnan a sa'a. Wayarshi ya dauko, bugu daya aka dauka, yace Oga aiki ya kammalu ganinan zuwa.
A firgice Idi yatashi jin Balki bata motsi, saman shimfidarshi ya duba sosai hankalinshi yatashi ganin irin jinin daya bata ta, saurin kama Balki yayi yana girgizawa amma ko motsi batayi.
Sam ya manta cewa Balki karamar yarinyace, bata wuce shekara 11 ba amma yayi mata haka. Zufa ce kawai take zubo mashi. Saurin saka kayanshi yayi yana zagaye adakin, yarasa abinyi.
Muryar Hajiya yaji tana kwala mashi kira, saurin zubewa kasa yayi ya dora hannu saman kai zufa tana kara zubo mashi. Har kofar dakin Hajiya tazo tana kiranshi amma be amsa ba.
Ganin dakin a rufe tace kila ko yafita yadawo. Juyawa tayi ta koma ciki. Lekawa Idi yayi seda yaga tashige ya sauke ajiyar zuciya. Kayanshi yashiga hadawa babu bata lokaci, gaba daya jikinshi rawa yakeyi.
Seda yadauki duk wani abunshi me amfani sannan yasa zanin gado ya rufe Balki, bude kofar dakin yayi yadan leka, ganin ba kowa yasashi saurin fitowa. A hankali ya bude gate din da gudu yabar kofar gidan.
Larai da Barira da suke zaune suna farin cikin samun dubu daya da Auta yayi hankalinsu ne yakai gidan da Balki tashiga. Barira tace anya wancan ba barawo bane kuwa? Larai tace nima haka zance.
Kallifa yanda yafito ga kaya a hannunshi kuma ya kwasa aguje. Barira tace kai Allah de ya kyauta, da nayi Sata ai gara na mutu ina Bara. Larai tace gaskiya Balki ta tsaidamu, tashi muje idan yaso semuce ma Hajiyar mu 'yan uwan mamanta ne.
Barira tace gaskiya kam, tunda take zuwa bata taba irin wannan dadewar ba. Auta tashi mutafi mana, naga se wani lumshe ido kakeyi ko bacci kakeji? Kai yadaga mata, Barira tace zo na goyaka banaso kayi mani bacci anan. Goyonshi tayi suka nufi gidan Hajiya.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
c332fda452e04edda39f2b7a32b5d3cd
Chapter 6 · 0% Book details