Part 25
Almajirai Ma Yaya Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 18 min read
Har tuntube Larai takeyi wajen sauri ganin Alhaji ya mike yana shirin shiga gida, hada gudu suka hada wajen isa wajenshi, kafin su isa Larai ta lankwashe kafa ta makale hannunta tare da rufe idonta ta kama hannun Barira tana dangyashi.
Dama haka suke duk lokacin da zasuje bara da kansu wajen masu kudi. Suna zuwa Barira tafara abamu saboda Allah da Annabi, sadaka bayin Allah, abada kalilan asamu kasiran. Saurin juyowa Alhaji Bashir yayi ya kashe wayar da yakeyi.
Malan Abu megadi da yazo fitowa yayi saurin komawa ya labe jikin kofa ganin abinda yake faruwa. Hamdala yayi da Allah yasa baya waje Mabaratan suka zo, kuma agaban Alhaji ma suka zo. Barira ta bude baki zata kara magana kenan Alhaji ya daka masu wata tsawa.
Ba shiri Larai tayi saurin bude ido, da sauri ta kara rufe idon gudun kada ya ganosu. Cikin masifa Alhaji yace dalla Malama ki rufe mana baki, taya zakuzo kurika damun mutane, Kallarki, ko kunya bakiji ba ace kamar kina bara.
Ya kamata ace kina can kina aikin karfi amma saboda mutuwar zuciya zaki dauko wata musaka kina neman kudi da ita, idan ita bazata iya aikin karfi ba meze hana kibarta gida ke kije kiyi aikin kirika sama maku abinda zakuci mana.
Kawai bakusan yanda mutum yasha wahala ya tara kudinshi ba haka kawai da rana tsaka kurika bin gidajen mutane kuna damunsu, wallahi dukiyata ba saboda Mabarata na tara taba, yanda nasha wahala na tara dagani se iyalai na zamuci.
Idan kinga wani yaci kudina to aikin karfi yayi mani sena biyashi lada, amma haka kawai bazan rika bama kattan banza kudina ba. Kuma wallahi daga yau idan kuka kara zuwa kofar gidan nan sena sa an daureku.
Ku bace mani daga kofar gida, masu matattar zuciya kawai, ai duniya babu talaka se rago, duk wanda kaga yana bara to be nema bane, haka zakuzo a asara ku kare a wahala batare da kun mori rayuwarku ba.
To yanzu ko wanda yake a nade idan yana da zuciyar nema wallahi bazeje yana Bara ba, idan baze iya aikin masu kafa ba ai akwai aikin zaune. Dan haka kutafi kubani waje. Cikin gida yashige yana masifa, da sauri Malan Abu yashige dakinshi.
Bude ido Larai tayi jiki a sanyaye suka juya suka bar kofar gidan, Barira tace ikon Allah, yau mun hadu da gamonmu, ashe dama wannan mutumin beda kirki? Haba, shiyasa kafin kaga Almajirai a kofar gidanshi da aiki.
Muma tsautsayi ne ya kawo mu. Larai tace aini bani ma da bakin magana, idan zuciyarshi tana aiki ina ruwanshi da mutuwar tamu, kaji mani mutumi da karfin hali. Kowane aiki mutum zeyi ai yaji ze iya ne.
Barar ma ai iya wace, wani yayi mana yaga idan ze dace, haka kawai dan munje nema wajenka zaka rufemu da fada kamar wasu 'Ya'yanka. Kinsan Allah dande gidanshi mukaje, kuma inajin tsoro kada yasa akullemu amma kinsan bana barin seta kwana.
Dariya Barira tasa tace kinji ki da karfin hali, kome yayi mana ai mune muka kai kanmu, da bamuje ba zezo har inda muke yayi mana ne? Ai abinda yafada gaskiya ne, wallahi ni naji Bara ma tafitar mani arai.
Haka kawai saboda abun duniya arika wulakanta mu, lokacin da nake zuwa masissika ina aikin karfi mutane har kwantar da kai suke akan nazo nayi masu sissika, kuma idan nagama haka zasu biyani da gero.
Meyasa babu wanda yake wulakantani alokacin? Saboda banje nayi 'yar murya ba, amma yau danaje nema wajen wani gashinan nasamu rabon zagi, a duniyar nan yanzu waye ze zageni tunda banida iyaye? Amma gashi katon Allah ya zagemu tass.
Tabe baki Larai tayi tace ke dama Barira haka kike, kincika tsoro, dama ai tun jiya da naga Lantana tazo kun dade kuna magana nasan akwai abinda ta kintsa maki. Shikenan, idan kikace kinbar Barar nide bazan bari ba.
Ki fada mani idan kikayi sissika ana daukar kudi ana baki? Geron da za'a baki ko saidawa kikayi bazaki samu dari biyu ba, idan kika fara ciwon jiki kudin da kikayi aikin baza su isheki siyen magani ba.
Amma idan Bara kikayi fa? Bakida wani ciwon jiki kuma kici mekyau, kuma kisamu kudinki, aike sheda ce, wata rana har dubu biyu muna samu idan mukaci sa'a. Kinfiso kije arika baki kwaya kinasha kina kashe kanki.
Barira tace haka ne fa, maganarki gaskiyace, shikenan, dan wannan ya zagemu ai wsu zasu bamu, kuma daga yau baza mu kara zuwa gidanshi ba. Murmushi Larai tayi tace, ko kefa, ai dama haka Bara ta gada, wata rana ka samu wata rana kuma ka rasa. Muje gasu Auta can da alama sun samo abinci.
**** *****
Kwance Nazeeru yake yayi kuka harya gaji, bacci ya daukeshi, karar bude kofa ne yasashi saurin tashi yana goge ido. Sayyadi yagani yana fadin Malan yace abudeka amma daga yau kada ka kara, tausayi kabani shiyasa naje na bama Malan hakuri, danshi yaso abarka se zuwa dare sannan abudeka.
Fitowa Nazeeru yayi yana goge kwallar data zubo mashi, jikinshi gaba daya ciwo yake mashi, haka ya nufi wajen da suke zama. Anas yau ko aiki beje ba, yana tare da Shattima, abincin da suka samo haka sukaci suka ragema Nazeeru da sauran kokon da suka siyo.
Suna ganinshi suka kamoshi, lallashinshi sukayi tayi yana kuka. Kokon yafara sha, sanna yaci abinci jikinshi se rawa yakeyi, yana gama ci ya amayar da abinda yaci, ruwa Anas yayi saurin debo mashi yabashi yasha.
Shattima se kuka yakeyi, kwanciya Nazeeru yayi yafara rawar sanyi, Anas yace katashi muje ka kwanta zanje nasiyo maka magani. Shattima ka tsaya awajenshi yanzu zan dawo.
Chemist Anas yaje yace abashi maganin zazzabi, tausayinshi me Chemist din yaji yace baka da lafiya ne? Anas yace abokina ne Malan ya kulleshi tunda safe beci komai ba se yanzu aka fiddoshi yanacin abinci yayi amai kuma jikinshi yana ta rawa kamar yanajin sanyi.
Girgiza kai mutumin yayi yace jeka kamoshi kuzo tare, da gudu Anas yatafi yaje suka kamo Nazeeru suka kawoshi Chemist. Suna zuwa mutumin ya hada mashi tea, seda ya shanye sannan yakawo magunguna yabashi.
Kallonsu Anas yayi yace yaushe zaku shiga karatu? Anas yace se munyi sallar isha'i. Mutumin yace to kubarshi anan ya kwanta zuwa anjima idan akayi magriba se kuzo kutafi nasan zuwa lokacin zeji sauki Insha Allah.
Anas yace ammade bazaka tafi dashi gidanka ba ko? Murmushi yayi yace kana tsoron kada na sace shi ko? Shikenan idan babu inda xakuje kuzauna daka can waje idan ya farka seku tafi tare.
Anas yace zamujirashi a waje to. Dariya mutumin yasa ganin yaro me wayau, hannun Shattima yakama suka fita waje suka zauna suna wasa. Nazeeru kuwa saman tabarma ya kwanta nan take bacci ya daukeshi.
Fadila ce diyar Hajara ta dawo daga Islamiya tana ta wasa tana tafiya, wani ne yace yauwa Ado ga wannan yarinyar nan ta dawo daga makaranta. Saurin tashi Ado yayi, da gudu yasha gaban Fadila.
Kallonshi tayi cike da tsiwa tace dalla meye haka? Ado yace se naci Ubanki, shegiya, Fadila tace to menayi maka zaka zageni kuma bade Ubana ba. Iccen da yake hannunshi ya kwada mata akai yana fadin dazu Uwarki nima ta zageni.
Ihu Fadila tasa, da gudu Ado yabar wajen yana zuwa suka ruga suna mata dariya, ihu kawai Fadila takeyi. Hajara da take zaune a tsakar gida tafito da gudu jin ihun Fadila, dede lokacin Babanta shima yadawo amashin.
Tana fitowa ta hadu dashi yana kokarin sauka yana kiran Fadila, tana zuwa Hajara tace Uban wa ya bigeki kika kware baki kina kuka? Ba na hanaki yima yara kuka ba, duk wanda ya dokeki kema ki rama.
Idan ya fi karfinki ki cijeshi. Baban Fadila yace dan Allah ya isa haka, ke Fadila me ya faru? Fadila tace ba wasu Almajirai bane banyi masu komai ba daya daga cikinsu yazo yana zagina shine ya kwada mani icce akai ya ruga wai yace ai Mama ta zageshi dazu.
Girgiza kai Baban Fadila yayi yashige gida. Hajara tace suna ina? Fadila tace sun ruga, Hajara tace ki kyalesu ai can ne wajen zamansu wallahi zasu san sun dokeki, zo mu wuce. Zaune ta samu Baban Fadila a tsakar gida.
Zama tayi tana fadin kaga wadannan 'yan iskan Almajiran ko? Wallahi seka dauki mataki akansu ko kuma ka hanasu zama a kusa da gidan nan gaba daya idan ba haka ba wata rana zasu nakasa Fadila.
Murmushi yayi yace saboda su ba 'YA'YA bane ko? Ashe akwai zafi idan aka zagi mutum? Dama ai na fada maki, duk yanda kayima dan wani kaima za'ayi maka. Yanzu haka kawai kinja ma yarinya duka, bataji ba bata gani ba.
Asalima bata gidan lokacin da. abun yafaru amma gashi yanzu sun rama akanta, wannan abun kadai ya isheki kiyi hankali, nan gaba bakisan abinda zasuyi mata ba, idan ke zaki iya kare kanki bazaki iya kareta ba.
Domin kullum tana fita makaranta ko kuma kina aikenta. Ni abu daya ne ya tada mani hankali, yanda har suka iya ramawa akan diyarki, kinga nan gaba bamu san meze faru ba saboda bazamu rike Fadila agida muce bazata fita ba.
Bawai banji haushi ba, tabbas naji haushi, bayan haushi ma zuciyata cike take da tsoro, kuma ba kowa bane ya jawo se ke, dole zan samesu na basu hakuri, amma kema sekin gyara halinki.
Duk yanda mutum yake ba'a rainashi, yanda kike takama Fadila diyarki ce suma suna da Iyaye, dan haka daga yau kada ki kara wulakanta wani Almajiri dan yazo bara gidan nan, idan baki bari dan Allah ba yanzu zaki bari saboda diyarki.
Tashi yayi yashige bandaki domin yin alwalar magriba. Hajara tace rabu dasu, sena rama maki, kuma zasu kara zuwa Bara gidanan wallahi bazan kara basu sadaka ba.
Seda akayi magriba sannan Nazeeru ya farka, sosai yaji dadin jikinshi, su Anas ne suka shigo suna murmushi ganin Nazeeru ya tashi. Me Chemist yace to Anas kaga dan uwanka yatashi ko? Dariya Anas yayi.
Wani magani ya bama Nazeeru yace gobe da safe idan kaci abinci kasha kaji? Nazeeru yace nagode. Mutumin yace kadena laifi kaga yanda Malan yayi maka. Nazeeru yace aide Allah ze saka mani.
Murmushi yayi yace haka ne, amma ka yafe mashi tunda kaine kayi mashi laifi. Nazeeru yace to ba karatu mukazo yiba meyasa zamu rika aikin wahala? Nide a Islamiyar garinmu Malaminmu baya samu komai.
Kullum karatu yake koya mana kuma idan muka gama gida muke tafiya. Girgiza kai mutumin yayi yace ai wannan makarantar ba irin taku bace, meyasa da Babanka ze kawoka nan bakace mashi baka so ba? Kwalla Nazeeru ya goge yace Babana da Mamana naga wasu mutane sun sakasu cikin rami sun rufe su.
Cike da tausayi mutumin yace Allah sarki, Allah yajikansu, kayi hakuri kaji, idan ka dage kayi karatu wata rana kaima zaka zama babba har ka temaki wasu. Nazeeru yace to ai anan bazan samu kudi ba, tunda karatu kawai ake koya mana.
Kuma idan naje nace zanyi aiki ba'a daukata, mu agarinmu idan Almajiri yayi aiki agidan mutane abinci ake bashi kuma wani lokaci hada kudima ana bashi.
Murmushi yayi yace yanzu kana so karika yin aiki? Kai Nazeeru yadaga, mutumin yace shikenan zan nema maka aiki matata tana da Almajiri da na kai mata kai, amma gobe kuzo idan na samu zan fada maka.
Murmushi Nazeeru yayi yace nagode. Anas yace to kai baka fada mana sunanka ba. Dariya yayi yace sunana Baba Kamal. Nazeeru yace mungode Baba Kamal. Dari biyu ya basu yace. Su sayi wani abu suci.
Godiya sukayi mashi suka tafi, sosai suka bama Baba Kamal tausayi, rufe Chemist dinshi yayi ya nufi gida yana addu'ar Allah yasa makwabcinshi beda Almajiri dan yanaso ya sama ma Nazeeru aiki.
Acikin maganganunshi ya gano yarone me son neman nakanshi shiyasa yaji har cikin ranshi yanaso ya temaka mashi musamman da yaji cewa Iyayenshi sun rasu, gashi yace ada yana zuwa Islamiya ya tabbata daya koma wajen 'Yan uwan Babanshi ne suka kawoshi Almajiranci.
Koda yaje gida beshiga gidanshi ba seda ya fara yima abokinshi sallama kuma yaci sa'a yana gida, awaya yakirashi se gashi ya fito, bayan sun gaisa yace kaga likita ikon Allah, dariya Baba Kamal yayi yace Ashiru ya kasuwa? Yace lafiya lau.
Baba Kamal yace ka ganninan daga Chemist nake ko gida banshiga ba inada magana da kai nace bara nafara tsayawa ko kana gida. Ashiru yace ko ta samu ne? Baba Kamal yace sosai ma.
Dama tambayarka zanyi ko Matanka suna da Almajiri meyi masu aiki? Ashiru yace haba ai kasan damina ta kusa zuwa Almajirai sun fara wahala, da yake akwai yara su Samira da Zainab shiyasa da Almajirinsu yatafi gida basu kara daukar kowa ba.
Baba Kamal yace dama wani yaro ne na yaba da hankalinshi, kuma yana da zuciyar neman nakanshi, gashide yaro ne karami amma yana da halin manya, yana bukatar aikatau shine nace zan nema mashi.
Ashiru yace amma gaskiya naji dadin wannan magana, dama kasan Mata da aikin ganin ido, kaga de su Samira sun girma zasu iya kowane aiki amma saboda ido irin na Mata wai ita Fiddausi bazata bar diyarta tarika aikin gida ba, har Zainab da take karama Farida tana sata aiki.
Banda abunta ai horarwa ne, Samira itace babba idan ta horu da aiki sauran yaran daga gareta zasu koya, nayi maganar harna gaji amma taki yarda kasan halin Fiddausi ai. Baba Kamal yace ina ruwan Uwar gida ran gida, se hakuri ai.
Ashiru yace yanzu de tunda ansamu me wanke wanke yazo duk wadda take da aiki zata zuba mashi abinci, ni kuma duk wata zan rika biyanshi dari biyu tunda ana bashi abinci, gara na raba gardamar kasan halin mata.
Idan nace surika biyanshi yanzu wata zatace Almajirin nata ne, amma idan nine na kawoshi sun san a karkashina yake. Baba Kamal yace amma naji dadi, wallahi ina matukar tausayin yaron dan Allah Ashiru ka saka ido akanshi.
Wallahi da ba nida Almajiri nine zan daukeshi saboda kaga ni Mata daya gareni, amma dole kai seka saka ido saboda kasan halin mata. Ashiru yace haba wannan ba wani abu bane, duk da bana zama gida ina kasuwa zan kafa masu doka, kuma zansa arika duba mani.
Baba Kamal yace shikenan nagode insha Allah zuwa gobe zan kawoshi, sede sunyi hakuri dashi da alama be taba yin aikatau a wani waje ba. Ashiru yace wannan ba matsala bace, akwai Samira zan sa tarika nuna mashi har ya iya.
Yanzu ma dana shiga zan fada masu zuwanshi gobe. Baba Kamal yace nagode agaishe da Farida amarya. Ashiru yace banda Fiddausi kenan? Dariya yayi yace rufa mani asiri kada ka hadani da Uwar gida dama haushina takeji gani take nine na saka kara aure. Dariya suka sa yayai mashi sallama ya tafi.
***** *****
Cikin ikon Allah washe gari Baba Kamal ya taho da Nazeeru dasu Anas gidan Ashiru saboda suma suga gidan da Nazeeru zeyi aiki. Bayan sun gaisa da Ashiru Baba Kamal yace to ga alkawari nan na cika, nizan koma wajen aiki.
Nazeeru ai kaga gidan babu nisa daga makarantar ku ko? Kai Nazeeru ya daga. Baba Kamal yace to inaso ka rike gaskiya kaga gidana nan, kuma kasan shagona, duk abinda kuke bukata kuzo, bana son rashin gaskiya.
Kuma kayi hakuri da duk abinda za'ayi maka akwai mata biyu agidan ba ruwanka da gulma, idan kaje ka gaishe da kowa, aikin daya kaika shi zakayi, kuma so daya zaka rika wanke wanke, kuma megidan zerika baka dari biyu duk wata.
Banaso akawo mani kararka kayi wani abu kaji? Kai Nazeeru ya daga, Baba Kamal yace ku ma Anas banaso ace mani kunyi wani abu na rashin ji kunji? Anas yace ni dama banda ni za'a rika zuwa inada wajen aiki, shida Shattima zasu rika zuwa.
Ashiru yace ai babu komai hakan ma yayi. Baba Kamal yace shikenan nizan wuce. A nan ya barsu yatafi, nan Ashiru yace su shiga ciki. Kasancewar tun jiya yayi ma Matanshi bayanin zuwan Nazeeru yasa suna shiga ya gabatar masu dashi.
Fiddausi tace yo Abban Samira na dauka wani babban yaro zangani naga wadannan yaran? Ashiru yace su Yara basu iya aiki ba? Tabe baki tayi tace amma de ai za'asha wahala kafin su saba.
Ashiru yace wannan de gidana ne, kuma nine na kawosu, idan kinji bazaki iya basu kwanoninki su wanke ba ai kina da Samira seta rika wanke maki, ke Farida ya kikace? Murmushi Farida tayi tace haba ai bakomai, kowama da koyo ya fara.
Tunda kace Samira zata rika nuna masu ai bakomai, itama Maman Samira fadi de takeyi. Fiddausi tace shikenan amma bama son kazanta kurika wanka kunji ko? Nazeeru yace to.
Ashiru yace nizan fita dama saboda sune na tsaya ban fita ba, idan akwai abinci ku basu suci, ke Samira ki nuna masu yanda zasuyi keda Zainab. Samira tace to.
Bayan sun gama cin abinci suka fara wanke wanke, Anas de yana daga gefe dan baya son wanke wanke. Haka Samira da kanwarta diyar Farida suka rika gwada masu yanda zasuyi, da yake Nazeeru yana son aikin lokaci guda ya gane yanda akeyi.
Shattima ma yana kallon yanda akeyi saboda yasan tare zasu rika zuwa. Bayan sun gama suka share wajen, Farida ta leko tace yauwa sannunku yaran albarka, har kun gama? Nazeeru yace E, tace yauwa nasan yanzu karatu zaku shiga ko? Sukace E, tace shikenan, kutafi seda rana kuzo ku karbi abinci.
Fiddausi tace ammafa abincin mutum daya za'arika baku, dan naga har ku 3 kukazo, kai wancan ma ko tayasu banga kayi ba, Anas yace ai nima inada wajen aiki. Fiddausi tace tonaji marar kunya.
Zaku iya tafiya, wahallu kawai, Iyayenku de su suka kwareku, gaku yara kanana amma sun kasheku da Almajiranci. Juyawa sukayi suka tafi. Farida tace haba Maman Samira meyasa zaki rika fadar haka agabansu bazasuji dadi ba.
Kuma kinga yara ne, tabe baki tayi tace aini banga abin tausayi a Almajiri ba, kuma wallahi ke Samira banaso naga kun sake masu, ko cikin kitchen banyarda surika shigar mana ba, saboda babu manyan barayi kamar Almajirai.
Idan kikayi sake wata rana tsaf zasu yasheki, haka sukayima wata kwata a Kankiya, shekararta kusan goma da Almajirinta, babu inda baya shiga a gidanta harya girma suna tare, amma lokaci guda basa nan yashiga ya kwashe masu komai.
Seda bincike yayi bincike sannan aka gano shine, harya koma garinsu da kyar aka kamashi, wasu kayan duk ya saida. Saboda haka ni bazan yarda da sakin fuska ga Almajiri ba. Iyakarsu tsakar gida, suna gamawa kuma su tafi, ko wannan zaman da sukeyi a zaure bazan yarda dashi ba.
Farida tace to Allah ya kyauta, ai ba duka aka taru aka zama daya ba, juyawa tayi tashiga daki jin karamin danta yatashi yana kuka. Kwalama diyarta kira tayi tana fadin Zainab zo ki karbo mashi madara yasha tea.
Fiddausi tace ke made har Abban Samira yafita baki fada mashi Madararshi ta kare ba, Farida tace wallahi mantawa nayi jiya da dare ban fada mashi ba, kuma kinga babu dadi yanzu yashirya zefita nayi mashi maganar.
Fiddausi tace kinada kudinne shiyasa. Samira dauko kayan miya ki gyara akai markade kafin kidawo zan dan kwanta idan kindawo ki fada mani sena fito na dora abincin ranar, wai yaushe ma ake komawa hutu ne? Samira tace saura sati biyu fa. Tace Allah ya kaimu maza kigama.
Fiddausi kenan da Farida matan Ashiru, Fiddausi shekararsu 15 da Ashiru amma tunda tayi haihuwar farko bata kara haihuwa ba, Samira tana da shekara 14 yanzu tana SS 1 a nan Day Daura makarantar gwamnati.
Ganin Fiddausi ba ta kara haihuwa ba yasa Ashiru ya auro Farida, segashi ta haifa mashi yara 2, Zainab da Saddik, inda Zainab take da shekara 9 tana Primary 3 yanzu, Saddik kuma an yayeshi.
Kasancewar Farida tana da wayau yasa take zaune lafiya da Fiddausi, duk yanda Fiddausi taso suyi rigima Farida ba ta kulata, hakan yasa itama ta hakura ta kyaleta, amma wani lokacin tana dan tabawa.
Baba Kamal kuwa matarshi daya Aisha da yaransu biyu mace da namiji, kasancewar bata dade a unguwar ba yasa basu saba da Fiddausi sosai ba, kuma halinsu bezo daya ba, bayan zuwan Farida se sukafi zama kawaye dan kusan sa'anni ne, hakan yasa Fiddausi ta dena shiga gidanta sede idan wani abun ya faru.
***** *****
Tun daga wannan rana samun abinci yayima su Nazeeru sauki wajen samu, kullum suke zuwa suyi wanke wanke shida Shattima Anas kuma a Makaranta yake tsayawa saboda shi aikinshi seda yamma yake zuwa.
Kasancewar karfe 9:00 suke shiga karatu yasa suke zuwa da wuri suyi wanke wanken sutafi makaranta, kullum tare sukeyi da Samira tana nuna masu yanda akeyi. Cikin lokaci kan kani suka iya komai, hakan yasa Fiddausi ta hana Samira zuwa tayasu.
Azaman da sukayi Nazeeru ya fahimci Farida tafi sonsu, babu abinda yake hadasu da Fiddausi se hantara da fada, gashi idan ranar girkinta ne basa samun abinci sosai dan Fiddausi akwai rowa, amma idan Farida ce seta cika masu roba.
Kuma ko nama sukaci seta saka masu, Fiddausi kuwa bata sa masu, idan sunci sa'a ta saka masu nama to kashine marar mamora. Haka de suke aikinsu, dan Nazeeru akwai hakuri, sarkin mita dama Shattima ne.
Damma Nazeeru yana hanashi yawan mitar da yakeyi, kuma ya fada mashi koda sunje gaishe da Baba Kamal idan yace akwai wata matsala ya hanashi yayi magana. Sam ba ruwanshi da shiga abinda be shafeshi ba.
Aikin da ya kaishi shi kadai yakeyi, kuma kome zaka aje baya taba daukar maka, amma Shattima akwai zalama, kome ya gani acikin kwano seya lashe shi, hakan yasa Nazeeru ya fara yimashi fada.
Wata rana Fiddausi ta aje kudi saman tagar kitchen Shattima ya daukesu, ya dauka babu wanda ya ganshi ashe Nazeeru ya ganshi, yana juyowa Nazeeru yace ka maida kudin daka dauka. Harze fara rantsuwa Nazeeru yasa hannunshi aljihu yaciro ya mayar mata.
Tun daga wannan rana Nazeeru yace baze kara zuwa da Shattima ba, ya rika tsayawa wajen Anas idan yadawo se suci abincin tare. Shattima yace Allah bazan kara ba. Nazeeru yace nide bazan kara zuwa da kai ba kawai kayi zamanka.
Anas yace gaskiya kada ka kara zuwa dashi, dama ai nafada maka Shattima yana sata kace bashi bane, mude gaskiya idan sata zaka rikayi zamu rabu da kai, kuma zan fadama Malan. Kuka Shattima yasa yana basu hakuri.
Nazeeru yace shikenan, amma idan ka karayi zamu rabu da kai. Tun daga wannan rana Nazeeru yarika zuwa wajen aiki shi daya, Anas da Shattima suna zama makaranta, kasancewar Shattima akwai shi da ci yasa baya jiran Nazeeru yadawo yake daukar kwano yana bin wasu Almajirai suna zuwa barar safe.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
ALMAJIRAI MA 'YA'YA NE
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
[email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey