← Book details Almajirai Ma Yaya Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
CHAPTER 5 OF 6

Part 35

Almajirai Ma Yaya Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 18 min read

Abu kamar wasa Nazeeru ya gama fahimtar karatun da akeyi masu duk da ba'a fara dashi daga farko ba, wajen karatun allonshi ma yana matukar kokari dan yafi sauran yaran da ya tarar kokari.
Shi kanshi Malan yana mamakin kokarinshi, sede yana matukar jin haushinsa saboda yana ganin yazo daga baya amma ya wuce sauran, kuma haka kawai jininsu be hadu ba. Wani lokacin har neman abinda ze sashi laifi yakeyi gashi Nazeeru baya bama Malan komai sede kudin laraba.
Ko kuma da asuba yasa akirashi ya aikeshi yin icce. Sayyadi kanshi seda yayima Malan magana akan irin aikin da yake saka Nazeeru kuma gashi yana zuwa wajen aiki ga makaranta.
Malan yace kana wasa da wanan yaron, kai da ka kalleshi kasan yana tattare da wata baiwa, idan kukayi wasa wata rana duk seya tafi ya barku anan, kuma ze iya zama wani babba. Da kallo Sayyadi yabi Malan cike da mamaki. Ze kara magana Malan yace bana son yawan magana, kaje kawai. Wucewa yayi hankalinshi atashe.
***** *****
Innar Shattima ce Gambo zaune a tsakar gida saman tabarma ta tasa mijinta Malan Fatihu agaba se kuka take mashi akan ya tashi suje ganin dansu, saboda jiya tayi mugun mafarki akanshi.
Tsaki Malan Fatihu yayi yace wallahi Gambo kina da matsala. Shattima de nine na haifeshi, kina tunanin zanje na sayar dashi ne? Yaro ko shekara beyi ba taya zamuje ganinshi? To bari kiji wallahi ko zanje ganin Shattima bayanzu ba.
Nafiso lokacin da zanje ganinshi yayi shekara, kuma bazezo ganin gida ba senan da wasu shekaru, saboda nasan abokina ze kula dashi kamar yanda zanyi mashi. Kawai kinzo kina maganar wani banzan mafarkinki na karya.
Waya ce maki yanzu ana mafarkin gaske? Dan haka kisama ranki salama kici gaba da yimashi addu'a zata riskeshi a duk inda yake. Gambo tace yanzu shikenan Malan nida ganin Shattima senan da shekara daya? Idan kuma na mutu fa? Malan yace babu wanda yasan lokacin mutuwarsa se Allah.
Share kwallar idonta tayi tace shikenan, tunda haka kace insha Allah daga yau na dena yimaka maganar Shattima, zan cigaba da yimashi addu'a. Amma kasani, kome Shattima ya zama kaine sila.
Malan yace tabbas nine sila, domin Shattima ze zama babban hafizi, ina fada maki se Shattima yazo garin nan ya bude makarantar allo tashi ta kanshi. Ko bama raye nasan ladar zata iskemu.
***** *****
Wasu manyan matasa ne suka sauka akofar gidan Malan Imam akan mashin, da ka gansu zakasan ba kananan katti bane, fuskokinsu duk sun dafe saboda shaye shaye. Bayan sun biya kudin mashin din suka dauko jakarsu zuwa kofar gidan Malan.
Ado ne yace lah! Gasu Goga sun dawo. Ai da sauri wasu Almajirai sukaje suka amshi jakarsu suna yimasu sannu da zuwa. Nazeeru da Anas suna zaune suna rubutun da Malan ya basu.
Gaba daya Almajiran manya da yara sun zagayesu kowa yana masu sannu da zuwa, sauran da suka rage basujeba basu da yawa, yawancinsu duk sababbin zuwa ne. Malan da yake cikin gida jin hayaniya ya fito.
Seda gabanshi yafadi ganin wadan da suke kofar gidan. Salati yayi yana fadin shikenan, annoba tazo. Nide wannan koyarwa bata amfane ni da komai ba se takaici. Nine na dora yaran nan akan hanyar neman nakansu saboda surika kawo mani kudi ashe daga karshe jaraba zasu zamar mani.
Gashi nan saboda neman nakansu sun koma sata. Ina addu'ar Allah yasa daga can inda sukaje su kara gaba ashe yau zasu dawo. Goga ne ya nufo Malan da sauran yaranshi su 3 suna washe baki.
Suna zuwa suka duka suna gaishe da Malan. Duk yanda suke da rashin kunya suna matukar girmama Malan, saboda wannan dabi'ace ta Almajirai, basu hada kowa da Malaminsu ba, haka inde zasu gaisheshi basa taba gaidashi atsaye.
Murmushi Malan ya saki yana fadin ashe manyan baki ne agarin namu yau? Kullum sena tambayi Sayyadi wai bakuyi waya ba, seya ce mani bakuyi ba, har wayarka nakira bata shiga inji yaushe zaku dawo? Dariya Goga yayi yace wallahi Malan kasan mun dade bamuje gida ba.
Shiyasa muka dan tsaya acan muka jima, kuma ma Akilu ne da Ilu sukayi aure shiyasa muka kara zama saboda idan muka dawo bamusan lokacin komawa ba, sede surika yimasu aike.
Malan yace masha Allah, Akilu da Ilu ashe kunshigo sahun manya? Kai gaskiya abu yayi kyau. Saura kai da Garbati kenan? Goga yace ai ni gaskiya Malan auren nan ba yanzu ba. Banaso idan nataho narika tunanin nabar nauyi agida.
Dama nide ba Iyaye ba, Kawu ne kawai shima yana sana'arshi kuma ina yimashi aike idan nasamu wani abu, amma wannan bazesa narika damuwa da gida ba akan ace nabar iyali.
Nafiso sena tara kudin da zasu isheni zama waje daya sannan senayi aure, kuma ma ba'a garinmu zanyi gini ba, nafiso yanda nataso cikin garin nan ace nazama dan garin gaba daya.
Malan yace wannan yana da kyau, Allah yayi taimako, gashi bamusan da zuwanku ba ai da an gyara maku dakinku. Goga yace ai ga yara can suna gyarawa. Malan yace to bari nashiga nasan Zaliha zata dora abincin dare se asa daku kafin ku fara zuwa nema.
Goga yace ai daka barshi ma zamuje muci kawai. Malan yace anyi haka? Goga yace ai bakomai, mungode da karramawa. Malan yace to sannunku da zuwa. Wucewa masaukinsu sukayi. Zufa Malan ya goge ya koma gida.
Goga yazo wucewa ya harbi Anas abaya yana fadin kai dan Ubanka bakasan mutane bane ka tsaya kana kallonsu? Dafe wajen Anas yayi yana fadin ai Malan ne ya bamu rubutu ko. Goga yace naci Ubanka, shege har yanzu kana nan da shegen lambonka.
Kai kuma lafiya ka tsareni da ido? Saurin dukar da kai Nazeeru yayi. Ilu yace ai Goga wannan sabo ne. Akilu yace idan baka san labarinmu ba kai Anas ka fada mashi, saura ka kuskure kasha duka. Wucewa sukayi suna ma Sayyadi da yake zaune magana.
Goga yace kaga ya Sayyadi, kaga Waliyin Allah magajin Malan. Akilu yace haba Sayyadi, wata nawa bama nan, ai se azo a tarbemu ko? Garbati yace shi Sayyadi kullum ai addu'a yake kada mudawo.
Dafashi Goga yayi yace haba, Sayyadi baze fadi haka ba, rana daya fa aka kawomu Almajiranci dashi, ko kamanta lokacin kana kuka nine narika baka hakuri. Dariya suka sa gaba daya hada Sayyadi.
Sayyadi yace Goga ba ka manta abinda yawuce. Ya hanya kun dawo lafiya ko? Goga yace lafiya lau, mutananka sunyi aure. Sayyadi yace gaskiya nayi maku murna, Allah ya bada zaman lafiya. Goga saura kai ko? Dariya Goga yayi yace idan kayi nima zanyi.
Sayyadi yace haba, ai mu yara ne. Goga yace naga alama kuwa. Garbati yace ai kai waliyi ne shiyasa. Dariya sukasa gaba daya, suka wuce. Girgiza kai Sayyadi yayi, aranshi yana fadin Allah yashiryeku.
Lokaci daya sukazo karatu amma abinda suka samu a karatun beda yawa saboda tun suna yara suka fara halin banza, abu kamar wasa gashi yanzu sun zama manyan barayi, dalilin rashin barinsu gidan Malan kuwa saboda suna badda kama ne.
Koba komai za'ayi tunanin yaran Malan ne, hakan yasa duk inda sukaje sata basa kwana se sun dawo gida. Kuma Malan kanshi yasan suna sata, amma da yake suna yaga mashi rabonshi yasa baya iya masu magana.
**** ****
Zaune Nazeeru yake atsakar gida yana ta wanke wanke cikin sauri saboda yau ya makara, lokacin da yafito ze taho malan ya sashi aiki, dama kuma yanaso ya makara shiyasa yake sashi aiki wani lokacin.
Gaba daya hankalinshi yatafi makaranta saboda malan me English shine ajinsu kuma double period zeyi. Seda ya kusa gamawa sannan Fiddausi ta kwaso wasu kwanuka daga dakinta, dama kuma tana sane ta barsu.
Dan ita sam bata son Nazeeru, shiyasa duk lokacin da take da girki Nazeeru seya makara a makaranta. Tuni su Samira suka tafi makaranta. Turo mashi kwanukan tayi ta nufi kwandon wanke wanken daya kife wadan
da ya wanke.
Ya mutsasu ta farayi tana fadin yanzu baka son wanke ma mutane kaya da kyau, kalli wannan kofin duk maiko ne ajiki. Wurga mashi tayi cikin ruwan kumfa, kara dauko wani kwano tayi tana fadin gaskiya duk basu fita ba.
Kai idan ka gaji da wannan aikin zan canza wani, haka kawai muna biyanka da abinci me kyau hada kudi ma ake baka amma kai kana yimana munafunci, da yake ku Almajirai baku da gaskiya.
Duk yanda mutum ya daukeku sekun munafunceshi. Dalla ni ka sake wanke mani kaya dukansu, ana maka magana kana wani dukar da kai kamar me gaskiya. Yaro karami da kai amma kasan halin munafunci.
Wallahi Iyayenku sunyi asara da suke turoku Almajiranci kuna yara. Kune sata, kune shaye shaye, a duniya babu wata alfarma da Almajiri zeyi maka koda kuwa kayi mashi komai na rayuwa.
Wallahi idan kayan nan basu fita ba babu inda zakaje, kuma bakada abincin yau. Kwallace ta fito a idon Nazeeru, Farida ce tayi saurin fitowa jin Fiddausi tana masifa. Farida tace haba Maman Samira, kinsanfa makaranta Nazeeru yake zuwa.
Dama amakare yazo, kuma yana kokarin yagama zaki maidashi baya, sannan kuma yaro karami kirika mashi irin wannan zagin haba Maman Samira.
Ki tunafa suma ALMAJIRAN NAN 'YA'YA nefa, kasancewarsu Almajirai ba shine ze bamu dama murika masu yanda muke so ba. Koda muke biyansu ai aiki sukeyi mana, meye laifin Nazeeru agidan nan.
Tunda aka kawoshi kika tsaneshi, ba'a haka arayuwa, komin kaskancin mutum da talaucinshi ba abun awulakanta bane, dan Adam yana da kima da daraja awajen Allah. Wannan yaron fa maraya ne.
Idan baki tausaya mashi saboda Almajiranci ba ai kin tausaya mashi saboda maraicinshi. Yanzu fa karfe 9 ta wuce, kinga duk darasin safe ya wuce shi gashi ko abinci beci ba. Tsawa Fiddausi ta dakama Farida cike da masifa tace ke Farida banason iyayi.
Wannan gidan fa ba naki bane ke kadai, yanda kike takama Ashiru mijinki ne, nima haka yake awajena, kuma daya kawo Nazeeru bece Farida ga Almajiri na kawo maki ba, asalima niyafara fadamawa kafin ke, saboda nafiki matsayi agidan.
Banason shiga harkar da ba taki ba, idan girkin kine kina ganin ina sa maki baki? Kome ya wanke nawa matukar a girkin kine inde be fita ba aje mashi nakeyi se ranar girki na sannan yakara wanke su.
Domin bazan rika bashi abinci abanza ba batare da yayi mani yanda nake so ba. Farida tace Allah ya baki hakuri, nima gaskiyace kawai na fada maki. Fiddausi tace kije masallaci kifada.
Ina ruwana da maraicinshi, idan shima Dane ban damu ba, saboda ba'a rikeshi agida ba aka turoshi Almajiranci. Farida tace Allah ya kyauta. Daki takoma cike da tausayin Nazeeru, tanaso ta fadama Ashiru abinda Fiddausi takemashi amma batason tace ta hadata da mijinta.
Se wajen karfe 10 sannan Nazeeru ya gama aiki, bayan yashare wajen yaje kofar dakin Fiddausi yana fadin yagama, saboda bata sa mashi abinci ba. Tana jinshi ta kyaleshi. Yana yin magana so biyu yaji shiru yadauki robarshi ya aje a kitchen ya fita.
Da sauri Farida ta dauko biredin Danta ta fita, tana fita haryayi nisa, kwala mashi kira tayi, yana zuwa se kuka yakeyi, tace kayi shiru kadena kuka kaji, amshi biredi ga naira hamsin ka sayi wani abu kaci nasan yanzu masu kosai sun tashi.
Godiya yayi mata yatafi, seda ya koma makaranta yasa kayanshi, Anas yace Nazeeru ya akayi ka dade haka? Dukar da kai Nazeeru yayi yana kuka. Matsowa Anas yayi yace me akayi maka? Labarin abinda Malan da Fiddausi sukayi mashi ya fada mashi.
Anas yace Allah ze saka maka, ga abinci nan da naga baka dawo ba naje bara kuma na samo me yawa, taho muci, Nazeeru yace bazanci ba. Duk yanda Anas yayi dashi amma kinci yayi, biredin ya aje mashi yace yatafi.
Kudi Anas yaciro ya bashi yace gashi ka sayi wani abu amakaranta. Nazeeru yace ga kudi nan Umman Zainab ta bani, Anas yace seka dawo kayi hakuri Allah ze saka maka.
Lokacin da yaje makaranta seda shugaban makarantar ya tambayeshi dalilin makararshi, Nazeeru ya fada mashi abinda yafaru yana kuka, seda ya bama shugaban makarantar tausayi. Yace kayi hakuri kada hakan yasa kadena zuwa makaranta.
Dama basa so karika zuwa Makarantar, ko da ka makara karika zuwa kaji, kaide ka kara dagewa nasan kana kokari, idan kayi ilimi wata rana kaima zaka zama babba.
Aranar Nazeeru be koma karbar abincin rana ba, kuma washe gari daya koma aiki daya gama be tsaya karbar abinci ba, ita ko Fiddausi ko ajikinta dama bata zuba mashi abinci se yazo yana ta magana sannan tafito.
Tun daga ranar idan ranar girkin Fiddausi ne Nazeeru baya tsayawa karbar abinci, yana gama aikinshi baya fada mata yake tafiya, sede idan yadawo washe gari yasha fada ta maido mashi wadanda basu fita ba. Sosai Nazeeru yakejin haushinta.
**** ****
Wani tsoho ne makaho tare da dan jagoranshi sukazo bara gidan Alhaji Bashir, kasancewar duk juma'a ana samun yawan mabarata a kowace unguwa musamman gidajen masu kudi.
Sanin halin Alhaji Bashir yasa da yawa mabarata suka dena zuwa gidanshi bara, domin sun san baya bada sadaka matukar ba ramadan bane, shima kuma baya badawa a kofar gidanshi sede a masallaci.
Yau ma kamar daga sama Malan Abu da yake gaban Alhaji Bashir yana niyar bashi albashinshi Hajiya da su Kausar suna daga gefenshi suna zaune awajen hutawa. Alhaji yasa hannu aljihu yaciro kudin yana shirin mika mashi, dan jagora ya turo kofar gate din.
Kasancewar hankalinsu baya wajen yasa basuji karar budewar ba. Ashe lokacin da Malan Abu yafita daya dawo yamanta be rufe kofar ba. Sautin muryar tsohon sukaji yana fadin albarka safiyar juma'a.
A zabure Malan Abu ya mike jikinshi yana rawa, Hajiya ce tace lallai Malan Abu kunnanka bayajin magana. Bawan Allah yana kokarin biyanka hakkinka amma kai baka gani, yau nawa ga wata? Ko ma aikata basu karbi albashinsu ba amma kai ka samu baka tsare naka.
Kausar tace ni wallahi har gabana ma ya fadi, wannan magana daga sama idan mutum karamin ciki gareshi seya zube, ga wata murya duk taci duniya yazo yana shiga hakkinmu. Hajiya tace ai shi beda laifi.
Ko nice naga gida abude ai dole nashigo. Gaskiya Malan Abu ka ji tsoron Allah. Alhaji da yake zaune ya gama cika ya mike tare da dakama wannan tsohon tsawa har seda dan jagoran ya kusa guduwa.
Jikin Malan Abu yana rawa ya nufi kofa domin ya bama wannan tsohon hakuri, muryar Alhaji yaji yana fadin dakata megadi. Tasowa Alhaji yayi ya matso kusa dasu, yana zuwa tsoho yace abamu saboda Allah Alhaji.
Kudin hannunshi ya watsama Malan Abu yana fadin shiga ka kwaso kayanka kabar mani gidana, dama ai na fada maka duk ranar da wani mabaraci yakara mani bara agidan nan abakin aikinka.
Dukawa Malan Abu yayi yana fadin ka dubi girman Allah kayi hakuri Alhaji, wannan aikin dashi na dogara, idan ka rabani dashi zan shiga damuwa, iyalina suna da yawa ga matata bada isassar lafiya.
Wallahi ba laifina bane, bansan ya akayi yashigo ba dan Allah Alhaji ka duba mani. Kausar ce ta matso tana fadin wallahi Abba kada ka barshi, rannan fa zamuje unguwa har muka bude gate na fita da mota besan nafita ba yana ta bacci.
Saurin kallonta Malan Abu yayi cike da mamaki. Nafisa ce tace dan Allah Abba ka kyaleshi, kaga Malan Abu ya tsufa baze iya aikin karfi ba. Dungureta Hajiya tayi tana fadin tafi kiba mutane waje.
Sakarya marar kishin dukiyar ubanta, idan aka barshi duk ranar da yake bacci barayi sukazo suka kwashe dukiyarmu yana da asara ne? Wallahi yau seya bar gidan nan.
Alhaji yace kima dena bata bakinki, dama akwai wani tsohon dan sanda yana cikin wadan da tsautsayin kora daga aiki ya fadamawa, to mutumina ne dama nayi mashi tayin aiki saboda naga yana zaman banza, gashi karfaffane sosai.
Nasan ze iya gadi sosai, shiyasa na amshi wayarshi nace yajirani zan nemeshi koda yaushe. Saboda haka ayau ze fara yimani aiki ma. Murmushi Hajiya tayi tana fadin haka nake son ji.
Kawayena duk agidajensu masu gadinsu dauke suke da bindigoginsu, wasu tsofafin sojojine, wasu kuma irin majiya karfi ne. Amma muna fama da wannan tsohon, wanda ko barayi sukazo bugu daya ya mutu.
Ai kawai Malan Abu ka koma gona shine zefi maka. Nafisa tace amma fa Momy tunda Malan Abu yake so daya barayi suka taba zuwa mana, wata kawata wallahi gidansu soja biyu suke gadi amma aka shiga aka yimasu sata.
Alhaji yace Nafisa shiga gida. Tsayawa tayi tana kallonshi, tsawa ya daka kata da gudu tashige gida. Kallon Malan Abu yayi yace kabar gidan nan nace maka. Tsoho yace Alhaji zanshiga maganarku.
Idan nine silar barinshi aiki ina neman alfarma da kayi mashi hakuri. Alhaji yace kai tsoho dallah ka rufe mana baki, wai mema ka tsaya yi acikin gidan nan? Kawai kuzo kuna damun mutane.
Mutum beda halin fitowa tsakar gidanshi ya huta shida iyalinshi sekun shigo kun damesu, yanzu kasan wane hali nake nida iyalina kawai zaku fadoma mutane gida? Ko bakaje makaranta ba nasan kasan ma'anar sallama ai.
Sa'arka daya kaidin tsoho ne wallahi da sena maka duka ko nasa a daureka, mutane bazasuje su nemi nakansu ba haka kawai kurika yawon bara kuna damun mutane, irinku ma kuna da manyan 'ya'ya amma saboda mutuwar zuciya baku hakuri da abinda suke baku kun fiso kufito bara.
Tsoho yace Allah ya baka hakuri, laluben dan jagorarshi yayi suka fice yana fadin kabi duniya a hankali de. Haka Malan Abu ya fito da ledar kayanshi, dukawa yayi yace zantafi Alhaji, ina me matukar godiya agareka, domin kayi mani halarci, kuma dama dan halak baya manta halarci koda kuwa wanda yayi mashi yaci zarafinshi fiye da haka.
Tabbas bazan taba mantawa da kai ba, domin kaciyar dani, ka sharyar dani, ka tufatar dani, duk da acikin izgilanci nake zaune agidanka amma hakkina daka kare mani ya sa bazan manta da kai ba.
Idan a zaman da mukayi na shekara da shekaru na bata maka rai ina neman afuwarka nide na yafe maka. Allah ya hada fuskokinmu, duk da nasan da wuya musake haduwa. Amma zan yimaka kwatancen inda nake saboda ko hakan zeyi maka amfani wata rana.
Duk da kasan garin da nake amma bakasan a inda zaka sameni ba. Idan kaje tashar garinmu, kace a kaika layin 'yar kuka ka tambayi gidan Malan Abu me Jima duk wanda kace ma haka ze kawoka har inda nake.
Alhaji yace kada kayi wahalar bani kwatancen gidanka, ni ko garinku ma ban tabawa zuwa ba, dalilin sanin sunan garin ma kaine ka fada mani, kuma kadena tunanin har abada zan zo nemanka, domin amfaninka yakare awaje na.
Naci moriyar ganga yanzu babu wani sauran amfanin da zatayi mani. Kaide tunda kasan na amfaneka shikenan, dama kuma ko baka fadaba ni nasan na biyaka hakkinka, da kake fadin ka yafe mani, ai ban cuceka ba.
Idan cuta ce kaine ka cuceni, kuma darajar aikin da kayi mani yasa zan yafe maka. Fita kabar mani gida, har abada bazaka kara ganina ba. Tashi yayi yafita idonshi yana fitar da kwalla.
Hajiya tace haba muma mun huta, amma idan gate ze budema mutum har se ranka yabaci kafin ya isa saboda son jikinshi. Alhaji yace muje gida nakira Sajan Gali anjima yazo.
Kasan wata bishiya inda tsohon nan da yaronshi suke zaune suna hutawa Malan Abu yaje ya buga tagumi, kasancewar tsohon baya gani yaron ne ya fada mashi ga mutumin da aka kora nan. Tsohon yace bawan Allah kayi hakuri nasan nine silar barin aikinka.
Malan Abu yace bakomai, koda ba kazo ba Allah ya rubuta abincina ya kare agidan nan. Dama hakuri nakeyi amma wulakancin da suke mani yayi yawa, sam basu san darajar dan Adam ba, idan mutum talaka ne beda daraja awajensu.
Tsoho yace suma zasu gamu da dede sune, domin duniya ba madauwama bace, yanda ya wulakanta ka insha Allah shima se Allah ya wulakanshi, yanda yaci mutuncina, insha Allah shima se anci mutunci zuri'arshi.
Allah ka kare wannan baiwar taka da naji tana bama mahaifinta hakuri akan kada ya koreka. Na dade ina bara, amma ban taba samun wanda yaci mutuncina irin haka ba. Insha Allah kudin da yake takama dasu se sun zamar mashi abun tsoro.
Yaro tashi mutafi. Malan Abu yace nagode tsoho Allah ya tsare gaba. Yace amin, Malan Abu yace amma bawan Allah daga ganinka bako ne agarin nan ko? Tsoho yace gaskiya kam ni bako ne.
Malan Abu yace ai naga alama, domin masu bara sun san halin Alhaji basa zuwa gidanshi. Tsoho yace nima yaune na taba zuwa unguwarnan bara, yau kwana na 4 agarin nan, dama idan naje gari yawon bara ina kwana 5 kafin natafi.
Yau munzo bara kusa da unguwarnan har tafiya ta kawomu nan rabon mu hadu da wannan wulakantattan mutumin ne. Ni mutumin Shargalle ne, amma ba cikin gari nake sosai ba, idan kaje wajen gari akwai wani me saida man fetur abakin titi.
Akwai wata hanya daga gefenshi, idan kabita zata kaika har gidana. Kaifa a ina kake? Malan Abu yace a Dargage n
ake. Tsoho yace Allah sarki, ai nasan garin sosai, amma yanzu can zaka koma ko zaka nemi wani aikin anan? Malan Abu yace nida kara aikin gadi har abada.
Muna sadaukar da rayuwarmu akansu amma su basa gani, muna hana idanuwanmu bacci domin su su runtsa amma basa gani. Kome kakeyi matukar suka fito zasu fita dole katashi kaje ka bude masu kofa.
Gaba daya karfina awajen bude gate yatafi, idan ana ruwa, iska suna cikin gidan muna waje, dakin da zasu baka badan ka kwanta ba sedan ka aje kayanka, kaida samun bacci me dadi babu rana.
Idan tsautsayi ya fado barayi suka shigo kaine mutumin farko da zasu fara illatawa, amma daga karshe se su baka sallama saboda ka nakasa su dauko wani. Na hakura da gadi tsoho, gara naje na nemi aikin karfi nayi komin wahalarshi, amma da yawa wasu masu kudin basa yima masu gadinsu adalci.
Suna mantawa da muhimmancin mu agaresu, basa nuna ma matansu da 'ya'yansu muhimmancin mu, karamin yaro ma seya taka ka yawuce. Allah ka kawo mana sauki a rayuwarmu. Tsoho yace amin, kaide wannan rayuwa kawai adeyita. Mu zamu wuce. Malan Abu yace insha Allah duk lokacin da nayo wajenku zaka ganni, amma wa zance? Tsoho yace ka tambayi gidan Tsoho makaho za'a kawoka. Yace to nagode, Allah ya sadamu da alkhairi.
Bayan sun tafi shima Malan Abu ya tashi yanufi bakin titi domin samun mashin din daze kaishi wajen hawa motar Zango saboda ba cikin Daura yake ba acan wani kauye yake gaba da Zango me suna Dargage yana me cike da bakin cikin abinda akayi mashi haka yabar garin Daura.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
ALMAJIRAI MA 'YA'YA NE


Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
[email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey
Chapter 5 · 0% Book details