Part 20
Almajirai Ma Yaya Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 10 min read
Lokacin da Anas yadawo ya samu dari biyu, sosai sukayi murna dama sunaso su sayi sabulun wanka dana wanki, anan Nazeeru ya bama Anas labarin abinda akayi masu.
Anas yace kuyi hakuri kada ku kara zuwa gidan, kuma Allah ze saka maku. Abincin da suka samo suka hauci, sede beda yawa dan Shattima ne kadai ya samo bara, haka sukaci suka sha ruwa dan yanzu sun saba da yunwa, komin kadan din abinci idan sukaci haka suke hakura.
Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya kullum Nazeeru yana kokarin neman gidan aiki amma saboda beda girma sosai yasa har yanzu ba'a daukeshi ba, Anas kuwa wajen wannan mutumin suke zuwa suna aiki ana biyansu.
Haka suke su 3, kowa ya sansu a makarantar, duk inda kaga Nazeeru tare da Shattima zaka ganshi, haka ma Anas sede idan yana wajen aiki, duk abinda wani ya samo baya cinyewa seya jira sauran, wani lokacin idan abincin kadan ne haka suke hakura su barma Shattima ya cinye.
Malan kuwa kwata kwata ya manta da wata amana da abokinshi ya bashi na Shattima, gaba daya kudin da aka bashi dubu biyar ya cinyesu ko naira be bama Shattima ba.
Yauma kamar kullum tunda suka gama sallar asuba gari ya fara haske Malan da Sayyadi suka tasa ALMAJIRAN zuwa gonar Malan zasuyi mashi cira, ko abinci babu wanda yaci haka suka tafi.
Dama duk lokacin da zasuje gona to aranar ko karatun safe basayi. Bayan sunje gonar kowa yafara aiki, kiraruwan da suke kwashewa haka suke dauresu waje daya saboda gidan Malan za'a kaisu.
Waje Anas ya samu ya kwanta ya rike ciki se rufe ido yakeyi, Sayyadi ne yazo da bulala a hannunshi yana fadin kai meyasameka? Da kyar Anas ya bude ido hada kukan karya yace cikina yake ciwo.
Nazeeru da Shattima ne suka karaso da sauri wajen ganin Anas akwance. Malan ne ya iso yana fadin Sayyadi lafiya? Sayyadi yace wai wannan yaron ne cikinshi yake ciwo.
Malan yace karya yakeyi, ai na ganoshi, duk lokacin dana sa su aiki haka yake cewa beda lafiya, kai Anas mike. Tashi Anas yayi da kyar yana goge idonshi. Malan yace wuce kaje kucigaba da aiki nasan karya kakeyi.
Cikin kuka Anas yace Allah Malan cikina yake ciwo. Shiru Malan yayi sannan yace shikenan, kazauna agama se muje na baka rubutu. Komawa yayi ya kwanta ya rufe fuskarshi da hannu yana murmushi.
Malan yace ku kuma me kuke jira? Saurin juyawa sukayi. Shattima kamar zeyi kuka yace Nazeeru yunwa nakeji. Nazeeru yace kayi hakuri kaga Malan ya zane wancan saboda ya zauna yace yunwa yakeji.
Kwallace ta zubo a idon Shattima yace nide gaskiya tafiya zanyi idan nasamo Bara sena aje maku kaga Anas shima beda lafiya. Juyawa Nazeeru yayi ganin kowa yana aiki hankalin Malan yana wajen Sayyadi suna magana.
Kallon Shattima yayi yace zaka iya gane gida ko? Kai Shattima ya daga. Nazeeru yace kayi sauri katafi, idan Malan ya tambayeka zance kaje kayi fitsari. Da gudu Shattima yabar wajen, seda ya bace sannan Nazeeru yacigaba da aiki.
Sosai Nazeeru yagaji, dan tunda yazo ba'a taba zuwa gona dashi ba se yau, duk yaji ciwo a hannunshi, bayan angama ya zauna yana ta kuka. Malan ne yace yauwa gaba dayanku ku taru.
Seda Sayyadi yagama kirgasu sannan yace ma Malan babu yaro daya. Malan yace wanene? Sayyadi yace Malan dan wajen abokinka ne. Malan yace Shattima ko? Kai Nazeeru zonan.
Ina Shattima yake? Nazeeru yace yaje yayi fitsari. Bulala Malan ya zuba mashi seda ya zube kasa saboda zafi. Malan yace ni zakayima karya? Duk inda yaje kaine ka sashi yaje, ai duk makarantar nan yafi jin maganar ka da kowa.
Wato kana so ka koya mashi halin banza ko? Dama tsintattar mage ai bata mage, duk yaron daka gani anan iyayanshi ne suka kawoshi, amma kai daga sama kazo haka nan naji tausayinka na daukeka saboda banaso kaje ka fada hannun banza, segashi kai kuma kanaso ka lalata mani yara.
Bazaka fada mani gaskiya ba sena koreka daga makaranta ta? Cikin kuka Nazeeru yace nine nace yaje ya samo abinci saboda yace yana jin yunwa kuma nasan bazaka barshi yatafi ba.
Malan yace lallai kam wuyanka ya isa yanka, nan gaba bansan yanda zaka zama ba, gara tun yanzu kafin ka girma na koya maka hankali. Sayyadi, ku wuce mutafi idan munje zan fadi irin hukuncin da za'ayi mashi.
Sosai hankalin Nazeeru da Anas yatashi, haka suka tafi sauran Almajiran se dariya sukeyima Nazeeru. Anas ne ya matso kusa dashi yace Nazeeru dan Allah ka gudu kada kabari ka koma wallahi Malan zaneka zeyi.
Nazeeru yace Anas idan natafi bansan garinmu ba, kuma kada barayi su saceni, gashi banaso natafi na barku, kaga shima Shattima nasan se Malan ya dukeshi, kawai muje idan ya dukeni ai Allah ze saka mani ko? Anas yace emana.
Bayan sun koma gida haka Malan ya tara yaranshi aka saka Nazeeru da Shattima a gaba, Sayyadi Malan yasa yayi masu bulala, Shattima bulala biyar akayi mashi, Nazeeru kuwa bulala goma, kuma masu zafi.
Anas se kuka yakeyi, sauran yara kuwa se dariya suke masu, bayan angama Malan yace kai Shattima tashi katafi, nasan baka da laifi, Sayyadi, adauki Nazeeru akaishi dakin horo kada afiddoshi seda dare.
Saboda kana sabon zuwa ne yasa bazaka kwana ba, gobe ma idan muka fita aiki ka kara cema wani yatafi. Kuka sosai su Anas sukeyi, Nazeeru kuwa da kyar ya iya tashi duk jikinshi ya fashe, se kuka yakeyi.
Haka aka tafi dashi, Malan yace kowa yatafi ya yo bara. Waje Anas da Shattima suka samu suka zauna suna kuka. Shattima yace nide zan koma wajen Mama. Anas yace idan Malan ya kamaka dukan daze maka seyafi na Nazeeru, kuma idan aka kulleka sekayi kwana 3 kafin kafito.
Cikin kuka Shattima yace to ai ni yunwa nakeji. Anas yace tashi muje musiyo koko idan mukasha semu ragema Nazeeru kadena kuka.
***** *****
Alhaji Nafi'u ne kanin Mahaifin Nazeeru zaune a falo ya tasa abinci agaba ya buga tagumi yana tunani, matarshi ce tashigo falon, waje ta samu tazauna tana fadin Alhaji lafiya wannan tagumi haka? Ajiyar zuciya yasaki tare da goge zufar data zubo mashi.
Girgiza kai yayi yace dole nayi tagumi Hajiya, nayarda da mutuwa kuma nasan duk me rai mamaci ne, amma nakasa mantawa da mutuwar su Yaya, yau kwana 3 kenan kullum senayi mafarkin Nazeeru.
Kuma shi kadai nake mafarki, yanayin da nake ganinshi aciki marar kyau ne, sede mafarkin danayi jiya yafi na kullum, zaune naganshi yana ta kuka, yana ganina yazo ya rungumeni yana fadin intafi dashi yunwa yakeji.
Wai baya samun abinci a inda yake zaune. Lokacin dana kamo hannunshi zamu tafi kawai sena farka. Anya Hajiya Nazeeru ya mutu kuwa? Idan ya mutu meyasa nake mafarkinshi banayin nasu Yaya? Hajiya tace haba Alhaji, taya zaka rika irin wannan maganar.
Kasanfa duk wanda ya mutu yariga da ya mutu, kawai saboda ka saka Nazeeru aranka ne yasa kake yawan mafarkinshi, addu'a kawai zamucigaba da yimasu amma wannan damuwar bazata amfaneka da komai ba.
Alhaji yace haka ne Hajiya, amma ina mamakin wannan mafarki. Shikenan Allah yajikan Yaya da Iyalanshi. Tace amin, kaci abincinka kada ka makara office.
**** ****
Wahidi, Sadaka, Almajiri bara iya, koda kanzo ne, kome wari ne Iyaya, wahi............. Kai dalla ka rufe mana baki, wane irin iskanci ne kawai mutane suna hutawa zakazo ka hanasu sakat, da ban fito ba kilama shiga kitchen din zakayi.
Shegu marasa tarbiya haka kawai Iyayenku suna can suna hutawa kunzo nan kuna damun mu. Hajara ce take ta masifa jin Almajiri yana bara suna kwance suna hutawa. Megidan ne yafito yana fadin haba Hajara, kai yaron Malan jeka yi hakuri.
Juyawa Almajirin yayi yafita, kallonta yayi tana ta huci yace haba Hajara, kalli dan karamin yaron da kike ma masifa, suma fa ALMAJIRAN NAN'YA'YA NE, ba'ace dole kibasu sadaka ba, amma magana medadi ma ai sadaka ce.
Kada kimanta wata rana kema kina amfanuwa dasu, so nawa ina samunki kina aikensu siyen wani abu ko kai markade? Amma duk da haka zaki samu karamin yaro kirika zaginshi haka. Suma fa ba laifinsu bane.
Iyayensu sune masu laifi, da suna zuwa suga yanda 'Ya'Yansu suke rayuwa babu wani Uban daze bar danshi, domin aganinsu karatu suka turosu, sede basa kare masu hakkinsu yanda yakamata.
Yanzu ina amfanin wannan zagi da hantara da kikayi mashi? Kada kimanta yau ko yaron da besan komai ba yasan me kyautata mashi, ina guje maki ranar da zakiyi dana sani akan wannan halin naki.
Ba tunyau nake fada maki haka ba amma kin kasa ganewa. Idan Almajiri yayi bara idan ma bazaki iya cemashi yayi hakuri ba, kiyi shiru ki kyaleshi da kanshi ze gaji yatafi, acikin Yaran nan fa bakisan bakin wani ba, kuma kowa da kika ganshi akwai baiwar da Allah yayi mashi.
Tsaki Hajara taja tana fadin yanzu saboda Almajiri zaka rufeni da fada? Murmushi yayi yace niba fada nayi maki ba.
Kawai gaskiyace na fada maki amatsayina na mijinki. Hajara tace to naji, amma daga yau kulle gidan zanrikayi danni wallahi bazan tsaya karar da miyan bakina wajen bama Almajiri hakuri ba.
Girgiza kai yayi yana murmushi yace Allah ya kyauta, ni nashirya fita zanyi. Murmushi tayi tace adawo lafiya.
Zaune sauran Almajiran suke saman dakalin gidan Hajara, Almajirin yana zuwa wani yace Ado ya naga ka dade? Wanda aka kira da Ado yace wallahi wannan matar tacika fada, se zagina takeyi.
Dariya sukasa wani yace da zaka je gidan ba seda nace kada kaje ba bata bada sadaka kace se kaje. Ado yace ai se Allah ya saka mani tunda banyi mata komai ba take zagina. Kutashi mutafi ankusa shiga karatu.
Wani yace ka kyaleta zata leko neman dan aike wallahi bazamu kara zuwa ba. Tunda bata ba da sadaka seta aiki mutum, Ado yace idan diyarta tadawo daga makaranta nima sena zageta. Dariya suka samashi suka tashi suka tafi.
Barira ce da Larai se yaransu zaune a kasan wata bishiya, Balki tana kwance a kafar Larai. Barira tace wai ni Larai kin duba abinda yake damun Balki kuwa? Larai tace kinsan halin Balki batason wanke hannu idan taci abinci, yanzu haka tsarki taje tayi hannunta da yaji.
Barira tace gaskiya baki kyauta ba Balki, kinga gashinan se zafi kikeji. Dago kai Balki tayi tace Allah ina wanke hannuna. Barira tace to meyafaru da wajen? Larai tace kema de da neman magana, kamar bakisan halin Balki da shegiyar karya ba.
Koma me tasaka ai ita zataji zafin. Tunda yanzu zafin yayi sauki kutashi kuje ku samo mana abinda zamuci. Tashi Balki tayi tana ware kafafuwa, Barira tace aifa, ciwo yazo ga ma iya.
Kai Auta tashi kaje wancan gidan idan kaje kace Mamanka bata da lafiya yunwa kakeji amma kada kaje gidan jiya kaji? Kai yadaga mata. Larai tace Barira tashi ga Alhajin nan yaude munci sa'a yafito da kafarshi gashi can ma ya zauna a kofar gida.
Saurin tashi Barira tayi tace lallai yau zamu samu kudi, dan naga alama mabarata basa zuwa gidanshi saboda kullum a mota yake fitowa kuma kullum gidan a kulle. Balki kama Auta ki rakashi idan yashiga sekije kema kiyo Barar.
Balki tace nide bazan kara zuwa wancan gidan ba, dungureta Larai tayi tace kaji shegiya 'yar bakin ciki, duk cikin gidajen da kike zuwa ki fada mani gidan da ake baki abinci me dadi da nama kamar wancan gidan? Saboda bakin ciki kuma sekice bazaki kara zuwa ba.
Barira tace yimata ahankali Larai, Balki kije kinji, kinga nima Aina'u Babanta ya dauketa ya kaima Yayarshi wai bayaso ina zuwa da ita kinga ai da kinsamu kawar zuwa Bara. Balki tace to zanje, amma ai bayanzu ba se anjima.
Larai tace kede kika sani idan baki samo abinci ba yau bazakici komai ba, kuma daga yau bazan kara zuwa dake ba. Barira tace shikenan tunda tace se anjima zataje, kila tasan dede lokacin da ake bata abincin ai.
Kama hannun Auta idan yaje seki jirashi yafito muma zamuje wancan gidan idan kun dawo ku zauna anan. Tashi sukayi suka nufi wajen Alhajin da suka hango yafito kofar gida, suna tafe su
na addu'ar samun nasara.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady?
08028525263
ALMAJIRAI MA 'YA'YA NE
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
[email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey