← Book details Almajirai Ma Yaya Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
CHAPTER 1 OF 6

Part 15

Almajirai Ma Yaya Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 16 min read

Dariya Larai tasa tana fadin da gaskiyarki Barira, muda mudena Bara se na zama babbar hajiya. Barira tace tunda mun samu na yau kuma mun cika cikinmu hada guziri gara mu hada kayanmu yamma tayi.
Larai tace gaskiya kam ai yau Bara tayi mana rana sosai, mun kwana biyu bamu hada irin wannan kayan ba. Amma gobe da wuri zamu fito banason muna makara. Barira tace gaskiya kam.
Hada kayansu sukayi suka tasa yaransu zuwa bakin titi domin su samu abun hawan daze kaisu gida, suna me cike da farin cikin samun da sukayi. Kafin su kai gida ankira magriba, haka kowa ta nufi gidanta.
**** ****
Zaune Shattima yake a zauren Malan yana kuka, gabanshi kwanon tuwo ne da alama shine yagama ci, sede dalilin kukanshi saboda be koshi bane. Domin matar Malan bata da kirki, kamar yanda mijinta yake itama haka take.
Tuwon ma dan Malan yace mata ta zuba mashi da bazata bashi ba, shiyasa ta zuba mashi dan kadan, hakan yasa daya gama yasa kuka dan yaje yace akara mashi ta koroshi da masifa.
Kuka kawai yakeyi yana tunanin gida. Malan ne yashigo tare da haske fuskar Shattima, karasawa wajenshi yayi yana fadin kai Shattima lafiya zakazo kazauna anan kana kuka? Dago kai Shattima yayi tare da goge idanushi yace bankoshi da tuwon ba.
Daure fuska Malan yayi yace naga alama Shattima ka manta inda kazo, bakaga sauran yaran bara suke zuwa suyo ba? Kaima saboda kana sabon zuwa ne, kuma Dan abokina shiyasa ka samu haka.
Ka tashi kaje waje ga ruwa can ka wanke hannunka kasha ruwa kajira ayi sallar isha'i ga kwalinan a bayanka ka shimfidashi ka kwanta anan saboda dakin yarana baze isheku ba.
Wucewa yayi ciki yana gungunai. Nazeeru da Anas da suke zaune a kusa da zauren suna cin abinci sunajin duk abinda sukeyi. Fitowa Shattima yayi yana kuka ya nufi wajen tukunyar ruwan da take aje akasan bishiya.
Girgiza kai Nazeeru yayi yace yanzu shikenan Anas haka ze kwanta? Murmushi Anas yayi yace dazu ba na fada maka Babanshi ya bama Malan kudi da kayanshi yace yarika kula dashi ba.
Ai dama na fada maka, wannan Malamin beda tausayi shida matarshi, duk wanda iyayenshi suka kawoshi da kayan abinci da kudi, idan suka bama Malan da mutum yayi kwana daya yake koroshi cikin sauran yara.
Shiyasa ni tunda na saba da makarantar nan ba ruwana da zuwa wajen Malan sede idan zanyi karatu. Idon Nazeeru ne ya cika da kwalla. Tashi yayi yaje ya kamo hannun Shattima saboda tunda ya ganshi yaji yana tausayinshi.
Yacika kankanta, idan ka ganshi zaka dauka be kai shekara 8 ba. Da kallo Shattima yabi Nazeeru, murmushi yayi mashi yace zomuci abinci. Da sauri Shattima yabi bayanshi suka zauna suka fara cin abincin, dan yau su duka suka samo bara kuma me yawa ne.
Malan yana shiga gida matarshi tace Malan kai da wa naji kana fada a zaure? Tsaki Malan yayi yace nida wancan yaron Shattima mana, shiyasa fa wani lokacin banason akawo mani idon sani.
Wai kuka yakeyi be koshi ba. Dariya Zaliha tayi tace kai Malan har ka bani dariya wallahi, ai dama ina fada maka, duk yaron da Ubanshi ya kawoshi ALMAJIRANCI ai yasan me ya kawoshi yi. Idan yanaso danshi yarika ci yana koshi ai baze kawoshi ALMAJIRANCI ba.
Shiyasa nace maka bazeyuwu ace mune zamu rika bashi abinci ba. Dalilin da yasa Iyaye suke kawo 'Ya'yansu ALMAJIRANCI nesa da gida saboda basu so surika sama ransu zuwa gida.
Sun fiso sufi maida hankali akan karatunsu, saboda haka ka saki Shattima yashiga cikin sauran yara domin zefi saurin sabawa da makarantar, kuma hakan ne zesa ya fahimci cewa ALMAJIRANCI aka kawoshi.
Jinjina kai Malan yayi yace maganarki haka take Zaliha, nima nayi wannan tunanin, Allah ya kaimu gobe ki hado mashi kayanshi kawai na hadashi da wasu yaran. Zaliha tace ga jakar kayan sawarshi can.
Sabulan kuma zan saka mashi guda daya sauran kuma zanyi amfani dasu, kasan kona saka mashi abanza za'a sace mashi. Malan yace ai babu laifi, gara yaje yasan zafin nema zerika tattalawa. Kawo mani abincina naje muyi sallah dana dawo zanci.
**** ****
Washe gari bayan sun gama karatu Malan yakira Shattima yabashi kayanshi yace daga yau acikin sauran yara zerika kwana, kuma yaje yarika nemo abinda zeci.
Jakarshi ya dauka yana kuka ya nufi wajen su Nazeeru. Hannunshi Nazeeru ya kamo yana lallashinshi, Anas ne ya dauki jakarshi ya kai mashi inda suke aje nasu.
Haka suka kamashi suka tafi Bara tare. Nazeeru yace wai Anas meyasa jiya kabi su Hamza kukaje wajen wancan mutumin na bayan layi Kasanfa kayan da yake hadawa basu da kyau?
Rannan naji wasu suna fadin da yaga 'yansanda yayi saurin boye kayanshi. Anas yace amma kuma ai na samo naira dari, kuma bansha wata rana da wahala ba, acikin shago ne muke hadawa, gashi kai abinci ma roba daya kawai ka samo.
Kai kullum bazaka dage kanemi kudi ba gashi omon wanki ma yana maka wahala. Nazeeru yace kasanfa babu kyau mutum ya samu kudi ta hanya marar kyau. Malaminmu na islamiya yace gara mutum ya kwana da yunwa da yaci haram.
Dariya Anas yayi yace nide kadena wannan maganar kawai muje munemo abinci yunwa nakeji. Nazeeru yace towai menene yake baku kuna hada mashi? Anas yace nima bansan ko meye ba, wani abune baki muke nadewa a farar takarda.
Nazeeru yace kila maganin basur ne shima ai baki ne. Anas yace kila ba. Nazeeru yace inde wannan ne ai ba komai, amma meyasa yake boyewa idan yaga 'yansanda? Malan na garinmu yace duk abinda mutum baze iya yinsa agaban mutane ba to abu marar kyau ne. Anas yace nide muje tunda na samu kudi ai shikenan.
Kaima idan zakaje anjima se mutafi. Nazeeru yace gaskiya bazanje ba, zan kara komawa naga kozan samu aiki a wani gida. Anas yace tunda kafison aikatau aishikenan, gashi ka kara jawo mana Shattima. Nazeeru yace dan Allah mutafi dashi kaji? Anas yace shikenan mutafi.
**** ****
Tun daga wannan rana su Nazeeru suka zama su 3, sosai yake tausayin Shattima, duk da ba wani girmanshi yayi ba amma yafishi jikin girma, kuma Nazeeru yana da matukar wayau da nutsuwa, Anas kuma akwai wayau sosai, shiyasa Shattima ya koma kamar kaninsu.
Duk abinda suka samo tare sukeci. Idan lokacin tafiya aikin su Anas yayi haka yake bin abokan tafiyarshi yabar su Nazeeru da Shattima sutafi yin Bara domin su samo masu abincin dare shikuma idan yasamo kudi dasu suke amfani wajen siyen abubuwan bukatarsu.
Kwata kwata Malan yadena sakarma Shattima fuska, yanda yakema sauran yaranshi haka yake mashi, shima Shattima ganin Nazeeru yana kula dashi yasa ko zauren Malan be kara shiga ba.
Idan yaganshi ma boyewa yakeyi, gashi idan beyi karatu ba Malan dukanshi yakeyi sosai. Jikinshi duk sahun bulala ne. Ganin irin dukan da Malan yake mashi ne yasa Nazeeru ya fara koyama Shattima karatu.
Zaune Nazeeru da Shattima suke suna fira dan Anas yabi abokan tafiyarshi, wasu ALMAJIRAI ne sukazo suna tsokanar Nazeeru, ko kallonsu Nazeeru beyi ba, wani ne yasa kafa yayi kwallo da robar Nazeeru.
Shattima yace dan Allah kuyi hakuri. Dayan ne yakamo Nazeeru yana fadin kai dan Ubanka jiya nace ka zuba mani abinci shine kayi saurin shigewa wajen Sayyadi ko? Nazeeru yace nide ka sakeni.
Kawai na samo abinci na shine zakace na baka, wallahi ka sakeni kona fadama Sayyadi. Dunkule hannu yayi ya kaimashi naushi, ihu Shattima yasa da sauri ya saki Nazeeru suka ruga suna dariya.
Sayyadi yana zuwa yace Nazeeru meyafaru? Cikin kuka ya fada mashi abinda yafaru. Sayyadi yace kayi hakuri, kaima karika dagewa kana ramawa idan wani ya bigeka, kasan kowa 'yancin kanshi yake nema anan.
Kamashi yayi yace muje ka wanke bakinka kada ka kara kulasu. Lokacin da Anas yadawo Nazeeru ya fada mashi abinda akayi mashi. Anas yace wallahi sena rama maka, Nazeeru yace ka kyaleshi sunfimu girma baza mu iya masu komai ba.
Anas yace kaide ka barni kawai ko aboye ne sena rama maka. Nazeeru yace nagode.
**** ****
Zaune Hajara take a tsakar gida tana tsefe ma diyarta kitso, megidanta ne yayi sallama yashigo, murmushi tayi tana fadin Baban Fadila sannu da zuwa. Zama yayi yace yauwa Maman Fadila sannu da aiki, tsifa akeyi? Fadila tace sannu da zuwa Baba.
Yace yauwa sannu Fadila ya makaranta? Tace lafiya lau. Tashi Hajara tayi ta kawo mashi abincinshi da ruwansha. Budewa yayi ya faraci suna fira. Muryar wani karamin yaro sukaji yana Bara maganar ma bata fitowa sosai saboda be iya ba.
Tsaki Hajara taja tana fadin wallahi wadannan Mabarantan sun fara isata, inbanda rashin sanin darajar haihuwa surika turo kananan yara suna bara. Yanzu dan Allah kalli wannan yaron, maganar kirki ma be iyaba amma wai aka turoshi bara.
Baban Fadila yace Allah sarki, kaizo nan. Shigowa yaron yayi da kwano a hannunshi. Kallonshi yayi yace ina Mamanka? Yaron yace tana can batada lafiya. Kwallace ta cika ma Baban Fadila ido.
Karbar kwanonshi yayi ya zuba mashi rabin abincinshi yace karba kaje ka kai mata. Hajara tace lallai Baban Fadila bakasan halin iyayen wadannan yaran ba. Wallahi idan ka bincika lafiyarta kalau.
Shekaran jiya Maman Ahmad take bani labarin wata yarinya taje karama da ita tana kuka wai Mamanta bata da lafiya kuma yunwa takeji. Haka ta dauki abinci ta bata, yarinyar tana fita kamar ance ta leka ta hango wasu mata sun boye suna jiranta ta fito.
Kasan Maman Ahmad bata barin seta kwana, aiko tashiga kwalama yarinyar kira, ai da gudu ta isa wajen matan, tana zuwa suka hada kayansu suka bar wajen. Tun daga ranar ganin Maman Ahmad ta ganesu basu kara zuwa bara gidanta ba.
Tunda naga wanna yaron nasan cewar karya yakeyi. Baban Fadila yace kai amma sun cuci kansu, taya zasu bar yaro kamar wannan yarika shiga bara, shin sun san akwai mace agidan ma ko babu haka kawai suka turoshi? Gaskiya wannan ba dabi'a me kyau bace.
Hajara tace shiyasa wallahi bana basu sadaka, gara na bama Almajiri abinci dana basu, saboda idan ka bincika sunada kwari amma suke fitowa bara saboda mutuwar zuciya. Shiko Almajiri ba'a gaban iyayenshi yake ba.
Baban Fadila yace to Allah ya kyauta, amma wannan ba hanyar dazata bulle masu bace suka dauko, domin wannan duniyar abun tsoroce. Amma kada ki gajiya dan kin bama Almajiri sadakar abinci saboda temako ne.
Kuma duk wanda kaciyar alokacinda yakejin yunwa zaka samu lada me yawa, suma yaran ba laifinsu bane. Masu laifi sune Iyayensu, kuma kowane hali suka shiga sune zasu dauki alhakin . Hajara tace Allah ya kyauta, bara na karo maka abincin. Yace a'a kibarshi wannan ma ya isheni.
Yaron Barira yana zuwa suka amshi abicin suna farin ciki. Larai tace kaga yaron kirki irin albarka, kullum haka zaka rika fada idan kaje bara kaji? Kai ya daga mata. Barira tace naga Balki ta dade kode bata samu bane.
Larai tace aikin san yarinyar tawa akwai zafin nema, gashi akwaita da kawo abinci me dadi, kina ganin wani lokacin hada nama take kawowa, gaskiya mutanan gidan can duk da suna da kudi amma suna bata sadaka duk sanda taje bara.
Barira tace gaskiya kam Balki tana kawo medadi, semu kara jiranta ta zo mu canza unguwa kuma. Yarinyar da aka kira Balki ce ta fito daga wani gida me bakin gate se gyara daurin zani take tana washe baki. Hannunta rike da kwanon abinci hada nama.
Megadin gidan ne yadan leko yana washe baki yace maza kitafi kada wani yaganki, gobe ma idan kikazo zankara baki abinci me yawa kinji? Amma kada ki fadama kowa. Dariya Balki tayi wadda bazata wuce shekara 11 ba.
Tana zuwa Larai ta rungumeta tana dariya, Barira tace gaskiya yau Balki kinyi kasuwa, haka akeso kuruka dagewa kunji? Kai ta daga tana ta saka hannu cikin zani tana ya mutse fuska. Larai tace yunwa ko? Kutashi mucanza waje se muzauna muci, idan muka gama se akara nemowa.
Abinda basu sani ba shine gidan da Balki take zuwa bara ko mutanan gidan basu san tana zuwa ba, ada da taje megadin yake bata abinci idan yayi saura, daga baya kuma yafara janta dakinshi, haka zesa tayi ta mashi wasa da mazankutarshi harseya gamsu sannan.
Idan tagama yakawo abinci yabata, wani lokacin ma nashi yake bata duka seyace ma mutanan gidan ansace ko ya zube, ko kuma yasa kudinshi yasayi wani. Ayau datazo bayan tagama mashi abinda take mashi shima yafara wasa da ita,hakan yasa taje take ya mutsa fuska saboda zafin da takeji.
Kowa yasan Idi megadi a kauyensu dake Kanda yasan dan iska ne, yaran gidan ma saboda sunada wayau yasa ya hadiye zalamarshi, amma har masu talla be kyale ba, sede acikin gidan babu wanda yasan abinda yakeyi, kasancewar irin gidan nan ne da basu cika fitowa waje ba.
**** ****
Wata motace ta iso bakin gate din wani babban gida tana ta horn amma ba'a bude ba. Da sauri megadin yafito daga bandaki jikinshi yana rawa yaje ya bude. Bayan motar tashiga gate din kafin megadin ya kulle Nazeeru da Shattima sukayi saurin shiga.
Sam megadin be kula dasu ba, kasancewarshi ya manyanta hakan yasa baya aiki da sauri. Murya suka bude suka fara Bara, agigice megadin yajuyo jin muryar Almajirai acikin gidan.
Wani babban mutumi ne yafito daga cikin motar fuskarshi a daure, fitowarshi tayi dede da fitowar matarshi da wata budurwa, suma jin sautin bara ne yasa suka fito. Nazeeru da yayi saurin kama Shattima dan ya tsorata da yanayin fuskar mutumin ganin ya nufosu.
Saurin juyawa Nazeeru yayi tare da kama Shattima dan gaba daya tsoro ya kamashi. Tsawa Alhajin ya daka masu hakan yasa suka tsaya. Karasowa yayi kusa dasu, ko ganin girman megadin beyi ba ya rufeshi da fada.
Inda sabo megadin ya saba da masifar megidanshi, saboda babu abinda ya tsana irin ayi mashi bara koda akofar gidanshi ne, se gashi yau har cikin gida aka shigo. Alhaji yace haba Malan Abu, so nawa zan fada maka banason Mabarata surika shigo mani gida? Ko harabar gidannan banaso narika ganinsu amma yau har cikin gida zaka barsu su shigo.
Cikin rawar murya megadin yace kayi hakuri yallabai wallahi banga lokacin da suka shigo bane, kuma da alama wadannan bakine ayi hakuri baza'a sake ba. Hajiyar ce tace kaima de Malan Abu, wannan aikin yafara fin karfinka anyi anyi da kai ka hakura a samu wani saboda bakada lafiya sosai ga jikin girma.
Risnawa megadin yayi yace ayi hakuri Hajiya ina samu da wannan aikin idan na barshi zanshiga damuwa. Tsaki yarinyar tayi tace kai dalla kufita kubar gidannan, idan kuka kara zuwa ko kofar gidan nan ne senasa an zaneku.
Ubanwa yace Iyayenku basu rikeku a wajensu ba zasu turo mana ku kurika hanamu sakewa, kalleku, ya kamata ace kuna gaban iyayenku amma saboda basu san darajarku ba ko wayon kirki bakudashi amma suka kawoku ALMAJIRANCI.
Cikin tsawa Alhajin yace kubace mani daga gida, wannan gidan ba irin gidajen da kuka saba shiga bane, idan na kara ganinku anan senasa an kulle ku, kunci sa'a ma bakuda wayau da sena zaneku sannan zakufita.
Cikin kuka suka bar gidan. Seda Alhaji yakara jama megadi kunne ya kuma tabbatar mashi idan yakara ganin Mabarata a harabar gidanshi abakin aikinshi. Megadi yace insha Allah baza'a kara ba. Alhaji yace ai laifinka ne.
Kodan kana ganinsu irinka shiyasa baka iya dukansu, nafiso na samu megadin da zerika zama a wajen gida da katuwar bulala duk wanda yagani ya rabi katangar gidana yayi mashi dukan mutuwa, gobe idan akace yadawo baze kara zuwa ba.
Amma naga kai kana tausayinsu kila kaima cikin 'Ya'yanka akwai wadanda ka kai ALMAJIRANCI a wani waje ko? Dukar da kai Megadi yayi sosai ranshi ya baci da maganganun Alhaji, duk da ya saba da jin magana marar dadi agidan amma ayau ranshi ya baci.
Juyawa Alhaji yayi ya mikama Hajiya jakarshi suka shige ciki suna kumfan baki. Zama Megadin yayi ya buga tagumi. Da ace idan yabar gidan nan ze samu wani aikin da tuni ya dade da barinshi.
Shi kanshi yasan ya manyanta idan yabar wannan aikin da kyar wani ze daukeshi aikin gadin saboda mutane basa son tsoho, kuma shi yanzu yanajin dadin aikin gidan nan, saboda bude gate da rufewa kadai yakeyi.
Gashi yana samun kudinshi akan lokaci, kuma yana cin abinci ya koshi shiyasa yake hakuri da duk abinda ake mashi dan mutanan gidan basa girmamashi.
Su Nazeeru da Shattima kuwa suna fita suka saka gudu, basu tsaya ko'ina ba seda sukayi nesa da gidan sosai, kasan wata bishiya suka zauna, Nazeeru ya kifa kanshi saman kafarshi yasaki wani irin kuka. Duk da beda shekaru masu yawa amma yasan hantara da wulakanci.
Dukawa Shattima yayi yana bashi hakuri. Sosai Nazeeru yaji haushin abinda akayi masu.
***** *****
Alhaji Bashir wani hamshakin me kudi ne, yana zaune a cikin garin Daura, inda yake zaune a unguwar Fegi shida Matarshi me suna Hajiya Zinatu, da yaransu 3. Babbar ciki itace Kausar, ta gama Danfodio sokoto.
Se kannanta Baffa da Nafisa, Baffa yana F.G.C Daura SS1 sede yace shi boarding yakeso hakan yasa aka barshi, amma Nafisa Day takeyi inda take JSS 2. Alhaji Bashir mutum ne me masifar son iyalanshi, sam baya son talaka hakan yasa baya shiri da Mabarata.
Almajiran da suke kusa da su babu wanda besan halinshi ba, hakan yasa basa zuwa gidanshi Bara, ayauma Nazeeru da Shattima yawo ne ya kaisu unguwar tsautsayi yasa suka shiga.
Halinshi daya da Matarshi da Kausar hakan yasa suke zaune lafiya, sam Alhaji beda temako, idan kaga ya bada sadaka to Ramadan ne yazo, sam beda tausayin nakasa dashi.
Yana matukar son kudinshi, dalilin da yasa yake dagama Megadinshi kafa saboda sun dade dashi, a kalla sunyi shekaru 15 tare hakan yasa yake kyaleshi da tuni ya canza wani.
Duk ranar da yadawo ya samu Mabarata a kofar gidanshi duk mutanan unguwar se sunjishi, haka kuma Megadi ya shiga 3 aranar. Hajiya Zinatu ma bata kaunar talaka, shiyasa ko sadaka itama bata badawa.
Da su bada sadaka gara abinci ya lalace azubar, meyi masu aiki kanta idan kaga ta tafi da abinci gida to wanda yafara lalacewa ne, dan Hajiya akwaita da son abin duniya, da ka ganta kasan bata gaji arziki ba.
Kullum cikin kididdige abincin da me aiki zata dafa take, sam bata bari adafa abinci da yawa, wani lokacin ma sede me aikin ta kankare kanzo ta kaima yaranta domin dede wanda zataci ake bata. Da Hajiya taga abincin yana kanzo seta hauta da fada tana fadin tana barin abinci yana kanzo idan bata gyaraba zata sake wata.
Haka me aikinta take zaman hakuri da ita, saboda tasan samun aiki yanzu yana wahala, dadinta daya tana samun albashinta akan lokaci, kuma abinci ana cika mata robar datake ci.
Sede wulakanci kala kala tana ganinshi. Nafisa ce kawai take darajasu ita da Baffa, amma Kausar babu sauki, Allah yayita da jin kai.
Wannan shine labarin gidan Alhaji Bashir.
Bayan Nazeeru yagama kukanshi yakama Shattima yace mutafi makaranta kaga munzo anyi mana fada kuma yace ze zanemu, bazamu kara zuwa bara agida me kyau ba. Shattima yace gaskiya bazamu kara zuwa gidan nan ba. Nazeeru yace ai kuma Allah ze saka mana.
Shattima yace nide gida zan koma kaga Malan baya kula dani kamar yanda Baba yace. Nazeeru yace kayi hakuri Anas yace duk wanda yazo guduwa aka kamashi dukanshi akeyi.
Shattima yace to kai se yaushe zakaje wajen Babanka? Nazeeru yace aini Babana da Mamana duk an rufesu arami, kuma garinmu akwai nisa bazan iya zuwa ba. Amma Malan yace inzauna anan wata rana zan zama Babba. Kuma nasan Abba na binni wata rana zezo wajena.
Shattima yace idan kazama Babba nima zaka maidani gida ko? Nazeeru yace sosai ma, kuma nima har gidanku zanje. Murmushi Shattima yayi yace nagode. Nazeeru yace mutafi nasan Anas yadawo yana jiranmu.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
ALMAJIRAI MA 'YA'YA NE


Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
[email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey
Chapter 1 · 0% Book details