← Book details Sawun Giwa Part 9 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 5

Sashe 5

Sawun Giwa Part 9 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Dan Allah mudena dagewa akan ra'ayinmu garayuwar yaranmu domin kuwa yadda muke da hakki akansu suma sunada hakki akanmu kuma sunada nasu ra'ayin kamar yadda muke dashi, kuyi dubada abbey dakuma yah jawal, dudda cewar Allah ya hukunta cewar zainab ba matarshi bace, amma har abada baya kallon hakan akullun dubin zasuyi abbey ne yashiga tsakanin soyayyar su wanda har yayi sanadin kinyin auren ɗan ƙanenshi amma ita tashi ƴar tayi auren wanda inba'akai zuciya nesaba akayi yaƙi da sheɗan wannan al'amarin ze iya shiga tsakanin zumuncinsu har wata hatsa niyar yabiyo baya, dan Allah mukiyaye muriƙe girmanmu musani iya kacinmu da ƴaƴanmu addu'a dakuma nasiha akai idan suka karkace amma mudena yimusu shishigi a rayuwarsu wanda muma Bama Fatar amana, Allah yasa mudace 🤲

Shekaru dayawa sunja abubuwa nata sauyawa, tsakanin maisoon da sheikh sudais kuwa sedai muce Allah yaƙara kauce musu da sheɗan tsakaninsu hakama duka sauran ma auratan, rayuwa tayi musu daɗi sedai sam barka dama duk wani tsanani yana tareda sauƙi kuma kowacce rayuwa danada nata ƙalu banen domin kuwa kursum nacan na fuskartar nata aƙasar Ghana, sedai Allah ya kyauta..... wannan family guda ukku sunkoma tamkar family ɗaya, family su maisoon family sarki Muhammad bilal, family sarki Hassan, abin gwanin birgewa, sedai Fatar Allah yaƙara haɗa kansu..!

TAMMATBIHAMDILLAH

anan nakawo ƙarshen wannan labari metaken SAWUN GIWA kuskure danayi aciki Allah ya yafe mun inda nayi dede kuma Allah yasa mu anfana dashi..

Daga ƙarshe iname baku haƙuri abisa jikirin da wannan book yasamu kafin mu kammalashi, wlh banida lafiya ne sedai ina ɓoyewa ne domin bazeyu kullun kace bakada lafiya ba idan wani ya yarda wani tunanin zeyi rena musu hankali kakeyi amma dan Allah kuyi haƙuri.

Dan Allah kutayi da addu'a Allah yabani lafiya domin seda ita ake komai. Ngd sosai sosai da soyayyarku gareni Allah yabar zumunci 🤝

Autar alheri ✍️
Chapter 5 · 0% Book details