← Book details Sawun Giwa Part 9 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 5

Sashe 3

Sawun Giwa Part 9 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acikin wannan lokacin cikin maisoon yazama ko ƙaƙa abin se wanda yagani gabaki ɗaya tafita kamanninta kuma gaya hartana neman shanye watannin haihuwarta amma bata haihuba, hankalin gimbiya Rumaah, memartaba har sheikh sudais dukkansu atashe yake, hakama gimbiya zaitun da basam kebawa labarin abinda ke faruwa....yau tana zaune a pert ɗin gimbiya Rumaah wasu hadimai su biyu namata tausar kafarta, yayinda gimbiya Rumaah ke kitchen dakanta tana yiwa maisoon ɗin haɗin zogale da cocumber domin shine kawai abin cinta ayanzu. Mararta taji tana murɗa mata sosai sedai tadake batace komaiba sabida tasabayin irin wannan ciyon marar tun cikinta na wata bakwai, dudda tanajin wannan kamar yabanbanta da saura, kusan minti 3 takarajin wani wanda yazo mata duka tareda ciyon tsara lokaci ɗaya bayanta yarinƙa wani irin sara nafitar hankali kamar zerabata biyu, runtse idonta tayi daƙarfi tareda cije bakinta tana salati hakan ya ankarar da hadiman datake tare dasu, cikin sauri suka shiga jera mata sannu yayinda ɗayar taruga kitchen domin sanarwa da gimbiya Rumaah abinda ke faruwa, ɗayar kuma ta tsaya jin maisoon ta damƙi hannunta daƙarfi tana anbaton Sunan Allah. Acan kuwa wannan hafimar na sanarda gimbiya Rumaah abinda ke faruwa a parlor suka dawo karaya domin ganin halinda maisoon ɗin take ciki, sedai me? Sawo kansu parlor yayi dede da faɗowar baby cikin iyawar Allah da buwayarsa yana tsadara kuka, ai dasauri suka ƙaraso cikin tsananin mamaki da farin ciki

Gimbiya Rumaah taɗauke baby boy ɗin kyakkyawan gaske me tsananin Kamada sheikh sudais kamar antsaga ƙara, kana tadubi maisoon domin tayi mata sannu setaga wani nishin takeyi cikin azaba, dasauri tamiƙawa hadimar babyn hannunta kana tariƙe maisoon ɗin tana mata sannu har idonta sun cika da kallah sabida tausayinta, aiko bata ɗauki wani lokacin ba taƙara haifo wani babyn shiba boy kamar wancan bawani banbanci. Wata irin kabbara gimbiya Rumaah tasaki tana ɗaga yaron sama kana tana kallon na hannun wannan hadimar kuma tajuya ta kalli Maisoon se kawai tasaka kuka, akuma Dede wannan lokacin sheikh sudais yafaɗo parlor kamai wanda aka turo...!

Autar alheri ✍️

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 5

Page 97 & 98

"Ido yazaro ganin jinjiri ahannun mahaifiyar shi gakuma wani a hannun hadima fuwa, cikin tsananin mamaki yake binsu da kallo kafin yasamu zarafin yaƙarasowa tsakiyar parlor bakinshi na rawa amma yakasa furta koda lalima ɗaya binsu kawai yakeyi da ido...seda maisoon tayi saurin riƙo hannunshi ganin kamar yashiga shuck tukkunna yajiyo se kawai yarungumeta tsam ajikinshi batareda yadamu da yadda takeba cikin rawar murya yake maimaita alhamdulillah bini imati rabbi, alhamdulillah, alhamdulillah ya rabbi kafin kuma yaɗagota yana kallo sekuma yaƙara maidata yana murmushi tareda share ƙwallar idonshi. Gimbiya Rumaah ma kukan takeyi tareda dariya lokaci ɗaya. "My butti duk waƴannan yarana ne ? My butti twins fa ohhh yah Allah alhamdulillah. "Itadai maisoon kallonsu kawai takeyi tana murmushi kafin tabuɗe baki ahankali tace "my sheikh kacirewa babys dinki mabiyiya mana, inaso natashi, tayi maganar tana ƙara matse hannunshi cikin nata. Se a lokacinma hankalinshi yakaiga babys ɗin dase wutsil wutsil sukeyi domin ko gimbiya Rumaah farin ciki yahanata cewa komai balle tasamu zarafin aikata wani abun...cikin sauri yamiƙe yanufi pert ɗinshi kamar ze tashi sama, ko minti ɗaya beyida fitaba yadawo da kayanda suka ajiye gida domin irin wannan lalurar, aiko cikin gwaninta ga aikinshi ya yanke musu uwar tafiyar kana yasaka hannu yaɗauki matarshi kamar ya ɗauki baby yanufi bedroom ɗin gimbiya Rumaah da ita, ruwan zafi yahaɗa dakanshi yate maka mata tayi wankan bayan ya fidda mata duk jinin dake mararta, sa'annan yariƙota suka fito, hakan yaƙara komawa pert ɗinsu yaɗauko mata kayan sakawa, sedai dayazo wucewa parlor gimbiya Rumaah yayi mamakin rashin ganinta itada babys ɗin domin har angyara wurin kamar ba'ananne aka haihuba,,,,Hakan yakaiwa Maisoon kayanta tasaka tareda temakonshi kana yazo yahaɗa mata tea me zafi yabata tasha, yanayi yana mata sannu cikin begen sonta da ƙaunarta domin jiyakeyi tamkar yahaɗiye ta yaƙara haifota sabida tsananin sonta da Farin cikin dayake ciki.

Gimbiya Rumaah kuwa pert ɗin memartaba sarki Muhammad bilal tanufa da baby's ɗin jikina rawa tashiga gyaransu acan...shikanshi memartaba daya ganta da baby's seda yayi mamaki, amma jin matar sheikh sudais ce ta haihu wannan abin baƙaramin Farin ciki yasakashiba, Sega gudan sarki ana shirin baby's dashi.😂

Cikin lokaci kaÉ—an gimbiya Rumaah tagama shirya yaran kana tayi musu shimfiÉ—a kusan sarki Muhammad bilal

Itama ta zauna suka zubawa yaran ido kawai suna kallah suna murna sam sunƙi ma fatitowa dasu balle wani yasamu yagani😂 acan pert ɗin gimbiya Rumaah kuwa sheikh sudais yakasa ya tsare akan matarsa wani irin kulawa yake bata ta musamman seda yaga tafito tass kamar ba itace ta haihuba kana yanutsu yashiga kiran ammin shi yagaya mata wato gimbiya zaitun...aiko zukuga murna gunta abin ba'acewa komai domin aranar tayi shirin zuwa Dubai...bayan yasanarda itace yakira yah jawal dakanshi yasanar mishi da haihuwar maisoon...aiko yayi mutukar farin ciki ananne yake sheda mishi suma suna asibiti yanzu Aisha ta haihu itama ta haifi ɗa namiji. "Masha allah alhamdulillah shine abinda yafito daga bakin sheikh sudais yana girmama uban giji me kyauta da ƙari..anan yah jawal yashiga sanarda family nasu wannan abin farin cikin, kai gaskiya faɗin farin cikin da wannan ahalin keciki ɓata lokacine, mom kam dataji labarin haihuwar autar tata har kukan farin ciki itama seda tayi.

Maisoon kuwa dataji Aisha ta haihu tuburewa sheikh sudais tayi akan cewar dole seya kawota Nigeria anyi musu bikin suna tare itada Aisha daƙyar yasamu ya lallaɓata tadena rigimar shima dayace mata anan za'azo da Aisha ayi musu bikin tare.

Su iyayen yara kam dasukaji kasa zama sukayi balle tsayi cikin ƙanen lokaci yarima basam yacika pert ɗinsu dakayan babys ɗinshi kamar za'a buɗe wani shagon, hakama talal abokin sheikh sudais shima yabaza tashi rawar....da yamma jirgin daya ɗauko gimbiya zaitun tareda memartaba sarki Hassan yasauka kuma nasu na sauka wanda ya ɗauko yarima junaid da anty meenah ma yasauka domin sam yarima junaid besan cewar aranar iyayen nashi zasuzoba da ababu abinda zesa suyi tafiyar daban daban,,,,ita kuwa anty meenah shine dakanshi yaje gidanta yace tazo sutafi domin kuwa yasan idan itace kaɗai zata tafi bazeyu tasamu viser ranar ba, shiyasa yajanyota koba komai anty gimbiya zataga yayarta akusa da ita, ahakan motocinsu sukabar filin jirgin suka nufi masauta.

Lokacinda da maisoon taga anty meenah baƙaramin daɗi tajiba hakan suka baje nan pert ɗin gimbiya Rumaah daga ita har su gimbiya zaitun suna Sha'anin farin cikinsu domin kuwa basajin kunyar iyayen mijin nata sabida su basu ɗauketa surukaba, gimbiya Rumaah da gimbiya zaitun wata irin kulawa suke bawa maisoon ta musamman koyaya tamotsa zasuce minene?

Haihuwa da kwana biyu mutanen Nigeria suka sauka Dubai aiko maisoon ta tasawa sheikh sudais sabuwar rigima ganin bada Aisha akazoba, daga yah fawan sesu mama da anty zainab sekuma abban yah fawan😂

Shikam ganin abin nata dagaske ne yasa yaje pert ɗin memartaba sarki Muhammad bilal yasanar mishi tareda cewa yariƙi abbey akan yabari aɗauko Aisha... murmushi memartaba yayi kana yace "sheikh ɗin abbey wannan matsalarku ne kaida matarka sabida hakan kakirashi dakanka, ba yadda beyida memartaba ba akan yakira abbey amma yaki, shikuwa yayi hakanne sabida shi sheikh sudais ɗin yakira abbey dakanshi domin susamu kusanshi sosai da iyayen matarshi.

Aiko hakan dayayi andace domin kuwa ba yadda sheikh sudais ya iya hakan dole yakira abbey, bayan yagaisardashi cikin mutuntawa ne yasanardashi bukatarshi tason akawo Aisha domin suyi biki atare... murmushi kawai abbey yayi domin kobe tambayaba yasan rigimar maisoon ce amma baze hanaba kodan ganin cewar ita isha batasan ɗakin maisoon ba, hakan yasa yacewa sheikh sudais badamuwa su awurinsu amma zasu gayawa mijinta idan ya amince shikenan Allah yasa ayi lpy aƙare lpy.. ameen ameen sheikh sudais ya amsa kana sukayi sallama aranshi yana addu'ar Allah yasa mijin aishar ya amince....shikuwa abbey bayan sungama waya da sheikh sudais yakira yah muhseen yafaɗa mishi buƙatar mijin ƙanwar tashi domin yaji mizece...to abinda abbey besaniba itama Aishar rigima takeyiwa yah muhseen akan cewar seya Kaita taga yaran maisoon ko amaidoda maisoon ɗin gida, shiyasa yanajin zancen abbey yayi hamdala aranshi kana yace "badamuwa abbey zamu shirya tafiya in sha Allah.

Tofa acikin kwana biyu suka gama komai natafiya inda aka tafi duka family kowa ba'abariba bancin dady da abbey sukam cewa sukayi bazasujeba...misalin ƙarfe 5 na yamma jirginsu ya sauka ƙasar abu dabit wato Dubai, sheikh sudais dakanshi yazo tarbarsu shida mukarrabanshi kuma ƙennenshi yarima junaid da yarima basam sekuma amininshi talal, cikin farin ciki da mutuntawa yatarbesu inda suka rungume juna shiga yah muhseen harsu yah jafar, cikin farin ciki dajin daɗi ganin ahalin matarshi dakuma karamcinsu gareshi. Hakan suka ɗunguma zuwa masarautar kusan mota goma sha shida suna tafe ana musu jiniya abin gwanin birgewa... lokacinda suka sauka masauratar maisoon na zaune a parlor itada duka iyayen nasu dasu anty meenah. Da mamaki gimbiya Rumaah ta kalli hadima fuwa tace "fuwa baƙi mukayi agidan ne? "Kanta a ƙasa tace "aa ranki yadaɗe inaga yallaɓai sheikh ne yadawo tareda su yarima domin sune suka fita ɗazu damotoci dayawa. "Tofa sheikh dabayasan fitada mota samada ukku shine yau da wannan motocin to ina yaje hakan? Kafin hadima fuwa tayi magana yarima junaid yashigo parlor dasauri ko sallama beyiba yace "anty gimbiya albashir... dasauri maisoon ta kalleshi sedai kafin tayi magana sukaji sallamar mutane dayawa sun shigo parlor, ido tazaro tareda miƙewa tsaye daƙarfi tana faɗar.....!

Autar alheri ✍️

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 5

Page 99 & 100
Chapter 3 · 0% Book details