← Book details Riqon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 8

CHAPTER 25

Riqon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Abubakar ya zama bai da :abokin hirar da ~ya
wuce t.v sai' kuma tunanin RuKayya wanda yake
kwana dashi ya kuma tashi da shi wannan ita ce
rayuwar Abubakar a sabon gidansa. Satin
Abubaka biyu ya kasa daurewa ' ya nufo
Dandagoro bayan ya sha jinyahar ta tsawon
kwana uku’, shi kadai babu wanda ya sani, duk
'wanda ya. kalle shi a yanzu zai fahimci halin da
yake ciki saboda irin ramar da yayi ya zama
kuma wani (so silent) kamar ba
shi ba.
Lokacin da ya iso gidan Kaka bata nan 'sai dai
Lami_ wadda ke ta darzar ’wanki, Abubakar yaja
kujera 'yar tsugunne ya zauna a gajiye kamar
wanda yasha gasar tseren gudu ya gaji. Ya
gaishe da Lami cikin sakin fuska, La‘mi ta amsa
cike da, tausayin Abubakar din yanda yabi ya
zabge kamar bashi. ba, ita dai daukar alhakin
yaron ya isheta haka. Ta zauna akan kujerar da
take wankin akai tana kallon Abubakar dinda yake
tambayarta k0 Rukayyar
ta dawo?
Lami ta sassauta murya kamar mai tsoron wani
ya jiyota, tace. "bata dawo ba, sai dai k0 in fada
maka
inda take". Abubakar ji yayi tamkar ta tsunduma
Shi
cikin gidan aljannah, don tun kafin ta fada mashi
ya soma jero mata ruwan godiya. Ai tana fadi
mashi tana Bakori gidan qanin“ mahaifinta tsam
ya mike yai mata kyauta mai tsoka ya fice ya
fada motarshi, kai tsaye ya dau hanyar‘ Bakori,
bayan ‘ya tsaya gidan man Dandhgoro ya shake
tankin motarshi taf da mai
,,,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,,,,,
Bakori gidan qanin mahaifin Rukayya ne marigayi,
uWarsu daya ubansu daya, yana zaune a
gidanSa_ shi da matansa guda ukuTasallah,
Lantana da kuma‘ amaryar su Larai. Yana da'
ya' ya a qalla sun kai ishirin da wani abu, wasu
sunyi aure wasu kuma basu yi ba, suna nan mata
da maza.
zuwan Rukayya garin ba qaramin mamaki ya
bawa Kowa ba, saboda tun Rukayya tana yarinya
suke son Kaka ta rinka: turota tana ganin 'yan
uwanta suna zumunci amma Kaka taqi, ita allan
kalafar bata yarda Jika tai nesa da ita ba, sai dai
ta dauketa suje su wuni tare su dawo. Wannan
ne: yasa ba wani zumunci mai qarfi ‘tsakanin
Rukayya da'yan uwanta.
Don haka yanzu da tayi aure tazo masu wannan
dogon zaman ba qaramin mamaki ya _ basu ba,
don haka sukai tunanin aurenta ne ya mutu.
Itama kuma ta tabatar musu da hakan.
‘ Kawu yaji haushi ba kadan ba, don ’ a ganinsa
irin hakan ceke sawa a guji auren zumunci don
gudun bata zumunci. ‘
Rukayya taji dadin zama a cikin kauyen
’saboda 'yan uwanta da kowa na son ace ' 'yar
gayun nan 'yar uwarshi ce hakan ne yasa har
rububinta ake a cikin yara da matasan gidan. ‘
“ Jamilu .yana daya daga‘cikin matasan " gidan‘
'yan gayu masu ji da karatun N.C.E,
wanda yana ganin Rukayya zuciyarshi ta ayyana
mashi ya samu matar aure irin wadda yake burin
aure, don haka ya yi kane-kane ya hana kowane
saurayi na gidan raBarta don gudun‘ kada ma
wani' yai masa shigar sauri..
Duk da bai furta son da baki ba amma aiyukanshi
sun nuna, don duk inda Ruqayya zata jeshi ne
mai kaita da sabon mashin dinshi Jincheng roba-
roba, a gidan har sun fara fahimtar inda ya dosa.
lnda ita kuma Rukayyar ‘ take daukar duk
zumunci ne kaWai;
A yanzu haka ta riga ta shirya komawa gida gobe
don haka yau shirye shiryen taflya _ kawai take,
tun safe suke yawo da Jamilu tana bankwana,
.zuwa yanzu haka gidan Mariya . zasu qanwar
.jamilu dake aurc cikin garin, amma basu samu
fita ba sai bayan sallar magariba. '
Tayi kyau sosoi cikin riga da siket na shadda
maroon colour, ta yane kanta da (milk) ’ din
mayafi mai Shara-Shara, sai dai yana da
dan girma ba Iaifi Ta Saka takalminta mai tsinin
dunduniya. ita kanta tasan tayi kyau balle Jamilu
da ya goyota saman mashin dinsa, sai yaba
kwalliyar yake tare da kwarzanta ta. ' ita k0 sai
dariya take mashi, don ta'san duk zolaya ce irin
tasa, don haka ta biye mashi suna ta kWasar
dariya. '
Suna qokarin hawa titi Abubakar na ‘ qokarin
shiga layin_ da suka baro, idanuwanshi sukai
tozali da su suna ta kwasar dariya, wani irin
gingimemen abu ya tokare mashi zuciya ~wanda
yasa saura kadan da motar ta kwace mashi. . " _
Ya taka wani mahaukacin birki wanda « yasa
qura ta tashiya juya kan motar yai a sukwane ya
rufa masu baya, ya bar jama'ar wurin na faman
atishawa tare da Allah Ya isa ga wanda bai ma
san sunayiba saboda an shiga haqKinsu kuma
hakan haramun né a Musulunci.
’Abubakar bai samu shan gaban su ba har sai da
suka sauka daga kan babban titi suka hau .
Karamin titi sannan ya samu nasarar shan
gabansu da mota, ya haske su da farin hasken
fililun motarsa
Jamilu ya ja birki a haukace, sannan ya soma
aunawa mai motar zagi. itama Rukayya ranta yai
masifar Baci, sai da Abubakar .ya gama qare
masu kallo suna ta kare-karen idanuwa tare da
zage-zage sannan ya bude motar ya fito.
' Tun kafin ya qaraso Jamilu da Rukayya suka
sakko daga kan mashin din suka kaucewa
. dogon hasken da_Abubakar ya haske su dashi.
Abubakar na qarasowa Jamilu ya cire hannu da
zummar ya mare shi, Abubakar‘ yai caraf da
hannun ya rike gam,’ muryarsa a sanyaye ya ce.
"Ina zakaje mani da mata?" Jamilu ya fincike
hannunshi cikin zafin zuciya yana fadar. ‘ ‘ "Uwar
wacc ce-matar taka?" .
‘ Abubakar ya nuna Ruqayya ' da danyatsanshi
manuni ba tare da yayi magana ba.
. Takaic'i , ’ya_ .kama Jamilu, ya haske. '
Abubakar da kallon banza kafin' ya ce.
"Lallai kai ka tabbata mahaukaci, qaramin ,dan
shaye-shaye. To k0 salansa kake sha qarewar
hayaqi ni na fika iskanci".
Abubakar ya ce, "Ai na lura tunda har ka
iya daukar matar aure" Haushin maganar
Abubakar ta kama
Jamilu har ya daga, murya yana nuna Abubakar
yana auna' mashi ashariya, abinda ma ya janyo
hankalin 'yan tsirarun mutane masu wucewa
kenan sukayo kansu tare da buqatar jin ba'asin
maganar Jamilu ne ke ta faman kora masu
jawabi '
cikin bacin _rai, sai da'aka gama sauraronsa
‘sannan aka ,bukaci jin ta bakin Abubakar wanda
ya harde hannuwa a 'Kirji yana kallon su' daya
bayan daya. Ya maida kallonsa akan '
Rukayya,yace ita ya kamata ku tambaya, gata
nan".
. Jamilu ya dubi Rukayya yana rawar haBa, ya
ce. ’ "Ai ni nasan wallahi bata sanshi ba, irin
yan iskan gari ne kawai, k0 kin sanshi Rukayya?"
Sai data tabe baki kafin ta ce
"Ni ban sanshi ba". Ai kuwa jama'a kamar jira
suke aka
hayayyakowa abubakar, don Jamilu qarfin hali ma
har kwalar rigar Abubakar yake ciyowa wai a
duke shi. Ai kafin ma ya cire hannun nashi daga
kan kwalar abubakar ya dunkule yatsun
”hannunshi ya kai mashi ‘wani dan marayan
naushi a mahagurba, yai wani irin ihu ya dafe
wurin da tuni ya baci da jini.
Abubakar ya qara mika hannu ya cakumo shi
yana Kokarin sake narka mashi wani naushin
jama'a suka tattare masu zakalkalewar ciki suka
dawo neman sasanci naya saki wuyan rigar
Jamilun, amma babu alamar zai saki din duk da
idanuwan Jamilu da suka
yo warwaje yana ta kakarin wahalar Majiya masu
qarfin ciki ne suka fara qokarin bambare hannun
Abubakar din, amma k0
gezau bai yi ba, don haka aka soma rokonsa da
ya sake shi din '
Bai saurare su ba ya maida kallonshi akan
Rukayya dake tSaye tana ta rawar haBa tare da
rarraba na mujiya, ya daka mata tsawa.
"Yanzu kin sanni k0 sai na kashe: shi
tukunna za ki sanni?" ‘ Rukayya jiki ya dauki ciri,
muryarta na rawa ta ce ‘
"Idan na sanka sai me? Ina ruwana da kai?
Mugu, azzalumi kawai, wallahi Allah sai
. Yai mana sakayya". Abubakar yayi wani
malalacin murmushi‘
sannan ya saki Jamilun .yana fadar.
’ "To kaji k0 ni wane ne a wurinta, mijinta
ne data gudo ta bari kuma kaine baka sanni ba
amma ni na sanka shi yasa ma tun farko ban yi
niyyar taBa lafiyar jikinka ba, kaine kaja da
taurin kai irin naka, amma kayi hakuri". Jamilu ya
rasa abinda zaice sai faman
mazUrai yake Abubakar ya ”tura ‘hannu cikin
aljihu ya damtso kudi mai yawa ya soke mashi
cikin aljihu yana fadar.
ga wannan‘ ka rage zafi".
Bai bari yace'wani abu ba ya damki hannun
Ruqayya tana turjewa tare da borin kwacewa
haka yaja ta da qarfi ya sakata a mota ya rufe ya
zagaya ya shiga mazaunin dirrba yaja suka tafi.
Kai tsaye gidan Kawu ya nufa ya kulle Rukayya a
motar shi kuma. ya nufi cikin gidan, saukinta ma
akwai AC a ciki daya kasheta.
da zafi
‘ A zaure ya samu kawu a kwance yana sauraren
rediyo, Abubakar ya durkusa a gabansa suka
gaisa. Bai gane Abubakar dinba sai da yai mashi
bayani sannan ya shaida shi. Nan fa Abubakar ya
sanar da shi duk abinda ke faruwa tun daga
dalilin barin Ruqayya gidanshi.
har zuwa yanzu. Mamaki ya kama Kawu ya rinqa
zuba
sallallami yana fada akan danyen hukuncin Kaka
da kuma wautar Jamilu, daga,qarshe yaiwa
Abubakar naisha da kuma fatan' alkhairi. Yasa ya
kira Rukayyar itama yai mata nasiha sosai
Ya so su kwans sai gobe su juya, amma
Abubakar ya ce a‘a, saboda zai je office.goben.
Kawu yasa RuKayya ta kwaso kayanta,“ ya
zubaSU mota sannan sukai gaba bayan yaima
kawu kyautan kudi masu yawa sannan suka
kama. hanya babu wanda ya kula wani, Ruqayya
ta gaji da kukanta har tai shiru. Bai ce mata ci
kanki ba har burci barawo yai awon gaba da ita
Basu iso Katsina ba sai karfe goma .saura 'da
yan mintina, maigadi ya bude_ mushi qofa ya
kutsa .motarshi a ciki kai tsaye gurin ajiye motoci
ya faka motar tashi sannan ya fito a gajiye yake
likis dan da kyar ma yake iya daga. kafa ya
budema Rukayya dake Zaune yana kokarin kaukar
ta ta farka a tsorace
gami da ture hannayen nasa Ya yi murmushi
sannan ya matsa yana fadar ., . ‘ "Ki fito mun.
iso" Ruqayya ta bata fuska tana fadar:
Ni wallahi bahu inda zan matsa ‘sai ’ka . maidani
gaban uwata
Abubakar yai dariya“ sosai kafin yace
”Wacece uwar taki kuma? Kidai ce kakarki me
sangartar dake, kuma yarinya ke da qara ganinta
qila sai kin koma wankan jego“ Rukayya ta
harare-shi tare da tabe mashi baki ta dauke
kanta ta turo mashi qeya.
Shi daria ta bashi don haka bata ga lokacin da ya
janyo hannunta ba sai dai ji tayi an sureta gaba
daya anyo waje da ita ; ‘
Rukayya ta soma shure~shure tana zillewa amma
bata kufce daga hannuwansa ba har$ai da ya
danganata da katafaren falon gidan wanda wurin
zilIe-zillenta tasa suka fadi akan‘tayils, amma duk
da haka nan bai saketa .ba, tana cikin
hannuwansa sai da ta gartsa mashi cizo a
hannuwan sannan ya sakcta ita kuma ta zabura
ta mike ta” kwasa aguje 'ta barshi, falon,
amma‘sai ta kasa bude qofar a bude take ba kcy
aka Saka ba k0 sakata ba amma ta datse Haushi
ya kama Ruqayya, ta rinqa jijjiga qofar da ko
gezau bata yi.
Abubakar yana kallonla ya mike yana dariya yai
shigewarsa kicin hankalinsa a
kwance
Hmmmm lol jama,a wai ya za,a kwashe da
kakalle ne idan har taji labarin habu yaje ya
dauke matarsa?
naku har kullum A,I,S KE CEWA i luv y'll
cont it
RIKON KAKA
Chapter 4 · 0% Book details