← Book details Riqon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 8

CHAPTER 24

Riqon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Abubakar ya amsa da, "Insha Allahu". Sannan
sukai sallama da Alhaji ya tafi abinsa cike da
qarrfin gwiwa ya dauki mota ya nufi Dandagoro
zuciyarsa cike da addu'a tare da fatan samun kan
Kaka ta bashi matarsa k0 ya samu natsuwar
zuciyarshi.
Karfe tara na dare ya iso qofar gidan Kaka, ya
faka motarshi ya’fito ya kukkulle' qofar motar,
sannan ya ‘nufi .cikin gidan ”zuciyarshi cike da
fargaba ya . soma jera sallama. Daga daki ya jiyo
muryar Kaka na
amsawa, don haka ya nufi dakin kai tsaye yana ta
faman addu‘a a zuciyarshi. Ya yaye labulen‘ dakin
ya shiga Kaka na daga kwance da hasken wutan
lantarki
Ya durqusa daga bakin qofa yana gaishe daKaka
cikin girmamawa-, tamkar babu abinda. ya faru,
ta amsa mashi cikin sakin fuska, abinda ya fara
bashi mamaki kenan wanda ya. sashi tantamar
anya kuWa Rukayya tana gidan‘.’
' Gabanshi ya yanke ya fadi,yaja daga
tsugun0n da yayi ya zauna yana kallon Kaka ya
ce
‘ "Harkun kwanta kenan?" Kaka ta ce, "To me
muke jira?" Ya danyi jim yana ta sakesake a
.zuciyarshi, so yake kawai Kaka ta tare shi da
maganar Rukayyar amma tai burus ta share shi,
abinda ya Kara sashi cikin rudani kenan, ya rinka
waige-waige cikin dakin, babu ta inda ya hangi
alamarta. '
Wata zufa ce ta soma keto mashi da yaga ya
share fiye da minti talatin a zaune, ita Kaka ma
tuni har ta soma barcinta. Ba yanda ya. iya
shima haka ya mike ya fice jikinsa a kasale bai
‘xo da Shirin kWana garin ba, amma kuma yanzu
baiga ta tafiya ba ina zai sa kanshi yanzu ’ idan
aka ce Rukayya ta Bace?
Sai da ya leka (toilet) yaga babu kowa a _ciki
sannan ya wuce‘ tsohon dakinsa ya budc ya
shigé ya kwanta akah katifarsa, babu alamar
barci a cikin idanuwansa haka yaita juyi shi kadai
a cikin daki daga qarshe kuma ya mike yaje‘ya
‘dauro alwala ya dawo dakinsa yaita . jero
nafilfili: yana addu'ar Allah Ya bayyana
mashi ruky
Bangaren Rukayya kuwa tunda ta jiyo muryar
Abubakar yana sallama ta wantsara ta. fada
bayan gado tai kwanciyarta, tana jinshi ya qaraci
zamansa har ya fice sannan ta mike ta haye kan
gadon tai kwanciyarta.
Washegari misalin qarfe. takwas Abubakar ya
gama shirin tafiya (office) ya shiga dakin 'Kaka
da niyyar yai ma Kaka sallama,‘ akai sa'a
Rukayya tana kewaye tana watsa ruwa, saboda
wankan safen da ya riga ya kama mata jiki, don
haka har ya gama yiwa ‘ ,Kaka sallama ya filo ya
hau motatsa ya tafi
bata sani ba. ~
A moto Abubakar ya rasa abinda ke
mashi dadi, ya shiga cikin matukar damuwa da
tashin hankali Tabbas ya sani Rukayya bata
gidan Kaka, to ina ta tafi? To kuma idan har bata
'zo gidan ba ya akai Kaka bata tambaye shi
.yaya Jika ba? Sannan bata tambaye shi yaushe
ya dawo daga tafiyar shekara daya da rabin daya
tafi ba, da kuma bata daure mashi ba ta ‘ :karbe
shifaran-faran anya kuwa babu wata
maqarqashiyar da Kaka ta :shirya masa‘? ldan
kuma akwai ta yaya zai iya ganewa tunda bata
bashi fuskar hakan ba? Da wannan tunae tunanen
har ya iso (office) dinsa zuciyarsa babu dadi duk
ya fita hayyacinsa. Shi ji ma yake tamkar bai da
lafiya, saboda da qyar yake iya jan qafafuwansa,
sai kace mai ciwon lakka kwatakwata bai da
kuzari a jikinsa.
Cikin kwana uku duk inda Abubakar yasan
Rukayya zata iya zuwa sai da yaje ya nemota,
amma bai sa meta ba gaba daya ya zabge ya fita
hayyacinsa, shi baima san zuciyarshi ta kamu da
son Rukayyar ba sai *yanzu data kufce mashi,
don haka washegardi safiyar.juma'a yana tashi.
daga (office). Karfe hudu ya nufo dandagoro
gidan Kaka, ya yanke :‘shawarar zai sanar da ita
kawai tunda barin kashi a ciki baya maganin
yunwa. . ‘ Da sallamarsa ya shiga cikin gidan
babu kowa a. tsakar gidan sai Lami mai aiki tana
“wanke a’laiyyahu a bakin famfo sai da ya gaisa
da ita sannan ya wuce dakin Kaka kai tsaye inda
yake jiyo sautin redio wanda ya karade gidan da
wakar mutanen Niger wadda aka sako a gidan
radio, Abubakar ya yaye Labule cike da mamakin
'yau. Kuma Kaka kida ake sha
‘ kenan, ita da take fada idan wani ya kunna'ta .
ce xa'a cika mata kunne.
Ya yaye labulen dskin tare ‘ da sallamarsa, sai
dai wa zai gani? Rukayya ce kwance akan gadon
da radio a kusa‘da ita daga' ita sai farin dogon
siket irin
'budadden nan, sai 'yar Bingilar bes dinta iya
cibiya mai siririn hannu, babu k0 kallabi akanta.
Ai Abubakar bai san lokacin da ya fado cikin
dakin ba yana kiran sunanta
"Rukayya, dama kina nan kika barni nai
.ta wahalar _ neman ki?"
RuKayya maganar tasa ta daki dodon kunnenta
tamkar saukar markade bata san lokacin‘ data
zabura ta mike ba ido waje
Abubakar ya bita da kallo tundaga sama har
qasa, kafin ya hadiye Wani abu mai kamar yawu
a abakinsa, ya langaBe kai cike da alamun
gajiya ya ce . "Kin tayar min da hankali Rukayya,
kin 'wahalardani, kin wahalar da zuciyata.
Haba Rukayya, me yasa kika biyewa Kaka ku ka
~ dauki alhakina?"
Rukayya ta cigaba da kallOnShi cike da mamakin
kalaman ,dake 'fitowa .daga bakinshi, shi kanshi
bai san lokacin da suke fitowa daga baccin nashi
ba, sai dai abinda ya sani kawai shi ne. gaskiyar
abinda ke zuciyarshi ne yake ‘ furtawa ganin tayi'
shiru tana kallonshi‘yasa " shi matsawa da niyyar
damqo hannunta. ' , Tai saurin ja da baya tare da
bata fuska, cikin sanyin murya Abubakar ya ce . ‘
"'Fushi kike. dani? Kiyi haquri, nasan nayi kuskure
kimin afuwa insha Allahu hakan ba zata sake
kasancewa b...". . Tsakin da Rukayyar taja ne ya
'katse shi daga cigabada zayyano jawabin naSa,
ya bita da‘kailo cike da mamaki. A dai ,dai nan
kuma
Kaka ta fado dakin riqe'da butar data fito daga
makewayi da ita sai faman haki take, ta dubi
Abubakar. ' "Kai malam, fice min daga daki kaji,
mutumin banza mutumin wofi". Abubakar ya juya
inda take yana fadar. . "Haba_ Kaka, yanzu‘
dama Rukayya tana gidan nan shi ne ku ka
Kyaleni cikin tashin . hankali tsawon sati guda?
Duk da dai ni din
mai laifi ne amma ai..Kaka ta katse shi, "Habu ba
surutu na
nema ba da kai, cewa nai ka fitar min daga
‘ daki kawai"
_ Abubakar ya langobe kai, "To naji zan fita
amma tare da matala".
’ Yana maganar ya nufi inda Rukayya take da
niyyar cafko hannunta, Kaka ta daga butan dake
hannunta ta maka mashi akai duk ruwan dake
ciki suka juye mashi a jiki, yai saurin rike butan
yana fadar '
"Allah Ya baki hakuri nasan nayi laifi koma dai
me: akai min ni dai hakuri ne nawa, kuma ‘
zan ta baki shi har sai ranar da kika huce kika _
bani matata".
Yana gama maganar ya juya jikinshi a sanyaye
ya bar dakin Kaka ta raka shi da harara har ya
fice sannan ta maida kallonta wurin Rukayya ta
ce
"Ke kuma sakaran banza kinyi tsaye sokoko yana
ta tsaraki da wannan dadin bakin . nashi da yake
ba wayau ya isheki ba. Yo in nice har ya isa ya
matso inda nake ma ban rotsa mashinkai ba inga
ta karyar rashin kunya". Rukayya dai bata 'tanka
ba sai dai ta koma da baya ta zauna akan. gadon
bata da ta cewa ita ganin abin ma take tamkar a
shirin film in banda abin Kaka k0 giyar wake
tasha ta yarda ‘ta Kara komaWa gidan Abubakar
mutumin da bai sonta, bai qaunarta, haka kawai
ya cigaba dabautar da ita a banza. _ .
_ Bangaren Abubakar kuwa‘ ganin Rukayya ya
rage mashi tashin hankali a cikin zuciya saboda a
yanzu yasan inda take yaqi guda ya rage mashi
wato yanda zai yi ya shawo kan Kaka ta? bashi
matarshi ya sani ba abu bane
mai sauqi ba yin hakan. to amma ya ya iya da
samarin kakarsa? Haka dai zai ta haquri harya
samu ya tadda nasara. Duk da baizo da shirin
kwana garin ba amma a yanzu dole ya tare don
baiga ta tafiya ba har sai ya Shawo kan Kaka. '
Sai dai duk yanda yai zaton' abun ya wuce nan,
don gaba daya Kaka ta ida birkice mashi. k0
kadan bata sauraren shi da ta gama ya samu
wuri ya tare a gidan saita tura Rukayyar ta
“tafi wurin .dangin mahaifinta wai ta gaishe su
tai masu kwana biyu.
Lokacin da Abubakar ya fahimci Rukayyar bata
gidan ba qaramin tashin hankali ya shiga ba, ya
tisa Kaka gaba yana fadar.
"Don girman Allah Kaka ina kika tura mani
mata‘?" _ ' ‘
Sai data harare 'shi kafin tace“habu tun wuri ka
fita idona in rufe na fada maka, na kuma
maimaita maka takardar sakin yarinyar nan nake
jira kaqiji to mu zuba‘ na rantse sai dai kaga
sammaci, don wallahi kotu zan maka ka". ' -.
Abubakar ya dafe kai yana maimaita.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wai Kaka sai
yaushe zaki ji tausayina ne? Kullum ina qokarin
in ’kwatanta maki ba zan iya sakin yarinyar nan
ba, amma kinki ki yarda na fahimci’ so kawai kike
ki kasheni da raina? Yarinya da aurena akanta
amma ki daukéta ki kaita wani 'wurin da ban san
k0 ina bane don dai kawai kinga banda yanda
zanyi. ' ‘
’ Kaka ta ja filo ta haye saman gado tana fadar,
“In “ma da yanda zaka yi din ba sai kayi ba, aure
ne ance ba'a yi ka bawa yarinya takardar sakinta
tunda ba kai bane autan maza ba kaqiya. To ba
sai kai ta riKo ba duk ranar daka gaji‘ka'saki
amma Rukayya kam kai da gininta sai dai a gidan
wani. Tana can na kaita inda 'zata samu mijin da
ya fika tayi aurenta, kai kuma saki ne kai ta riqo.
Gaban Abubakar ya yi wata mummunar faduwa
da bai taBa yin irinta ba, tabbas yasan Kaka
‘tana da sanin addini dai dai gwargwado, , amma
hakan bai hana shi gasgata zata iya aurar da
Rukayya da aurensa ba saboda yasan shekaru
sun ja akwai rudu da rikicin tsufa a
a
tattare da ‘ ita. Wasu irin hawaye masu zafi suka
tarar masa a cikin idanuwa, yanzu ya zai yi?
Wannan wane inn bala'i neya tunkaro shi'! Lallai
yana cikin jarrabawar rayuwa.
Ya bude bakida niyyar ya cigaba da yiwa Kaka
magiya sai gani ya yi tana kwasar munshari, lallai
ashe ya dade cikin duniyar tunani bai sani ba.
_Jiki a sanyaye ya. mike yai gaba. Washegari
tunda sanYin safiya ya shirya ‘ ya koma Katsina
bayan ya ajiye mata kudi
masu yawan da zata yi amfani daSu. ' " Sai daya
kwashe tsawon sati biyu bai dawo garin ba har
saida ya turo mata su Oga Mahmud . tare da
matarsa Hajiya Maimuna' suma sukai nasu
lallashin da ban baki amma Kaka taKi sakkowa
daga dokin naqin da ta hau, kira kawai take idan
bai kawo' takardar sakin da tacc ba sai ta ishe
shi har gida da takardar tsammaci. Ba yan'da su
Hajiya Maimuna suka iya haka suka dawo bayan
sun juye mata sakon
tarkacen kayan abincin da Abubakar ya shake
masu but din mota, ya ce a kawo mata.
Duk rashin arzikin, da take mashi bai jin zai Iya
hana ta abu daya daga cikin abubuwan jin dadin
rayuwar da yake bata, duk da yana jin zafi da
kuma ciwon rashin tausayin da take nuna masa
qarara, bayan yanzu shi abin
shi yanzu shi abin a tausayawa ne mutumin da
yakr zaune da matarsa kamar Suhailat amma
yanzu ya zama gwauron qarfi da yaji, komai shi
yake yiwa kansa dai-dai da sharar falukansa da
gyaran daki daga girki kafin ya fita (office) sai ya
samu dan dama k0 da kunu ne k0 ruwan (tea) ya
ci da bircdi sannan ya tafl, haka idan ya
daw0_duk uwar gajiyar daya' kwaso sai ya age
ya dafa abinda zai ci sannan yai wanka ya
zauna, tunani ya aure shi babu inda yake jin
dadin zuwa shi yasa yake zamansa a gida daga
shi sai maigadi ,sai kuma yaronsa Laminu mai
kula da fulawoyi shi ne kuma ke mashi wanki da
sauran 'yan aikace aikacen da ba'a rasa ba. '
Hmmmmm su kaka manya gaskia na tausaya ma
habu
A,I,S
RIKON KAKA
Chapter 3 · 0% Book details