Sashe 4
Rigar Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
https://www.arewapen.com/book?id=6a454e3380928ee61577c33d
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
©️Fertymerh Xarah💞
2
Duk da iskar dake kadawa a qarqashin icce da suke zaune hakan bai hana zufar Jaddi dake fita a goshinta tsayawa ba, tana zaune a kan dutse, idanunta sun yi luf-luf, zuciyarta kuma tana dukan sauri saboda firgicin mutuwar da ta gani a gabanta. Ta kalli Nurayyah, wadda take tsugunne a gabanta tana hawaye, sannan ta yi wani irin nishi mai nauyi.
"Nurayyah..." Jaddi ta kira sunanta cikin muryar da ba ta fita da kyau. "Mu koma gida kawai, ba zan iya zama a asibitin nan ba idan mutuwa ce, na gwammace na mutu a dakina cikin mutunci, maimakon na mutu a kan wannan layin na wulakanci."
Nurayyah ta girgiza kanta da sauri, hawaye na zuba a kuncinta. "A'a Jaddi! Ba za mu koma gida ba, ba ki da lafiya, jikinki zafi yake yi, numfashinki kuma bai daidaita ba, dole ne likita ya duba ki zan koma ciki na sake rokonsu, ko ma na nemo wani likitan daban..."
"A'a Nurayyah," Jaddi ta katse ta, tana rike hannun jikanyar tata. "Kin ga abin da ya faru da wannan bawan Allah, kuma ga wata matar ma da ɗan ta ne a kusa da mu, amma nurses din nan suka kyale wancan tsohon ya mutu kaman dabba ni ma haka kike so ki gani? Mu koma gida Addu'arku ta fi mini maganin da ba a ba ni da tausayi da rashin adalci."
Sun dauki lokaci mai tsawo suna wannan saqa da warwaran. Nurayyah tana tsoron rasa Jaddi idan suka koma gida ba tare da an yi mata komai ba, ita kuma Jaddi tana tsoron wulakancin asibitin ya kashe ta kafin ciwon ya yi kisa daga karshe, ganin yadda Jaddi ta dage, Nurayyah ta yarda cikin damuwa.
Nurayyah ta mike ta goge fuskarta. Ta bar Jaddi a zaune, ta nufi bakin titi inda ta tari wani Adaidaita Sahu (Napep), ta fada masa unguwar da zai kaisu bayan sun yi ciniki, Nurayyah ta taimaka wa Jaddi ta mike da kyar, suka shiga napep, tafiyar duk a shiru aka yi ta, Nurayyah na kallon titunan Kaduna amma zuciyarta tana can gida, tana tunanin yadda za su yi da ciwon nan.
Suna isa kofar gidansu, mai Napep din ya ajiye su Nurayyah ta taimaka wa Jaddi ta fito tana dingishi, daidai lokacin ne Malam Musa, makwabcinsu wanda kowa ya san mutumin kirkine da son mutane, kamar ma shine matsayin uba a gareta yanzu, tunda duk abinda take so na makaranta idan Jaddi bata da kuɗi wurin sa take zuwa, yana kokarin fitowa daga gidan sa.
Malam Musa ya tsaya turus ganin yadda Jaddi take tafiya kaman wadda za ta fadi, ga Nurayyah fuskarta duk ta kumbura saboda kuka.
"Subhanallahi! Jaddi, me yake faruwa? Nurayyah, lafiya daga ina kuke haka?" Malam Musa ya tambaya cikin kulawa da tashin hankali.
Nurayyah ta kasa boye damuwarta. Nan take ta shiga ba shi labarin komai tun daga layin da suka bi, yadda aka rika shigar da masu kudi, har zuwa yadda wannan dattijon ya rasu a gaban kowa ba tare da an taimaka masa ba. Tana maganar tana kuka, muryarta na rawa. "Baba Musa, asibitin ynxu babu adalci babu tausayi sai son zuciya, saura kaɗan Jaddi ta rasa rayuwarta a wurin saboda rashin adalcin su."
Malam Musa ya jinjina kai, ransa ya baci kwarai. "Wannan gaskiya ne Nurayyah, rashin tausayi ya yi yawa a yanzu, ku kwantar da hankalinku, shigo da ita ciki ta kwanta ta huta kada ku sanya damuwa a ranku."
Ya kalli Nurayyah ya ce, "Karki damu, yanzu zan aiko Lawali mai Chemist, Lawali ya san aiki, kuma zai zo har gida ya duba ta, ya ga abin da ya kamata a ba ta kafin gobe mu ga abin yi."
Cikin kankanin lokaci, suna shiga gida, Jaddi ta kishingida a kan katifarta, ba a dade ba, sai ga Lawali ya shigo, sanye da wata yar riga mai aljihuna da yawa, rike da wata karamar jaka ta magunguna, shima mutum ne mai barkwanci da tausayi.
Ya gaishe da Jaddi, sannan ya fito da na'urar auna suga da ta hawan jini, ya debi jinin Jaddi ya auna.
"Jaddi, kin ga dai yadda kuke wasa da jiki ko?" Lawali ya fada yana murmushi don ya kwantar musu da hankali. "Sugarki ne ya dan yi sama, sannan kuma ga tashin hankali da kika sa wa kanki jinin ya hau kaɗan, karki damu, zan ba ki wani magani yanzu da zai saukar da shi, sannan na baki wasu allurai da za a rika miki na kwanaki biyu."
Ya fito da wasu magunguna ya mika wa Nurayyah, ya yi mata bayanin yadda za ta ba Jaddi ya kuma tabbatar mata cewa nan da sa'o'i kadan Jaddi za ta ji sauki idan ta samu barci, bayan ya kammala, ya fita yana yi musu fatan alheri.
Nurayyah ta sauke ajiyar zuciya. Koda yake har yanzu akwai damuwa a ranta, amma taji wani sanyi ganin cewa a cikin unguwar su, akwai mutanen da har yanzu suke daraja talaka kuma suke taimakawa ba tare da nuna bambanci ba, ta zauna a gefen Jaddi, tana shafa kafarta, tana kallon kakar tata har barci ya ɗauke ta.