Sashe 3
Rigar Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
daban, ku fada min nawa ne? Ko duba nawa ne zan fita na nemo muku, muddin dai za a duba min shi, dan Allah kada ya mutu a hannuna," ta faɗa tana kallon su gwani ban tausayi. Nurses din ko kallo ba ta isa ba a gurin su, ɗaya daga cikinsu tana danna waya, tana tabe baki, dayan kuma tana rubutu a wani littafi, sauran kuma suna maganar samarin su, da ƙyar ta sami wata ta kula ta, " ki daina mana surutu a nan kowa ma da tasa matsalar ya zo koma ki zauna, idan kudin ne da ke ai sai ki tafi asibiti mai zaman kansa (private)," daya daga cikinsu ta fada ba tare da ta kalli matar ba. Ana cikin wannan hatsaniyar, kwatsam sai aka ji wani nishi mai karfi daga inda wannan matashin da yayi faɗa ɗazu yake. Mahaifinsa, wanda ya dade yana fama da numfashi, farat daya sai ya fara wani irin fizge-fizge. Idanunsa suka karkata zuwa sama, kirjinsa ya fara dukan sama-sama. "Baba! Baba! Me yake faruwa?" Matashin ya shiga ihun kiran mahaifinsa. Nan take hankalin kowa ya tashi. Nurayyah ta mike tsaye, tana kallon yadda dattijon yake kokawa da numfashi na karshe, mutane suka fara taruwa a kansu, Nurses din da dazu suka nuna halin ko-in-kula, suka ga abin ya zama na gaske, sai suka rugo da gudu da stethoscope a hannunsu, "A ba shi iska! Matsa ku ba shi wuri!" Nurse din tana kokarin danna ƙirjinsa, tare da ɗora stethoscope ɗin. Amma ina, rai ya riga ya yi halinsa, nishi na karshe ya fita, sannan jikin dattijon ya yi sanyi qal, ya koma tamkar busasshiyar icce a kan kujerar asibitin. Wani irin shiru ya biyo baya, shiru mai nauyi da radadi, daga nan kuma sai ɗakin ya ruɗe da kukan matashin nan da kuma zage-zage daga mutanen dake gurin. "Kun kashe shi! Saboda son kudi da rashin adalci kun kashe shi, bamu yafe ba Allah ya isa!" Wani ya fada cikin fushi. Fada ya barke tsakanin ma'aikatan asibitin da kuma samari da ke wurin, kowa yana huci kamar zaki. Nurayyah tana tsaye, duk jikinta rawa yake yi, idanunta sun kafe akan gawar dattijon nan, itace gawa ta biyu da ta taɓa gani a rayuwarta bayan ta mahaifinta, jikinta ya dauki rawa, wani irin tsoro ya ziyarce ta, tsoron da bai taba dukan zuciyarta ba, ta kalli Jaddi, wadda yanzu hankalinta ya gama tashi, Jaddi tana kallon gawar, tana ambaton Allah, amma idanunta sun nuna tana jin cikin tsoron ko itama nata lokacin ya kusa, kada ta mutu a wurin itama ba'a duba ta ba, musamman yadda numfashinta yake neman gagararta. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un... Nurayyah, mu tafi... mu tafi daga nan," Jaddi ta fada cikin muryar dake nuna cewa ranta ya baci kuma ya firgita. Nurayyah bata tsaya wata-wata ba, tana ganin yadda mutane ke dambe, wasu na kuka, wasu na kiran jami'an tsaro, ta damki hannun Jaddi da dukkan karfinta, hannun yarinyar mai shekara goma sha shidda yana karkarwa kamar an hura mata iskar sanyi, ta ji kaman idan basu bar asibitin nan ba, itama za ta rasa Jaddi a wannan layin na kaskanci. Cikin rawar kafa da sauri-sauri, suka ratsa ta cikin taron mutanen, suka fita wajen asibitin. Suna fitowa babban titi, Nurayyah ta ga wani wuri a gefen titi karkashin wata bishiya mai inuwa, inda akwai wasu duwatsu na zama, ta kai Jaddi ta zaunar da ita, sannan itama ta zube a kasa a gaban kakar tata, tana gumi duk da sanyin yammacin da ya karu. Nurayyah ta kalli hannuwanta dake rike da na Jaddi, ta ga yadda fatar jikin kakar tata ta tsufa, ta ga yadda jijiyoyin jikinta suka fito, ta ɗaga kai ta kalli ginin asibitin Barau Dikko daga nesa, asibitin bata kasance gurin neman lafiya ba a ganin ta, ta koma mata kaman karkashin kasa inda ake binne mafarkin talakawa da cin amanar su. [17/07, 12:07 pm] Ummi A'isha: *RIGAR ARO*