← Book details Rigar Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 22

Sashe 17

Rigar Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

yanzu babu kunya, sanda suka iso school aka bude mata motar ta fito, ta fito cikin wani irin taku na daukar hankali, dalibai da ma'aikatan dake kusa suka zuba mata ido, Tana yin wata irin tafiyar qasaita kamar matar governor da gaske tafiya ce ta mutane masu kuɗi, mulki, da aji, an elitist composure sai wani yatsina fuska take tana bin mutane da kallon banza irin ga matar governor nan. Abin da ya fi ba kowa mamaki shi ne, yau da jami'an tsaro (securities) take inda aka soma tunani may be dan anyi magana ne akan su yau tazo da su dan ta tabbatarwa mutane da cewa da gaske ita matar Binnani ce, duk inda ta saka qafa suna take mata baya fuskarsu ba annuri ga baqin glass da suka manna a ida uwansu, duk inda ta bi ana nuna ta da yatsa, creating a ripple of whispers. Shigar ta aji ya sanya malamin dake tsaye da sauran dalibai duka suka yi shiru ana kallonta, ta nemi guri ta zauna guards din suka koma bayan ta suka tsaya kowane fuskarsa ba annuri, malamin ya kasa magana cos duk sun ji lbr matar Binnani ce, a hakan ya cigaba da darasi har ya gama ya fito, tun daga nan kowa ya shiga tsoron ta ko kuma abinda zai haɗa su da ita, bayan sun gama duka lectures na ranar ta fito her guards trailing closely behind her. Fadila da taji lbr yanda maganar ta bi school yasa tazo ta ganewa idanun ta for the first time ta kasa gane Nurayyah saboda wani irin kyau da tayi da kuma wata tafiya ta ɗaukar hankali da take sai ka rantse dama Nurayyah yar babban gida ce idan baka san asali ta ba wallahi mutuwar tsaye tayi har sanda Nurayyah ta qaraso gare ta tana mata murmushi cikin yin far da ido, fadila ta bata rai eyeing her up and down with sheer disbelief kafin ta ce, "Ashe da gaske ne abin da ake fada, wai matar governor ta shigo makarantar nan yau! Ance kin zo da securities yau ma... but wait Nurayyah, wadancan manyan motoci guda biyu da wadannan mutane guda uku dake take maki baya a ina kika same su? Me kike shirin yi da rayuwarki are you feeling happy da abinda kike yi yanzu?" Nurayyah ta hade girar sama da ta kasa, ganin yadda idanun mutane ke kansu, ta sa hannu ta riko hannun Fadila, suka matsa jikin wata bishiya a gefe guda inda babu cinkoson mutane, seeking a moment of absolute privacy. Nurayyah ta tsaya tana kallon Fadila dake ta faman huci, ta daidaita tsaiwarta cikin natsuwa ta ce "Duka a gurin Faruq na same su, motocin gidan su ne, wannan mutanen kuma guards ɗin babanshi ne. Yace babanshi baya nan yayi tafiya shine ya kira uku daga ciki suka zo And shi zai biya su duka, it's a financial deal, ai babu wata matsala insha Allah just pray for me ke kin cika tsoro wlhy." Wani irin bacin rai mai zafi ne ya mamaye zuciyar Fadila, a wave of pure frustration. Ta ji jikinta gaba daya yana rawa saboda takaicin yadda Nurayyah ta nutsar da kanta cikin kogin karyar da zata iya halakar da ita a kowane lokaci. Fadila ta kura mata ido, jikinta har rawa yake saboda bacin rai ta ce, "Lallai Nurayyah, baki da hankali ko kadan! Wannan wace irin rayuwa ce ta hauka da kika dauko wa kanki? Karyar da kika sani sarai zata zo ta bayyana gobe ko jibi? Kina so ki nuna wa duniya abin da baki da shi? Menene abin burgewa anan, the luxury cars or the securities guards, sunan ki kike so ki bata da mutuncin ki a idon mutane saboda fake life ko kuma saboda wata banza dake can tana rayuwar ta and ta manta dake! Wannan hanyar da kika dauko ta karya ba zata kai ki ga nasara ba, rayuwar bogi ce wacce zata ruguje miki at anytime, and your facade will crumble into pieces! Ranar da ta ruguje, zaki zama abin tausayi a idon kowa, ni dai har ga Allah banji dadi ba kuma bana son wannan rayuwar!" Nurayyah ta lumshe idanunta a hankali, absorbing every sharp word, tana sauraren maganganun Fadila, if not fadila then who? Waye zai gayamata maganganun nan marasa dadi ta haqura ta kyale shi fadila kaɗai ta kai wannan matsayin, ta saki wani gajeren murmushi na gadara da nuna isa, a cold, prideful smile, ta ce "Kwantar da hankalin ki Fadila, zan daina idan lokaci yayi, ba zan dauwama a haka ba. But for now, yanda na zama wata a makarantar nan kowa ke girmama ni har malamai na ɗanɗana wannan daɗin da respect, gaskiya bazan iya dainawa yanzu ba, idan na daina mutane zasu gane qarya nake yi dama ni kuma bana son haka so I have to sustain this high status profile, dole in karasa abin da na fara." Fadila ta ce, "Wace irin girmamawa Nurayyah? Malamai da suka girme ki wasu suka haife ki kike jin dadin su baki girma dan kawai kudi da mulki na qarya, bakya tsoron ranar da asirin ki zai tonu? Idan Faruq ya tona miki asiri ko mutane suka gano gaskiyar ki fa? Your reputation will be utterly ruined!" Duk yanda Fadila taso nuna mata gaskiya tare da hujjoji, Nurayyah taqi ta gane taqi ta saurare ta, da ta ga fadila zata bata mata lokaci da surutu da bazai amfane ta ba sai ta katse ta " idan mun je gida zamuyi maganar shikenan yayi maki ko" kafin fadila ta bata amsa ta soma tafiya cikin izza fadila ta bita da kallon mamaki, tana kallo aka bude mata mota ta shiga aka rufe, kusa mutuwar tsaye tayi a wurin sanda motocin suka fice daga school ɗin, da kyar ta iya jan qafafunta da suka mata nauyi zuwa motar ta. [17/07, 12:07 pm] Ummi A'isha: *RIGAR ARO*
Chapter 17 · 0% Book details