← Book details Rigar Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 22

Sashe 12

Rigar Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

https://www.arewapen.com/book?id=6a454e3380928ee61577c33d

©️Fertymerh Xarah💞

9

Bayan sun iso harabar makarantar, wannan karon tare suke da driver, shi ya fito ya buɗe musu kofa suka fito, Fadila ta kalli Nurayyah tana murmushi,  kafin su soma tafiya duk wanda ya dube su zasu burge shi ance akwai abotar da idan tayi yawa har kama da juna ake kusan haka ne a wurin su musamman Nurayyah less din ba qaramin fito da ita yayi ba ko dan bata taba saka abu mai tsada bane? ya fito da cikar dirinta da kyan siffa, tafiya take cikin natsuwa, Idanuwanta manya-manya masu tsantsar haske da fari kalar madara sun fito radau, idan ta ɗago su tana kallon mutane sai kaga kowa ya shagala wajen kallon karsashi dake cikinsu, hancinta siriri ne mai tsini wanda ya zauna daidai tsakar fuskarta tamkar an zana shi da fensir saboda tsari, bakinta ɗan ƙarami idan tana magana ko murmushi kwarjinin fuskarta yana ƙara bayyana ne gaba ɗaya, ga fararen haƙoranta dake jere gwanin ban sha'awa, fatar jikinta kuma  ta fito da wani irin sheƙi a hakan ma dan bata sami hutu da kulawa ba, Nurayyah kyakkyawar halitta ce ta gaske.
Fadila bata kyaleta ba har sai da ta rakata lucture hall din su, sanda suka shiga kowa ya zuba masu ido yana kallon su musamman mazan class din cos basu saba ganin su a ajin ba, abin ka da mata masu kishi nan da nan wasu na soma bata fuska suna yatsina fuska sanda suka ga Nurayyah musamman da suka ga hankalin mazan ya koma kansu,
Fadila ta raka ta har ta sami guri ta zauna inda ba kowa, Nurayyah ta zauna ba tare da ta damu da irin kallon hargitsawa ko kishin da matan suke jifar ta da shi ba, ta gyara zaman ta tana kallon gaban ajin cikin natsuwa da nuna aji na gaske, a nan ne fadila ta dube ta tana murmushi tace, "Alright babe, you are good to go, I have to run to my own class now, see you after lectures, take care!"  tayi mata bye-bye  ta fice ta nufi nata sashen karatun.
​Tana  zaune bayan tafiyar fadila tana jiran isowar lecturer, sai ga wani kyakkyawan saurayi ya taso daga inda yake zaune ya nufe ta, yana tafiya cikin wata irin izza matan hall din suka soma kallon sa cos da yawa a ciki sun jima suna crushing din sa bai taba kula su ba amma yau da ganin bakuwar fuska shi da kansa ya tashi zai je gurin ta, Kai tsaye ya nufi inda Nurayyah take zaune  ya zauna a kujerar kusa da ita daidai yana satar kallonta, Nurayyah ta juyo ta ɗago manyan idanuwanta ta kalle shi da wani irin kallo na basarwa dake nuna he is not welcome gaba ɗaya cos tana son ta nuna masa tana da aji, ya dube ta  yace, "Honestly, I couldn't resist coming over, you look absolutely breathtaking, my name is Faruq, what's yours?" Nurayyah ta yi jim kamar bazata yi magana ba tace  Nurayyah, ganin tayi masa magana ta kula shi sai ya soma jan ta da hira sama sama yana tambayar ta yaushe ta fara karatu a ina take da sauran su, wani ta amsa wani ta mashi shiru,

​A yau kam Nurayyah ta tsinci kanta cikin tsantsar farin ciki da nishadi mai yawa ba irin na jiya dake cike da tsarguwa ganin yau ta dauki attention na mutane da yawa sai zuwa ana mata magana tana basarwa, bayan sun gama lectures na ranar, suka fito harabar makarantar tana tsaye tare da fadila suna jiran isowar driver, Faruq yana hango ta tsaye da fadila yaxo gurin su da murmushi a fuskarsa yayi sallama fadila kawai ta amsa Nurayyah kuwa sai wani jan aji take yi tana kawar da fuskarta gefe kamar bata san da zamansa a wurin ba, fadila tana tsaye a gefe tana kallonta da mamakin yanda Nurayyah ta canza lokaci ɗaya, faruq yace "Please Nurayyah, just give me a minute, I just want your digits, please!" Nurayyah ta yi masa shiru cos tana kunyar fito da wayar ta ma ya gani, shiyasa tun da take zaune a aji bata yi yunquri fitar da wayar ta ba kamar yanda taga sauran dalibai kowa da wayarsa a hannu.
Chapter 12 · 0% Book details