Part 2
Rash Boyayyen Masheki Part 1 Complete Hausa Novel · about 62 min read
Page 5
********** ********* **********
Rhyeno Estate
school bus ce ta yi parking sai ga su su uku sun fito suka shiga, Farida Karima da Bilkisu, motan ta ɗauka hanya zuwa makaranta, su na shiga kowacce ta zauna in da ta ke zama. Cikin haraban gidan kuwa tweens ne tsaye jikin mota ƙiran sport su na sanye da kaya iri ɗaya har ta gyalansu iri ɗaya ne da takalmi, ƙyawawa ne kuma farare ƙal haka dukkan su yaran gidan su ke, ana ganin su anga jini ɗaya kuma family ɗaya, Fancy ce ta fito da ɗauke da key a hannuta na basu haƙuri akan tsaida su da ta yi, ita ma sha Allah ɗinkin riga da pensil skirt ce jikin ta wanda atamfan ta haska ta, motan ta shiga ta yi mata key suka nufa Kasu dan su a can suke karatu, suma su Kandy, Beauty da Beasty na su motan suka hau suka nufa poly su a can suke karatun dan yanzu level 3 su ke. Gidan ya rage Pazars ne da matan su, Mom wato Maman Kandy tare su ka fito da Pazar B har mota ta raka shi sanan ta juya ta koma nabta part din, can sai ga Pazar M shima da Mamancy wato Maman su Hauwa'u shima motansa ya hau, yana sanye da kaya irin na Pazar M dansu sun fi sa ƙananan kaya, dan Pazar M shine minister of health shi kuma Pazar B minister of education. Bayan fitan su da kaman awa 1 Pazar Q da matar shi Aunty wacce ita ce maman Bilkisu, ita kaɗai ta haifa kuma ya aure ta ne bayan maman yaran shi maza ta rasu, shi ma Pazar R ya fito cikin ɗinkin zamani na manya kaya wanda ya sha uban aiki, matarsa Hajiya babta rakoshi ba saboda tana barci dan bata jin daɗi, tare suka fita suka shiga mota ɗaya suka nufa cikin gari gurin nasu business din. Bayan Aunty ta dawo zama ta yi tana kallo a Main parlour anan sauran suka same ta kowan ne cikin farin ciki suka gaisa da junan su, dan haka suke gaba ɗayan su cikin ƙaunar juna da rayuwa tare. Duk cikin su Aunty ita ce ƙarama dan su Mom sun girme ta, dukkan su ƙyawawa ne ma sha Allah, kuma farare sai dai kowa da kalan na sa haske, yadda mazan su ke ƙaunar junan su haka su ma matan suke, sannan duk ka yaran su ma haka su ka son juna.
" Hajiya, wallahi kwanan zamu ne ma wasu ma su aiki kinga har 9am su Atika ba su zo ba." faÉ—in Aunty ta na mai da kanta ga T.V,
" Zan mu su magana idan sukazo yau." cewan Mamancy ta na latsa waya kuma a take Atika da ƙanwar ta shatu sai wata zulai suka shigo, gaishe su su kayi sannan Hajiya ta musu faɗa a kan zuwa latti domin aikin gidan da yawa duk da na su shara ne da wanke-wanke kawai suna da me girki daban dan ita anan ta ke kwana.
********* *********** ***********
Badikko
Yau sai 12am ta dawo gida da ga gidan wata Hajiyan da take ma aiki ko da ta koma gida babu wanda ta kula ta shige ɗakin su ta zauna taci doya da kwai da aka ba ta a can gidan, ruwa ta sha sannan ta yi hamdala sai ta kwanta dan ta rantse a yau baza ta ɗaga ko tsinke a gidan ba, duk ihu Mamansu Rabi a banza dan Ramlat ko a jikin ta, ko da Rabi ta shigo a fusa ce da sauri Ramlat ta miƙe ta ci dam mara ta na ce wa
" Wlh idan ki ka taɓa ni sai na rama kar ma ki fara dan kinsan bazan da ku miki ba " da ma inbdai rashin kunya da tsaurin ido ne Ramlat akwai ta dashi duk da Rabi ta bata shekara 3 dan ita Ramlat tana 19yrs ne. Fita Rabi ta yi sai ga Aunty ta shigo ta na ce wa
" Ke ba ƴar iska, wlh Baban ku ze shigo za ki sani, bakya gani na da mutun ci, ko ruwa ba zaki fita ki ɗibo ba, uban wa ze ɗiba ruwan?." ta kai ƙarshen magana ta na shirin dukan Ramlat
" Aunty ke ma kin sa ni kowa ya hanani shiga gidan sa É—iban ruwa to ya kike so ayi?."
" Shegen halin ki na dukan yaran mutane ba dole kowa ya hana ki É—iban ruwa ba."
" Kinsan haka shi ne za ki turani to?" ta faɗa ta na warware ɗan maran ta, kwantawa abin ta tana kuma ce wa " Ba ni ki ka sa Baba ya duka ba ai wlh sai nan da sati 1 zan ci gaba da miki aiki." Aunty rai ɓa ce ta fita haka Rabi ma, ko da baba ya dawo aka faɗa masa ƙarya da gaskiya sai ya dauko wannan bulalan ta sa ta gado ya nufa cikin ɗakin su, da ma ta ji ƙaran babur din shi, da sauri ya tsaya yana kallon ta tana rawar sanyi alaman zazzaɓi me zafi take yi.
" Subuhanallah Ramlat me ke da munku.?" ya faÉ—a ya na aje bulalan a gefen ta, É—agyar da buÉ—e idanuwan ta sannan ta ce.......
END.
Daga Alƙalamin Pretty Sk.
https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Æ™asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauÆ™i.âœï¸
ð‘ð€ð’ð‡ ÆðŽð˜ð€ð˜ð˜ð„ð ðŒð€ð’ð‡ð„Ƙðˆ
á‘ᖇᗴTTY ÕK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ
page 6
" Zazzaɓi ne kawai!", Na faɗa wa Mama amma ba ta ba ni magani ba kuma taita sani aiki, a haka naita lallaɓawa, ruwa ne na ce ma ta na gaji bazan iya ɗiba ba, shi ne na kwanta." kai ƙarshen maganan ta na hawaye, tsaki Baba ya ja sannan ya fi ce can sai ga su Aunty harda Umar, sun ji shuru ba ta fa ra ihun duka ba, shi ne su ka leƙo.
" Lafiya ku kamin tsaye ha ka?." Ramlat ta faÉ—a ta na koma wa ta kwanta, sannan ta jero ma Aunty abin da ta ce ma Baba, ta ke ta haÉ—e fuska dan ta san halin Mijin na ta.
" Wato ke gaki ƴar iska, lafiyan ki lau ki ke ƙaryan ciwo?." Aunty ta faɗa ta na kallon Ramlat da mamaki dan tasan halinta sarai, acikin kwanaki nan wani raini ta koya. Baba fita ya yi ya je ya kira wani me chemist , ko da ya iso, Baba ya futa bayan Ado me chemist ya biyo bayan shi, bayan Baba ya fito da ga ɗakin, can sai Ado me chemist ya fito, Baba ya biya shi kuɗin sa, sai ya ko ma gurin Ramlat din, su dai su Rabi na su ido, sun san halin Baba idan ɗan suna ciwo su na shan kula. Ramlat ta kalli Baban na ta wanda ke mata ya jikin.
"Baba inajin yunwa, zan sha tea." bai ce komai ba ya kuma fi ta, dariya ta sanya har su Umar na ji, sai su ka shigo suna kallon ta.
"Yarinyar nan kin riƙa" cewan Radiya ta na riƙe Kwankwaso, kafin Ramlat ta yi magana su kaji sallaman Baba cikin sauri ta ko ma ta kwanta ko da ya shigo ya umarci Radiya da ta ha ɗa ma ta tea din aiko ta haɗo ta ba ta. amsa ta yi ta kai baki da ƙyar, rabi ta sha sannan ta mi ƙa ma Umar sauran dan sun fi shiri yaron be da damuwa, amsa yayi ya koma ge fe ya na sha, a ranan Aunty ta sha faɗa haka su Rabi akan abin da su kayi ma Ramlat, ita dai ta na jin su hankalinta kwance.
******** ******* *********
*KIKINAU*
"Maryan É—an turamin Film É—in nan na kalla" Maryam amsa wayan Ramlat ta yi ta tura ma ta wani Nigeria film É—in da Maryam ta yi download dan sun ga poster kuma an ce ya yi daÉ—i sosai, Hajara ce ta shigo da sallama da É—auke da babba plate a jewa ta yi ta na ce wa.
"Bisimillah ga ma ra imani dukka na Annabi ya ce ya ƙoshi." suna jin ta faɗa ha ka su ka kalli plate ɗin, alkaki ne wanda yaji ruwan sugar ya ga ma jiƙa shi kuma yana ta walwal kwanin sha'awa, ta ke su ka sauka su ka fa ra ci, Zainab ma na shi go wa ta ɗauka biyu ta ce ya ishe ta dan ba ta wani cin sugar.
" Mama ta yi?." Ramlat ta yi tambayan sai Hajara ta ba ta amsa
" A'a Abbuu ne ya ka wo."
" Gaskiya ya yi daɗi." Maryam ta faɗa ta na lasan ruwan zaƙin.
******** ********* ***********
"Wallahi sai sun san ɓoni akan me dan na ba da shawara shi ke nan, aiko sun taɓo match, dole na san abin yi."
" Ka din ga kai zuciyan ka ne sa Abdulmasheed kaji."
" How? Hmmmmmm dole salon wasan ya sauya." wayan shi ya ci ro ya yi kira bu gu uku aka É—auka
" Gobe inaso na ganka sanann ka faɗa ma Babban yaya shima ya zo gobe nasan kai kaɗai ne zaka iya samun numbersa." ya na kaiwa nan ya kashe wayan. Baba Abdulqadir ya yi murmushi dan gobe ze ga yaran shi da ma so ya ke su dawo balle ma Babban yaya yana son ganin ya lafiyan shi ya ke, amma be san da munsu gashi Abdulmajeed ya kira su da ya ke shi ne ya san dole gobe za su dawo Nigeria. cikin faɗuwar gaba ta re da sauri-sauri ta nufi part din su bayan ta aje ma su Pazars drinks, yanda ta buɗe ƙofan da rufewan ya sa dukka su ƴan matan suka yi saurin ɗago wa, ko wacce da abin da ta ke yi amma kusan su hudu waya su ke latsawa
" Baby lafiya kuwa?." cewan Hasty ta na du ba littafin karatunta, dukkansu kallon ta su ke yi dan ha ka ta buÉ—e baki a hankali ta ce.
" Na zo da labari gu da biyu, bad one and good one." ta faɗa ta na ƙara sawa cikin su, zama ta yi kusa da Husty, sai Fancy ta ce.
" Start with good one than bad din."
" Ok, firstly tommorow Uncle ze dawooooo." yadda sautin kalman ƙarshe ya yi sai yai kaman a tare su ka ƙarasa cikin ihu da murna, su na ta hamdala sai Beasty ta ce
" Ki ce mu shirya zamuga Uncle wayyo daÉ—i, dama banda ko sisi..."
" Mayyan kuÉ—i kawai, ai sai mu ji bad din duk da ba ze tsora ta mu ba tin da munji maganar kuÉ—i." Kandy ta kai nan ta na mai da Idon ta ga Baby wacce annurin fuskarta ya É—auke lokaci guda, dukkan su suka sassauta jin daÉ—in su su na sauraro ta
" Pazar M ya umarci da a sanar mai shi ma ya zo goban nan."
" Baby wa kenan?." Butter ta tambaya sai da baby ta ja dogon numfashi sannan ta furta kalmomi masu harÉ—e harshenta
" BABBAN YAYA." daram, durum, dam, daan, zuciyoyin su ya bu ga sannan zu fa ya fa tsatstsa go mu su duk da A.C da ke aiki, duk cikin su Hasty ta fi kowa jin tsoro dan ta san case É—in ta da Babban yaya.
" Mun shiga uku, mun mutuuuu." kaman za tai kuka ta faÉ—a, sai Kandy ta ce
" Me ya sa Pazar M, ze ma na ha ka, Allah ya soo munji, me ya ka mata mu yi toh?."
" Two Hijjab gareni kawai , wayyo Allah." Hasty ta faɗa da muryan ƙasa-ƙasa, sai Beauty ta tari numfashi ta.
" ke nima biyu gare ni ya kama ta mu je kasuwa amma banda kuÉ—i, wake da kuÉ—i a account dinsa?" dukkan su suka ce babu sai Kandy ta ce
" I have 7k but ......" Ba ta ga ma magana ba Baby ta katse ta da ce wa
" Mukira Uncle ya turo mana sai mu je amma yanzu 7pm yamma ya yi, ko an barmu sai dai mu ari motan Pazar Q."
" Eh, ai muna da ke Baby, za kije ki riƙon mana Pazar. "
" No Kandy wata ta je Pls "
" Ke fa za ki tambaya, dan ko gun Pazar B ne tsaf ze ba ki key" a jiyan zuciya ta sauke sannan Besty ta ƙira Uncle Video call aikuwa cikin ɗan lokaci ya ɗa ga, da ya ke a system ne sai ta aje yadda zasu din ga ganinshi dukkansu, motsi wayan nashi ke ta yi sai kuma ya aje wayan ta ke fuskan shi mai kyau da ƙawa ya bayyana ya na mai sakin murmushi, fari ne ƙal kaman dukkan su, tweens ne kawai haske su be kai na su ba dan su hasken Mom su ka ɗauko, ga hancin su duk irin ɗaya mai tsayi dai-dai wa dai da, da an gansu an ga jini ɗaya sak ɗan dukkan su sun ɗauko fuskokin Pazars ne, fararere ƙwawawa ma su ka ma da shuwa-Arab, gaishe shi su ka yi, ya amsa da kai kawai ya na ta blushing abin shi ya na kallon ƙannan na shi ma su kama da juna wanda za'a iya za ta Babansu ɗaya ha ka Mama ɗaya, cikin murya shi mai daɗi da ɗan gurɓace wan yaran nasara ya fa ra magana
" Gobe zan da wo Sister's." ganin babu wanda ta yi alaman farin ciki ya sa ya kuma magana sai suka É—a ga kai alaman sunji sannan ya kuma magana.
" Babban yaya koh?." a tare su ka ɗa ga mai kai sai ya yi murmushi ya san ƙannan na shi sam basa son Babban yaya ya da wo, Baby ta bu ɗe baki a hankali ta ce.
"Uncle Plsssssss we need some money immediately." ya ri ga ya ma san dalilin kiran, a ta gefan shi aka mai magana dan ha ka ya kalle su ya na magana da sauri-sauri saboda ze koma bakin aiki.
" Sister's am sorry kiran gaggawa amma karku damu, balallai Babban yaya ya dawo gobe ba sa bo da ga ba É—aya Numbers din sa basa shiga na different countries, samun shi ze yi wahala sosai and zan tura muku kuÉ—in a account din Fatima sai ku raba." kai suka É—aga sannan suka mai godiya ya kashe kiran. Walwala su ce ta da wo ta re da murna sai su kai hamdala su kaci ga ba da harkokin su tin da an ce Babban yaya balallai ya da wo gobe ba.
******* ********** ******* **********
*BADIKKO*
Yau tin da ta wayi gari babu wanda ya shiga harkanta sa bo da abin da yafaru jiya, Aunty har kuka tayi saboda Baba in ranshi ya ɓaci sai haƙuri kawai, sukan su Rabi da yau bakinsu ya mutu, wanka ta fito sannan ta shirya ta sa kayanta tare da Hijjab, fitowa tayi ta kalli Aunty dake shara ta ce.
"Mama ina kwana" harara ta maida ma ta sai ta fi ce abinta ta na murmushi tare da tina rayuwar baya.
Labari
***** Baba mai suna Harun haifaffen Kaduna mazauni Kinkinau layin masallacin Ustaz sai kuma ya siya gida a badikko suka dawo sa bo da yafi kusa da gurin kasuwancinsa, ta yi missing ƙawarta aminiyar ta dan a gidan su take wuni, harta kowa na unguwan ya sheda ƙawancan su, tin ta na jaririya Mahaifiyata ta rasu a cewan Babanta, gurin Maman su Rabi ta taso cikin wahala da azaba sam basa raga mata ita
da yaranta, ga shi ita yarinya ce me natsuwa da girmama na gabanta, ta na musu biyayya iyakar yinta, da ƙyar ta samu ta kammala junior level, islamayi kuwa a aji hudu ta bar zuwa, Mama ba ta bin Malamai amma tasan kan sharri babu ranan da ba zasu jamata duka ba shi kuma Baba baya bincike sai duka, shekara 3 kenan da dawo warsa unguwan sannan wata 7 kenan da ta fara zuwa aiki gidan wata Hajiya ta na ba ta 5k duk wata sai ta kaima Mama amma ko sisi bata ba ta. cikin kwanankin da be fi wata ɗayan ba ta fetse da zama ma ra kunya ba na gida ba har da ƴan layi da su ka tsane ta duk da sai wanda ya shiga gabanta ta ke mai raddi, Mama wanda a yanzu ta ke ce ma ta Aunty sai dai in agaban Baba ne. ta ɗaura ɗammaran nan da sati 3 wanda shine bikin su Radiya sai ta baƙan ta mu su kafin subar gidan, sunyi ma ta abubuwa da yawa, sharri babu wanda basa mata, a yanzu tsayinsu ɗaya dasu harma ta huce su, ta dai san a duku ba za ta bugu musu ba, yanzu ko ta zo da abinci ita da Umar kawai ke ci da kuwa su ta ke ka wo ma wa su ra ba, ta rantse kuɗin watannan idan an ba ta ba zata ba yarda ko sisi ba za ta sissiyan abubuwan buƙa ta ne, Mama in zata hana ta sai ta ce za ta faɗa ma Baban dan dama be san ta na zuwa ba rufa-rufa aka mai, ta yi shuru ne kawai sa bo da ba ta don su samu matsala da tini ta tona abin da ke faruwa.
Cigaban labari
A dai-dai ƙofan chemist ta tsaya dan ganin akwai wani aciki bayan ya fito ta shiga tana gaishe Ado, amsawa ya yi sannan ya miƙa ma ta 1k amsa ta yi ta mai godiya ta futa ta na jin daɗin dan kuɗin Alluran jiya ce sukai ra ba dai-dai da me chemist din ko wa ya dau 1k. ta na ta zance zuci harta shiga gidan Hajiyar domin yin aikinta.
END
*Daga alƙalamin Pretty Sk*
[6/1, 15:56] á‘ᖇᗴTTY ÕK âœï¸âœï¸âœï¸: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

story & written -------
á‘ᖇᗴTTY ÕK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ
page 7
************* **********
************** ******************
KINKINAU
yau ma kamar kullum ta dawo da ga islamiyya kenan ta shiga gida anan ta tadda Zainab da wani suna hira wato sabo saurayinta, dogo ne mai ɗan duhun fa ta, sai faman hira suke suna murmushi ƙara sawa ta yi ta gaishe shi aiko ya amsa cikin sakin fuska kaman ya san ta, sannan ta shige gida abinta
" Masha Allah ashe ƙanwarki ta fiki kyau duk da tana sanya da niƙaf amma masha Allah kawai." Muhsin ya yi maganan da si gan wasa dan ha ka Zainab ta ce
" Uhmm na ji ai da ma nasan ni banda kyau." sai ta miƙe tsaye ta na turo baki duk cikin wa sa
" Ha ba gimbiya, ita ta isa ta fiki kyau wasa na keyi na janye kalman, My haƙarƙari zauna abin ki" sai suka kwashe da dariya dukkan su, ta zauna suka ci ga ba da hiran su ita kuma Ramlat ta shiga ɗakin su.
****
" Sis gaskiya Zainab ta yi sa'a nasan wanda nagan ta dashi a wajen nan." Ramlat ta faÉ—a ba ya ta cire hijab din ta sai Hajara ta ce
" A ina kika san shi?."
" ya na kawo wasu yara islamiyyan mu, gaskiya mutum ne mai kyauta da sakin fuska ba shida da mu wa."
" Ma sha Allah ha ka ake so, naso nima na ganshi amma akwai wata ran ai ba zan fita yau ba."
" Hmmmmmm ai Yaya Muhammad da Yaya Usman sun fishi kyau." Zainab ta faÉ—a a lokacin da take shigo wa, sai maryam ta ce
" Uhmmm bawani nan Usman fa be da tsayi." sai suka kwashe da dariya sannan Zainab ta kuma magana ta na kallon Ramlat
" Ramlat ta shi ki faÉ—a mana wane ne yafi kyau aciki tin da duk kin san su." sai su ka mai da hankali akan ta sai ta ce
" Yaya Muhammad na Hajara shi be da damuwa, salihin ba wa ga kyauta, toh na baki 70%, shikuma na Maryam ya shin 20% zan bashi mutum sai uban kishin tsiya....."
"Tab ana nuna min wariya anan gurin amma ai fari ne dai." Maryam ta faÉ—a ta na dan hararan Ramlat
" Eh amma kinsan dai halin shi ga faÉ—a, ba gaira ba dalili za kisha fa ma Husaina." cewan Hajara
"Uhm sai Yaya Muhsin shi kuma na ba shi 95%...."
" Iyyema yarin yar nan ba bu mai 100%?."
"Gaskiya babu ana wa result din sis Hajara"
" To Allah Ubangijin ya baki mai 100% Æ´ar autan mu."
" Ameen Zainabu tahhhh."
" Ramlat ba ma kunya , ah to ya yi ma na." Hajara ta miƙe ta fita dan du ba girki, su kuma su ka ci gaba da hiran su kwanin sha'awa.
********* ************* *************
Babu wanda ya fita agidan yau sa bo da suna shirin tarban Uncle, misalin 1:30 Uncle ya da wo kar kuso kuga yadda familyn ke nu na mai ƙauna da kulawa, wanka ya yi sannan ya fito su ja haɗu a daining danyin lunch, su 18 ne ko wa da yalwataccan murmushi, Uncle mutum ne mai wa sa da dariya, do go ne mai cikan haiba da kamala be san abubuwa biyu a rayuwan shi, rashin kunya da tsiwa shi yasa su ke shira da ƙannan na shi duk da akwai ma su wannan halin
"Ya maganar BABBAN YAYA." faÉ—in Pazar M ya na shan ruwan kwakwa, sai da hantar Æ´am matan suka, dan jin sunann Babban yaya, sai Uncle ya ce
" har yanzu duk ka numbers din ba sa tafiya kuma last call dimu ya ce china za shi."
" Okh ai wallahi idan ya dawo gidan nan, ya shigo kenan ba shi ba barin ƙasar nan, kusan 2yrs be zo ba ba shi da aiki sai ya wo zuwa neman magani, ni fa ba yadda da wannan yaron da suke ta re na ke ba kawai shaƙa tawa su ke zuwa ƙasashen duniya." Pazar B ya kai magana ya na jan tsaki sai Pazar Q ya ce
" Wai Adamsi?."
" Eh mana shi, basu da na yi sai ya wo hmmmm."
" Pazar M Insha Allah za mu sa mu numbers din shi.
" Shike nan Allah ya sa." wayan Uncle ne yahau Ringing ganin new number ku ma True-caller be yi identifying number ba ya sa be ɗauka ba, sai da ta katse har sau biyu, dan abinci suke ci ne, su na ga ma cin lunch, su ka ko ma Main parlour suna hiran su, Baby sai labari take ba shi ya na ta dariya, ya na son familyn shi, su Pazars kallo su keyi a babban T.V su kuma Momcy na su hiran suke na manyan muta ne,, take aka fara haska labarin da ya girgiza Nigeria a satin nan, Video ne wanda aka saki yanzu a Social Media, hakan ya sa kowa na Parlour ido ya koma kan T.V dan jin cikakken rahoton abin da kunnuwan su su ka jiyo, cikin majigin TVn wani mutum ne ke zaune kan wani dogon gujera, ya na san ye da baƙaƙen kaya wanda ko ina na jikin sa a rufe ya ke harta kwayan idon shi ya sa glass magana ya fara yi ciki wani kalan murya mai amo da cika kunnan me sauraro.
" Ƴaku mutanen Nigeria barkan ku, ni ne wannan ɓoyayyen masheƙi wanda ku kafi sani da RASH masheƙi, a yau ma zan dauki ran wannan shahararren dan kasuwan nan mai suna Ibrahim Sani Greto ...."
"Ibrahim greto kuma, wai ni waye wannan ɗan Iskan yaron ne, kaman babu hukuma a ƙasar na, ha ka last week ya nuna ya kashe wani Doctor a kebbi state" cewan Pazar Q ya na jin ba bu daɗi har ransa, ai kafin ya maida idon shi ga T.V RASH ya yan ka Ibrahim Sani Greto, sai jini ke zu bowa da ga jikinshi, salati su ka hau yi dukkan su suna ta duba wayoyin su ganin ko ina an haska wannan mugun videon dan direct ne, kuma masheƙin yakan kashe kowa sannan ya datsi tashoshin TV ya musu ƙurar, daganan sai muta ne ɗauka a sa me dukka Media sai abin ya yaɗu.
" RASH! RASH!! shi ne babban matsala muta ne a yanzu, kashe mutum a gunsa ba bu wahala, gashi sai bincike akeyi amma ko ma kama ɗaya ba'a samu ba, ya kashe babban ɗan kasuwan na Nigeria wanda ya ke zaune a Abuja wato Ibarahim Sani, kuma kafin shi ya kashe wasu, shin wai wanene RASH? RASH, RASH masheƙi sunan dake ta yawo kenan a media, hankalin mutane da ya wa ya na ta she saboda........" kashe T.V Aunty ta yi ba tare da me rahoton ya kammala zan can ba, ce wa ta yi
" Wallahi Nigeria babu tsaro ko kaÉ—an, wannan ai ba rayuwa bane." ta faÉ—a ta na zama kusa da Pazar Q sai shima yabce
" Mudai mu dage da Addu'a kuma Allah ya tona asirin mugun yaron nan RASH masheƙi." suka amsa da Amin.
Number da zu ne ya ƙara shigowa alaman Ringing sai Uncle ya latsa accepting ta re dayin sallama shuru har sai da yayi sau uku, sannan ya latsa wayan ya koma a speaker, a karo na hudu yana yin sallama da re da niyyan yanzu ze kashe kiran sai ya ji an ce
" Wa'alaikumul salam, da Uncle Aliyu Haidar na ke magana?."
" Eh ni ne."
" 1 minute."
abin da aka ce kenan sannan ya ji wani ya amsa ya wan ya fara magana, jin muryan ya sa dukkan su, suka natsu sannan Uncle ya ƙara volume don su ji da kyau.
" Nan da awa biyu da rani zan zo gida, na samu labarin Pazars na ne mana ka ce mu su inan ta fe." kafin Uncle ya yi magana ya kashe wayan, ta ke ya kira layin sai ya ji Switch Up, murmushi ya yi sanan ya ce
" Babban yaya ya na Nigeria ashe, sai ashirya tarban shi anjima ze dawo." Pazars, Uncle da su Mum sai murna suke yi suna jin daɗi banda ƴan mata 8 dinnan, ɗaya bayan ɗaya suka shige ɗakinsu da yake jiya Uncle yasa musu five hundred thousand, dan haka suka fito ko wacce ta shigan mutum ci, sanan Baby ta ɗau musu permision akan zasu kasuwa yanzu zasu dawo, Pazar Q ya basu key ya ce Fancy ta yi tuƙin dan ya fi yadda da na ta akan na Kandy dan ita akwai gudu da ganganci, cikin motan su ka shiga dircet wani Super market, suka shiga ga ba ɗayan su, yeard din hijabai suka siya da uban yawa ɗin kakkku, sai jallabiyoyi da niƙaf sanan suka koma mota kusan kuɗin ya ƙare dan haka Fancy ta ce
" Nidai inason 10k dan yanzu school za muje na amsa wasu takaddu."
" Babban yaya bala'i niwai ma ya zamuyi kunsan shi da yazo in ya shigo room din mu sunan mu sorry, muje dan ni gidan su ƙawata zaku kaini na amsa text books dinbta, akwai ƙura fa dan kunsan sauran." cewan beauty, sai Hasty ta ce
" Ya maganar hadda, yanzu sai ya ce sai munyi tilawa in ya zo, na manta yaushe rabon da na yi karatun Alkur'ani wayyo ni wayyo Allah na." ta faɗa Kaman ta yi kuka, motan ne ta tashi ta fara ta fiya sai suka yi playing Qur'an suna saurara sai mistake suke yi dan inbaka maraja'a to hadda na gudu wa. Baby, karis da Butter hankalinsu akwance sa bo da su suna zuwa islamiyya kuma basu hada tahafiz ba suna maraja'a sosai, Poly suka fa ra zuwa su Kandy suka shiga su ka ga ma komai sannan aka nufa Kasu nan ma masu case suka gama, sai suka je gidan ƙawar Hasty ta'ara abubuwa da yawa, suna komawa gida suka ƙyara ɗakin na su, su ka ɓoɓɓoye ƙananun kayan su, suka sha hijabai suka zauna kowa taɗau ƙur'ani suna ta maraja'a banda Karis dan ita case din ta a ta kaddun boko ne ɗauka ta yi tanata bita, baby ku wa hadisai ta dauko tanata hadda ce wa abinta dan ita akwai kwanya sosai..
End.
Daga Alƙalamin Pretty Sk.
[6/4, 22:08] á‘ᖇᗴTTY ÕK âœï¸âœï¸âœï¸: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

Page 8
**************** **********************
RHYENO ESTATE
Sanye ya ke cikin kayan police wanda ya ƙara bai ya na matuƙar kyaunsa, ya na da duhun fata, choculate colour ne amma me ƙyalli, dogo ne kaman Uncle, jikinsa duk a murɗe ya ke wanda ka na ganin sa suffar sa ta ƙar faffan namiji za ka ga ni, kyakkyawa ne a jikin farko, ya na da dogon hanci da man yan eyes, ya na da faɗi sosai ga dam tsen sa, sai ma sha Allan kawai, cikin farin ciki ƴan gidan suka mai tarba mai kyau kuma ta musam man kaman sun san da zuwan sa
" Uhmmmm ZAKI mai three stars wato ASP a yanzu, kana zamanin ka, gashi dai ka sake ziyaran dole tin da an turo ka Kaduna." cewan Aunty ta na miƙa mai abincin da ta zuba a plate, muryan shi mai amo da cika kunni, ba na ihu ba amma mai sautin daɗi.
" Auntyna kenan abin sai addu'a, dan kwana biyu kawai zanyi na koma, babban case ne ya kawo nan din."
" Ma sha Allah, to Allah ya taimaka." ya amsa da ameen, sai ga su Baby da Karis cikin ladabi suka gaishe shi sannan suka ko ma ɗakinsu dan da ma sun leƙo ne suka shin Boss ne ya iso, sai suka ga ƙanin Aunty ne da ga Abuja ya zo wato ASP Umar wanda ake kira da Zaki dan shi akwai ƙarfi da jarunta, suna shiga ɗakin na su su ka sanar ma sauran da cewa Zaki ne ya zo, aikam suka je suka gaishe shi dukkan su sannan suka koma ɗaki suna jin Aunty na mai albishir da ce wa
" Ka yi sa'a yau Babban yaya ze shigo." dauke farin ciki a fuskan sa da annurin, sai ya ce
"Alhamdulillah ki ce yau zamu haÉ—u?." ta ko É—a ga mai kai. anan Uncle ya sauko É—a ga part dinsa dan anan Uncle ze sauka.
" ya ka mata ka ma na two weeks mana." Uncle ya faÉ—a ya na kallon Aunty dan ta sa baki, aiko ta sa
" haka ne Zaki ka mana sati biyu mana kaji."
" Hmmm Aunty ba zaku ga ne ba, two days kawai zanyi, in da daman na dawo zan dawo domin ni yanzu Kaduna to Abuja zan din ga shiga no excuse, wani babban case ne kuma akwai abubuwan yi anan ne shi ya sa na zo, ina zaman zama na aka ɗauramin wannan bala'in dan basan ta in da zan fa ra ba." Ya kai ƙarshen ya na sauya yana yin fuskan shi zuwa ya na yin da muwa.
"Subuhanallah ka ce case din babba ne?."
" Aliyu sosai, yau ka dawo amma nasan ka sa mu labarin masheƙi wato RASH..... "
" Badai wan da ya yi kisan É—azu ba?." Aunty ta faÉ—a ta na zaro Idanuwa dan wuni yau ba ta hau online ba dan na T.V kawai ta ga ni amma hankalinta ya tashi sosai
" Shine Aunty, mutum kaman aljani, Ba'a ga ne harin sa, kisa na shida kenan amma biyu ya sa ke a media kuma dukkan su shahararrun muta ne ma su ji da kuÉ—i a Nigeria."
" Gaskiya an ba ka aiki Zaki Allah ya taimaka."
" To Ameen, Allah ya tsare mana kai." abinda Aunty ta faɗa kenan ta miƙa dan fyuta compound, su ma miƙewa su kayi suka nufi Compound din dan mota ta shigo gidan na su sun san Baban yaya ne, ga ba ɗaya jin mota ta shigo ya sa fito dukka mutanan gidan su ka dan tarban shi, dai-dai nan Pazars su ma suka fito daga ƙaramin Parlour dan a can suka wuni ko da Zaki ya iso a can ya je ya gaidasu ganin suna tattaunawa mai mahimmanci ya sa ya fita ba suyi hira ba. Bayan motan ta fa ka sannan wanda ke mazaunin Driver ya buɗe ya fito, saurayi ne mai kimanin shekaru 26 ya bayyana, ya na sanye da ƙananan kaya masu tsaɗan gaske choculate colour ne shima kaman Zaki, sai dai be kai Zaki tsa yi ba dai-dai ya ke. Babu in da Idanuwan shi su ka fa ra saukan sai kan bugun nunfashin shi wato Kandy, murmushi mai sanyi da ɗauke da ma'anoni iri-iri, da isar da saƙon ƙauna ke tasiri a cikin sa, suka sakar ma junansu na wasu seconi, sannan ya kalla su Pazars ya na faɗin "Ina yinin ku Pazars" su ka ɗa ga mai hannu, take ya danna Remote din hannu shi sai motan ta buɗe ga ba ɗaya, Wheelchair ya fara fito wa dashi ya ajiye a dai-dai ƙofan motan me na baya,, bayan wani ɗan lokaci fararen ƙafansa suka fa ta bayya na, ƙafa wanda za ka za ci ko ƙasa ba ya ta kawa, ƙafa irin na jarirai mai kyau gashi fari ƙal har ta farcansa farare ne me ɗauke da kwantaccen jan jini sai a tafin ƙafan na sa sai ya ba da style, sai gangan jikin sa shi ma su ma bayyana bayan ɗan lokaci ma sha Allah, duk hasken matan gurin da mazan sai na ga asha baƙaƙene agun wanda ya fito, fari ne ƙal wanda ya haɗu da jajaja, fuskan sa mai ɗauke da annuri da haiba sannan ga kamala ya bayya na, hannu ya sa ya cire glass din da ke fuskansa ta ke kwayan idonsa ya fito fari ƙal, cikin kuma ɓaƙi huluk, sai gemu wanda duk wanda ya gani yasan yabna shan gyara na zamani, ga hanci dai sak irin na Familyn sa, Allah ya yi mai kyau kwarjini da kamala, manya kaya ne jikin sa wanda suka ƙa ra bayyana tsayuwan gangan jikinsa, murmushi yake yi mai sanyi wanda har dimple dinsa suka motsa, kallon su ya ke dukkansu cike da so da ƙauna ma ra misal tuwa, kaman ya ta lo dan ta fiya sai dai me abin tausayi wannan Wheelchair din ya samu yahau da taima kon jikin motan da ya da fa, da ya ke wheelchair din me ta fiya da kanta ne aiko ya danna abu ajikin keken ya nufe su inda su ke tsatstsaye, ta ke Baby hawaye ya zubo mata dan ganin yayan su da sauri suka nufe sa suna ta jin daɗin kaman ba su su ne suke ta da hankalin su sa bo da ze dawo ba. dukka matan hawaye suke yi 2yrs ba wasa ba da ma tun can ba wani zama ya ke a gidan ba, da ya dawo kwana biyu yake yi zuwa uku za'a ne me shi a rasa a gidan ya huce shida jagoran sa kuma abokinsa Adamsi. babu abin da ya furta har sai da suka shiga Main parlour sanann ya gaida su pazars cikin girmamawa, ha ka su Momcy, sannan ƙananan shi suka gaisheshi wa inda suka sanya hijabai dukkan su kwanin sha'awa,
"Boss ya dawo ai komai dole muga sauyi dan ansan sauran." Hajiya ta faÉ—a ta na kallon Æ´aran na su, daya ke sunga ne me ta ke nufi sai suka yi murmushi kawai.
(U are welcome Boss)
************* ***************
"In ma ku faɗa gaskiya ko a'a banda damuwa, domin ni ban jira, take zan ɗa na kunamata sai in fasa kwanyar ka." bindiga ta sai akan wani wanda ya ke cikin cell, sannan ta janye ta na coka bindigan a jikin pocket din wandon jeans dinta, black wanda ya kwanta ma ta, sai riga me butura white da ta sa sai kanta wanda ta sanye p-cap sai bindin gashinta wanda tayi mai donut ya fito da ƙasan cap din, ba fara ɓa ce amma duhun ta me kyau ne bima'ana choculate colour ce mai matukar kyau, kyakkyawar gaske amma sam fuskarta babu alaman dariya a ɗaure ta ke amma kyau wune zalla a fuskan, cikakkiyar mace ce, son kowa ƙin wanda ya rasa inji ba haushe, fita ta yi da ga cikin cell din ta na duba agogon da ke tsintsiyar hannunta na Apple.
"Gobe da safe Zaki ze shigo ku tabbatar kun haÉ—a komai." ta faÉ—a ta na kallon mataimakinta sajent Nura, kafin ya amsa ta ma fice sai kuma ta dawo ta na faÉ—in
" Ku saki ɓawaron babur din can, ku goge komai dan gane da shi."
" Madam mashin fa ya sa ce badan Allah ya sa an kama shi ba fa......"
" Umarni na ba ka Nura." tana kaiwa nan ta fice motarta ta hau taɗau hanya zuwa gidansu, a take ya cika umarnin ta ɗan yasan Madam komai tayi akwai dalilin yinsa, buɗe cell din ya yi ya fito da wani sannan ya sallame shi. Ita kuwa tafiya take yi a motan ta na jin ba daɗi a ranta sa bo da rayuwa ta yi wahala a Nigeria, ta fahimci ba shine ya sa ci mashin ɗin ba sahun ɓarawo ya ta ka, horn tayi ta ke aka buɗe mata get ta shi gidan nasu mai kyau da tsari, parking lot ta je ta yi parking ta fito, waya da system kawai ta ɗauka ta shiga Parlourn nasu, babu kowa dan haka ta shige part din ta, wanka ta yi sannan ta yi sallan magrib, ta ɗanyi karatu Alqur'ani har aka kira sallan isha'i sai da ta gabatar sanann ta fita palourn anan ne ta tadda Mahaifiyarsu Hajiya da yayan nin ta twin maza Yusuf da Yunus masu kama ɗaya dan ita da take ƙanwar su da ƙyar ta ke banbance su saboda Yunus yafi ɗan sakin mata fuska akan Yusuf, su Lawyers masu zaman kansu, shi ya sa abubuwa da yawa ke ma ta sauƙi sa bo da su dan kowani case ta ka wo gunsu sai inda ƙarfi su ya ƙare, suna kama sosai dan mahaifin sa suka biyi amma mahaifiyar su ta nada haske ita, su uku kawai ta haifa, Mahaifin su yarasu shekarun baya, su mazan sune suka za ma mata uba. za ma ta yi cikin su suna ta hira cikin nishaɗi da walwala abin su.
End
Daga AlÆ™alamin Pretty Sk âœï¸ðŸ’ª.
[6/9, 07:44] á‘ᖇᗴTTY ÕK âœï¸âœï¸âœï¸: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

â€ï´¿ رَبَّنَا هَبْ لَنَا Ù…Ùنْ أَزْوَاجÙنَا ÙˆÙŽØ°ÙØ±ÙّيَّاتÙنَا Ù‚ÙØ±ÙŽÙ‘ةَ أَعْيÙن٠وَاجْعَلْنَا Ù„ÙÙ„Ù’Ù…ÙØªÙŽÙ‘Ù‚Ùينَ Ø¥Ùمَامًا﴾ ♥ï¸
ð‘ð€ð’ð‡ ÆðŽð˜ð€ð˜ð˜ð„ð ðŒð€ð’ð‡ð„Ƙðˆ
á‘ᖇᗴTTY ÕK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ
page 9
********** *****************
BADIKKO
Kwance take akan katifar Umar ta na shan choculate mai suna cash, murmushi ta saki dan yau kaɗai ta san ta ƙuntata ma su Rabi balle Mama yau ta shaƙa abin haushi, ta na jin ƙaran mashin ɗin Baba tayi sauri ta janyo hijab ta rufe jikinta, aiko ya na sauka a mashin din gurinta ya nufo bayan sun gaisa da su Mama a parlour, dubanta ya yi ta ce mai da sauƙi sai ya fita ta, da ya ke su Radiya na parlour haka suka kuma gaishe sa dan ɗazu bai amsa ba, yanzu dai ya amsa amma sama-sama, sai ya shige ɗakinsa.
Da ƙyar Baba ya sauka daga fushin da yake yi, a haka suka kwana dai badan ya haƙura ba, ko da gari ya waye ya bar gidan babu wanda ya shiga harkanta ita ma tana ta harkokinta, sannan ta fice, misalin 2:30 ta dawo, mama kallo take yi a madaidaiciyarT.V dake Parlour, 2k ta miƙa mata tana cewa
"Hajiya ta kore ni daga aiki sannan ta biya ni kuÉ—in aikin shine nace bara na baki 2k na dau 3k zanyi abubuwan yi da shi.".
Kaman ba za ta amsa ba sai ta amsa kuma ta ajiye a gefanta, Ramlat kallon Radiya tayi wacce ke ɗinki a keken ɗinkinsu, take jikinta ya yi sanyi da yanayin nasu, ko banza ƴan uwanta ne ta daure tayi haƙuri wata rana sai labari, hakuri ta basu da har sun share ta ganin abin ya kusa kaita bango yasa Mama tace
"To shike nan ya huce."
Daga haka sukai alƙawarin daina musguna ma rayuwarta dan a yanzu sun san ita ma tsaf za ta iya musu makirci wanda yafi na su, to menene amfanin sa kowa ya haƙura, haka Mama suka ba ya haƙuri akan duk abubuwan dasu kamata, da yake Ramlah yarinya ce mai haƙuri da sauƙin kai, sai komai ya wuce a gunta kuma da zuciya ɗaya.
************* **************
Ko bayan sun gama gaishesa da kai dai ya amsa musu fuskan nan tasa yadda dai ta ke kullum, a hankali dukan su suka silale zuwa ɗakin su, bayan sun wuce ya kalli Uncle da idanuwansa farare ƙal ya najin soyayyan ƙaninsa na ƙara ambaliya a cikin jikinsa
" Aliyu ya aikin na ka. "
" Alhamdulillah Babban yaya, nai ta kiran numbers din ka amma ba sa shiga sam." sai da ya saki É—an murmushi sannan ya ce
"Haka ne sai haƙuri da ni bara na ƙarasa ɗayan Parlour na kuma gaida su Pazars." Ya kai nan ya na kunna kekensa ta nufi ɗayan parlour, da ido Uncle ya bisa, yana mai jin tausayin yayansa, har ƙwalla sai da ya share ya na tuna lokacin da yake tafiya da ƙafafunsa lau. Ganin idan ya cigaba da tinanin zai sa ya tuna tashin hankalin da suka shiga a lokacin sai ya nufi part dinsa dan Zaki nacan na jiran sa, yazo zai hau stairs sai ya dawo yabi bayan Babban yaya dan rakasa duk da Adamsi na bayansa dan ya shigo yanzu.
Gaishe su ya ƙara yi suka amsa, Pazar Q farin ciki fal zuciyansa dan ganin Babban yaya, yana cikin ƙoshin lafiya, yana matuƙar kawaici rashinsa a kusa da shi, gashi ya na matuƙar son Babban yaya, fiye da sauran yaran gidan amma be taɓa nuna wa ba ko damuwan sa akan wasu abubuwan ba ya nuna wa.
"Allah ya dawo mana da kai cikin amiincin sa, ka sani mun gaji da yawon ka da sunan ka na neman maganin ƙafafuwan ka, ha ka Allah ya so ba kada wata duba ra ma guje ma Allah, idan ya nufa za ka sa mu lafiya In sha Allah za ka samu Babban yaya, sannan wannan mutumin." Pazar M ya nuna Adamsi sannan ya cigaba da ce wa " Ya kasa ba ka sharawa a kan ka na tsu guri ɗaya, yawan nan be da amfani a ƙalla kusan 8yrs ba ka natsuwa guri ɗaya, har kwanda da karutu ne amma yan zu ba bu fa, kai kam sai biye mai ka ke yi kaman bindi in ya ce muje sai dai ka bishi kaman bindi, hakan ya ishe ni." Murmushi suka yi dukkan su sanan Pazar B ya da sa
" Shuraim me yasa ka ke yawan can za numbers nea shekarun nan?. ba a samun ka sai dai in ka so ka nemi mutum?." jin tambayan ya yi kaman a sama sai ya kalli Adamsi, aiko su na haɗa ido sai Adamsi ya nufa ƙofa da waya a kunne ya na amsa kiran ƙarya kawai so ya ke ya gudu dan be san me ze idan sun tambaya sha, "Hello Sunusi, Alhamdulillah" ya furta ta na fice wa daga parlour, Shuraim ya girgiza kansa sannan ya ce
" Pazar babu dalili." abin da ya ce kenan sai shuru ya ra tsa babban parlour na wasu lokaci kafin Pazar Q ya katse shurun
"Shuraim akwai muhummin abin da ya sa Abdulmajeed ya nemi da ku da wo dan haka gobe zamu tattau na ku je ku kwanta."
" To Dad." da ga haka ya mu su sallama ya fita shi ma Uncle ya bishi har ze huce part ɗinsa sai ya koma ya juya ya nufi part din ladies, da ma sun san sai ya shigo kuma jiran na shi suke yi dan ha ka ya na Knowking Beasty ta je ta buɗe mai ya shigo shi kuma Haidar ya wuce dan ya san operation duty ze yi, dai-dai ta tsayuwan keken na sa ya yi, sai ya ga dukkan su sun ƙaramai girma bakaman da ba, yana son su dukkansu ya na ƙaunar su fiye da tinanin su amma sam ba ya nuna musu sa bo da in kowa ya nuna mu su kulawa akwai matsala. Gasishe suka yi ko wacce jikinta a sanyaya sai ya kalli Fancy ba tare da ya amsa gaisuwa ba ya ce
" Fatima a ina kika sa mu five hundre thousand jiya? misalin 9:37pm." Ras ga ban ta ya faÉ—i haka na sauran ma cikin in Inan da ya shiga bakinta ta fa ra magana
'' Un..c..le... Uncle, da ma...ya turo ma na ......"
" For What?." ya katse da da É—an zafi-zafi, ya sani da cewan Uncle ne ya tura musu sa bo da komai suke ya na sa ne amma so ya ke yaji me zasu ce, shima abin da duk su ka siya ya sani har da sauran Æ´an gidan komai ya sani sannan duk rayuwar da suke yi ya sani komai da komai, cikin rawar murya ta kuma magana
"Dukkan mu ne ya turo ma na sa bo da akwai abin da za muyi dashi." shuru ya ratsa duk abubuwan da suka siya ya sani sai ya ba sar, keken nasa ya murɗa har gaban glass din kayansu sannan ya matsa gurin dressing mirrow ya na ƙare ma lotions da turarukan gurin kallo ya bi da kayan gurin, ma sha Allah kaya ne shafa ne kaman me sun jeru sun tsaru sosai yadda kasan gurin saidai su dan kusan komai daban-daban, mai ɗaya ya dauka ya na dubawa ganin an sa Whiting Lotion for 3days only.
" Wa ke bleaching acikin ku?." ya tambaye su yan na riƙe da roban man, yasan babu wacce take yi dan duk hasken sune amma ya tambaya fuskansa ya na ɗaure dan ko murmushi ba ya musu to ina ma su ke ganin shi sai dai wa Uncle shi ne za ka ga ya na murmushi.
" Babban yaya wlh a siyyan kayan make-up ne mu ka haÉ—o da shi kuma sau biyu na shafa na daina." har Idon ta ya ciko da kwalla da ma ita akwai saurin kuka
" Husaina ba ha waye na ce abin ba." sannan ya ya dawo in da suke zaune dukkansu, har ran shi ya na ƙaunar dukkan su wallahi balle ma Baby wace kamansu tafi ɓaci duk da ba Maman su ɗaya ba. ya umarci kowa ya kawo mai ta kaddun su na makaranta duk suka kawo cikin ikon Allah duk suka cinye tambayoyin, sai da s kazo karatun Alkur'ani nanfa ido yaraina fata gun Beasty, Beauty, kandy,Hasty da Husty dan ba sa maraja'a, aiko sun sha faɗa sosai da umarnin zuwa gobe su tabbatar haddan izu goma ta dawo, koda ya futa babu wacce ta kwanta da wuri suka da ge da karatu ga shi ya yi season phone's din su. Part dinsa ne na farko dan haka ya shiga ya sa mu abokinsa Adamsi ya gyara ko ina kuma ya shigo musu da kayayyakin da suka zo da shi, zama ya yi kan lafiyayyen sopa, jikin shi be sann wahala ko kaɗan irin ƴan ga tan nan ne masu wuni a A.C, za ma ya yi tare da ɗaukan system ya shiga operating cikin matuƙar kwarewa. sai 2am yayi barci dan tini Adam ya kwanta a kan makeken bed din Shuraim...
* Koda yashiga nasa party din ganin Zaki na kwance ya ce
" Ya futan ba ko sai gobe?."
" Ai bar shi kawai dama wani shop na gani akan babban titi, na hango wani snacks ya burgeni a cikin kwalban, amma yanzu nafasa kuma agm gajiye na ke Aliyu."yakai ƙarshen maganan yana gyara kwanciya,
" Okh, mukwana lafiya ni dai wanka zan shiga. " da ga ha ka ya shiga toilet din yin wanka, ko da ya fito ya samu har Umar ya yi barci, nafila ya yi sannan ya kwanta..........
*********** ************
Cikin sauri ta kammala shiryawa sak irin shigan jiya, jeans black and white shirt, breakfast dinma a tsaitsaye yayi tafuce tana gyara gashin kan nata wanda yasha gyara, bread a bakinta tahau motan ta fuce. Isarta station kenan sai ga ASP Zaki ya iso, cikin girmamawa aketa gaisheshi yana amsawa da sakin fuska tare yake da Uncle a office dinta suka zauna ita kuma ta É—an fita dan ita direct gurin wani taje a can cikin station din dan amso wasu abubuwa,, zaman su na kaman minti 5 sai gata tashigo tana cin biscuits
"Sir Zaki good morning" tafurta cikin sakin fuska, ganin abokin aikin nata, É—ago kai yayi ya maida mata murmushin sannan
" Madam morning, excuse me" yafaÉ—a alokaci É—aya kuma yafuce dan amsa kiran daya shigo mai yanzu, zama tayi akan kujeran ta tana kallon wanda ke zaune yana latsa wayan hannunsa, ganin be É—ago ba yasa itama taÉ—au file din gabanta tana buÉ—e wa tare da faÉ—in
" Bisimillah, kar kace na ma rowan biscuit duk da kaɗan ne ya rane a ledan." daɗaɗɗan muryanta yamai amsakuwa a kunnsa tabbas yaji sallamanta kuma ya amsa daganan be sake jin maganan kowa ba sa bo da abin da yake yi a waya ya ɗauke mai hankali. ɗagowa ya yi yana kallonta ita ma anan ta ɗago ta na miƙa mai biscuit din take idanuwan su ta ke idanuwan su suka haɗe, Ita dai kallon shi take yi, ya sanya ƙana nun kaya wando jeans blue sai riga mai dogon hannu Black, gashin kanshi ya sha gyara tsaf sai faman ƙamshi ya ke yi, ga fararen idanuwan sa ma su sheƙi, murmushi ne kwance kan fuskansa. shikuwa ganin kyakkyawan mace choculate colour mai ko ka ce golding skin, kyan sura tana kallonsa da idanuwanta farare ƙal, be san me ya sa ba ya na son irin colour din akin ɗinta, gaba ɗayanta ta burgeshi kuma a karo na farko dayaji wani ya nayi akan wata yarinya.
"Amsa ma na akwai daÉ—i." ya ji ta kuma ce wa sai ya sauke idonsa da ga kallon ta, sauke nauyayyan ajiyan zuciya ya sa ki sannan ya ce
"Alhamdulillah" sai ta kai ƙaramin bakinta ta hauci, ya na kallonta ta na karatu ta na cin abin
ta kuma ta na ɗan kar kaɗa kanta, kallon ta ya ke yi ko ƙyaf ta ido ba ya yi, ita kam ta na jin wannan idanuwan na sa a kanta, ba ta ɗago ba amma ta ce
" Kallan fa?" sai ya sauke idonsa a karo na biyu, wlh tinda yake betaɓa jin mace ta burgeshi ba irin ta, miƙewa tayi ta nufa wani case tadauko document, yanata binta ta kallon yanda take tafiya sai da gaban shi ya faɗin, tana juyowa tanufesa hawa Desk din gabanahi tayi suna facing amma basu mazi juna a, kallon sa tayi tanamai haɗe fuskan bakaman ɗazu ba, bindiga ta janyo aya bayanta ta shaida zuciyar shi ta re da ɗaura bindingan a gurin ta danna har ya to kare da jikinsa sannan ta ce
" Kallon ya isa ko in tarwa tsa dai-dai nan." ta faÉ—a ta na É—an na bindigan a kan girjin sa sai ya lumshe idanunsa, ya sani a kallo É—aya ya yaÉ—a kuma ya ji ta mai
"Wlh na faÉ—a." ya furta kaman me raÉ—a, murmushi ta sa ki sannan ta koma gunta ta na faÉ—in
"Zan ko tsamo ka."
"Ai nashiga ba futa" ya ba ta amsa a dai-dai nan ASP Zaki ya shigo ya na ce wa
" Sorry na bar ku."
" Da yanzu zan wuce kasan akwai abin zanyi me mahimmanci kaɗauko ni amma ban yi a sara ba tin da na gani, na ji yamin." Uncle yakainan yana kallon Madam ta fahimci abin ya ce dan ha ka tai banza da shi ita tin da ta ke babu wanda ya taɓa kallon kwayan idon ta ya furta ya na sonta sa bo da tanada kwarjini agun maza, Zaki be fahimce shi ba ya zauna ya na kallon aminiyar sa wat o Madam da ke ha ɗa ta kaddunta.
" Gasu mun haɗa komai, a tina nina mu bi komai a sannu sa bo da sai mu san takunsa tukun zamu yi amfani da salon sa don kama shi" ta furta ta na mai miƙa mai files ya amsa ya na faɗin
" Karki damu Madam meerah, ai tin da aka saki a case din na sanki akwai kwanya, bincike yanzu aka fara." murmushi ta saki ta na ce wa
" Hmmm Zaki kenan, yau zolayan ya ta shi kenan."
" No gaskiya ce ai Meerah ba ra naje karna ɓa ta ma Uncle lokaci." da ga ha ka ya miƙe shima Uncle ya miƙe da ido tabi su kawai, Zaki na fita sai Uncle ya dawo ya tsaya a gabanta, ba ta ɗago ba amma ta ce
" lafiya? akwai abin da ka ke so ne?."
" Ina sonki ban taɓa jin yadda naji akan wa ta ba sai ke, bazan wuce ba, ba tare da na fa ɗa miki ba, I Love u. " shi kan shi be san lokacin ya furta hakan ba, ita ko a da ke ta ce
" Za ka iya tafiya toh."
" I need your digit.". sai da da ta kuma kalleshi sannan tace
" Sorry i can't." ta na kaiwa nan ta miƙa ta re da raɓa shi ta fice, ganin ha ka shi ma ya bi bayanta ya na murmushi.
END
Daga Alƙalamin Pretty Sk.
[6/10, 20:30] á‘ᖇᗴTTY ÕK âœï¸âœï¸âœï¸: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

May Allah ï·» accept all our righteous deeds bring us endless joy, peace, and prosperity.
✨ 🌙 🕋 Eid Mubarak 🕋 🌙 ✨
ð‘ð€ð’ð‡ ÆðŽð˜ð€ð˜ð˜ð„ð ðŒð€ð’ð‡ð„Ƙðˆ
á‘ᖇᗴTTY ÕK
Page 10
*********** ******************
Badikko
Kowa aikin gabansa kawai yake yi, cikin sauri-sauri ta gama wanke-wanken sanan ta yi shara, dan yau za'a kawo lefen Radiya gobe kuma na Rabi'atu, abu kaman wasa yau gidan lafiya lau, aiko misalin ƙarfe biyu ƴan kawo lefan suka kawo, har set uku masu ɗauke da kaya dai-dai wadeta irin na masu ɗan hali, don wani malamin makaranta ne za ta aura yana samu dai-dai wadai da, bayan sun wuce suka bubbuɗe kayan kwanin sha'awa. har maƙota suka fara leƙowa.
" Gaskiya kayan sun yi kyau Radiya, na É—auki powder." Ramlat ta furta ta na nu na Eman powder,
"ɗauka bara ma na duba miki wasu." zaɓan wasu ɗan abubuwan kwalliya ta yi ta bata, ko banza yau dai duniyan ta yi mata daɗi sosai, dan ha ka ta yini cikin walwala. Mama dai ido kawai ta sa mata ba ta ce ƙalaba.
************************
Rhyeno Estate
Da yake yau sunday babu makaranta, abin da sun manta rabon da suyi shine wanke-wanke da shara amma yau sune suka hau aiki sosai dan Babban yaya, tin Asuba ya zauna a Main parlour ya na azkar, sun sha aiki kaman me koda suka gama a Parlourn su ka zauna suna karatu, Allah yaso su ya mai da musu wayoyin, da ma da biyu ya amsa so ya ke ya yi bincike cikin wayan duk da ya na bin komai na su amma basu sa ni ba, sallaman su ya yi amma ya ce Hasty ta tsaya hakan ya sa hantar cikin ta kaÉ—awa, tasan dole ya yi mata magana duk da yau wata uku kenan da faruwan lamarin.
"ko da wa sa idan na ƙara samun labari irin wannan zakiga ne kuranki, wuce ki kiramin Karima." da rawar jiki tabar gun ta na shiga ta kira Karis wacce ita ma tasan dole a ne me ta, ita ta na zuwa warning ya yi mata ya sallame ta sai suka fara gaisawa da Zaki wanda lokacin suka shigo shi da Uncle. ta na shiga Kandy ta ce
"Ke me kika yi" Sai da ta sha ruwa ta zauna sanann ta ce
" Hmmmm wani teacher ne a school din mu ya ke bibiya ta, ga shi be da ɗa'a ko kaɗan, da ya ke ba section din mu ya ke ba to ni ban sani ba ya kan zo class din mu muyi hira kaman wasa ashe sona yake yi to ni kuskuren da nayi shine ranan na je staff room dinsa, wlh abu na je amsa sai malamin nan ya yi ƙoƙarin ta ɓani shine mukai faɗa na fita, koda washegari na je school a ƙasar Desk di na na ga paper ko da na buɗe sai naga an rubuta 'first and last warning from Baban yaya.' kuma har da sign din shi, ni ko ƙara kula shi banyi ba, jikina ya bani shima an yimai warning dan in ya ganni can za hanya ya ke."
shuru suka yi suna mamakin yadda komai Babban yaya ya na an kara kuma ya na bibiyan su, duk da ba ya ƙasar abin na ba su matuƙar mamaki, Hasty jan nunfashi ta yi dan tinawa da nata ''''Sabon page ta buɗe a Instagram ta yita daura videos din ta har da sauraiyin ta wani Nasir, to ranan da ga school suka je party sun sha rawa kuma duk ta ɗaura, aran Babban yaya yakira ta da daddare ya mata kashedi sannan da umarnin ta goge komai kafin ya iso, aikam ta goge dukka'"'.
"Hmmm gaskiya duk wacce ta aura Baban yaya ta shiga uku." cewan Beasty ta na cire hijab dinta sai Butter ta ce
" Hmmmmmm Allah dai ya kyauta, ni fatana gobe ya wuce kawai....."
" Bakiji Pazar M ya ce ba bu in fa ze kuma zuwa ba." Kandy ta katse ta
"Da mun kaÉ—e kuwa." da ga haka su ka can za hira amma kowanne su ya na mamakin Babban yaya kaman wani Aljani, kuma sun yadda ya na ji dasu dan sai kana son abu ka ke ba shi kulawa.
Bayan sunyi breakfast Pazars suka zauna a Parlourn baƙi sai Uncle, Shuraim, Pazar R yafara magana cikin sanyi-sanyi kaman Pazar Q dan ha ka yanayin shi yake
" Shuraim da ga yanzu ba zaka ƙara barin ƙasan nan ba ba tare da kwarkwaran dalili ba, sannan ina son kasani badan Allah yaɗora ma nakasa ba, da kai ne Abdulmajeed ze zaɓe, saboda ka can canta dari bisa dari, dole yanzu kai Haidar za mu daura a hanya." yanuna Uncle, sai da girjin Uncle ya buga sai Pazar M ya ce
"Acikin jam'iyar mu ne ake ta samun rashin jituwa sa bo da za ɓe ya kusa nan da 3mounth ha ka, Aliyu dole kai zan kaiwa jam'iyar domin tsayawa ta karan Gomnan Kaduna." dam gabansa ya kuma faɗin har ze yi magana sai yafasa saka makon hannun da Pazar Q yaɗa ga mai, sai Shuraim ya yi magana ya najin wani nishaɗi a ransa
" Gaskiya kunyi zaɓi dan ƙanina yasan komai dan ga ne da harkan siyasa, gashi yasan dubarun mulkin U.S kunga ze gyara mana Nigeria, kuma be da damuwa sanna...." Pazar M ya katse Shuraim cikin ɗan hassala
" Ai mun sani ko da lafiyar ka lau ba zaka yi yadda mu ke so ba, ka na da taurine kai, Shuraim a tinaninka kai gyaleka za mu yi a haka ba wani aiki a hannu, kai ne a nan yau kai ne acan gobe, ai ya ishemu a ha ka kai da bindika za mu ne mo muku aiki ban yadda da wani online business din nan ba." murmushi ya saki É—an jin an kira Adam da bindi.
" Kuma nan da wata 3 nake so dukkan ku kuyi aure inbma ku kawo wacce kuke so ko kuma munemo muku." cewan Pazar R sai a lokacin Uncle ya samu damar magana
" Banƙi ta ku ba, 27yrs na ke how zan iya mulkin jahar Kaduna Pazars, kun sani ina aiki a office din prime minister na U.S, da gobe zan koma dan akwai ni aiki sosai, Pls pazars ku duba ko a ha ka Babban yaya ze yi, ya fini cancanta ta kowani fanni......." Pazar B ya katse shi da ce wa
"Ai mun ga ma magana ka na da 2-3 mounth kafin kafara aiki, ko katura a É—auko maka dukka abubuwa ka ko kuma kabar shi amma kai da zuwa United States sai kahau mulki, maganan aure ne a farko dan dole ku yi aure kafin lokacin."
" Aure ni banda budurwa kuma banson yi yanzu, dan babu me auran gurgu, idan lokaci ya yi zan ne mi wata masakan, na barku lafiya." ya kai nan ya na reverse da keken sa ya fice da idanu su ka bishi har ya fita sai Pazar Q ne ya ce
" Share wan can, Aliyu kai fa ka na da budurwa ne?." yana jin ha ka sai ya tina Meerah sai kawai ya sa ki murmushin ƙarfin hali ya na ce wa
" Eh Pazar akwai wacce nake so amma bamu gama daidaita wa ba."
" Mun ba ka 3weeks sannan wannan maganan ya zama secret domin ga ba ɗaya jam'iyyar zamu girgiza." kai ya ɗaga kawai ya fita ya barsu dan za su tattauna ne, part din sa ya nufa sai dai kan ya shiga yaji muryan Shuraim ya kiran shi, juyawa ya yi ya nufesa, ya sauka a wheelchair din ya hau kan kujera ya na zuwa shima yahau sai da ya ɗaura kansa a kan cinyan Shuraim ya na sauke ajiyan zuciya, Shuraim kuwa gashin kan Uncle yake shafawa a hankali alaman rarrashi, har ze yi magana sai Shuraim ya sa mai yatsa a kan bankin dan haka ya yi shuru kawai sai shi Shuraim din ya kai bakinsa kan kunnunsa ya raɗa mai " ina ta re da kai duk runtsi duk wiya, karka saɓa musu umarni ka ji ƙanina." kai kawai ya ɗaga mai.
END
Daga alƙamin pretty SK.
Ina fatan kowa yayi babban sallah lafiya. Allah ya maimaita mana. Ameen.
[6/11, 07:41] á‘ᖇᗴTTY ÕK âœï¸âœï¸âœï¸: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

Page 11
********* **************
RHYENO ESTATE
A tabayan gidansu gurin shuke-shuke wato Garden suke zaune, ranta a haÉ—e ta ke magana dan ko gaisawa basu yi ba ta zauna dan kiranta ya yi a waya ya ce tazo gurin ta same shi
" Wani kalan soyayya muke yi Yaa Adamsi? 2yrs ban ganka ba sannan baka kirana ko chat sai ta facebook muke yaɗuwa, shima sai kayi one month ba ka hau ba, dana yi ma magana sai ka wani ce Babban yaya baya barinka, ba lokaci, how zamu ci gaba da rayuwa a haka, na gaji gaskiya na gaji, rabuwa zamu yi sa bo da kai ba na kula kowa sam amma ban samun kulawa agurinka, Why?." ta na kaiwa nan ta miƙe tsaye sai Adam shima ya miƙe yasan be kyauta mata ba, domin haka ya ke mata to ya ze yi baze iya saɓa umarnin Shuraim ba, amma kafin subar nan ko ma menene ze samu ayi maganar auran na su.
" I'm sorry My Sweet kandy, Insha Allah da ga yanzu zan kasance da ke koda yaushe, kuma zan gyara, ai yanzu muna nan ba'inda zan ƙara tafiya na barki, sai kiyi saving number da ma kira ki dan sabon sim ɗi na ne."
" ni nagaji da savings numbers din ka, da munyi waya yau to ban kuma samu ka da wannan number. "
" Ki ya ƙuri mana Insha Allah komai ya huce kuma jira na ke ki kammala karatu sai muyi aure."
" Uhmmmnmmn." Zama ta yi a in da ta tashi, haka shima ya yi ya zauna, zan can hira na ƙorafi suka bari zuwa na soyayya da kewan juna, Khadijah sam ba ta fushi da Adam domin ta na son shi sosai shima haka ya na son ta. Tin lokacin ta na yarin ya idan ya zo gidan suke hira sama-sama tin a lokacin ya ke furta ma ta yana sonta sai dai kawai ta yi dariya, har ta kai lokacin da ta fara son shi, kowa na gidan sun sani amma babu wanda ya shiga harkan su, harta Babban yaya ya sani sai dai ya sa musu ido kawai.
A Parlourn kuwa sai da suka dau mintina a ha ka sai Shuraim ya ce
"Kawai ka kira su haÉ—a ma ka komai gobe Adam sai yaje ya amso maka." da kai ya amsa sanan shuraim ya ci gaba da magana
" Ka na da budurwa ne?." ya kuma ɗaga kai, "Wow ƙanina hakan ya yi, to yaushe za ka nunamin ita?" Sai a lokacin Uncle ya buɗe baki ya bashi labarin haɗuwar su da Meera, a fili Shuraim ya ke nuna farin cikinsa, da bashi shawaran daya je gidan su dan ƙara tabbatar mata da ya na sonta.
************ **************
KINKINAU
Muwaɗɗa Malik shine littafin da suke karantawa a masallacin, sati da lahadi ne kawai karatun, 9:30pm su ka kammala dan awa ɗaya da rabi suke yi. yanzu ma sun kammala kenan sai suka yi addu'a tare da salatin Annabi sannan kowa ta wuce, sai Ustaz kaɗai dan yana son yagama haɗa ta kadun sai ya futya, yana gamawa ya fito yakulle masjid din da mamaki yake kallon Alhaji Abdulqadir da ke jikin motansa, ƙara sa wa ya yi ya na ce wa
" Alhaji lafiya kuwa baka tafi ba, ga dare na yi fatan lafiya."
."Malam Ustaz motar ce taƙi tashi nayi-nayi, yanzu na kira driver da mechanic zasu zo."
" To ko zamu shiga ciki kafin su izo ne ?."
" Karka damu Mal.Ustaz zan shiga cikin mota na zau......"
" A'a gaskiya ba ra nayi maka iso kawai, dan ma mota ta ta na gareji ana dubamin da na kaika da kaina." bajira ya faÉ—i komai ba ya shige gida, murmushi Pazar Q ya yi dan yanajin daÉ—in karatun malamin nan, cikin É—an lokaci ya mai iso, aikuwa suka shiga har Parlour suka zauna, Umma ta fito suka gaisa, Ramlat wacce ke Kitchen da niyyan É—iban abinci dan yau barci ne ya É—auka akan prayer-mat bayan tabsha maganin ciwon kai dan da shii ta dawo, Umma ta shigo Kitchen din ta na ce wa
" Abbuu ya yi baƙo ki haɗo mai abinci kikai mai, ni zan shiga ciki." da kai ta amsa mata sannan ta ajiye na ta ta shiga haɗa musu, bayan ta kammala ta daidaita hijab dinta ta kai musu, hira suke yi akan littan da aka kammala last week Umdatul-ahkam. Gaishesu ta yi suka amsa sai ta ajiye musu komai data ɗauko sai Abbu sa ta kira sauran matan suzo su gaida shi, dan Alhaji Abdulqadir Musa ƙanƙara akwai mutumci, cikin ɗan lokaci su ka shigo dukan su, gaisheshi suka yi cikin ladabi ya amsa ya na mai jin daɗin a ransa sannan ya ce
" Masha Allah Malam Ustaz, wacce za'a bani aciki ." dukkansu suka yi dariya sai Abbuu ya ce
" Ai su ukun nan an riga ka sai dai naba ka waccan." yanuna Ramlat ya na murmushi, ita ma murmushi ta yi ta ce
" To Baba sai da safe." a tare suka tashi suka wuce amma su na jin ya na ce wa
" Wai Baba ta ce min ta na ganina ɗan saurayi me jini a jiki." dariya suka yi ta yi har suka shiga ɗaki, suma Abuu hira suka ɗan yi sannan yaci abincin kaɗan ya na kammalawa aka kira da cewan sun iso,, aikuwa suka yi sallama ya wuce, har sai da ya hau mota tunkun Abbu ya kulle gidan. yana jin daɗi dan tina maganarsu ta ƙarshe da ya ce mai
" mubar wasa ba tada miji kace?."
" Eh Alhaji, su uku ne zamu aurar nanda lokaci kaÉ—an."
" In babu damuwa ina neman ma Babban yaro na ita, sai dai shi masaki ne ƙafarsa ɗaya ba lafiya tin wa ni faɗi daya taɓa yi shekarun baya."
" Allah sarki, ai dukkan mu muta ne kuma ba'a gama mana halitta ba, bamu san yadda Allah ze mai da mu ba nan gaba, kowa yasan ku kuna da mutumci w aye zeƙi haɗa jini daku."
" A'a kadai fara jin ta yarinyar ta wa kaji zuwa ko next week sai muyi maganan akai idan na zo Saturday, ka ga sai ka haÉ—a su gaba É—aya tin da nan da 2 mounth ka ce." da haka suka bar maganan, ko da ya shiga É—aki sai da ya labarta ma Umma ita fatan alkairi ta yi amma tanajin ba daÉ—i wai masaki ne, zata so itama ta auri lafiyayyen mutum kaman Æ´an uwanta.
************ **************
RHYENO ESTATE
yana isa gida part dinsa ya wuce, dare ya yi dan har Aunty ta yi barci ma, shima wanka ya yi ya kwanta.
Acan ɓangaren Shuraim kuwa ya na kwance akan bed ya rufe idonsa abubuwa da yawa ya ke tinawa, a haka har Adam ya shigo, zama ya yi sannan ya fara magana
"Boss everythings is ready." sai Shuraim ya buÉ—e idanuwansa a hankali, sai ya kalli Adamsi ido cikin ido yana wani murmushin da ni kai na bansan fassaran ta ba sai ya ce
" Okh, wato kai É—an soyayya kabarni ka je can kai da khadija, wai na yarinyar nan har ta san wani love?."
" Meka mai da Sweet-kandyta ......" ya katse maganan dan jin Pillow a fuskan sa.
*** "Assalamu alaikum." abinda yafaÉ—a kenan sai yayi shuru, kusan 2mnt suka É—auka ahaka sai sautin muryanta mai daÉ—in gaske yashiga kwanyarsa.
" Wa'alaikumul salam, meke tafe dakai " tafurta tana shafa lotions ajikinta dan tin tana wanka taji wayanta nata Ringing tana fitowa ta duba amma ganin number kuma True-caller tasa Aliyu Haidar tasan shine sai da yakira sau biyar ana shida ta É—aga,
" Bansan me zance ba amma wlh naji makamu sosai, in badamuwa kimin ƙawataccan gidan ku gobe zanzo muyi magana dan da gaske nake"
" wanda yabaka number dinnan tsaf ze kawoka gidan mu, amma banda lokaci hira gaskiya yanzu kafaÉ—a abinda ke bakin ka kawai"
" I love U, kuma auranki nakeson yi "
" When " saida zuciyarshi ta tsaya na wani lokaci dan jin abinda tace, har number yaƙara dubawa itace dai, saida yaseta kansa sannan yace
" Nanda wata biyu indai yamiki"
" Hmmmm yayi kazo ka nemi izini, amma bansan soyayya ban iyaba kaima na amince ma ne dan naji har raina na aminta, bansan damu da kira aƙalla duk bayan 2dys waya sau 1 yayi kuma zan baka time dan bakoda yaushe nake son kira ba."
" Na shiga uku, wlh Beauty bazan iyaba gaskiya "
" Not beauty I'm Meerah or Ramlat "
" Ohhh sorry Madam "
" Goodnight " kafin yace komai tatse kiran, dariya Zaki yasa wanda yake gedan Haidar yana cewa
" Wlh Aliyu kayi sa'a kasan Ramlah kuwa, ta tsani soyayya kuma batayi, a Abuja tayi karatu dani acan muka haɗu, ni kaɗai take abota, a duk lokacin da namiji yace yana sonta to sai anyi da gaske inba haka ba sai tace zasuyi faɗa, wani rana har dambe takeyi da wasu dayake macece me kamar maza akwai ƙarfi da brain, ga tsiwa."
" Kace nakwaso ma kaina"
" aikuwa amma akwai riƙo da addini sosai ga bin gaskiya " a haka sukaita hira abinsu har sukai barci.
Bayan wata É—aya abubuwa dayawa sun faru daga ciki akwai sa ranan auran Uncle Aliyu da Meera, bayan iyayenshi sun je har gidan su kuma yayyan ninta sun bashi dan mahaifinta ya rasu, hakama gurin su Ustaz sunata shirin dan duka su huÉ—un zai auran, dan tin washe garin ranan yasami Ramlah da maganan aiko batai musuba ta amince dukda kuwa ance mata baya iya tafiya.
Zaune take tana waya da Zaki akan case din dasuke dan jiya aka ƙara sakin wani kisan gilla da RASH yayi, hankalinta ya tashi sosai domin Babban jami'in Police aka kashe
" RASH mutum saikace aljani bamusan harin saba bamusan farmakin saba, ba sheda baya anfani da kowani abu gurin sharing Videos dinsa kawai datsan gidan Televisions yakeyi, taya zamu kamashi? "
" Karki ɗaga hankalin ki nanda 1 weeks zan shigo Kaduna bikin ki, zamu tattauna kuma ya kamata kidau hutu domin kiyi dilka kinsa...." Ƙet ta kashe wayan, batasan tunawa da maganan zatayi aure ji take kaman tace ta fasa amma tinda ƙannan mahaifinta sunshiga maganar tafasa, rufe Idonta tayi tana tina kwata-kwata sau 6 suka taɓa waya da shi koya kira bata ɗauka abubuwa sunyi mata yawa, amma kullum safe, rana da dare sai ta ga saƙon sa na soyayya tin bata karantawa har tafara a yanzu ita da kanta ma take duba wayan nata ko zata ga yaturo, agogo ta kalla ganin 3:15pm yasa ta dau wayanta tashiga contact, number shi wanda ko saving batayi ba amma tahaddace ta, Kira tayi amma harta katse ba'a ɗaga ba tsaki taja har zata aje wayan sai ga kiranshi, tanson ɗagawa amma dole tajira sai da yakusa katsewa tayi accepting takai kunne, muryansa taji ya yi mata amsakuwa, sai tasamu kanta da lumshe idanu gaskiya tayi kewanka sosai.
" Madam yau kece kika kurani, Wow naji daÉ—i Alhamdulillah faÉ—amin mekike so ko nazo ki gan nine?"
" Ba komai yanzu haka uku tayi tini " sai tayi shuru annan taci gaba da cewa "banga ni bane" jitai haushin kanta yakamata sai ta katse wayan takifa kanta a kan Desk cikin 2mnt SMS yashigo, cikin sauti ta buɗe tana karantawa, ta kara ta yafi sau 10, tanata jujjuya wayarta ƙiran hot 11, tana sakin murmushin dabatasan dalilinyin saba, saƙon yafara kaman haka (Imandhayaty - pillar of my heart, a gaskiya kinsani cikin farin ciki mara misaltuwa, ashe kindamu dani nagode sosai, kikulamin da kanki zuwa dare zankira ki Please ki ɗauka, busy nashiga yau shiyasa ban turo ba). aje wayan tayi tanajin daɗi a ranta, take kuma Idanuwata su kai kan rubutun dake facing dinta wanda akasa RASH, annurin fuskarta ya ɗauke sannan ta na tambayan kanta 'waye kai ? yaushe zaka bayya? kuma a ina ? Ina nan ina jiranka............
END
Daga Alƙalamin Sk .
[6/12, 12:43] á‘ᖇᗴTTY ÕK âœï¸âœï¸âœï¸: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

Page 12
*********** **************
KINKINAU
Bayan wani lokaci
Su huɗun suke zaune a Parlourn Umma suna kallon wani series me daɗi na korea, sallama sukaji ana yi tare da knocking get din, Zainab da ke zaune a kujeran dake kusa da ƙofa ta fita ta na amsa sallaman, sai ga ta ta shigo ta na faɗin
" Ramlat, sahibaty ce ta zo kingant.." ai kafin ta ƙasar har Ramlat ta fita da sauri, a tsakiyar cikin gidan suka haɗu sai suka rungume juna ita da ƙawarta, sannan suka shiga Parlour gaisawa suka yi da Maryam, Hajara cikin sakin fuskan sannan suka koma ɗakinsu, bayan ta ɗauko mata ruwa mai sanyi da zoɓo ta yi mata godiya ta na ce wa
" Mama bata nan ne?."
" Eh namesake, gaskiya na ji daÉ—in zuwan ki, Maman Rabi ta barki kenan?. "
" Kedai bari yanzu shiri muke yi sosai balle da su Radiya suka yi aure, anko na zo siya karya ƙare, ace Sahibaty ba ta yi ankon ba ai babu daɗi ba."
" Ai in ba ki yi anko ba babu magana kinsan kece kaɗai ƙawata, sai dai class mate kawai shiyasa ni bandamu da ankon ba, ban zuwa shagali kowa nasan babu me zuwa na wa gashi saura sati biyu."
" Hmmmm haka ne ai, ni ko anko bangani ba, na manta na tambaye ki lokacin da kika zo gidan mu ko colour din na gani." ta faɗa ta na kai zoɓon bakinta
" Hmmmmmm ya yi kyau gaskiya, zan nu na miki anjima."
" Tom, yanzu dai tin da ni ce babban ƙawa yakamata nasan ango tun kafin biki takwara"
" Hmmmm ni kai na ban san shi ba Ramlat."
" Kamarya Ramlat? Badai har yanzu be zo ba?."
" Eh takwara Abbu ya ce min bayanan ne, sai ana gobe biki ze dawo kinga."
" To amma ku na waya?."
" Har yau be kirani ba gaskiya, Uhmmm be damu bane share kawai." daga nan suka sauya hira da abubuwan da zasu na biki, ita ma Ramlat badikko ta ba ta labarin yadda suka shirya da Maman Rabi, dariya suka dinga yi. sai misalin biyar na yamma 5pm ta shirya ta amsa ankon amma Ramlat Kinkinau sam taƙi amsan kuɗin ankon, a haka suka rabu cikin ƙaunar juna da cewan in tazo biki kwana biyu zata yi tako amsa mata. Hijab Ramlat ta cire tanajin tausayin ƙawarta domin ta sha wahalan rayuwa a baya amma yanzu ta ga ta canza ta yi fresh abin ta, da yake tana da kyau sai yanzu kyawun na ta keta ƙara bayyana.
******** ********* *******
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, babban masallacin juma'a USMAN BIN AFFAN MASJEED KINKINAU. misalin biyu bayan an idar da sallan Jumma'a wanda muta ne sun cika maƙil kamar kowacce Jumma'a dan bautan Allah, 2:00pm dai-dai aka aura auran muta ne sama 20 wanda aciki na jiyo an ambaci Muhammad Bashir da Hajara Abdullahi Saleh Ustaz, Muhin Sunusi da Zainab Anas Saleh, Usman Usman da Maryam Abdullahi Saleh Ustaz sai Aliyu Haidar Abdulqadir da Ramlah Musa wato Meera bi sa sadakin dubu dari biyar adalan ba ajalanba. Kabbara aka kuma yi sai kuma can naji an kuma cewa, sai Shuraim Abdulqadir da Ramlat Abdullahi Saleh Ustaz, aure ya ɗauru an gama ɗauran yau, nan ma sai kabbara ke ta tashi da ga ta ko ina, kowa a gurin fuskarsa a sake yake banda Shuraim da ke kan kekensa ya haɗe rai sosai, ya yi kyau sanye ya ke da sky blue na shadda iri ɗaya da na Aliyu Haidar. Adam da ke gefan sa ya tsugunno sai tin sa ya ma faɗin
" Dama har da kai auren?" furzar da iskan bakinsa ya yi sannan ya koma yadda ya ke cikin sakin fuska sai ya ce
" Hmmmm ban sani ba amma naji a jikina kan cewa Pazars ba zasu barni haka ba amma mubar maganan sai mun koma gida." ɗaga kai Adamsi kawai ya yi, sai ga Zaki ya ƙaraso cikin walwala, shima manya kaya ne ya sanya wanda suka mai kyau sosai, ya ce
" Ango ango iyyeee ai ni banji an ce da kai ba ma sha Allah Babban yayanmu." Shuraim be ce komai sai ya miƙa mai hannu suka gaisa. Alhamdulillah taro ya watse a masallaci bayan an ci an sha an rabar domin an yi wasan kuɗi iya kuɗin. Motoci 6 ne su ka shiga babban gidan su, suna isa muta ne ne cike aciki kowa cikin an kon wani tsadaccen leshi Black and pitch. guɗa kawai ke tashi ango Aliyu sai murmushi yake yi wanda wani annurin ya sauka a fuskan shi, ya yi kyau sosai cikin ɗinkin babban rigan, shida ƴan uwan sune matasa kaman shi, dan shi be da friends duk suna U.S.
A cikin gida kuwa, mutane ne sosai ƴan uwa da abokan arziƙi, can ɓangaren ladies kuwa sun sha ɗinki iri ɗaya fitted gown sai na bayanshi wanda zasu sa saboda Boss. Masha Allah sunyi kyau sun sha make-up ga wasu ƙawayensu wasu sunyi ankon wasu kuma kayan nomal one jikinsu, Aunty ce ta shigo ɗakin ita ma cikin ango ɗinkin Buubuu sannan ta sanya hijjab ƙaramin, ta na shiga wasu suka fara gaishesta ta na amsawa sannan ta ce
"Kufito a É—auki hotuna sun dawo." ta ke Æ´an matan suka hau guÉ—a, sannan ta kuma magana "kunsan kuwa har da Babban yaya aka daura ma aure yau kuwa."
" Aunty wani babban yaya?." Cewan beauty
"Wanda kuka sani Yayanku Shuraim mana. muna sai yanzu muka ji mun daisan harda part ɗinshi aka gyara, sannan ɗazu ta ƙofan baya munga ana ta shiga da kawa." ta na gama faɗin haka ta fita tabarsu duk sun hangame baki, Hasty ce ta yi ƙarfin halin ce wa
" Mun shiga uku, Babban yaya, yanzu duk shirin event din dinner yata shi a banza in dai yaje kenan."
" Keta event kike yanzu ya yi aure kenan zaman gida dole wayyo allah na." Kandy ta kai nan ta na zama a kan gado, ji take kaman ta yi kuka, a haka suka fita dukkansu suka sha hotuna shi dai Shuraim fuskan nan a haɗe kaman hadari kuma yaƙi tambayan su Pazars akan maganan auran.
END
Daga alƙalamin pretty SK.
[6/12, 12:46] á‘ᖇᗴTTY ÕK âœï¸âœï¸âœï¸: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

If your Mum is alive, may she have a long life to witness your success🤲