← Book details Rainon Soja Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 18

Sashe 4

Rainon Soja Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanda yake shafa mata baya yana mata magana yasa Khalil sakin cup din ba tare da ya sani ba . Nan take ya fashe yana tarwatsewa ruwan Cofee din yana fallatsa har inda suke. Wannan yasa Aliyu Haidar ɗagowa daga jikin Ma'eesha yana kallon saman. Kallon kallo suke yi tsakanin su . Kamin Ma'eesha itama ta ɗago tana saurin kallon daga inda taji ƙaran nan .

Gani tayi Khalil ya kama karfen benen daga sama yana dirkowa ƙasa sam bai tsaya bi ta hanya ba. Bude ɗan ƙaramin bakin ta tayi don ta dauka yanda ya dirko to fa ya karairaye ya gama. Tun kamin ya ƙariko Aliyu ya kalli Ma'eesha yana cewa “ Go and rest”. Da sauri ta furta “ Ya Khalil baiji ciwo ....cewa nayi kije ki huta......!!! Yayi maganan yana ɗaga Murya . Da gudu tayi baya tana cewa to.

Isowa inda Aliyu Yake Khalil yayi kana ya furta “ Ali haidar meye na ga kana mawa ma'eesha yanzu? . Wani irin kallo Aliyu yayi masa ba tare da yace komai ba. Kasan nasan ka fiye da kowa a cikin gidan nan . Ɗan ɗaga gira Aliyu yayi kana yace “ Go direct to the point ”. Cike da fushi don Ali dan rainin hankali ne nan Khalil ya furta “ nasan ka nasan yanda kake lalata ƴammata da ko wacce mace ta shigo gonarka. Kai din ɗan iska ne ba mutumin kirki ba , kai Ƙwarto ne shahararre....Don haka daga yau kar ka sake hugging ɗin Ma'eesha bare har ka shafa wani ɓangare na jikin ta..........!

*To masu masoyana makaranta littafin rainon soja anan na dasa aya....✍🏻 Sai mun hadu a night update....Ina sake faɗa don Allah kar ki karanta mun idan baki biyani zufa na ba , rubutun ba sauki ne dashi ba bare kuma tsara labari....ga masu buƙatar karanta littafin Regular payment ₦500 vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932....Maman teddy's write✍🏻*
[12/18/2023, 7:59 PM] Real~Mamanteddy: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

Page 14
______________________
*Alhamdulillah mun dawo daga ɗan gajeren hutun da muka tafi na kawo maku Cigaban wannan littafi Mai taken rainon soja...ina fatan Ubangiji Allah ya bani ikon kammalawa cikin aminci kaman yanda muka fara. Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban yafe ba😭...ga masu buƙatar payment regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*
________________________

Don haka Ma'eesha ta isa munzalin da Mutum kamar ka koda na kirki ne bai kamata ya shiga jikin ta bare kuma kai . Khalil ya ƙare maganan tare da shan kunu yana haɗe giran sama da ƙasa tamau. Kallon sa Ali haidar yayi yana sakin wani shu'umin murmushi kana ya kauda kan sa can gyefe yana duban inda Ma'eesha take itama idanun ta akan su , don zuciyar ta ya bata da akwai wani abun ne shi yasa Khalil ya dirko daga saman bene hawa na ɗaya . Ganin kuwa yanda fuskar sa tayi tamau yasa ta Fahimtar tabbas da akwai abun da Ya shiga tsakanin shi da Ƙanin nasa .

Ganin yanda Ali Haidar yayi masa banza yasa Khalil ƙara fusata nan ya cigaba da cewa“Miskilancin banza da wofi wurin iskanci kafi kowa shahara ”.

Dariya Aliyu yayi yana shafa sajen fuskar sa tare da cewa“ Khalil kenan! Wai duka wannan sababin saboda Kawai hugging ɗin Ma'eesha da nayi daga faɗi Kasan da zata yi shine kake ta wannan maganganun....kaman ta waye Ni Ali Wacece kuma ma'eesha a tare dani? . Maganan lalata mata da kake yi ai wannan ya isa ya tabbatar maka da cewa Ni Lafiyayyen namiji ne. Sannan mene zanji a jikin wannan Yarinyar? Ka dube ta fa ka gani ƙwailah da ita mene zanji a jikin ta ya Khalil.

Ni kake faɗa mawa magana? Khalil yayi magana yana takowa daf dashi don Zuciyar sa ya fara tafarfasa .

Juyawa Ali haidar yayi yana ƙara kallon ɓangaren da Ma'eesha take kana ya Juyo yana zuba ma Khalil Lulun idanun sa . Cike da Miskilalliyar Muryar sa ya furta “ Kaci albarkacin ta bana so muna saɓani a gaban ta...don Allah ya Khalil mu daina irin wannan Abun yanzu , Kar ka manta tun muna yara muke samun matsala akan ma'eesha a yanzu ne har ka nuna kasan darajar ta? . Ɗaga kafaɗa yayi alamun bai dame shi ba . Yana juyawa tare da wuce Khalil da ya tsaya yana kallon sa .

Takawa yayi yana isa inda Ma'eesha take sai raba ido take don tsoron sa Ma'eesha keji ƙwarai da gaske .

Wuce ki bani wuri!

Ya furta fuskar sa babu alamar wasa ko sakewa. Sum-sum ta juya tana wucewa tare da bashi wuri . Ya Khalil ina kwana . Ta furta da Sauri tana raba shi ba tare da ta jira Jin amsar da zai bata ba . Cike da fara'a ya furta lafiya lau Ma'eesha maza ki yi break fast .

Takaici ne ya kama Aliyu , Humm Wai me Khalil yake nufi ne? Son Ma'eesha yake yi ko mene? Zuciyar sa ta fara masa wannan tambayoyin. Saurin Girgiza kai yayi yana cewa “ a'a Sam ba haka bane ba , don Khalil a wannan watan za'a sanya baikon sa da Rahama. To mene wannan tijaran nasa yake nufi kawai saboda nayi hugging ɗin ta. Ya manta Meye ban sani ba na jikin Ma'eesha. Hattara tsarki Ni nake yi mata amma a yanzu yake faɗa mun munanan maganganu....ko yana tunanin ina jin wani abu dan gane da ita...Aikin banza sai na shayar dashi mamaki tare da shi za'a yi mana baiko dole na fidda ɗaya a cikin biyu , Maryam ko Mimi. Hummmm....sauke numfashi yayi mai huci kana ya cigaba da maganar zuci da cewa “ Duka ba zaɓi na bane....Mami ke liƙa min su , a wannan karon i must accept it. Dole na zabi ɗaya don na ƙaryata tunanin Khalil akaina da Ma'eesha.............✍🏻

Tom kunsan night update Babu yawa🥱 mu tara ana safe lafiya....muje yanda al'amarin zai kasance . Shin waye Mimi??? Sannan kuma Wacece Maryam? Wacce a cikin su Ali gadanga zai zaɓa😄 ya kuke kallon wanga tafiyar......ku Cigaba da biyo alƙalamin mamanteddy✍🏻 . Yau inshallah zamu bude Comment GRP don jin sharhin ku bisa ga wannan labari na rainon soja.......!
[12/20/2023, 7:52 PM] Real~Mamanteddy: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

Page 15
______________________
*Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban yafe ba😭...ga masu buƙatar payment regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*

#Always Alhamdulillah🙏🏻 ________________________

Da wannan tunanin ya nufi falon Mami inda Ya tadda su duka a Dinning table suna breakfast. Takawa yayi yana isa gare su tare da jan kujera yana zama , Bin sa da kallo Mami tayi a ranta tana cewa “ Da'alama Khalil ne ya hana shi wahalar da Ma'eesha da wannan masifaffen morning exercise ɗin nasa”. Dariya ta Gimtse ganin yanda yake cika yana batsewa ita dai Ma'eesha tun da ya zauna tayi ƙasa da kan ta tana sabgogin ta don bata son su haɗa ido bare ya ce tayi wani laifin. Gaishe da General Saleh yayi kana y juya yana ma Mami Barka da Safiya...daga nan kuma ya ɗaure fuska yana mami na fara serving din shi ....Kallon Mami yayi yana cewa “ Mami kina gida gobe? ”.

Ɗago fuska mami tayi tana kallon sa kana ta ɗan Girgiza kai tare da furta “ A'a gobe ina so na leƙa gidan Hajiya na gaida ta ....da wani Abu ne Haidar?. Girgiza kai yayi alamu a'a , yana Cigaba da Karin kumallon sa....Sam Ma'eesha ta' rasa' samun natsuwar ta , haka ta kasa sakin jikin ta .

Kallon Haidar tayi tare da kallon Daddy cike da zazzaƙar Muryar ta wanda tana fara magana Haidar ke furta yi mun shiru ki rage mun murya. “Daddy Uncle Haidar gobe zai koma ko yaushe? ...Dariya ne ya kama General Saleh Wanda sai da yayi mai isar shi kana yace“ Ma'eesha bagaki ga Uncle ɗin naki ba? Ki tambaye shi mana....ya kare maganan yana kallon inda Ali Haidar yake ,yana jin duk abun da suke cewa amma tamkar baiji ba ko baya a gurin. Muryar Daddy ne ya katse su yana Cewa “ Ali kayi shiru Ma'eesha fa tambaya take yaushe zaka koma? . Dariya mami ta sheƙe dashi tana buɗe baki zatayi magana Muryar Jidder ya katse su wanda cike da masifa ta furta “ Tun da gidan na uban ki ne dole ki ƙosa ya koma ”.

Shiru Ma'eesha tayi ta tsaya turusss gwiwar ta yayi sanyi qlau.

Wannan wacce irin ɗabi'a ce kike dashi Jidder? Wani irin mugun hali ne ke gareki? Ina yawan faɗa Miki ki kiyaye mawa Ma'eesha billahil Azeem ranar da na shige Miki ba zakiji da daɗi ba ......! Mami ta furta tana ƙanƙance idanun ta cike da faɗa don ranta ya ɓaci. Muryar General Saleh ne ya katse su yana furta“ Maza Ma'eesha kiyi karin kumallon ki ,idan kin gama kizo Falo na yau zancika Miki alƙawarin ki ....Buɗe baki Ma'eesha tayi tana wangalewa tare da washe shi tana furta “ da Gaske Daddy?”.
Chapter 4 · 0% Book details