← Book details Rainon Soja Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 18

Sashe 16

Rainon Soja Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hummm Jidder idan zaki biyo Ni bismillah amma mayafi bana takan shi a yanzu . Mami ta furta tana mai saurin ficewa daga Falon .

Da Sauri jidder ta bi bayan ta , don itama a yau tana son sanin Wacece Hajara , duk da Tasan Ƙanwar Mami ce , Amma bata san menene yabar da ita gida ba , kuma sannan a yanzu a wani hali take ? Tabbas zata so ganin ta Wannan yasata bin bayan Mami cikin Sauri , Don sau da yawa kafiyar Aliyu da gayunsa ana cewa “ Babu inda yabar ƙanwar Mami wato Hajara , sai dai ita kuma rashin son jama'a musamman talakawa , sam bata son raɓuwa da ƙaasƙantattu , a cewan ahalin Wai ita wayayyace Shiyasa . Bayan Mami jidder tabi inda ita take Driving, Mami ba ɓangaren Hannun dama gaba Ɗaya hankalin ta baya jikin ta duk ta ƙosa ta gan ta gata ga Hajara , damuwarta na tsawon shekaru ”.
Early in the morning
7:00am......

Gudu take yi kaman tare da jijjiga jikinta tana kaiwa da komowa takaici duk ya ishe ta ga zufa dake tsatstsafo mata . Ƙwallah na bin kuncinta . Tun da nake ban taɓa ganin mugu irin Uncle Aliyu ba . Ta furta tana kallon can inda yake daga nesa yana kallon yanda take running exercise ɗin, shikam Hannun sa Ɗauke da Wani mug na coffee yana kaiwa bakin sa a hankali ƙwance ”.

Go! go...!!!

Ta tsinkayi Muryar sa daga can yana mata magana ganin ta tsaya , tana hutawa .

Da Sauri Ma'eesha ta ɗaga ƙafafunta tana cigaba da gudun tare da kukan zuci dana zahiri .

Fiye da minti talatin tana a haka , kana ta fara ganin Jiri Jiri na ɗibarta .

Cak taja ta tsaya tana ganin hazo² 🫨 tana ganin duniyar na juya mata zuwa gida da yawa . Cike da ɗaga murya babu wasa ya furta “ Tsayuwar mene kike yi anan , Ma'eesha na iso inda kike ranki zai ɓaci , zan zane ki anan Wurin , a haka ne zaki je training ɗin Sojan? What kind of nonsense exercise is that? . Zaki Cigaba ko kuwa sai na ƙariko nan??? Ya ƙare maganan cike da Tsawa da Ɗaga murya mai tare da amsa kuwa na cikakken Gwarzon namiji”. Maimakon ya ga tayi wannan kiɗimewar da ta saba yi a duk sa'ilin da taji Muryar sa ko faɗan sa amma a yanzu sai gani yayi tayi baya luuuuuuuuui tana zubewa a ƙasa sharaffff”. Hasbunallahu wani'imal wakeel Innalillahi wa'inna.....ƙasa ƙare magana yayi da Gudun sa a matuƙar kiɗime ya nufo inda take yana ɗagota cak tamkar bai ɗauki mutum ba , kaman ƴar tsana ya ɗaga....yana mai barin wurin tare da nufar moton sa yana bude gidan baya yana shimfiɗa ta , don ya lura Ko numfashi bata fitarwa ,ƙwance take tayi sharɓan wannan yasa hankali a tashi ya fice daga Barikin Sojojin yana nufar Wata asibiti na kuɗi (private hospital) dake kusa dasu .

A harabar asibitin tun daga saman Upstairs ɗin Wannan katafaren Asibitin Nurses da gudu suka fara saukowa zuwa Farfajiyar ajiye moto inda suka hango Aliyu Haidar fuskar sa a kiɗeme, haka gumi ke zubo masa . Idanun sa sun kaɗa sunyi jah . Ɗagota yayi tamkar ƴar tsana yana saɓa ta tare da wani irin manna ta da ƙirjin sa . Su kam Nurses hango kalon handon jikin sa na soja ne yasa su gudu irin haka , don sun san halin sojoji da bakar zuciya . Ƙarikowa garesa suka yi suna kai hannu tare da Kokarin Amsar Ma'eesha tare da cewa “ Yallaɓai kawota mu bata taimakon gaggawa”. Hummmmmm wata irin numfashi ya sauke tare da Ajiyar zuciya mai nauyi, fuskar sa ta sauya , a hankali cike da sarewa da karaya ya furta “ Rayuwata ce! 💔, ku yi mata kallo tun daga nan , idan zaku iya tada mun Ma'eesha na tsaya , idan ba zaku iya ba , na yi gaba na nemi asibitin da suka amsa sunan su ....idan kuma kuka ce zaku iya ,amma kuka ɓata mun lokaci abubuwa suka wuce sai daga baya kuka gaxa... wallahi tallahi na rantse da ALLAH Ma'eesha ta mutu a asibitin nan ko wani Abu ya ƙara samun ta kowa na Asibitin nan babu mai fita da rai .😲buɗe baki Nurse Zulfa'u tayi kana ta kalli nurse narret tana cewa “ Sister ma'amshe ta.....Saurin katse ta Nurse narret tayi tana kai Hannun ta tare da Amsan Ma'eesha daga hannun Aliyu kana tace “ Cool your mind Sir , everything will be okay ” .kamin ta jira jin mene Haidar zai furta da Sauri ta nufi Emargency da Ma'eesha .

Yallaɓai taho ga wuri ka zauna kamin mu fito .

Muryar nurse Zulfa'u ya katse Ali wanda yake kaiwa da kawowa , Goshin sa har wata jijiya ya fito masa na tsananin tashin hankali . Kallon banza ya watsa mata yana cigaba da kaiwa da komowa hankalin sa sam baya jikin sa . Baya ma sani Mene yake fadi a halin yanzu , tun daga zuwan sa , baya tsammanin zai dawo natsuwar sa sai idan Ance masa Ma'eesha ta dawo hayyacin sa. Tabbas a yau a kuma yanzu ya fahimci har a yanzu Ma'eesha rayuwar sa ce! Ba wai kallon da yake kokarin mata bane a yanzu , har a yau soyayyar nan nashi da kulawar da ya saba tun daga yarintar ta babu abin da ya ragu . Fiye da mintina talatin yana a haka gumi ya jiƙa shi sosai , don tuni nurse Zulfa'u ta gudu ta bar sa anan , don ta tsorata da lamarin Aliyu Haidar, ita ko a labarai bata taɓa jin na soja irin wannan ba. Zafin ransa yayi yawa ƙwarai .

Wannan yasa ta nufar emergency don ayi komai a gaban ta , idan Ma'eesha ta tashi to ta tsaya idan kuwa aka samu akasin haka , tabbas ita zata fara guduwa daga Asibitin tun kan a sanar mawa Aliyu Haidar ”.

Shikam Ogan namu Aliyu Haidar jin shiru tsawan mintuna kusan Arba'in yasa Shi fara tunanin nufar emergencyn , dai dai nan Wayar sa ta fara ringing tare da waƙar mum my heart ❤️. Wannan yasa shi fahimtar mai kiran tun kamin ya kai hannun sa ya ɗaga sunan Mami ya bayyana masa . “ Cikin sauri tare da dai daita natsuwar sa yana ƙaƙaro murmushin dole tamkar wacce Mami ke a gaban sa ya furta “ Mami Howfar? How is your day? . Fine HAIDAR where is my baby love ? Ina Ma'eesha na take ? Ta katse shi cike da annashuwa . Ƙirjinsa ne ya buga masa da ƙarfi wannan yasa shi ɗan kai hannun sa yana dafewa kana yace “ Mum she's well , Yanzu ta samu barci amma zuwa Anjima zan kira ki kiji Muryar Babyn naki.

Murmushi Mami tayi mai sauti kana tace “ Alhamdulillah har naji sanyi da ya kasance tana lafiya a yanayin ka ko baka faɗa mun ba nasan Baby Ma'eesha tana jin dadin zaman ta anan , Ka kula mun da ita sosai Ali kana jina ?"…yeah...Yessss Mami ya furta cikin ɗan kame kame . Cikin sanyi cike da rashin Fahimtar komai Mami ta cigaba da cewa “ Ina SO Aliyu ka kula mun da Ma'eesha don Allah ko bayan Raina, bata da kowa da ya kai ka a rayuwa , ina so ka riƙe Ma'eesha ba matsayin ƴar uwa ba , ba ƙanwa nake so ka riƙe ta ba , ka riƙe mun ita tamkar rayuwar ka! A taiƙaice da da hali ka gatanta fiye da kowa ciki har Dani kai na. Ka ɗauke ta tamkar ƴar da ka haifa ko ma fiye da haka . Idan kayi mun wannan To ka gama mun komai Aliyuuu don Allah ka sauke zafin ranka a kan ta , still now she's a child yarinya ce ƙarama ka fini sani ka kula mun da ita sosai ko bayan rai na ”. Mami ki daina wannan maganar inshallah nayi Miki Alƙawari zan kula da ita ”. Daƙyau Haidar thank you my SOJA . 😬 dariyar yaƙe yayi yana jan Ajiyar zuciya tare da cewa “ Love You ma'am , bye bye ”....ƙitttt ya datse kiran yana Fara nufar emergency don ganin halin da Ma'eesha ke ciki .

Kai tsaye ya faɗa inda yaga Wayan babu Ma'eesha babu labarin ta tamkar ba anan aka shigo da ita ba😱 . Keeee!!! Ya daka ma wata nurse Tsawa inda sai da kayan aikin hannun ta suka faɗi ƙasa . Malama ina yarinya ta take ? Ya furta a zafafe idanun sa suna jajir tamkar garwashi jijiyo na ratso masa ta ko ina . Itace Ma'eesha ko? Ta far...far... farfaɗo an kai ta Ɗakin hutawa”. Ta ƙare maganan tana inda inda don ta tsorata da Aliyu . Huuuuuuuwwwww.....Ya Jah numfashi mai ƙarfi kana tamkar ba shi ba , ya furta “ Na gode na gode da kuka taimaka wurin ceto mun rayuwar ta . Zaki iya kaini ɗakin da take . Special room muka kai ta sir , amma muje na kai ka yanzu . Thanks....ya furta yana bin bayan ta ”. Sun fito daga emergency room dinnne kiran taxt massage na mami ya shigo masa inda idanun sa ya fara rawa yana ganin Saƙon kaman ba dai dai idanun sa ke gani ba .

Ga abun da ta rubuta kamar haka ya fara karantawa .
_Hello Am sorry my son , na manta ban faɗa maka duk da Abin na raina , ka tayamu farin ciki mun ga ƙanwata Hajiya Hajara wacce ta ɓata Tsawon shekaru goma sha biyar . Yanzu haka tana gidan Hajiya , kuma tana cikin ƙoashin lafiya 🤗 naji a yanayin ka ɗazu kamar kana busy shiyasa Nima na manta . But a ko wani lokaci kuka dawo zaku haɗu inshallah, please take care of my baby girl , idan ta farka kace mamin ta na gaishe ta ”._
Chapter 16 · 0% Book details