← Book details Muwaddat Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Muwaddat Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

k'arar da k'aramar wayarta ta d'auka ne yasa tayi saurin tura masa sakon ina zuwa, sannan ta mirgina ta d'an mika hannunta ta d'auki wayarta , babanta ne yake son ganinta sai alokacin ta tuna bataje ba ,gashi Kuma tunda garin Allah ya waye ba taje ta gaida baban nata ba ,ta mike da sauri ta nufi matattakalar bene da zai sadata da falon babanta .

matashiyar yarinya ce muwaddat son kowa kin Wanda ya rasa , kyakkyawa ce ajin farko wanda za'a iya sakata a cikin sahun farko na jerin kyawawa Matan duniya , duk da ba fara bace sol , amman muna iya kiranta da wankan tarwad'a, chocolate colour bambamcinta da farar mace kad'an ne ,doguwa ce mara kiba, ba kuma siririya ce ainun ba, tana da murjajjen jiki irin na ya'yan hutu kalar fatarta lu'kwi luk'wi masu zuba sheki, dara daran idanunwanta da dogon hancinta sun taimaka wajen fito da kyan fuskarta, tana da d'an k'aramin zagayayyen baki mai kyan fasali, kmr irin na Muhammad auwal ,game da fararen hakora kuwa ba'a magana ,kallo daya zaka yiwa muwaddat ka fahimci gata ya wadata tattare da shagwaba ajikinta , duk da fuskarta batayi Kama da shagwababbiya ba, Amman in kaga yadda take sakewa tana zuba shagwaba a gaban iyayenta sai kayi mamaki ....
Yadda fasali da kyawun surarta take haka Muhammad Auwal yake kusan komai nasu iri daya bambancinta dashi ,shi fari ne sol ita kuma chocolate colour..

Mmn sudais
[12/19, 11:01 PM] +234 806 956 2358: 💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~

alhamdullahi am back again.

warning!!!

for the first time !!!! i will like to say," don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people, if you read it ,is for your own risk.

WATTPAD @HAUESH

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

page 2

..tana hawa benen mahaifinta, ta d'an zuge kofar glass din parlour'n tashiga bakinta d'auke da sallama, sai alokacin gaanta ya fad'i sakamakon tunawa datayi da kanta babu d'ankwali ,daga ita sai wata hadaddiyar doguwar rigar, yar saudiyya wacce ta sha stone work ,amman kanta babu komai ,hakan ne yasa dogon gashinta data had'a ta tufke da ribbon suka bayyana .

har ta shiga parlour'n tana fargaban fad'an da dad dinta zai yi mata idan yaga kanta babu dankwali,
jikinta a sanyaye ta k'arasa gaban dad ta d'an durkusa ta gayar dashi kana tace" dady gani .

alhaji muhamud mai agogo ne zaune cikin tangameman parlour'n shakatawarsa, wani d'an k'aramin table ne agabansa, cike da kayayyakin motsa baki iri iri..
alhaji Muhamud ya d'an d'ago ya dubi yarsa muwaddat cike da fara'a da sakin fuska, sannan yace "muwaddat me kike yi acikin gidan nan tun safe baki lekoni ba .

tsadadden murmushinta tayi sannan tace dady babu abinda nake kawai a kwance nake, ina d'an hutawa, jira nake sai ka sauko sai na gaisheka.

" ok babu damuwa ince duk kanen naki sun tafi makaranta ne?
"eh sun tafi har ma direba ya dawo "to mai maman taku takeyi da bata zo ta kwashe wad'an kayan abinci ba?

"dady wanka tashiga, amman nasan zuwa yanzu ta fito"
yace" yanzu hk baki ci abinci ba ,kika je kika kwanta ,maza ga abinci nan ki zauna kici "dady bana jin yunwa ,ni bama yanzu zanci abinci ba .

"anya muwaddat kina kyautawa rayuwarki tunda kika xo gidan nan kullun sai ayi miki fad'a akan cin abinci amman bakya ji, wai ke yar gayu ko ?
tayi murmushi kawai, shi kuma yaciga da mgn "ina kika ta'ba ganin ana gayu ciki babu komai.
ta sake yin murmushi sannan ta mika hannunta ta d'auki apple guda d'aya ta kai bakinta ta gutsura tana niyyar tashi yace "ba tafiya zakiyi ba, ki zauna ina son muyi magana dake"
ta mike cikin natsuwa ta koma kan d'aya daga cikin kujerun na alfarma dake zagaye da parloun ta zauna tana jiran abinda zai gaya mata.

ya dubeta kana yace "muwaddat me yasa baki son d'aura d'ankwali?
" wato kin fi son kullun sai na miki fad'a akanshi ko?
"tace dady kayi hakuri wallahi mantawa nayi kuma kaina tsantsi garesa idan na d'aura d'ankwali baya zama sai yayita zamewa yace "zaki san gashinki mai tsantsi ne duk ranar dana saka aka aske miki kan na gata gayu..

muwaddat ta d'an langwa'be kai a kujerar tana dry yake, tasan fad'a kawai yake bazai iya aikata hakan ba..

"au gani kike da wasa nake yi, shi yasa har kike dry ko?
cikin shagwaba tace "to dady to ita umminah tana ina da har zata bari a aske min gashi?
"ai tunda bakijin magana daga ke har ummin taki na daina saurara muku tunda bata iya kwa'barki komai kike so sai ta biye miki, nan gaba in kuka yi wasa agaban ummin taki zan sa bulala in zaneki in ga yadda zatayi "a'a d'an Allah dady kayi hakuri na tuba bazan sake ba , in dai kan d'ankwali ne daga yau zan dinga d'aurawa "

sukayi 'yar dariya gabad'aya sannan yace "wai kuwa kinsan ma abinda nake shirin yi miki magana akai ?
ta girgiza masa kai "bansani ba daddy "yace to karatu nake son na samar miki a jamiar United Kingdom ...

muwaddat tayi saurin dafe daidai saitin zuciyarta dataji yayi wani irin mahaukacin bugu da karfin gaske, saboda tsanar karatun da tayi ,a tsarinta sam tafi bukatar yin aure akan wani karatu, ta girma da muradin son yi aure da wuri saboda yanayin halittarta ,sai dai tsawon lokacin nan bata samu wanda yadace daita ba kmr kaninta auwal wanda take ganin da wuya ta mallakesa arayuwarta, tunda ta kammala karatunta na diploma ,ta cire rai da wani karatu, nest budget dinta shine aure,ita aure take so ba karatu ba. sai dai ahankali zantuttuka mahaifinta ke shiga cikin kunneta kafin daga baya tace "wani irin karatu kuma dady ?
"nifa banida muradin tsanata karatu mai zurfi"

"kin ci gidanku dole kiyi karatu mai zurfi domin shine burin mu iyayenki, na asali da iyayen goyonki ,guda nawa kike yanzu da zakice baki da muradin karatu idan bakiyi karatu a halin yanzu ba uwar me zakiyi?
aranta tace "aure mana daddy ......

" yanzu ne daidai ki natsu ki tsaya kiyi karatu amatsayinki na yarinya yar shekara ashirin da haihuwa "daddy ni dai banason karatun nan yanxu kabarni kawai iya dilomar ma dana ta isheni .. "

"haba muwaddat ni fa nafi son kiyi karatu mai zurfi Allah yasani, "to da kika nace baki son karatu,aure kike so ko me ?

muwaddat ta d'an noke kai ala'mun jin kunyar mgnrsa tana dry "kinga nifa Allah yayoni da mugun son karatun boko bansani ba kodan nasan dadin karatun ne?
"ki taimaki rayuwata dataki ki cigaba da karatu, kafin muwaddat tace wani abu hjy hajara tashigo parlour'n wanda tun kafin ta k'arasa shigowa parlour'n take jin yadda alhj yake jaddawa muwaddat zance karatu mai zurfi yake son tayi.

da sallama tashigo parlour'n tana "cewa ka rabu da wannan yarinya mara wayo kawai ,in da kai ya waye da karatu nan ,shine ita take cewa bazatayi ba, tasamu guri ta zauna tunda bataso "idan bakiyi karatu ba uwar mezakiyi uhmmmmm?

"ki duba kiga yadda mata suka samu cigaba a dalilin karatu mai zurfi, ita kanta ummin taki tafison kiyi karatu mai zurfi kafin aure,amman shine dan iya shege kike cewa baki son karatu?
"baki son karatu sai me?

muwaddat tayi shiru tana jin kmr fito ta sanarwa da iyayenta burin zuciyarta, amman kunya tattare da fargaba ya hanata "ki dai gaya mata gsky karatu na da mutukar mahimmanci agurinta bari ummintata takaraso muji mai zatace, alhj muhamud
na gama fad'ar hk ya mike tsaye ya sa kai ya fice yana takaicin rashin son karatun da muwaddat take yi...

a harabar gidan yaci karo da motar dataje d'auko kanwarta da suke ciki daya, direban gidan na k'ok'arin daidaita tsayuwar motar yana ganinta ya fad'ad'a faraarsa sannan yaja ya tsaya yana jiran fitowarta, hjy mukarama ta fito a natse tana sanye cikin shiga ta alfarma doguwar riga ce har kasa sanye ajikinta da madaidaicin hijab, amman kallo daya zaka mata kasan cewar akwai gidan rana da tsantsar gogewa irinta 'yan boko atattare daita.

ta k'araso ahankali inda d'an'uwanta yaja ya tsaya yana jiran k'arasowarta "kar dai fita zakayi Yaya ?
"eh fita zan yi wai kafin ki karaso,dama wacan 'yar taki ta nemi 'bata min lokaci da tuni na bar gidan "

"me kuma baby muwaddat tayi ?
"da ita kullun bata wuce laifi agurinku shiyasa sam bata son zuwanta garin nan amman nake matsa mata "

"ai duk ke kike d'aure mata gindi amman nasan yanxu idan kika ji abinda tayi sai ranki yafi namu 'baci yadda nasan kike da kulafucin son tayi karatu.. "au akan karatu ne?

"akan shine mana wai yanxu nake mata maganar sai cewa tayi ita bata da muradin cigaba da karatu"

hajiya mukarama tayi murmushi tace "manta da wannn shirmen nata karatu d'an ada tayi sa, dan ma inaji tsoron gur'bacewar da rayuwa tayi yanxu ,ai da tare aka had'asu da bunayya "

"nima abinda naso kenan amman naga kamar ita bada raayin ma yin karatu, ni dai zan fita idan kin shiga kinsan yadda zakiyi daita "

"ai tafiya ma zamuyi zaman shirun ya isheni ni kad'ai a gidan daman itace abokiyar hirar tawa sukayi sallama yayi hanyar waje ita kuma ta k'arasa cikin gidan

*********
alhaji mahamud shine asalin mahaifin muwaddat, sai dai ba a hannunsa ta taso ba, ta girma ne a hannun k'anwanrsa da suke uwa daya uba daya , wato hjy mukarama da mijinta alhj ishaq , hjy mukarama da mijinta suna mugun son muwaddat ,babu irin kulawar da gatan da basu nuna mata ba , ko d'an cikinsu albarka .
Chapter 2 · 0% Book details