Sashe 30
Mutum Da Duniyarsa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Aliyu kasan miyasa na kiraka kuwa?”.
“A'a baba”.
Zama malam ya gyara sosai yana murmushi, “Wato Aliyu abari ya wuce shike kawo da rabon wani Na hango maka”.
Kallon malam, Aliyu yayi dan bai fahimci inda zancen ya dosaba.
Malam yakumayin murmushi “Zancen yarinya Jiddah nake magana wadda mukaje saudia, wannanfa damace akaro Na biyu tazo mana, Na fahimci tun a saudia akwai wani Abu a ranka game da ita, amma sakaci irin naku da wautar k'uruciya yasaka yima lamarin rik'on talala Wanda lallai idan kayi wasa zaka ciji yatsa a daga baya. Zancen danake maka yanzu haka tun muna saudia naji Sarkin Musulmi yana waya da Mai d'akinsa akan sha'awar naimawa d'ansa auren Jiddar”.
Da sauri Sheikh Aliyu ya kalli malam cikin waro fararen idanunsa.
“Ba ido zaka zarominba, kana sontane? Kokuwa hasashenane kawai nakeyi?”.
K'asa Sheikh Aliyu ya maida kansa yana susar k'eya, fuskarsa d'auke da murmushi yace, ”Inason na cika maka burinka natun farko Baba, sannan harga ALLAH yarinyar ta kwantamin arai”.
“Alhamdllh Aliy, lallai nayi farin ciki, ALLAH yaymaka albarka. Tofa a wannan karon bazamuyi sanyaba, dan insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zanje musami mahaifinta da zancen, sonake ana gudanar da taronan da za'ayi washe gari a d'aura auranku”..
Acikin Zuciyaryarsa yace, “ALLAH dai ya tabbatar Baba”.
★★★★
Tun a ranar malam baiyi sanyaba ya Kira Uncle Yahya sukayi maganar.
Wannan zance ba k'aramin farin ciki ya saka Uncle yahya ba, dan haka shima baiyi sanyaba ya doka waya zuwa Adamawa domin gayyato kawunansu guda uku suzo ayi dasu, dan baya son Abba ya sake basu Matsala a wannan karon. Sannan yakira Abba ya Sanar masa shima, da to kawai ya amsa saboda a time d'in suna tare da Hajia Hindu.
Washe Gari tunda asubahi su Kawu Safiyanu suka baro Adamawa kuwa, cikin amincin ALLAH saigasu sun iso da wuri, sun huta sannan sukaje suka gaida Umma da tayata murna, Albarka dai Jiddah dasu Zarah sunshata. Uncle Yahya dai bai fad'a Mata abinda ya kawosuba, dan yafison a kammala komai sannan.
Daga nan gidan ABBA suka d'unguma, dukkan Abinda za'a iya buk'ata Na tarbar bak'i saida Uncle yahya ya tanada daga gidansa suka tafi dashi, dan baya buk'atar abinda zai 6ata ransa a gidan Abba.
Abba yayi mamakin ganin su Kawu Surajo sosai, dan haka yayta bin Uncle yahya da kallon tuhuma, yayinda shikuma yay biris tamkar bai gansaba. Sunyi kusan zaman mintuna talatin kafin hajia Hindu ta shigo gaishesu tana wani yatsine-yatsine, babu Wanda yabi takanta, dan Uncle yahya ma ko kallo bata isheshiba.
Tunda ta fita take masifa wai Uncle yahya yakawo su Kawu Bliya maula, duk sunzo sun cika Mata gida da warin talauci.
Tun Uncle yahya da Abba na zuba idon ganin hajia Hindu ta kawo ruwa har suka fidda ransu, dan haka Uncle yahya yamik'e ya fita, mintuna kad'an yafara shigowa da kulolin abinci, dandanan ya cika tsakiyyar falon da kayan arzik'i, ko zama baiyiba daga ajiye Na k'arshe sukaji shigowar mota. Hakanne ya saka Abba had'iye tambayar dake ransa suka mik'e suka fita domin tarbo su malam.
Gaisuwa sukai cikin mutunta juna, kafin Kai tsaye malam da kansa yafara fad'in abinda ya kawosu, dan a ganinsa da zafi-zafi akan daki k'arfe.
Kafinma Abba ya tofa nashi tuni su Kawu Safiyanu sun bada Jiddah tareda addu'ar sanya alkairi.
Dad'i ya cika zuciyar malam, cikin fad'ad'a murmushinsa yace, “Muda mukazo Neman izinin Fara Neman so Kuma sai ace amma bamu?”.
Kawu Surajo yay Y'ar dariyarsu ta manya, “Ai malam Kai ubane, kimarka tawuce kazo Neman izinin zance kawai ka tafi, dan kaima mai iya aurar da Hauwa'u ne ko bama a wajen, to balle kuma babban mutum irin Sheikh Aliyu yaga yarinyarmu yace yanaso harma a tsaya jan dogon zance, badan badan bama mu saimuce ama d'aura ka tafi da amaryar kawai”.
Dariya suka sanya gaba d'aya suna musabaha, Malam yace, “Wlhy da hakan zata kasance danayi murna kuwa. Amm to indai hakane mizai hana indai bamuyi gaggawaba ranar juma'a ta sama kawai a d'aura”.
“Malam indai hakan yamaka tomu bamuda ja wlhy, tunda dai yarinyarnan ta ta6a aure, banga wani abun jan jikiba ma”. Uncle yahya ne Mai maganar’.
Atake kowa yayi na'am da wannan magana, ganin haka shima Abba saiyabi ayarin masu amsawa cikin yak'en dariya. Take annan malam ya ajiye sadaki naira dubu d'ari biyu, amma sai su Kawu Bilya suka nemi a rage.
Malam yace, “Lah-lah bazamu rage ko sisiba, k'arawama yakamata muyi, wato abinda muka kasa fahimta da 6al6alcewar aurarrakinmu na wannan zamanin da sakaci Na yawan sakin aure to k'arancin Sadaki yana ciki, inda za'a ajiye dukkan bidi'oi dake gudana yanzu a shagalin bukukuwa aringa tsawwala sadaki ga masu aure to lallai sai ansamu sauk'i sake-saken aure. Yaro ya biya dubu hamsin ko talatin sadaki, da anyi aure taimasa ba dai-daiba saiya sauta, idan anyi magana yace ga matanan ledar ruwa tafisu wahala, to yasan daya samo y'ar dubunsa d'ari biyu ta Isa masa wani auren, inda ace ana saka musu sadakin Mai tsauri mahaifin yarinya yace baya buk'atar kowacce bidi'a amma sadakin y'arsa dubu d'ari biyu ko uku ko hud'u to wlhy saisunji shakkar sakin, dan sunsan kafin su tara wani sadakin sun jigata, sannan za'a canja tunaninsu ga wanann shaid'ancin Na fati-fati dasukeyi, kunga mutum da kud'in sadaki zaiji kokuwa da kud'in bidi'ar aure?. To ni yarinyata jiddah ma ta girmi sadaki dubu d'ari biyu wlhy, kaf yarana ban yarda abani k'arancin sadaki a kansuba, bankuma yarda mazan sukai mafi k'aranci ba suma, sannan bana biyama yaro sadakinsa, zandai taimakeka da wani abun, amma kud'in sadaki ka nemo kayanka. Wannanma Aliyun da kansa ya bada abinsa”.
Kai su Kawu duk suka shiga jinjinawa cikeda gamsuwa da maganar malam d'ari bisa d'ari, dajin a ransu suma zasuyi aiki da wannan shawara Mai k'yau da nagarta gamai hankali.
Fita sukayi sukabar su malam suci abinci, Wanda saida uncle yahya yayta rok'onsu sannan suka amince.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan tafiyarsu Malam su Kawu Surajo tasa Abba gaba sukayi zuwa gidan Umma, lokaci Zarah da Jiddah basannan sunje gidan Aunty Nafisa, walida da Umma ne kawai a gidan.
Mamaki sosai Umma tayi, ita tunaninta ma ko dama Abba ne yakai k'ararta itada Uncle yahya wajen su Kawu Safiyanu akan barin Jiddah taje Saudia. Amma da suka zauna sai taji jawabin nasu bai doshi canba, tuni farinciki ya lullu6eta, dan ita wlhy d'ari bisa d'ari ta amince da wannan zance, saidai tabisu da addu'ar ALLAH ya sanya alkairi kawai.
Abba dai tunda aka zauna baice Uffanba, hakan kuma bai damu Umma ba, Ana cikin maganarma saiga su Jiddah sun dawo. Da hanzari tayi niyyar komawa cikin rawar jiki, Uncle yahya yace, “Daure ki shigo kinji Jidodona, k'arfafa zuciyarki kinji Y'ar albarka duk iyayenkine”.
Jikinta na tsuma Zarah ta kamo hannunta suka ida shigowa, tuni harta had'a zufa, muryarta na rawa ta gaishesu.
Kawu Surajo yace, “ALLAH ya yaye miki kinji Hauwa'u, ALLAH ya warware wannan k'ulli cikin hikimarsa da rahamarsa, Yakuma gaggauta saka miki”.
Da amin duk suka amsa, sai dai banda Abba dayay shiru yana saurarensu dajin haushin su Kawu surajo, kenan suma sun amince da k'aryar ciwon Jiddah Na shirme?, babu Mai bashi amsa dan da zuciyarsa yakeyi.
Kawu Bilya ne yaymata bayani akan abinda ya faru, sosai mamaki ya kamata, wannan babban malamin da duniyar musulinci ke alfaharine zaice yana sonta da aure? Halan kallon tsoro yaymata? Ina ita ina shi?.
“Kinyi shiru Hauwa'u, ko bak'ya sonsane? Kinsanfa yanzu ke bazawarace, kinada damar za6en miji da kanki, wannanma munyi miki katsalandan ne saboda ganin nagartarsa, kuma tunkan aurenki Na farko yanemi aurenki ALLAH ne kawai ya k'addara saikin aurin wancan da kika fito, ammafa idan baimikiba lokaci bai k'ureba, ki fad'a mana tunda ba d'aurawa akayiba”.
Idon Jiddah Na kwarar da hawayen da batasan daliliba tace, “Kawu duk yanda kukayi wlhy ni Mai biyayyace a gareku, zankuma kar6i dukkan abinda kukazomin dashi hannu biyu, dan nasan bazaku cutaminba”.
Ajiyar zuciya duk suka sauke, kowa yashiga saka Mata albarka sannan aka sallamesu. Dad'i tamkar zai kar Zarah da Walida, tunda suka shiga d'aki sai kwasar rawa suke, harda rairama Jiddah wak'ar amaryar ya sheikh.
Itadai shiru tai musu, saima kanta data kife a filo tana cigaba da hawaye marasa dalili.
Tuni zancen auren Jiddah yagama karad'e dangi, kowa yaji saiya tayata murna da wannan canjin alkairi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Su malam suna dawowa yakira Aliyu ya shaida masa yanda akayi, dad'i sosai yaji a ransa, Wanda har kamilallaiyar fuskarsa saida ta nuna, ayayyanawa yake aransa nanda kwanaki sha uku zai zama ango a Karo Na biyu kenan, wannan hikimace ta ubangiji kawai, dan baima ta6a hasashen aurenba a kusa balle Mata biyu a lokacin da bashida tazarar nisa.
Sosai malam yaymasa nasiha akan adalcin had'a Mata biyu da shawarwari, dukda yasan shimad'in yasani.
Sheikh Aliyu yay godiya da kar6ar nasihar malam hannu biyu. Shi duk saima yaji shakkar tunkarar Maimunatu da batun, gashi dama batada lafiya a y'an tsakaninnan, kuma yana k'yautata zaton cikine da ita, dan dukkan alamun mace Mai yaron ciki sun bayyana a gareta, shiyyasama datak'i yarda yakaita asibiti bai matsa mataba yadai samo Mata magungunan da bazasu cutar da itaba.