← Book details Mijin Kwaila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 8

Sashe 4

Mijin Kwaila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anee dake zaune sai juya cokali takeyi tama gaza gane a duniyar datake ayanzu.

Kusan 5mns daga kiran zahra ba zahra ba isha'q?

Badon kada tabata rawarta da tsalle ba dataje anyi duka mai yuwuwa Sam bamazata jura ba.

Zuciyarta na ayyana mata wama yasan mesukeyi a d'akin kai namiji munafuki tafada aranta zuciyarta na suya.

Kamar daga sama suka ganshi ya runtumo a guje yana haki da dariya ga zahra da katon filo a hannu tana biye dashi.

To be continued
*MIJIN 'KWAILA..2*
*Chapter 7*
*By Maman Meenat*
Zagayowa yayi yazauna mazaunin direba,yayinda zahra tasake takurewa gefe guda itakanta tagaza tantance dalili kokuma hujjar dayasaka tsananin kunyar yaa isha'q takeyi har haka.

"Maa princess, wanann kunyar duk tawace?"tura baki tayi gaba tana kauda kai gefe.

Sake kallonta yayi yana dad'a mamakin wai zahranshi ce tagirma haka acikin abunda baigaza shekaru uku ba,haka kawai yakejin zallar nishad'i yana zagaye dukkanin gabobin jikinshi.

Dan rausayar dakai yayi gefe" Haka yakamata ki tarbi mijinki zahra,babu d'an oyoyonnan ma bare nasamu tagomashin kiss dinnnan irinna I miss u"
Yafad'a yana kashe mata ido d'aya.

"Innalillahi,"
Shine abunda tafad'a aranta,saikuma tadafe kirji idanuwa waje aranta tana maimaita wai kiss?

Tabdijam!

Lallai ma yaa isha'q zuwa turai dinnan yaqaro wulakanci.towaima kawai saita kama yimashi kiss saikace wata er-iska.

Jin tayi shiru bata tankaba yasakashi mi'ka hanunshi"let me see ur books I know maa lady is very talented.

"
Fito da idanuwa tayi waje,cafd'i inazata kai kunyarta idan yaa isha'q yaga bra din dake acikin jakartata
Da inna-inna tasoma magana",iyye na'am hmm ayma bakomai acikin jakar ban'ajiye komai bafa."
Tafad"a yayinda tasake kwakume jakar a kirjinta.

Zuba mata idanuwa yayi,komai na zahra is differ to others.

Dariya sosai tabashi amma saiya dake yace"bani mana ingani nadaisan matata tanada kokari sosai".

"A'a nikam banida kokari pls kabarni."
Tafad'a kamar zata fashe da kuka.

"Shikenan is ok." Yafad'a yana sa'ka hannunshi na hagu Wanda badashi yake driving ba acikinnata,ahankali yake murza hannunnata yana mamakin tsananin laushi da santsin da hannun yakedashi.

Yayinda agefen zahra takejin kamar tasaki fitsari a wando tsabar tsorata datayi gawani kunyan yaa isha'q din datakeji haka kawai.

Rasa hanyar kwatar hannunta tayi,saikuma dabara tafad'o mata arai.d'an zabura tayi tasoma soshe-soshe isha'q dasauri ya gangare gefen titi yasoma tambayarta lafiya.

Tadanne dariyarta ganin yanda ya rikice tasake kya'be fuska kamar zata fashe da kuka"wayyo kilafa cinnaka ne ya cije
Tafad'a tana masa gwalo ganin ba'ita yake kallo ba.

Isha'q kam tanayin gwalon akan idanunshi yaganta ta side-mirror don haka tuni yagane shirinta.

Rikicemata yayi yana fadin "oh babi let me see" jawota yayi yasoma shafa cikinta data nuna alamar anan kwaron ya cijeta.

Gaba d"aya zahra tagama tsurewa,wayyo Allah garin neman gira zata rasa ido.

Shikam gogannaka d'age rigar yasoma kokarin yi kasancewar motar tinting ne glass din babu mai ganinsu.

'Kara zahra tad'an saki dafad'in"wayyo pls yamadena zafin ashe bama cinnaka bane ba."
Bakaramar dariya tabashi ba yasaketa yana murmushi kawai
Sai dai yad'auke y'ar jakar dataketama kumuiniya.

Aitaana ganin haka takulle idanu shikenan dai karshen tuka-tuka tik!

Abunda take boyon saiya gani.

Hannayenta tasaka takulle idanuwanta dashi,yayinda isha'q yasoma bud'e jakar abunda yagani acikine yabashi dariya yadauki guda daya wata pink colour yana juyawa tayi kyau over.

Kallonshi ya maido akan zahra dakejin kamar kasa tatsage tashige ciki don kunya
"Iyye ammatana angirma duk wannan size din nakine".

" Shikennan deeja kingaama cutata abunda nake gudu kenan,zahra tafad'a aranta.

Amma afili kasa kallon isha'q dintayi,kanta boye acinyoyinta tace "nifa banawa bane ba,nibanma san dashi a jakata ba."
"Dagaske,kina nufin bazai maki ba."
Isha'q ya tambayeta da sigar zolaya.

Duk da bata d'ago kantaba cewa tayi "nodai banawa bane ba."
"Naji,tunda kince banaki bane barin gwada maki idannaga yayi maki tonasan nakine inkuma yamaki yawa nasan banaki bane ba ."
Dasauri tad'ago kan dafad'in "iyee kace mene".

Bakaramar dariya tabashi ba,y girgiza kai
" yakamata infara yaqi da sabuwar kunyar nan taki tun yanzu donnasan my wifey tatashi daga kwaila takoma big madam.

Ya'ilahee isha'q kam yanason kasheta da tashi salon fa.
*LOADING..*
*MIJIN 'KWAILA...2*
*Chapter 04*
*by Maman Meenat*
Wani mayataccen kallo takebin zahra dashi wanda bazaka ta'ba iya tantance kona menene ba,lokaci guda tsanar yarinyar da kiyayyarta ya'kara samun gindin zama a zuciyarta
Kama hannun anee tayi tazaunar akan 1seater, ranta matuka ajagule yake.aneesa dai aneesa tata y'ar gatanta da batasan kwa'baba bare kyara itace yarinya karama tama wannan lahani?

Taso kwarae awajen ta lakad'awa zahra dan karen duka.Amma kuma data tuno insun bugeta zasu tonawa Kansu asiri yasakata yin murmushin takaici ta bayan gida ya kaamata ta'bulloma yarinyar nan.don taga alamar lallai wankin hula yanason kai y'an maza dare.

Aneesa kuwa ganin mum batace komai ba yasakata sake hasala tamike tana kundume-kundumen zagin saitaga bayan zahra,Dr.aysherh tana hanata amma inaaa kitchen tanufa tararumo wu'ka tayo kan zahra dake tsaye gefe ko gezau batayi ba saima sake kunburi datakeyi kamar kububuwa.

Da gudu Dr.aysheeh ta rike anee tasoma mata fad'a"au kinason tona mana asirine aneesa?

Kilumama y'ar mutane wu'ka kibarmu da tsugunne tashi da alkalai?

To banason raahin hankali kin gannin nan."
"Shige muje..."
Tafad'a tana kama hannun aneen da idanunta ke fitar da ruwan hawaye.

Bedroom suka shige har saida Dr.aysherh ta maida kofar ta murza key kafin tace"zauna inbaki extra care kafin muga abinyi".

Y'an gwaje-gwaje tayima anee tasamata magani a Inda zahra ta cijeta sannan taja hannunta suka zauna tasoma tambayar abunda yahadata da zahran.

Anee bata rufa mata komi ba ta sanar da'ita yanda sukayi.

Murmushi Dr.tayi kafin tace"lallai aneesa ada ina tunanin nahaifi jaruma jajurtatta dazata tsaya da kafafunta ko bayan babuni,amma ayau na tabbatar haryau *igiyar 'kuruciya* tana jani injaka dake.har yaushene zaki biyema yarinyar da batada hankali ki hada jiki da ita?

Kada kimanta itaafa renon tuwon dawa miyar kuka ce,kekuwa renon cake da ice-cream ce bazaki taba hada jikinki danata a mazauni d'aya ba.kina ganinta yarunya wannan me zubin 'kartan koni sainayi da gaske in cimmata
Sannan shi zama da kishiya Aida hila da munafurci akeyin galaba,zaunawa zakiyi kisiye zuciyar kowa a gidannan da kyautatawa shi kanshi isha'q din ki zame masa chewing gum kitakura duk wata hanya dazata sadashi da had'uwa da wannan akuyar yarinyar itakuma a gaban kowa kijata a jikinki tayanda duk me kikace tayi baza'a karyata ba.

Amma daga karkashin kasa zataci ubanta,saita bar gidannan da kafafunta.

Ajiyar zuciya anee ta sauke itafa duk tama manta da makaman yakin data tanada don d'ana bom dinta azuciyar isha'q tazauna yarinya karama na shirin dasamata hawan jini.

Kwafa tayi da shu'umin murmushi lokaci guda ta tuno shawarar nafee kawarta batasan lokacin data fashe da dariya ba.

"Don't worry mum I will hndle this prblms with my hand"
Murmushi Dr.tayi "yh I know, I will thrust you my dear."
Cafewa sukayi kamar kawaye,
Sai alokacin anee tasamu natsuwar zuciya.

Da taimakon mum dunta suka gyara gidan saika rantse wani Abu na 'barna bai faruba,wanka tasoma fesawa duk kuwa da azabar da kan nonon yake mata lokacin da ruwa ya ta'bashi aranta tana ayyana miyagun aguguwan da zata aikatama zahra ada batasan ta tsani yarinyar ba amma yazuwa yanzu tariga da ta hakikancema kanta lallai kiyayyar Zarah me karfi ce aranta.

Doguwar riga ta shadda ta zuba ta kashe d'auri abunta tayi kyau kwarai dinkin yadace da yanayin jikinta mara kiba sosai.

Sai kusan 4:pm mum din tata tawuce bayan ta'ajiyemata maganin mata kala-kala nasha dana shafawa da gargadin tadena wasa dasu don dasune ake juya kan nimiji dan ubanshi ko wanene.

Anee aranta cewa take"inako zanyi wasa da damata ai damara yanzu na daura shege ka fasa.

Kitchen takoma tasake shirya tuwon semovita da miyar egusi,Wanda tasan gwaggo rabi tana matukar so da tsimakon inna delu.

Don dai on her own idea bazata iya girki mai ma'ana haka ba.

Gefe guda ferfesun naman sane dayaji albasa da spices yana tashin kamshi sai macaroni data sake gyarawa ta hada lemon kwakwa da dabino tagama komai with tym.

Zaunawa tayi tasake tsular uwar kwalliya cikin very cotton na lallausan gown din material, tana mutsuka humra a hannayenta tajiyo horn din Dr.rukayya saida ta bankama kofar harara tamike da azama kallabi a hannu tanufi get din.

Alokacin tuni tagama parking a parking loat,anee kam tana zuwa hanan tacafe sama tana juyawa tana dariya da lakatar hancinta"y'ar mumy yau ina kika 'boye kikamun wayo baki dawo da wuri ba?"
Tafad'a tana dariya da satar kallon fuskar Dr.Rukayya don ganin yanayin karbuwar sabon salon nata.

Kamar yanda ko ta zatan hakance ta tabbata don murmuahi mumyn tayi tana bada amsa"office tasaka driver yakaita wai yau wajena zata wuni."
Anee tasake dariya tarike hannun hanan tahad'a da hand bag din mummyn suka jero atare kamar 'kawaye,duk da mummy tana korafin anee tabata jakar kada kaya sumata yawa,kiyawa tayi saima sake tsokano hanan take da zance"autar mummy gobe kada kibi mum asibiti zamuje saloon mugyara kanmu da farcenmu and amaki wani hadadden style na kitso yana a wayata muje kigani yanada kyau Sosai."
Dad'i yakashe hanan don akwaita dason kwalliya tasoma murna Dr.ru'kayyama farin ciki yagama cikata.

Saida taraka mum har part dinta data sake gyarawa ta feshe da air freshener takama hannun hanan sukabar d'akin bayan ta dauki kayan dazata canja acewarta subar Mummy tahuta takwaso gajiyar office.

Dr.ru'kayya tayita samata albarka,sam tama manta da wata zahra agidan abunda bata ta'ba yiba kuwa,don ka'ida kullum tadawo saita tambayi ina zshran amma yau rana d'aya kissar anee tasaka tama manta da 'kurar data kwaso wata wai ita zahra.

Hmm....

Anee kam jin har tabar part din mum bata tambayi zahra ba ranta'kal tafara d'ana makaminta na farko kenan.

Dakanta tahad'ama hanan ruwa a toilet d'inta tayi mata wanka duk da hanan tana no'kewa itafa tafara zama ammata
Anee kam baki ta ta'be yanda kirjin hanan yake kamar shafen siminti bata raba d'aya biyu haaka na zahra yake,kai namiji barshi da jaraba yo inba jarababa anan har kace kayi aure?

Tsakin dabatasan yafito ba taja"mtsww"
Dasauri hanan tace"Anty lfy?"
Shafa kanta tayi"zuciya ke tashi kanwata.'
"Eyya sorry anti let me tell mum"
"No!"
Am ok now"
Anee tabata amsa tana gyara mata zaman top din jikinta.

Fira tadinga jan hanan wanda haakan ya d'aukemata kewar zahra batamako tambayi ina zahra dinba.
Chapter 4 · 0% Book details