← Book details Mijin Kwaila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 8

Sashe 2

Mijin Kwaila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aibanan yakamata kazoba wajen waccen kwailar yakamata kakoma tunda harzaka iya bata dukkanin tym dinka abinda kagaza bani.kagoyata akan gadon bayanka kana dariya da ita abunda baka taba kwatantawa agareni ba.saikaje kagama lagujeta sannan kadawomun nan kana zaton zan kawarma da kishin ruwanka ko?"
Saikuma tasoma kuka tanacewa"don Allah isha'q meyasa baka sona,meyasa ka tsaneni why...isha'q why...u hate me"
Baibari taqarasa ba yahade bakinshi danata yasoma bata darasi mai zafin dayasakata manta awacce duniya take,dayake er hannu ce sannan kwarai isha'q yakaranci lagonta adan zaman dayayi da ita .

Saida ya tabbatar tagama shiga hannu sannan yarabu da ita yadauketa cak ya aza bisa cinyarahi ahankali yasoma magana"kidena cewa banasonki anee kisani ke babbace bazai yiwu duk abunda nayima zahra yazama lallai saina aikata agarekiba kamar yanda itama bata samu 100%na abunda nake baki,itafa goyon kadai kikesha kekuwa megoyonma sha kikeyi ba?...."
Yakare maganar yana daga mata gira.

Ta kyalkyale da dariya kamar ba itace maiyin kukaba,fadawa tayi jikinshi suka haura babban filin jirgin Aminu kano...bansani ba killa jidda suka nufa
Zahra kam tana gama wankanta fitowa tayi abinta daga ita sai pant data saka tun a toilet, batako dubi inda kayan shafa sukeba takutsa karkashin gadonta tajawo wata yar bakar leda tulin gorubane da magarya aciki saikuma taura.

Qirgawa tayi taware wasu agefe,takulle ledar tamayar kasan gado tadauki goruba guda tadage dai-dai karfinta tana gwaguya tana wasa wakokinta wanda rabi duk shirmene take jabga abinta.

Wardrobe tabude saikuma taruntse ido tace"yasin duk Wanda na cafko shizan saka..."
Tadora hannunta cikin wardrobe din tasoma lalube,asa'a kuwa talalabo bakar jallabiyya tabude idanu taganta rigar bakace doguwa har kasa sai-dai hade take da hularta Wanda akama ado da kunnen zomo..

Bata damuba tazura rigar tazauna gaban dressing mirror tana taunar goruba tanama madubi gwalo da malgwada baki tana fiddo harshe da idanuwa.

Ahaka tagama cin gorubar tajefar tsakiyar Chinese carpet dake malale adakin tasoma fesa kwalliyarta wanda tasoma da foundation tace"hmm ainaga bidiyon make over na wayar Anty hafsa....yama take cewa...tadauko foundation tafara wannan shine foundation tadai fara acting like professional make over din.

Sai daifa tun awajen saka foundation takauce hanya don saida tagama zazzage akwatinta tas babu brush na shafa foundation hakan yasaka daukar zanin data cire tajabgashi akai tasoma danbarama fuskar abunka da liquid yakuwa daddanqare mata.

Bata damuba tasoma jagira"ummmm cinko ma zanyi"
Tafada lokacin datasoma durza eye pen akan girarta ganin kamar baya fitowa yasata cillar dashi dafadin"shege kadama kayibaga kwalli ba"
Tafada da murguda baki bayan tasoma jagiran da kwallin matsayar jagirar agefen kunne bashine yafi 'kayata zahra ba a'a yanda tad'ora jagirar asaman ainahin natural gira da Allah yabata.saiya kasance giranta daban jagiran daban.

Takuwa bishi ta zagaye da foundation maimakon concealer dabata gani acikin kayan shafar nataba.

Wannan yabama girar tata damar cakulewa tazama tamkar ta gwaggon biri,duk da haka zahra saida ta danqara powder akan goshinta kasan habarta cheeks nata amatsayin highlight kai ranar zahra sam bata hango na biyunta wajen kyauba.

Musamman yanda tajabga janbaki meruwan ganye akan lebennata takuma tattakura tazagaye abinta da bakin kwalli,
Tasoma sakin murmushi tana tsuke baki kamar yanda taga masu nuna make up din sunayi bata raba d'aya biyu wajen gwanancewarta akan kwalliya kota amare tayi..
*Nace ba mr's hamza...mizz Ayushh...hajara ghandi ko zakuzone zahra tamaku ranar sallah*
Daga wannan tsakar gida tanufa,gidan tsit bakowa kasancewar rana tatake sosai wannan yabata damar nufar get wajen maigadi..saidai bata hangoshiba taja tsaki afili tace"wajen gwabama zanje inhaye bishiya insha shagalina"
Kai tsaye garden tanufa,wata ringijejiyar bishiyar gwaba tahanga yayanta sun nuna kwarae hakan yasakata hadiye yawu ta takarkare tamakale bishiyar tasoma tsinka tana gatsawa intaji zaqi ta cinye,intaji bauri tajeho kasa....

Tana sama gwaggo rabi takaraso wajen daya kasance wajen hutawarta saboda rana,acewarta batason rabar esay tana bugunta ga ni'ima daga Allah.

Karkashin bishiyar gwabar ta shimfida dardumarta da casbaha a hannunta tadan kishigid'a tana lazumi.

Zahra hankalinta yana akan gwaba sam bataga zuwan gwaggo rabiba wannan yabata damar cilli dawata rusheshiyar gwaba Mara dadi afili tace"katuwar banza saigirma ba dad'i"
Gwaggo rabi datadan saurara jin siririyar murya bisa bishiya yasata sake natsuwa
sai dai fa batayi auneba taji jifaaa tuiiii!

Gefen kafarta tajanye dasauri tana fadin"kai jarababbun tsuntsaye basason barina insha Inuwa"
Takai dubanta akan gwabar da niyyar dauka sai kuma tajefar dasauri ganin shacin hankoran mutum fici-fici...jikinta yabata ba lafiyaba,
Ahankali cikin fatgaba tad'aga kanta mezata gani....

Zahrace tawatso idanunnan nata amatukar tsorace don harga Allah batasan dazuwan gwaggo rabiba face sambatu datajiyo daga kasa...

Wata razananniyar kara gwaggon tasaki dayasaka zahra durowa wa....

Loading......
*Anty Alaweeen dai
*MIJIN 'KWAILA....2
*chapter one*
*written by Maman meenat*
*Editing A'isha Abdullahi T.

Fulani*
*HAPPY SALLAH....
....... *KOTU* tayankema zahra d'aurin shekaru tamanin agidan yari....itace Kalmar dataci gaba da amsa kuwwa acikin kunnuwan isha'q wsnda yafarka firgigit kamar wanda aka tsikara da allura,ahankali yasoma bin dakin dayake ciki da kallo.Tabbas dakinsune ba kotu ba,musamman dayakai dubanshi akan fuskar gimbiya anee daketa kwasar baccinta hankalinta kwance abinta.

Ahankali kuma dukkan abunda yafaru acikin mafarki yasoma dawo masa aka tamkar dai magijine aka kunna masa dake nuna mashi hoton komai din yanda yafaru"yasalam"Kalmar
Daya furta lokaci guda yasoma sharar zufar data tsatsafo akan goshinsa,
'Wai meke shirin faruwane dashi dakuma Amanarshi *zahra* wai zahra in prison, kaii!

It will never happened"Abunda yake maimaita wa kenan saika dauka shida wanine yake maganar.

Durowa yayi daga bisa gadon dayake kwance bayan yasake tulama anee katon blanket dasuka rufa dashi,takuwa juya gami da sake ruqunqume bargon abinta.

Yajuya yanufi wardrobe bayan zura fara kal ta jallabiyya daya biyo baya,ficewa yayi adakin baiko dubi hanyar toilet ba baretane yasaka ran wanka,a tym din zahra kawai yake burin yayi tozali da kyakyawar fuskar ta me debemashi damuwa.

Dakinta yanufa wayam bata ciki sai dai ga tulin kayan wardrobe dinta nan data fidda gaba daya tawatso atsakar dakin.Saikuma gefe guda tarin yayan magarya ne datasha tajuye yayan a plate da alama shanya abinta tayi.

Yagirgirzakai zahra badai rigima ba,abunda ya raya acikin zuciyarshi.yanufi part din mummy sai dai bai karasaba yahango zahran kofar kitchen da y'ar roba a hannunta,ranshi yabashi da'akwai abunda takeson aikatawa....Saikuma mafarkinshi yadawo fess akan idanunshi yanufeta dasaurin gaske tana hangoshi tasoma dashe bakimta duka,karasawa yayi kusa da ita yarage tsawonshi tahanyar durkuwasa yakasance tsayinsu yazamo dayane yakama hannayenta dake rike da robar yana juyawa"menene wannan" shine tambayar daya watsa mata.

Tsurama ruwan ciki idanuwa tayi,saikuma tarage murya sosai tace"inka yarda amana idanna fada maka bazaka fadama kowa ba?"
Tayi maganar tana kafeshi da idanunta masu shagaltar dashi.

Numshe nashi idanuwan yayi ahankali yace"nayarda"
Zahra datayi kasa'ke saikuma tace"Amanatun...Amana..wa'azabatun azaba,yaro gwaggo rabi zan zubamawa ahanya daga tataho tana masifa saita fad'i mukuwa musha dariya,"tafada tana dariyar tun kafin abun yafaru.

Gaban isha'q yasoma bugawa da sauri-sauri yarike robar hade da yan yatsunta yatsura idanuwanshi cikinnata har saida ta kauda nata idanun tanacewa"nidai kadena kallona haka idanunka sai ingansu kamar na mage
"Mage kuwa?" Isha'q ya tambaya yana murmushi kasa-kasa,zahra data murguda baki tace"eh mana,jinake kamar inta kallonka fa..."
Yasaki dariya akan saikuma yace"bani wannan robar kada kisake attempting yima wani mugunta hakan babu kyau, halin yn wutane kekuwa nasan yar aljannah ce koba haka bane?"
Zahra tasoma murmushi sosai tana gyada kai,bakuma tayi kokarin hanashi robar hannun nataba.

Isha'q amsa yayi yaje yazubar harya dawo tana inda take atsaye,kama hannayenta yayi "oya muje kiyi wanka..Ina jamee(me aikinsu) tazo tagyara dakinki.

Zahra wadda tamakale kafa tace" nidai yaya saikayiman goyon kura"
"Goyon kura kuma zahra"
Isha'q ya tambaya donshi baimasan wani goyon kura ba,tace"eh kokuma kayiman makawuya ba"
"Yasalam!

Nikam duka wadannan ban sansu baamafa,"
Bude idanuwa tayi saikuma Amana asaki kukan shagwabar data tsiro dashi kwanannan na babu gaira babu dalili.

Tuni isha'q ya sunkuceta sama yasoma shillawa yana juyawa da'ita dukansu dariya suke kyalkyalawa yayinda zahra tamakale wuyanshi
Tamau tana sheka dariya abinta..

"Yau nashiga ukuna ni rabi'atu mezan gani da namata..."
Gwaggo rabi tafada lokacin datake karasowa wajen rike da casbaha a hannunta.

Bama Susan da zuwanta ba baretane abunda dake fad'i.

Hakan yasake 'kona mata rai,tadage iyakar karfinta ya caulama isha'q carbin abayanshi abunda yazo mashi a bazata yasaki zahra dasauri.

Tasulmiyo batakai kasaba yasaka duka hannayenshi ya tareta,suka fad'i atare yayinda zahra tafada akan ruwan cikinshi...

Idanunta suka nitse cikin nashi,suna hada idanuwa tamashi gwalo,shikuwa ya lakace hancinta duk suka sheke da dariya...

Abinda yadada tunzura gwaggo rabi tace"au dariya nabaku tabbatattu,shikenan isiyaku kazama sallamamme akan wannan 'kwailar yarinyar dababu ibanda ta'iya sai jaraba..gotai gotai dakai kadauki yar cikinka kana wannan hauka da ita..."
Sauran maganar tata tatsaya cik!

Hango anee dake labe jikin kofar dazata sadaka da kitchen din tana hawaye...

Loading.... *Anty Alawee*
*MIJIN 'KWAILA...2*
*Chapter 6*
*by Maman Meenat*
*Maman Shaheed tawa,baki baya iya furta girman matsayinki gareni.Ana'uhubbukki fisabilillah*
*One luv hajara ghandy
*Kuyi hakurin jina shiru kwana 2,matsaloline sukasha 'karfina.Adaitaman Afuwa filis*
Runtse idanuwa anee tayi zuciyarta na suya kamar zata tsaga kirjinta ta fito.

Dasauri Dr.rukayya ta kauda kanta kamar bataga mesuke aikatawa ba.

Gwaggo rabi madai a wannan gabar kawar da nata kan tayi,don ba shirginta bane.

Oganniya anee dai itace tami'ke fuuuu tanufi part dinta ranta yana mata zafi tare da suya.

Babuma wanda yakula da tashinta,ishaq dayayi masauki da dining chair yana sauke numfashi tare da d'aga hannu alamar sallamawa yana dariya.

Itama zahran dariya take sosai,tayasar da filon 'kasa tana cewa "matsoraci kawai"
Dariya sukasa duka hada hanan suka had'a hannayensu waje guda a dunqule(boxer).

Haka sukeyi idan sukai abun gwaninta insunajin nishad'i.

Agurguje dai
Yanayi yakan canja tattare da abubuwa masu damar gaske wasu mukan gansu a zahirance yayinda wasu a badini sukan faru
Irin wannan wulkitawar yanayin da sannu -sannu wanda hausawa sukance jariri angone, ahakanne rayuwa kaf tasauya a wannan babin.

Wasu y'an mata ne zaune bisa wani dutse karkashin bishiyar mangwaro da inuwarta ta rinjayi girmanta.

Cake ne da lemon Cway a hannun kowaccensu ahankali suke ci da alama kuma magana me muhimmanci suke tattaunawa a tsakaninsu.

Farar wadda tadire lemon hannunta tadubi y'ar bakar me lukutin jiki tace"nadai gayamaki haba lokaci yayi dazaki gane kin girma yanzu fa ba daba bane ba."
Murmushi d'ayar tayi dacewa"nifa sweety kingaza fahimtanane Allah kunya nakeji haba!

Wai kawai sai awani ganni da breziya.taafada tana kulle idanuwa.
Chapter 2 · 0% Book details