← Book details Me Zanyi Da Ita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 15

Sashe 15

Me Zanyi Da Ita Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wata d’aya ya rage biki a kuma lokacin ne ‘kannen Ahmad manga mata masu ji da kansu suka iso gidan d’an uwansu da set d’in akwatinan lefe za’a wuce dasu dangin uban shaheeda da suke Abuja.

Mamaki ne ya hana momma magana da suka samu a sashenta suka ce taje taga lefen da Imran ya had’a. Baki sake take kallonsu kafin ta furta “shi Imran d’inne ya had’a lefe ba tare da sanina ba saboda bai mayar dani uwa ba ko mai?” Tsaki hameedah tayi tana tauna chewingum sai kuma ta tintsiro d’ankwalinta gaban goshi tana watsawa momman kallon raini tace “yo da ke har wata tsiya kike d’aukan kanki d’a dai kin haifa amma baki isa kice zaki juya shi ba wannan kam sai yarda muka ga dama kin dai juya ubansa mun’kyale ki yanzu kam the table

Don haka muka saka dole ya auri shaheeda mu juya shi son ranmu kema ki d’and’ani rad’ad’in da mu kaji da kike juya yaya manga ki taso kiga lefe idan kinga zaki iya idan kuma ba haka ba kya gani a jikin surikarki kuma ‘yar kishiyarki shaheedah.” Ran mommah ne ya ‘baci har ta gagara ‘ko’karta furta ko kalma d’aya ce ga hameedah yarinya ‘yar cikinta da take tsaye take mata fitsara. Suma duka sauran ba wanda bai furta albarkacin bakinsa ba sannan suka juya suka tafi suna dariya da shewa burinsu ya cika sun ‘batawa mommah baiwar Allah zuciya. Tsahon lokaci tana zaune a wajen ta kasa mi’kewa tufka take a ranta kawai da warwara tabbas idan ba’a yi wasa ta bari a kayi aurennan zasu ci galaba a kanta za kuma suyi duk abinda suka ga dama hawan jini suke neman cusa mata da ciwon zuciya,ita bata ga abinda tayi musu a zahirance da bad’inance kawai dai ‘kiyayya ce suke mata su kansu da basu san asalinta ba balle tushenta. Ya zama dole tayiwa tufkar hanci lefe dai ba zata je ta gani ba kuma Imran zai zo ya sameta zata nuna masa ita d’in nan dai itace wacce ta haifeshi ta d’au cikinsa wata tara ta kuma shayar dashi nononta na tsawon watanni sha takwas.

Tsawon lokaci mommah na zaune a parlournta ranta a matu’kar ‘bace ta gaji ta gaji da tozartawa da wulakancin dangin miji, mafita kawai take nema tun daga parlournnata tana jiyo su tana jiyo ba’ka’ken maganganu da suke jefo mata masu kama da gugar zana hakan ya ‘kara hassala zuciyarta taji kuma zata iya komai don ‘kwatowa kanta ‘yancinta ciki kuwa har da samowa Imran aure ko da a cikin d’iyoyin friends d’inta zata nuna musu tana da iko da d’anta kuma ba wata shegiya da zata yi mata tin’kaho da d’anta alhali sanda tayi na’kudarsa ko wacce cikinsu tana can shanye da baki tana barci.lokaci yayi da zata farka daga barcin da take ta amshe matsayinta na uwar d’a mai cikakken iko akansa fiye da kowa a duniya.

Shigowar shatu ne ya farkar da ita dogon tunanin da ta tafi, shatu da hanzari ta ‘karasa wajenta ta dafa takanta ganinta cikin damuwa, tana son mommah jinta take tamkar innaji don haka sam bata son ‘bacin ranta kuma zata iya gogawa da kowa idan har yace zai shiga gonar mommah.murya can ‘kasa tace “Mommah menene meye ya sameki? Wad’ancan mutanen ne ko?” Momma ta girgiza kai tana janyo shatu jikinta “Bakomai shatu yau naji ina burin dama ke budurwa ce da ma ke kin kai muzalin aure da ba abinda zai hanani aurawa Imran ke da nayi alfahari da haka”shatu ta zaro ido “aure mommah ai nayi ‘karama” Murmushi mommah tayi kafin ta furta “shi yasa a zancena kika ji nace dama, duk da haka ba matsala insha Allah ba zan rasa wacce zan ‘karawa Imran a matsayin mata ta biyu ko da hakan yana nufin za’a yi tashin hankalin da ba’a ta’ba yi ba da wad’ancan mutanen” shatu ta ja ajiyar zuciya tana kallon mommah da hawaye yaso zubo mata ta kuma tabbatar na zallar’bacin raine. A zuciyarta ta ‘kudurce tabbas sai tayi maganin mutanennan a yau kuwa ba sai gobe ba taji itama a zuciyarta dama ita d’in budurwace a aura mata Imran da kuwa tayi sa’a kuma sai taci uban shegiyar shaheedan mai goshi kamar fitilar jirgi dama ta tsaneta tunda sanda ta ganta a kanainaye a jikin Imran. Shigowar Imran ne da ‘kamshin turarensa ya sata kai idonta kansa yayi kyau sosai cikin wani black yard african attire d’inkin zamani bai kai gwiwaba haka nan hannunsa gajerene kuma rigar tad’an kama shi kad’an an yi masa ratsin light brown daga gefen aljihun da kuma rigar ta lura yana son irin kayan yawanci shigarsa kenan yayi kyau sosai duk da kansa ba hula. Bai ko kalli sashen da take ba ya ‘karasa inda mommah take fuskarta a had’e sosai. Zama yayi sosai kusa da ita yana dafa kafad’arta had’e da zubawa shatu harara, kafin ma yayi magana ta mi’ke don ta san ma’anar hararar tasa ta shige bedroom d’inta murya can ‘kasa tace kyau kamar aljanni sai zallar ba’kin hali”.

“Please mommah na mai ya faru ne naga fuskarki ba walwala? Kuma su anty fannah sunce kije kiga lefe kin ‘ki why mommah?” Kallonsa tayi kallon cikin ido kallone da tun suna yara suka san tana yi musu idan sunyi mata babban laifi. Da sauri ya rusinar da idonsa baya jurewa wannan kallon baya son sa yana razana shi ya kuma san duk sa’in da mommah tayi shi ranta ya kai ‘kololuwa a ‘baci “ please mommah am sorry duk da ban san laifina ba” “ sorry for what Imran? You are sorry because ka wula’kanta ni ka nunawa duniya bani da amfani a wajenka ka nunawa duniya dani da babu ni you can make decisions about anything aurenka Imran ace sai dai ace nazo naga lefe? Ana yar min da magana baka neman albarkata baka damu da farincikina ba ko da yaushe sai ‘bacin raina nagode kaje ka yi aurenka kaje mutanen da kake tunanin zasu baka farin ciki su baka fiye da wanda ni zan baka Allah ya sanya albarka a aurennaka but put this in your mind bani ba ‘yan uwana a bikinka ba zamu zauna muga ‘baci rai ba.” Daga haka ta mi’ke ta shige d’aki jikin Imran ne yayi sanyi ji yake kamar yace ya fasa baya son ‘bacin ran mahifiyarsa bai san me yasa zuciyarsa ta kasa ha’kura da shaheedah ba, tsawon lokaci yana zaune kafin shatu ta fito tana ‘yar wa’karta ta “uwa tana da girma mahaifiya tai mini komai” da sauri ya kalleta gani yake kamar da shi take da shi d’in kuwa shatu take amma ya kasa ta’buka komai yana juya kalaman wa’kar shatu a zuciyarsa.

Ko da ta fita bata zame ko ina ba sai wajen mai gadi, da murmushi y tareta don yana son shatu musamman yarda take girmamashi ga kyauta akai akai “uwata ta kaina ya aka yi?” Ya fad’a yana mata murumushi shatu tayi ‘kasa da muryarta “Baba taimako zaka yi mi please amma bana son kowa ya sani” ya girgiza kai “ shatu danger yau kuma wa ya takaloki?” Dariya tayi kafin murya can ‘kasa tace “wasu ‘kadangarun bariki zanyi magani ga dubu biyu ‘kai’kayi zaka siyo min don Allah” Baba ya ware ido “Aa fa shatu’kai’kayi kuma mai zaki yi dashi?” Ta had’e rai idan ba zaka taimakeni ba shikkenan bara na tafi” ganin tayi fushi yasa yace “zo uwata zan taimakeki ai ba zan’ki mai taimakona ba” ta mi’ka masa kud’in tana dariya.
Chapter 15 · 0% Book details