← Book details Me Zanyi Da Ita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 15

Sashe 13

Me Zanyi Da Ita Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita kuwa tana can zaune fuska a tur’bune tana kallon mahaifiyarta “amma anty wannan yarinyar wacece? A gaban mutane fa ta disgani wai muciya da zani yanzu idan tasa Imran ya ankare da halittata fa ya fasa aurena” zainabu ta girgiza kai “bai isa ba bashi da wannan right d’in baby don na riga Na d’inke zuciyarsa a jikin taki tsaf ba zai ta’ba kallon wata mace bayan ke ba da sunan so” murmushi ta saki “wallahi na yarda da lamarinki anty gashi nan ma yanzu sai kirana yake tun d’azun na tabbata ya kasa sukuni ne”zainabu ta girgiza kai “ba zaki gane irin yarda na tsani Dijah bane saboda ita fa manga ya’ki aurena har an saka rana ta da yana had’uwa da ita yace ya fasa aurena bayan na tabbata ba yin kansa bane tsubbun su na fulani ne ya kamashi” Shaheeda ta girgiza kai “kullum fa anty sai kin bani labarinnan ko hadda ne yaci ace by now nayi haddarsa ni yanzu damuwata ayi a saka ranar nan na kama shi a hannuna ina son Imran to the extent.” Zainab ta dafa ta “shaheedah na sani na san kina son Imran amma fa bana so ki sashi sosai a zuciyarki don bana son lokacin da aikina zai kammala ki kawo min cikas bance kada ki so shiba a’a nafi so ma ki so shi sosai ko bakomai ba ko don dukiyarsa yaci a soshi, duk da kema na san don hakan kike sonsa da bashi da ko sisi ko shine aljannu don kyau ba zaki aureshi ba,aurenki da Imran ba fashi don nima shine burina, sai dai ina da wata manufa mai ‘karfi akan haka kuma kada ki sake ki bijire min a lokacin da bu’kata ta tazo” shaheeda murmushi tayi kafin ta janye jikinta ta mi’ke tsaye ta furta “Allah ya nuna mana lokacin bari inje in gaishe da inlaw ta kada tace bani da kunya.” Zainabu ta had’e a rai a zuciyarta tana tunanin lokacin da zata cimma burinta da ya jima a zuciyarta.

Murya can ‘kasa tayi sallama a ‘kofar parlourn idanunta akan shatu tana jin tsanarta a ranta. Momma ta amsa mata sallamar fuskarta ba yabo ba fallasa su kuwa su nahna ba wanda ma ya kalleta. Sum-sun har ‘kasa ta dur’kusa ta gaida mommah. Amsa mata mommah tayi fuskarta fal fara’a tace “Ya gida ya mutanene gidannaku?” Kanta a ‘kasa tace “lafiya lau” hafsa ta bita da wani kallo a zuciyarta tace munafuka. Shatu kuwa ‘kara ‘kare mata kallo take tana son ganin wani aibu a fuskarta sai dai bata gani d’in ba fuskarta ba yabo ba fallasa tana da kyau dai-dai nata sai dai daga ganin goshinta kasan bata da gashi tsam ta mi’ke “mommah bari na kawo mata ruwa” momma ta gyad’a kai “kin kyauta kuwa mah girl hakan yayi”

Shigowar Imran yayi daidai da kawo mata ruwan da tayi. Yana ganinta yayi saurin had’e rai. Ita kuwa shatu bata ma san yana yi ba ta isa gabanta ta ajiye mata ruwan ta kuma ‘ki yarda ta kalleta ta hau zuba ruwan, da azama Imran ya ri’ke hannunta. “Kwashe ruwan nan ki tashi daga nan kafin nayi ball dake wa yace miki ita ‘kazamace da zata sha ruwanki.” Kallonsa shatu tayi kallon da bata ta’ba yi masa sai taji zuciyarta ta buga bata ta’ba ganin zahirin kyansa ba sai yau da suka yi so close dashi, taushin hannunsa a cikin nata yasa ta zubawa hannayensu ido. Kamar a mintsineshi da sauri ya janye hannunsa, itama shatu hakan ya fargar da ita ta janye idonta da sauri ta mi’ke jikinta a sanyaye tayi hanyar d’akinta. Mommah kuwa ranta ne ya’baci tunaninta haushi shatu taji daji saboda furucin da Imran yayi a Kanta.mi’kewa tayi ita ma ta bi bayan shatunta. A kwance ta ganta akan gadon. Ta zauna a bakin gadon taja ‘kafarta “ Tashi shatun mommah tashi maza kije ku tafi da nahna za tayi miki shopping d’in school.” Da sauri ta mi’ke tana murmushi “mommah yaushe zan fara zuwa?” Mommah tana murmushi tana duban shatu ta lura shatu sam bata da ri’ko shi yasa kullum take cikin walwala ko tunani da wuya ka kama ta tanayi always zuciyarta fresh take as babies hearts. Tana kallonta ta fice da d’an saurinta. Ko da suka fita parlourn tuni suka tarar Imran ya fice da gimbiyar tasa.

Da sassafe shatu tayi shirin school ta fito kenan ta tarar da masu aiki a kitchen hannunsu duk hand gloves da alama uban ‘kyankyamin su ke yiwa girki. Da fara’a ta shiga tana kallon Daniel tace “ shugaban yan girki abincin waye wannan?”cikin gwarancin hausarsa yace “Babyn mommah kayi kyau wow!” Harara ta zuba masa “tambayar da nayi maka kenan?” Daniel yana dariya ta shagala da kallonta yace abincin oga Imran ne” murmushi ta saki tana dubansa ta juya ta shiga store cikin abinda bai fi second biyar ta fito a guje “daniel zo ka fita da ‘bera” daniel ya zaro ido “‘bera kace mai kyau you mean rat?” Tsaki taja “kayi sauri ka tsaya kana surutu sai ya shige wani wajen” yana shiga ta rufo ‘kofar da key “idan ka cireshi ka gaya min sai na bud’e.” Ta bud’e peppe soup ta tara yawu a bakinta ta tottofa ta mayar ta rufe tana dariya, sannan ta ciro wata leda a jakarta ta tsiyaya ruwan cikin shayin dariya take sosai “yau zamu ga ‘karsheb tsafta zaka sha yawuna ka sha kuma ruwan hammata ta.” Da sauri ta bud’e daniel jin Imran na’kwala masa kira.” Kaga ‘Beran?” Ta wurga masa tambayar bayan ta lura yana kallonta “ban ganta ba” ficewa tayi tana cewa “ta gudu kenan bagware wai ban gan taba sai kace ‘beran macece?”

Not edited.....

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍

NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-14

Tun da ta ganshi a parlourn hakan yasa ta zama don taga ko zaici abincin,shi kuwa yana dinning a zaune ya had’a tea ba tare da ya dubeta ba da alama sauri yake don haka da azama ya d’aga cup d’in tea d’in ya kur’ba ya kuma bud’e bowl d’in peppe soup d’in ta zuba a plate ya kai baki yana kur’ba dad’in peppe soup d’in ya ratsa har kwanyarsa ya lumshe ido yana sake zu’ka. Dariyar da shatu ta saka ce yasa shi saurin bud’e idonsa sai kuma ya had’e ransa yana dubanta tana ta she’ka dariya har da tuntsirawa,jikinsa ne ya bashi tabbas akwai dalilin dariyar tata don haka da sauri ya ture plate yace”ke zo nan” tana ‘kunshe baki ta fara shirin guduwa “wallahi kika d’aga ‘kafa daga wajennan ko da one step ne zaki ga abinda zan miki zo nan nace.” Hantar cikinta ne ya d’uri ruwa har ta juya zata wuce ba tare da taje d’in ba taji ya dam’keta ta baya gashinta yaja taji zafi sosai don haka ta runtse ido.”Don Allah ka sakar min gashi akwai zafi fa to wai mai ma nayi maka?” Tayi maganar cikin muryar shagwaba bai mata magana ba ya jata zuwa part d’insu a parlour ya wurgata saman kujera”gaya min uban me kike wa dariya ko na baki wahala nan dai ba mai cetonki balle kice wallahi idan baki gaya min ba ko school d’in da kike zumud’in zuwa ba inda zaki”Jin yace ba zata school ba ne hankalinta ya tashi duk d’okinta da takeyi zai ruguza mata shiri ta fara rawar baki”kada ki sake kiyi min ‘karya ina da abinda zan saka a jikinki in gano gaskiya don fad’a min gaskiya kafin na gano da gaskiya.” Ya fad’a cikin’kara tsare gira. Hakan ne ya sake razana ta tayi saurin cewa “idan na gaya maka gaskiyar zaka barni in wuce school?” “Fad’i ina jinki” ya fad’a yana tsareta da ido. Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “Don Allah kayi ha’kuri a cikin peppe soup ne na zuba yawu na a tea kuma na zuba maka ruwan hamma.....” da sauri taga yayi toilet yana kakarin amai hakan yasa ta suri school bag d’inta tayi waje a guje. Ya dad’e yana amai kamar ya amayar da kayan cikinsa ‘karshe ya fito har wani jiri yake ji kamar ya kifa haka ya kwanta akan gado yana maida numfashi har ga Allah yarinyar nan ta cuceshi cuta bata wasa ji yake kamar ya fito da kayan cikinsa ya sauyasu ha’koransa kuwa da harshensa ya dirje su yafi sau nawa har rad’ad’i suke masa zazzafi mai zafi ya kamashi haka ya ‘kudunduna a gado duk da yana da important issue haka ya ha’kura da fitar.

A school an kar’beta ko da suka gwadata suka ga gwara kawai su kaita primary five tunda tana da sharp brain idan yaso a gida a samar mata lesson teacher.
Chapter 13 · 0% Book details