← Book details Me Zanyi Da Ita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 15

Sashe 11

Me Zanyi Da Ita Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da yammacin ranar kuwa ‘yan matan mommahn gaba d’aya suke a kitchen suna tayata d’ora sanwar dare, shatu na gefen Nahna tana tayata had’a salad. Ta dubi antynnata kafin tace “ Anty Nahna ku nawa ne’yan uwan innaji?” Nahna murmushi tayi tana dafa gashin kan shatu data gyara mata shi ya sauka har tsakiyar gadon bayanta. “ Mu biyar ne Mommah ce babba sai adda maryamu sai hamma hisham sai ni sai kuma hafsa shekara d’aya ne tsakaninmu da hafsa. Mu kad’ai ne a gidanmu babanmu bai kara aure ba shi yasa sam ba abinda yake d’aga mana hankali bamu da yawan da za’a samu sa’bani a cikinmu muna son junanmu kamar mu had’iye kanmu, shi yasa sam ba muyi Farin ciki da auren da ammar zaiyi ba, mun so ya auri jininmu ta yarda zamu sake tashi tsintsiya mad’aurinki d’aya, amma hakan bai yiwuba kana tasa Allah na tasa amma Allah’s plan is better than ours right?”murmushi shatu tayi ‘kaunar dangin innajinta yana sake ratsa ta musamman ganin yarda suke nan nan da ita. Sai kuma ta kama hannun nahna race “me kika fad’a daga ‘Karshennan ina so in iya irin maganar nan” Nahna ta sake sakin murmushi kasancewarta ma’abociyar murmushi, tana jan hancin shatu tace “ kin san turanci?” Shatu Ta d’aga kai “ Na sani innarmu idan tana koya min karatu tana yawan ce min sai na iya abcd sannan zan iya turanci “ Nahna tace “ To wannan maganar da nayi shine turanci kice kin iya abcd?” Shatu cikin dariya tace “ kai na iya fa har’karshe kuma har rubutu na iya da karatun hausa Na abcd kuma na iya su boy girl, man da woman kai har su cup fa na iya.” Da sauri hafsa da mommah suka juyo nahna kuwa murmushi tayi kice “ yarinyar tawa kanta na ja ba zama kiyi wuyar shiga school ba.” Momma farin ciki ya cikata “ai kuwa gobe za’a miki register a school ko primary 4 su kaiki shekara nawa kika ji innajinki na fad’ar shekarunki?” Shiru tayi tana lissafi sai tace “ haka dai da zata mutu ina shekara sha uku “. Hafsa tace nawa kenan a karatun book?” Wani kallo tayi mata tace “ kai mhmn thirteen d’inne ban sani ba aradu har dubu munje da innaji tace min thousand sunansa “ gaba d’aya suka hau tafa mata. Momma cikin farin ciki ta jata ta rungumeta tace “lalle maryama tayi ‘ko’kari am so proud of her .”

Shigowar amaryar dahda ce ya dakatar dasu daga hirar da suke, ko magana bata yi musu ba ta bud’e fridge tana wani gatsine sai kuma Ta d’aga waya murya cikin kissa take fad’in “ Am coming dear naje samo maka drink d’in da kace ne.” Tana fad’a tana kallon mommah da take murmushi ‘kasa-‘kasa, “0key dear yanzu zan dawo kada ka damu zan maka abinda yafi kis.......” wani kallo mommah tayi mata da yasa ta gintse abinda tayi niyyar fad’a ta juya har ta kai ‘kofa momma tace “ kice masa har ya dawo daga kadunan da ya tafine? Kuma yaushe ya fara shan drinks na general kitchen..” wata kunya ce ta kama amarya ta juya da sauri ta fice, gaba d’aya suka saka dariya a kitchen d’in mommah tace “ kaji min shashasha right now fa na gama receiving call d’in and he told me yana kaduna amma kaji makira “. Suka sake she’kewa da dariya. Nahnah tayi tsaki “ Ni ba’kin cikina d’aya mommah da kuka amincewa imran ya auri ‘yarta ba kiyi masa jan ido ba, don sun ga d’anki ya taso da nasibi ga arziki ta ko ina ‘karuwar masa yake, kuma sun lura da matsanancin son da yake miki shi yasa fa suka shiga jikinsa idan ban da haka ina imran ina wannan yarinyar tana tafiya kamar bulala, ji fa ranar da muka had’u da ita a mall wallahi nunawa tayi bata son mu ba.” cikin takaici momma ta girgiza kai “ ki rabu da imran taurin kai gareshi kamar mutanen farko sau nawa na nuna masa bana so sau nawa na hanashi, amma ya’ki jin zancena amma lokacine zan nuna masa bashi da wayo daga shi har dangin ubannasa, muje dai zuwa a kuma juri zuwa rafi....”

Ita kuwa amarya tana fita d’akin hajja ta shiga ta zauna ta gaya mata’karya da gaskiya hajja ta hau kai ta zauna. “ kika ce sun zageki zainabu?” Amarya Ta d’aga kai hajja ta kuwa mi’ke zaune “ Ai kuwa tunda suka zageki ba ke suka zaga ba ni suka so zaga aka fake dake, to kuwa ba zai yiwu ba uwarki ni na sha mama na bar mata ban ga d’an abu ta kazar uban da zai zagar mana mahaifiya na ‘kyaleshi ba ke ko da kuwa sadakar yallar uwarsu ce muje madafar “ Amarya farin ciki fal ranta ta mi’ke ta bi hajja kitchen.

Tsaye hajja tayi ri’ke da ‘kugu tana musu kallon sama da ‘kasa “ Eeh lallai kuwa ba shakka na ta’kar’kare na d’au cikin manga, Na sha ba’kar wuya a haihuwarsa ashe dai ku na haifawa, an shigo cikin daula a dafa wannan a sauke wannan,A samu na banza aci ai nak, bama wannan ba uban me zainabu tayi muku kuka zageta? Ko kuwa sa’kon zagin kuka bata taje ta isar min hamsha’kai ?” Shatu ta zaro ido tana kallon amarya murya ‘kasa-‘kasa tace “ Allah ya shirya babba da ‘karya cab” gaba d’aya kitchen d’in ba wanda bai ji maganarta ba har hajja. Amarya ta zaro ido “ ke don ubanki ni nake miki ‘karya ko hajja?” Shatu Ta sake gyara zama tace “ duk wanda yayi ‘karyar ai addu’a nayi “ a sukwane ba suyi auneba suka ga ta zuba wa shatu mari hannu bibbiyu a zafafe hafsa ta janye ta tana mata wani banzan kallo “ kada ki sake ki sake dukanta me tayi miki? “ momma ta nuna musu hanyar ‘kofa “ ku fita “ ta’kofar baya suka fice sannan ta kalli hajja “ kiyi ha’kuri ba wanda ya zageta amma tunda ta fad’a miki kin yarda Allah ya baki ha’kuri” daga haka Ta fice bayan ta watsa wa amarya kallon banza.

Hajja bata shiga d’aki ba anan main parlour ta dinga zazzaga tijara zagi ta uwa ta uba ta dinga aikawa su mommah bayan amarya ta zauna ta sake fonfata wai har taji sanda suke cewa so suke ta mutu su sake mallake manga gaba d’aya har dukiyrsa hakan yasa ta sake sauke kwandon tijara zagi ta uwa ta uba. Ran shatu ya’baci musamman ganin yarda su nahna suka fara had’a kaya wai tafiya zasuyi da sassafe zasu bi flight d’in safe su tafi, haka ma hajiya mama tace bata son tashin hankali su taho kawai. Shatu kuwa ta’kudirce a ranta tsohuwa hajja ba zata kwana lafiya ba sai Ta gwammace kid’a da karatu.

Cikin dare shatu ta mi’ke daga gefen nahna da suka kwana tare a d’akinta, sad’af-sad’af ta fice. Murd’a ‘kofar hajja tayi a hankali ta shige ta mayar da ‘kofar ta rufe, dubanta ta kai kan hajja da ta saki baki tana barci tayi, har da yawun barci ta saki dariyar mugunta bayan ta kashe fitilar d’akin da fanka har da a.c . ‘Dif d’akin ya ba’kunci duhu ga windows dama duk a rufe, shatu ta shige ‘kar’kashin gadon hajja a hankali, kasancewar ba auki ne da ita ba zuruf ta shige . Muryarta ta kumbura ta fara fad’in “ke tsohuwa ke tsohuwar banza tashi maza ajalinki yazo....” Hajja da taji maganar daga sama a razane ta farka taji d’akin d’uf misalin dai duhun kabari da ake fad’a . “Kada ki sake kiyi mana ihu ba dai kince kin ‘konamu ba zuwa mu kayi ki ‘kara ‘konamu mun ja kunnenki ba kiji ba to yau a tsakiyar dajin aljannu zaki kwana kafin gari ya waye mu zu’ke jininki.......” Hajja jikinta ‘bari kawai yake murya a razane take fad’in “ Hajja kwananki ya’kare idan ban da shegiyar ‘karyata dama mai ya kaini cewa nayi fad’a da aljannu......😂😂🤣🤣🤣

Kai yau nayi typing da yawa so that ina jiran in ga ruwan comments.

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍

NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-12

ELEGANT ONLINE WRITERS..........
Chapter 11 · 0% Book details