← Book details Me & My Lion Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 5

Chapter 13 & 14

Me & My Lion Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Dagudu ta isa parlor kuma bata fasa kiranshiba. Ina cikin bedroom ɗinshi yagama rage kayan jikinshi kenan yajiyo sassanyar muryarta tana Kiran my lion, baki yataɓe aranshi yana faɗar "marar kunyar ƙarya kawai, juyawa yayi zeshiga toilet yariƙe Handel ɗin ƙofar toilet ɗin kenan itako tana faɗowa bedroom ɗin cikin farin ciki da ɗaukin ganinshi. Tsayawa yayi cak yafasa shiga yana kallonta cikeda mamaki rashin hankalinta na faɗo mishi bedroom babu nocking...itako failusha duban inda zataganshi takeyi kamar ance tajiyo kawai idonta yasauka akan rikitattun idanuwanshi masu bala'in kaifi da ladabtarda mutun, ido tawaro atake wani irin tsoro yarufeta, wanda yayi sanadiyar ɗaukewar nomfashinta ba wuccin gadi cikin ƙanƙanin lokaci murnarta takoma ciki, baki narawa take nunashi da yatsa amma takasa magana se kayarma jikinta keyi cikeda tsoro. Shikam ko gizau beyiba illa wata muguwar harara da yake Banka mata taƙasan ido. Azabure tayi baya tareda koma ɗauka ƙasa da gudu tana share ƙwallah domin batasan abinda yakawo wannan mugun gudannansu kuma har bedroom ɗin lion ɗinta (tofa lallai failusha akwai wauta waye zeshiga bedroom ɗin wannan bijimin Zakin batareda izinin shi ba) tana saukowa parlor fawan nashigowa domin Hajiya kaka tuni tabar parlor. "Ke little sis lpy kuwa miyafaru ne? Yatambeta yana riƙeta ganin yadda take afirgice.. "jiyowa tayi dasauri jin Yaa fawan domin ita batama ganshi. Aiko yadda taga shine sekawai tariƙemai hannu gamtana nuna mishi saman benen inda ta fito domin tama kasa magana. Kallon inda take nunamai yayi kana yace "miyafaru ne wani abin yafaru da Yaa shattima ne? Shiru ba amsa. "Failusha kinutsu mana kigayamin abinda yafaru, yafaɗa ya girgizata. Se alokacin tabuɗe bakinta dake rawa ɗaukar tace "Y.. Yaa fawan wancan mugun sojan ne yazo dakin my lion yanciki please kakira my lion yazo yaganshi, tayi maganar tana share ƙwallah kuma daganinta kasan duk aruɗe take. Mamaki Yakama fawan sosai jin abinda take faɗa kafin yaja hannunta sukoma Pert ɗin lieutenant shattima, domin bayaso su Mami suzo suganta Hakan hankalinsu tashi zeyi..binshi tayi domin gabaki ɗaya hankalinta atashe yake sabida bata taɓajin tsoron wani mahaluki ba aduniya kamar yadda taji tsoron wannan mugun sojan acewarta. Suna shiga suka zauna tanganemen parlorn shi kana fawan yariƙo yana faɗar "wanne soja kike magana little sis? Lion ɗinki? Ko wani daban? Cikin sauri ta shiga girgiza mai kanta kafin tace "aa ba lion ɗinna ba wannan sojan wanda yakusan kasheni a suleja shine fa magani yanzu a bedroom ɗin my lion. "Tofa wanda kikayiwa rashin kunya? "Eh tafaɗa tana tura baki gaba tunda ance tayi rashin kunya. "iKon Allah tomizekawoshi gidannan kuwa? Amma barana kira Yaa shattima yaƙarasa zancen yana zaro wayarshi daga cikin aljihu kana ya shiga Kiran lieutenant musayyeer. Sedai harta hanya ba'a ɗaga ba., beƙara kiraba domin yaji ƙarar wayar a cikin bedroom mamaki duk yakamashi. Tinani yakeyi waye zeshiga har bedroom ɗin babban yasu koda abokinshi ne kuwa? Domin idan Basu dasuke ƙanenshi ba babu me shiga bedroom ɗinshi suka seda lalura. To kodai Yaa shattima ne tagani ta ɗauka wancan sojan ne gizo ne yake mata? Duka shikeyiwa kanshi wannan tambayar dabame bashi amsarta.. ganin duk afirgice failusha take yasa yashiga kwantar mata da hankali haryasamu taɗan nutsu.. wayarshi ce taɗauki rurin neman ɗauki, Hakan yasa yaduba sedai ganin mekiran yasa yayi saurin ɗagawa yan faɗar "hello inawuni babbban yaya. Daga ɓangaren shattima kuma. Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi yaname tsotar lips ɗinshi naƙasa kafin yabuɗe baki kamar bayaso yace "my lovely bro. "Na'am yayanmu. Gani ina parlor ka. "Okay I'm coming, yana gama faɗar Hakan ya yanke wayar.

Itako failusha ƙofar fitowa bedroom ɗin tazubawa ido, dudda maganar da Yaa fawan kemata sam bataji shi burinta kawai lion ɗinta ya fito taganshi domin yarama mata abinda wancan mugun sojan yayi mata. Buɗe ƙofar yayi ya fito sanye yakeda ƙananun kaya ajikinshi farare ƙall ga dukkan alamu fari daga cikin kalar dayakeso, wayace maƙale a kunnenshi kamar yadda taganshi wancan ranar. Ido suka suka haɗa da failusha data jima da miƙewa tsaye tana nunawa fawanshi, cikin fisgo magana tace "Yaa fawan shine wannan fa yadakeni kuma yasaceni, kakiramin my lion yazo yaganshi mugune wl...fawan bebari taƙarasaba yayi sarin riƙeta gudun kar tasha wani rabon dukan cikin zaro ido yake faɗar "kee little sis shinefa lion ɗinki, shine kike gaya masa Hakan? Sanin Yaa shattima ne bakiyiba kome? Yafaɗa cike da mamaki dakuma tsoro, kenan duk ɗauki da soyayyar datakeyi lion ɗin ita batama sanshiba? Itako failusha afirgice tajiyo tana kallon fawan cikin mugun tsoron jin abinda yake faɗa kafin taɗago kuma ta kalli lieutenant dako kallon inda suke beyiba balle yasan da abinda sukeyi. Cikin tsiwa tajoyo zata saukewa fawan tijara sekawai idonta yadauka akan wani tanganemen hoton shattima dake manne a bangon parlor wanda computer ke sarrafawa izuwa launukan yanayin shekarunshi, tun yana ɗan shekara 12, har zuwa shekarunshi na yanzu, cikin firgici tawaro ido kaninshi ɓaro ɓaro ayanayin data sanshi wato shekaru 11 da suka wuce, domin wannan lokacin beyi girman yanzuba kana be ajiye sumaba ko kaɗan su fuskarshi, bata gama kallonshi sekawai yaƙara chanjawa kafin tayi wani motsin yaƙara chanjawa izuwa yadda yake yanzu cikakken namiji kuma bijimin Zaki, yana sanye cikin kayan suna sojoji riƙeda ƙaramar binfiga, yana ɗanata tankar zeyi harbi, fuskarnan a ɗaure tamau tamkar besan minene dariyaba.... ƙafafunta ne suka fara rawa cikin firgici da tashin hankalin data shiga lokaci ɗaya. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai take maimaitawa ganin wai lion ɗinta ne yayi mata wannan muguntar yanemi kasheta duk sonda take masa. Shin miyasa yayi mata Hakan ? Yadena sonta ne yanzu kome? Ko kuma dama can basonta yakeyiba itace kawai ke haukata shi tuni yamanta da Ita? Ita kaɗai keyiwa kanta wannan tambayar daba me amsa mata ita Sheshi? Atake taji wasu irin hawaye masu zafi sun zubo mata a fuska, Hakan yasa ta runtse idonta da masifar ƙari.

Hannunta taji anriƙo, Hakan yasa taƙara runtse idonta daƙarfi..amma taji riƙon harcikin kanta sabida tsabar laushin hannun..bata buɗe idontaba taji ana janta, dudda Hakan besa tabuɗe idontaba domin gabaki ɗaya tagama karaya. Bata tashi buɗe idontaba seda taji anjefata akan bed Hakan Yasa tawaresu afirgice tana bin wanda yajefotan da kallo, gabantane yayi mummunan faɗuwa ganinshi tsaye agabanta fuska a ɗaure tamkar hadari, waigawa tayi tanani inda zata gan Yaa fawan sedai wayam bayanan. Abinda failusha bata saniba shine tunda tafara kallon hotunan shattima dake juyawa fawan yabar parlor ganin yadda yayan nasu yagame Gabas da yamma babu alamun rahama atareda shi... nomfashi taja daƙarfi tanajin yadda gabanta ke dukan tara tara, amma ƙoƙarin danne tsoronta takeyi wanda ya riga ya bayyana.


Shiko zama yayi agefen bed ɗin yana dannar wayarshi kusan minti biyar kamar bazeyi maganaba can kuma seta tsinkayo cool voice ɗinshi yana faɗar "to marar kunya mikuma yakawoki Pert ɗina? Kuma har bedroom babu nocking waye yabaki wannan damar? Yatambaya kamar bashine yayi maganarba. Shiru tayi kamar bata jinshiba kusan kusan minti biyu, Shima kuma yashareta, Hakan sukaci gaba da zama har kusan 10:30 nadare amma bekoma bi takantaba hasalima aikinshi yake yi hankali kwance akan laptop ɗinshi. Ita kuwa izuwa yanzu tagaji da zaman ɗakin fita takesonyi kodab tagayawa Dady abinda shattima yayi mata domin wani irin zafin abin takeji aranta, dan kawai batada yadda zatayi dashi ne. Ganin bayada niyyar yin magana Balle yabata damar taya yasa tamiƙe tamkar kazar da kwai yafashewa aciki, tanufi kofar fita, seda tariƙa Handel ɗin ƙofar taji cool voice ɗinshi yadaki dodon kunnenta, ta hanyar faɗar.....!


ME & MY LION paid book ne idan kintashi biya zaki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 2276776261 sha'awanatu kasim uba bank. Kana kkituramin shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 or 09112799371 on Whatsapp


Autar alheri ✍️

*🌹🦁🌹ME & MY LION🌹*🦁🌹


Special and romantic love story 💋💓🫣

Writer by Autar Alheri ✍️


🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🦁🦁🦁🦁🦁
🌹🌹🌹🌹
🦁🦁🦁
🌹🌹
🦁


Oh'oh'ohhhh 🤭🤭🤭
Wannan kabcen tabbas zegigita duniyar makaranta littafen Hausa ze hautsina brain ɗinsu, kana ze cika zukatasu da shauƙi tareda begen reality love❤️🫂 na haƙiƙa 💯


Book one
Chapter 2 · 0% Book details