← Book details Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 21

Sashe 16

Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban san dalili ba,amma sam ban ji farincikin maganar ba,duk da ina ta fatan me bani wannan kud'in,na k'agi murmushi na ce"na gode sosai Nazifi,Allah ya saka da alkairi,ka yi masa godiya".

Ya ce"kar ki damu,goben k'arfe takwas za a fara fatin nasa,ke kuma sai ki shirya k'arfe biyar na yamma,za mu zo mu tafi da ke,inda za mu fake kafin lokacin ya yi".

"Kai Nazifi! Ya fa kamata ace kun yi min bayanin aikin nan,ya za a yi min abu kuma ayi ta yi min dabaibayi,na rasa gane inda kuka dosa".

Ya yi murmushi ya ce"to me kike ci na baka na zuba? Gobe ne fa".

"Ni dai kawai ka fad'a min malam" Na yi maganar ina had'e gira.

Ya ce"to gaskiya wani zarge za mu yi wa Salim,ko dai na ce tuggu za mu had'a masa,mu yi masa d'aurin goro,yanda bai isa ya ware ba,kawai dole ya aureki".

Na yi jim sannan na ce"ina jinka,wane irin tuggu kenan? Ya za mu yi?"

"Ya za ku yi za ki ce,ke aikin ki sai mun kammala namu,mu ne masu aiki ba ke ba". Ya fad'a ya na dariya.

Na ce"duk da haka ka sanar min yanda abun zai kasance"

Ya ce"d'akin Salim za mu kai ki,a wani irin yanayin da duk wanda ya gan ki zai ce ya yi miki fyad'e..."

Na yi saurin katse shi "ban gane wani yanayi ba!".

Ya ce"za ki gane bayan komai ya tafi daidai.Idan muka yi nasarar shigar da ke,ke kuma sai ki yi k'ok'arin tabbar wa iyayensa abun gaskiya ne,ki nuna musu Salim sato ki ya yi,don ya miki fyad'e".

"Amma idan na yi masa haka anya na yi masa adalci kuwa?" Na fad'a, jikina duk ya yi sanyi

Ya ce"idan ba za ki iya ba babu dole,sai ki hak'ura,ko kuma ki samo wata hanyar da ki ke ganin za ta tilasta masa aurenki".

Na kama baki ina nazari,don gaskiya na san idan na yi wa Salim sharri,ban yi daidai ba,yanzu ko darajar Baby ai bai dace na yi hakan ba,da wane ido zan kalle ta? Kuma ko kowa ya yarda Salim zai sato ni ya min fyad'e banda Baby,tunda ta san duka tsakaninmu da shi,amma na yarda hakan ne kawai zai sa ya aureni a y'an tsakanin nan,ina jin tsoron jinkirtawa har a d'aura aurena da Habib ban ankara ba,sai dai na san ko na yi nasara ya aureni ba lallai na samu wata daraja daga gare shi ba,saboda MATAR SHIGE BA TA DARAJA!
Amma na yarda ni mace ce, don haka na saka a raina shiga gidan nashi ne babban aiki,karkato da hankalin sa gareni,da cusa masa soyayyata shan ruwa ma zai fi shi sauk'i,matuk'ar na zama matarsa.Don haka na yarda da wannan aikin na su Nazifi,amma na saka a raina zan yi ta istigfari daga baya,kuma bayan komai ya zama normal zan nemi yafiyar Salim

Idan aikin ya yiwu fa kenan!

Nan na fad'a wa Nazifi na amince,kuma goben zan shirya kamar yanda ya ce d'in,na yi masa godiya ya tafi,ni kuma na shiga gida. Ashe wani babban kuskuren na sake tafkawa! Idan banda ragon tunani irin nawa,ta ya zan yarda da zancen wai wanda zai min aikin,ya biya min kud'in? Shi da ya na da kud'in da zai yi kyautar dubu d'ari biyu,amma ya tsaya a wannan aikin wanda idan aka kacaccala kud'in bai fi ya samu hamsin ba? Na sake kuskuren da ya hanani zaman lafiya. Nan gaba dai za ku ji...

Bacci na kad'an ne a wannan daren,ina ta tunanin yanda wannan wasan mara kyau zai kasance gobe,yanzu idan abun ya b'aci ai na tabbata ni da su Nazifin duka sai mun yi zaman gidan d'an Kande.Gefe guda kuma ina tunanin irin halin da zan jefa gogan nawa a ciki,idan aikin ya yi kyau,ai zan b'ata masa suna a idon danginsa,kuma ba ni da tabbacin Baby za ta rufa min asiri a yanda take k'aunar d'an'uwanta.Sannan ina tunanin irin yanayin da iyayena za su shiga,idan suka ji wannan babban lamari,da kuma yanda Habib zai ji.Amma fa hakan ba zai sa na janye ba,saboda ina son Salim gaskiya

Na janyo turaren shi,na kafa hancina na lumshe ido,ina neman bacci.

Washegari da safe duk a sanyaye na tashi,har Anti ma sai da ta gane hakan,ta kalle ni da kyau ta ce"wai ni kam Zinatu meye damuwarki a y'an kwanakin nan? Har fa kin fara ramewa,ko tunanin auren ki ke yi?"

Haka nan na ji saukar hawaye,na share ina gyad'a mata kai alamar e tunanin ne

Ta ce"ki kwantar da hankalin ki,za ki auri namiji me hankali kamar Habib shi ne har ki ke tada hankalin ki? Maza ba su da tabbas,amma ina kyautata zaton Habib ba zai sa ki kuka ba Zinatu,ki kwantar da hankalin ki".

Na gyad'a mata kai,ina share hawaye,sannan na sanar mata da yamma zan je gidan k'awata,don mu tattauna akan bikin.

Wajan azhar ina zaune kamar a mafarki sai ga kiran Habib,kamar ma kar na d'aga,don sharenin da ya yi ya ba ni haushi,na d'aga ina sallama murya a dak'ile

Shi ma ba kamar yanda ya saba yi min wasa da kalamai masu dad'i ba,yau kai tsaye ya ke yi min magana "Zinatu zan shigo da yamma za mu yi magana".

"Ni fa bana gidanmu" Na fad'a,cikin jin haushi

Ya ce"e na sani,kuma gidan Na'imar zan zo dama".

"Ban baka dama ba" Na fad'a cikin ba shi umarni

"Dama ban nemi izininki ba ai" Ya fad'a,kuma ya datse kiran bai jira cewa ta ba.

Na bi wayar da kallon mamaki,a bayyane na ce"e lallai Habibu ka samu dama,ka dad'e ba ka zo ba kuwa!".

"Yanzu Baby ki na ganin wad'annan kayan sun yi?" Salim ya fad'a ya na kallon kayan da ta zab'a masa,na zuwa wurin birthday

Baby ta narkar da kai ta ce"oh! Bros Allah sun fi wanda ka zab'a kyau fa,ni na fi son na gan ka da manyan kaya ne".

Ya yi murmushi ya ce"to shikenan,zab'inki shi ne nawa sisi".

Ta juyar da kai ta yi shiru,alamun ta shiga damuwa da tuna wani abun.

Ya ce"to y'ar rigima,me kuma ya faru?"

Ta ce"rok'on ka zan yi alfarma Yaya".

"Zan yi miki ko ta mene" Ya fad'a.

Ta ce"don Allah kar ka sha wani kayan maye,kamar yanda ka yi waccan shekarar,ka ga wannan karon Abba ya na nan,kuma zai je wurin".

Ya kama hannunta ya ce"wannan shi ne damuwarki?"

Ta gyad'a kai. Ya ce"na yi miki alk'awarin ba zan sha komai ba in sha Allah".

"Na gode" Ta fad'a ta na ficewa daga d'akin.

K'arfe shida daidai na kammala shirina,kuma ya yi daidai da kiran wayar Nazifi,ya na jirana a waje,doguwar riga na saka ta atamfa da wadataccen mayafina,na yi kyau sosai,na zabga turaren Salim kamar zan k'arar da shi,na yiwa Anti sallama na fita.

Sai dai ina fita na ga Habib ya na k'ok'arin gyara packing, zai fito daga motarsa,na yi saurin shigewa motar abokin Nazifi da suke ciki suna jira na,amma kafin ya ja mu tafi,Habib ya yi saurin zuwa inda muke,fuska babu walwala ya ce da abokin Nazifi "kai bud'e yarinyar nan ta fito".

Na bud'e,ba tare da na fito ba na ce"unguwa za su kai ni".

Ya ce"e,ki fito ni na kai ki".

"A'a, na gode" Na fad'a ina shirin rufe k'ofar.

Ya rik'e murfin ya ce"to ki zo,ina son magana da ke ko ta minti biyar ce".

"Ba zan samu dama ba gaskiya, idan na dawo sai ka dawo mu yi". Na fad'a ina rufe murfin motar,su ka ja mu ka tafi,mu ka bar Habib tsaye kamar an dasa shi.

Sharad'an mu ka dosa,can wajejen su Salim d'in,don kuwa gidan da na ga sun faka motar babu nisa da gidansu Salim.

Mu ka fito muka shiga,amma banda abokin Nazifi,na dinga bin matsakaicin gidan da kallo, d'akuna uku ne a ciki,sai band'aki,da wani wuri da nake kyautata zaton kitchen ne,ya shiga wani d'aki ya ce na shigo, na shiga da sallama

Babu komai a ciki sai katifa da kayan kallo,da wasu akwatunan kaya a gefe,da alama dai d'akin saurayi ne.Na rab'a gefe na zauna duk a tsarge nake

Muna nan zaune da Nazifi ya na yi min bayanin yanda aikin zai kasance,sai ga abokin nashi da na ji ya na ce masa Sabi'u ya dawo rik'e da ledoji.

Ya zube su a gabana,ya kalli Nazifi ya ce"to ta so mu wuce ko?"

Nazifi ya kalle ni ya ce"to Zinatu,bari mu je,anjima za mu dawo d'aukarki,kafin nan an fara fatin,ga abinci nan ko za ki ji yunwa".

Na ce "to,sai anjima".

Bayan sun fita na bud'e ledar,na ga abinci ne a takeaway, sai lemuka har kala uku, ba na jin yunwa amma sai na ji sha'awar shan lemon

Na bud'e d'aya,na sha kusan rabi,na matsar gefe,na d'akko wayata ina kallon hotunan Salim da sak'e-sak'e,ko minti goma sha biyar ban yi ba,na fara jin bacci-bacci,abu kamar wasa tun ina daddaurewa har dai abun ya rinjaye ni,na kwanta a nan k'asa,na yi fulo da gefen katifa tuni wani bacci me shegen dad'i ya sure ni muka tafi...
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

Page 17

Saukar ruwa me sanyi da na ji a fuskata shi ne ya farkar dani daga nannauyen baccin da na yi,na farka a firgice ina k'ok'arin bud'e idanuna da nake jinsu kamar ba nawa ba,wani irin yanayi nake jin jikina kamar dai wata ce aka saka zuciya da tunanina a jikinta

"Ke! Uban waye ya kawo ki d'akina!?"

Duk da ban gama wartsakewa ba,amma ba na jin akwai halin da zan shiga wanda zai mantar da ni muryar Salim,na bud'e idona sosai na kalle shi,sai na ga kamar ba Salim d'ina bane,don kuwa gani na yi kamar an canza idanunsa,ta idonsa kawai za ka fahimci ya na cikin tashin hankali mara misali.Lokaci d'aya na fara tunanin ta yanda su Nazifi suka kawo ni d'akin Salim,a iya sani na bacci na kwanta a d'akin da suka ajiye ni,kuma ban farka ba sai yanzu,kenan hakan ya na nufin cak suka d'auke ni? Kuma har ta ya ma suka shigo da ni nan d'in wani bai gan su ba?
Chapter 16 · 0% Book details