← Book details Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 21

Sashe 13

Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta rakoni har bakin titi na shiga adaidaita sahu na kama hanyar gida.Na yi ta tunanin halin da na jefa rayuwata a ciki,gefe guda kuma na gamsu da mafitar da Baby ta kawo d'ari bisa d'ari,sai dai ina gudun k'urewar lokaci,ace sai aurena ya rage sati biyu za a fara wasan? Yanzu idan komai bai yi daidai ba a sati biyun ya zan yi? Don ban ga alamar Habib zai sanar musu da na fasa auren shi ba,ni kuma gaskiya ina jin tsoron abin da zai biyo baya idan na furta na fasa auren.Kuma ita kanta Baby ban yi kuskuren k'in sanar mata an kusa aurena ba kuwa? Amma gaskiya ba zan fad'a mata ba,don ina jin tsoron ta janye taimakon ta,ta ce na hak'ura da Salim

Da wannan tunane-tanayen na k'arasa gida,lokacin ana shirin sallar magriba,don haka ina shiga gida na d'aura alwala na shiga d'aki,aikuwa Baba ya na dawowa ni ya fara k'wallawa kira,ina jin muryar Mama ta na fad'in,

"Wai wace Zinatu ka ke kira? Ai ba ta gidan nan tun d'azu".

Baba ya ce" Zinatun ce ta fita yau? Amma ai ga d'akinta a bud'e ko?"

Mama ta ce"zancen kake so,ai sai ka shiga d'akin ka d'akko ta".

Ina jin haka na kwanta akan sallayar kamar me bacci,don na san Baba akwai ganin k'wak'waf!

Aikuwa sai da ya zo ya d'aga labulen kamar yanda na zata
"Ke Zinatu!" Ya kirani da k'arfi

Na tashi firgigit kamar wadda aka tasa daga bacci na ce"uhm!"

Ya ce"wane irin shashanci ne haka bacci da magriba?"

Na tashi zaune na ce"kaina ne ya ke ciwo"

Ya ce"to Allah ya sawak'e,yanzu Na'ima ta kirani a waya,wai kun yi zancen za ki je gidanta ki kwana biyu,ta jirani kuma sai mijinta ya mata waya ga shi nan a hanyar shigowa garin,to yanzu dai ta riga ta tafi gidan,ke kuma gobe sai ki shirya ki je".

Na ce"to Baba".

"Ai ba to ba,saura ki je ki yi ta yawon naki a can,wallahi na ji ba daidai ba sai ranki ya b'aci".

Na sunkuyar da kai na yi shiru,ya wuce ya na fad'awa Mama ai ina ciki bacci nake yi.

Wajan k'arfe goma na dare ina kwance,kamar a mafarki sai ga kiran Salim,hannuna na rawa na d'aga har da in'ina wurin gaishe shi.Bai amsa ba ya ce"ke nutsu dalla,tambayar ki zan yi"

Na ce"to,ina jinka"

Ya ce"me ya kai ki shagon k'anwata yau?"

Gabana ya fad'i,na yi saurin fad'in"kitso na je".

Ya yi wata y'ar dariya ya ce"kitso ko? To ke da ita d'in ku iya takun ku,don duk abin da kuke yi a tafin hannuna yake".

Ya katse kiran,ba tare da ya bani damar wata maganar ba.

Na dafe k'irjina da har yanzu bai daina bugu ba,maimakon na yi nazarin maganar sa,da kuma tunanin yanda ya san na je wurin Baby,ina! Sai na fad'a wani shauk'in son shi,na ji kamar ba ni da wata damuwa a duniya,muryarsa ta mantar da ni duk wata matsala da take tunkaro ni.

KU NA GANIN MAFITAR DA BABY TA KAWO ZA TA SAMU SHIGA KUWA?

AKWAI WANI K'ALUBALE BABBA A KOMAWAR ZINATU GIDAN ANTI NA'IMA.

Ku dai ku biyo ni🥰
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

Page 14

K'arfe goma na safe na kammala shirin tafiya gidan anti Na'ima,na yiwa Mama sallama ta amsa kamar gaske.Sai da na biya ta gidan Ummi na gaishe ta,ta kwaso min kayan kitchen da zannuwan gado,labulaye da dai sauran tarkace wai duka nawa ne,a to tarkace mana! Tunda su suke ta shirin su,watak'il dai sun tanadi wata matar da za su aura wa Habib,don ni Zinatu na yi masa nisa

Ban jima ba na yi mata sallama na tafi,bayan ta yi min nasiha sosai wadda ba ta fashi indai zan zo gaishe ta.

Fuska babu yabo babu fallasa na shiga gidan Antin,don ina tunanin yanda zaman gidan zai zo min,indai za ta hana ni fita harka ta to fa tabbas tafiyar mu ba za ta yi nisan zango ba,domin kuwa ba na jin zan iya yin sati hud'u ban bawa idona hakk'insa ba,wato kallon Salim

Gidan nata b'angare biyu ne,don ta na da abokiyar zama,ita ce amarya,uwargidan babba ce har ta na da manyan y'ay'a guda uku,Nazifi shi ne babba,kuma mu na shiri da shi sosai,kun dai sanni da maza...sai k'annen sa Hafiz da Umar.Ita Anti Na'ima Allah bai bata haihuwa ba har yanzu,su na zaune lafiya babu wata matsala,shiyasa idan na je ma muddin Nazifi ya na nan,to na fi zama a shahen su,mu yi ta shan firar mu ta duniya.

Don haka yau d'in da na je,bayan ta nuna min kayan gyaran da yanda za ta yi min,na ce mata sai gobe a fara,na tashi na yi sashen su Nazifi,na yi sa'a kuwa ya na nan,a can muka zauna mu ka sha firar mu har la'asar

Na yi zaton ma Anti za ta min fad'an zama na a can, sai na ji ta yi shiru,na taya ta girkin dare muna yi ta na yi min bayanin wasu dabarun girkin,ni dai jinta kawai na ke,ina bin ta da ido.Washegari aka fara yi min gyaran jiki,tun daga ranar kuwa fatata ta fara kyau, cikin sati d'aya na zama kamar ba ni ba,kullum mu na waya da Baby, ko ba ta kira ni ba,ni zan kira ta mu gaisa,haka ma ta b'angaren Salim ba ta canza zani ba,domin kuwa kullum sai na jera masa kira,amma ba ya d'agawa.Lokaci zuwa lokaci bawan Allah Habib ya na fad'o min a rai,don tun ranar da muka yi wannan maganar...bai sake kiran wayata ba, bare ya zo,har Anti sai da ta yi min maganar sa,na ce mata mu na yin waya kullum,ba ni da matsala a zaman gidan,sai dai na fara k'osawa da rashin fita ko k'ofar gida,tunda ko aike na ba a yi,sau d'aya ma na ce zan raka Nazifi kasuwa,maman su ta ce na yi zama na,idan ana gyara ba a shiga rana.

Ranar da na cika kwana goma sha biyu a gidan, wata rana da yamma ina zaune sai ga kiran Salim,Allah ya sa ni kad'ai ce a wurin,don haka na d'aga da hanzari ina yi masa sallama.

"Wa alaikissalam" Ba saban ba yau ya amsa sallamata.

"Da fatan ka na cikin k'oshin lafiya?" Na fad'a,ina dafe k'irjina da ya ke ta bugu kamar na ga abin tsoro

"Kwatanta min gidanku" Ya fad'a, ba tare da ya amsa ni ba.

Sai na ji kamar a mafarki ne ba zahiri ba,yau Salim ke cewa na kwatanta masa gidanmu? Aikuwa sai zuciyata ta fara ayyana min watak'il ya yarda da soyayyata ne,har zai zo mu fara fahimtar juna.

Cikin zumud'i na ce"e...am...yanzu ba na gidanmu"

"Ki na ina? Koma ina ne ki kwatanta min,ga ni nan zuwa yanzu" Ya fad'a cikin d'an fad'a-fad'a.

Jikina ya yi sanyi,na fara tunanin zuwan na shi na lafiya ne ko akasin haka? Amma na fi kyautata zaton alkhairi ne, tunda na san ban yi masa wata kwab'a ba a y'an kwanakin nan.Don haka tiryan-tiryan na kwatanta masa gidan Anti,bai ce komai ba ya katse kiran,ni kuwa na tashi da sauri na shiga band'aki na yi wanka,duk da na yi d'azu na yi kwalliya,na saka doguwar riga,na yafa k'aramin mayafi,na yi zaman jiran shi.

Anti da ke ta hada-hadar girkin dare ta kalleni ta ce"to! Ke kuma ina zuwa haka,ki ka yi shiri ki ka kame a falo?"

Na ce"Anti Habib ne zai zo".

Ta ce"to! Ai da sai ki ce ya shigo,ku yi firar ku a cikin gida ko?"

Na ce"a'a,sauri ya ke yi,abu zai bani ya wuce".

Ta ce"to ai shikenan,ki gaishe shi".

"Zai ji" Na fad'a ina tashi don Salim ya k'ara kira,na san ya k'araso ne.

Sai da na fita na d'aga kiran,ban ma kai ga yin sallama ba na hango shi tsaye a kusa da motarsa,ya na sanye da farar shadda da bak'in glass,ya yi kyau sosai, sai na ji kamar na je na rungume shi na bud'e zuciyata,ya ga irin k'aunar da na ke yi masa, da kuwa babu shakka sai ya tausaya min ko da ba zai karb'i soyayyata ba.

A slow na dinga taku,har na k'araso inda ya ke a tsaye,na yi masa sallama na sunkuyar da kai,ganin yanda ya kafeni da ido tunda na taho

Bai amsa sallamar ba ya fara magana"Zinatu sunanki ko?"

Na ce"e,haka ne"

Ya ce"me ya sa kike son shiga rayuwata?"

Na d'ago na kalle shi,sai na ga tsakanin sa da Alllah ya ke tambayata, na maida kaina k'asa na ce"Allah ne ya jarabceni da son ka,wallahi ba yin kaina bane,kuma da alkhairi nake son ka ba sharri ba"

Ya ja dogon tsaki ya ce"me ya kaiki wurin Junaina?"

Gabana ya fad'i,don ban shirya k'aryar da zan yi ba,tunda ban tsammaci tambayar ba,don haka na ce"ni? Yaushe na je?"

Sai ya ciro wayarsa a aljihu ya yi y'an danne-danne,ya nuno min fuskar wayar, gabana ya fad'i ganin hotona a wayar,ina zaune a shagon Junaina.Na shiga mamaki da tunanin yanda a ka yi har ta min hoto ban lura ba,da kuma tunanin yi min hoton ma duka,lallai wannan Junainar makira ce ashe.

"Me za ki ce game da wannan hoton?" Ya tambaye ni,bayan ya maida wayar aljihu.

"Duk sanadin ka ne Salim,kai fa musulmi ne,don Allah ka tausaya min,ina son ka". Na yi maganar hawaye na zubo min

Ya ce"saboda ki na so na sai ki nemi cin mutuncin macen da na ke k'auna? Kin san matsayin ta a wurina kuwa?"

Na dafe k'irji,cikin firgici na ce"na shiga uku! Cin mutunci kuma? Ni d'in? To wallahi sharrin ta yi min,Allah ya isa tsakani na da ita!"

Ya daka min tsawa"ke! Kin ga dakata,ni ban zo don ki min rantse-rantse ba,na zo yi miki gargad'i ne da jan kunne,don wallahi ko ta waya ki ka sake zagin ta sai kin yi kwanan prison!"

Na saki baki ina kallon shi da mamaki,Allah ne kad'ai ya san irin k'aryar da ta had'a masa.To amma me yasa Junaina ta yi min haka?

"Idan kunne ya ji...!" Ya fad'a, ya shige motarsa ya tafi,ya bar ni tsaye,ko k'wak'kwaran motsi na kasa yi,kamar na had'iyi tab'arya.

"Zinatu!" Nazifi ya kira sunana da alamun mamaki
Chapter 13 · 0% Book details