← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 5

Sashe 4

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kuma duk lokacin da tai min haka sai naji girmanta da darajarta sun zube a cikin raina. Muna zaune bayan mun gama jajjagen kayan miya kawai Inna Harira ta kalleni, gashi rana ta fara budewa ta cillo min tsintsiyar kwakwa tana cewa.

"Tashi ki share gidan nan gayan bishiya duk ya sake batashi." Cikin turo baki tare da langabewa dan ta tausaya min nace.

"Inna Harira Kinga rana fa.?"

Tace dani.

"Eh wallahi na ganta sai akai me?"

Nace.

"Dan Allah ki bari zuwa la'asar sai nayi."

Sai cewa tayi.

"Iyeee! Lallai yarinyar nan, ince kiyi abu yanzu ki tsaya kina zabar lokacin da zaki yi? Toh yanzu nace kuma sai kinyi kodan wannan hasken naki ya ragu, yarinya abinda kowa yakeci shi kike dankara amman kinfi uban kowa haske a gidan nan? Toh yanzu zaki share gidan nan idan kuma kinki zakisha mamaki."

Sai bance komai ba na tashi ina kunkuni na fara sharewa kamar zan fashe da kuka....

MASARAUTA (LABARIN SOYAYYAH) YANA AREWA BOOKS👇

https://arewabooks.com/book?id=6284e72eef85a63a21dbc5f5

SO DA ZUCIYA

SHIMA YANA AREWA BOOKS👇

https://arewabooks.com/book?id=623f824f9c4af77be0e96e3d

🥰😍
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

_MSS XOXO WRITES ❣️_
[5/22, 9:58 PM] Miss Xoxo: _*MASARAUTA*_
_(A Cinderella story)_
👑💘

_LAST FREE PAGE: 5_
_(shafin karshe na kyauta)_

_NA:_

®️ _NANA HAFSATU_

©️ _ZAFAFA BIYAR WRITERS_

_wattpad:missxoxo00_
_Arewabooks:mssxoxo_

_BUSINESS:👇🏾_

_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_

_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_

_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_

_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_

_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_

_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_

_ARABIAN OIL PERFUMES_
_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_

_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_

_SKIN CARE PRODUCTs_
_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_

_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_

_instagram:yerwaincense_and_more_*

_WhatsApp: 08095215215_

__

**Da sassafe na tafi kogin Guzai ebo ruwa da wanka, Kasancewar kogin Bagaja ya kafe. Ba wani layi sosai . Mutane uku ne agabana. Don haka na zauna akan bokiti na ina rufe baki na da hammar data tahomin.

Sai dana cika babban bokiti na. Na ajiye a gefe, Tukun sannan na ebo wani a bokitin wanka. Na tsaya can bayan bishiyar darbejiya inda muke wanka wani sa'ilin.

Wanka na na fyalla na dauraye gashi na da guntun omon da muke wanke kai da shi. Ni kai na mamakin yawan gashi na nake, Ga cika ga tsayi. Dan basilin din dana lakato a leda na dakko na shafe a jiki na.

Na zura kayana. Na koma bakin kogi na daura gammo na dasa ruwana a kai. Dayan bokitin kuma na dauke shi a hannu. Ina tafe ina bitar karatu na.

***Na baro kogin Guzai gaba ki daya so nake na koma gidah saboda yadda cikina yafara kukan yunwa.

Can sai Adamcy da Nazifi da suke kira da Nazicy. Dake duk yuyar abokan nasu sun mayar da sunayen da cy a karshe tamkar wasu arna.

Yana gani na ya dashe hakora. Tsabar sauri har tuntube na danyi ruwana ya zubo. Domin sam banason su tsayar da ni.

"Tawaje na....Masoyiyar."

Ban kula shi ba nayi gaba. Amma tsabar nacin sa sai ya sake biyo ni yana kobarewa. Ya saka hannuwan sa ya dauke bokitin da ke kai na ya rike.

"Bani ruwana.." Na fada wani hawaye na son kufcemun.

"Haba tawaje na. Saboda me zan bar ki ki dauki sungumemen bokitin nan bayan gani da rai na. "

Hawayen da nake rikewa kar ya zubon suka fara yar tsere a fuskata.

"Adamcy dan Allah ka kyaleni."

"Saboda me zan kyale ki bayan kin san kaunar ki nake da aure...?"

"Aure?" Na fada murya ta a kausace saboda 'dacin maganar da yamun

"Eh aure... "

Na girgiza kai kawai Ina mai busar da iskar baki na mai zafi da radadin yadda ya fada a gadarance.

"To Adamcy bazan aure ka ba. Idan auren kakeso. Kaje ka auro budurwa babba mana. Ga su luba nan ta hayin dusa, Ga Rabi nan ta yan koko dasu sha'awanatu ta gidan wake da shinkafa..ga"

"Karki karasa Intee, Ni ke nagani inaso, Kuma ke zan aura koda kuwa zan rasa kowa da komai nawa."

Takaicin kalamansa yasa naja dogon tsaki. Na kwararo dogayen rantsuwa na dire hade da bubbuga kafafuna a kasa.

"To ka kwana da sanin ni Inteesar bazan yi soyayyah da kai ba don ni ba budurwa ba ce da har zanyi wani saurayi yanzu bare aure. Shekaru na dududu nawa a duniya eh? Nace nawa? Karatu zanyi insha Allah. yadda MASARAUTA ta temake mu zata debi yara mata suyi karatu haka zanyi insha Allah. Kama cire ni...."

Ajiye bokitin Adamcy yay a kasa. Ya shafa gashin sa daya shafa masa kunfan los yayi 'dai dai dashi kamar wani mace. Tsakiyar gashin yasa matajin kai acikin sa Ya sake dedeta tsayuwar sa. Yana mai jan kasan leben sa.

"Ni Adamcy dan gidan Alhaji zakiwa haka? Duk yankin kindau akwai wanda ubansa yaje makka bayan nawa uban? Kaf garin nan wakeda shagon kayan masarufi idan ba Alhajin mu ba? Ko kuwa kunada injin dake baku wuta? Shanu 'dai dai har nawa nace zan baki idan kika amince zaki aure ni? Eh? Ki ajiye wauta a gefe kidubi zahiri, Shayi da burodi sekin gaji da shi Intee, Indomin ukasha da tsiren tanimu sekin ture, zuwa cikin birni duk sati na miki alkawarin nan zamu dinga zuwa hutawa. Akwai gidan kawu na acan.."

Dogon tsaki naja. Na sauke ajiyar zucia kawai.

"Adamu bazan yi soyayya da kai ba, Ballantana aure ya shiga tsakani na da kai.. Ai bani kadai ce mace a kindau ba. Na kuma gode da kaunar da ka nuna mun. Allah ya baka wata ta gari Amin."

Ban tsaya jin tacewar sa ba, Nayi gaba abuna bayan na sunkuce bokiti na. Nan na barshi a tsaye na tabbata mamakin kalamai na yake. Ni kuwa zucia ta fes . Nayi gaba abuna, inata Allah Allah sha biyun rana tayi muje kofar gidan hakimi a raba mana kayan makaranta.

*NEWYORK CITY*
(Manhattan: Borough of Newyork)

"Kai Nasser tashi ka kira yayan ku, wallahi idan mukayi missing flight sai ransa ya 'baci."

Haj zaynab ta dubi Nasser dan ta. Dake zaune kan hannun kujera yana latsa wayar hannun sa.

"Mami.. Wallahi banason ya hau ni da fada."

"Zaka tashi kaje ka gaya masa ko kuwa sai na saba maka?"

Ba yadda Nasser ya iya, Adole ya mike, Ya shiga haura matattakar benen, gaban sa na tsananta buguwa saboda yasan masifar halin yayan nasu."

"Knock knock"
Ya furta hade da kwankwasa kofar dakin.

"Yes! Who's there?"

"Itz Nasser! Mami tace kazo mu tafi kar muyi missing f...." Ai be karasa fada ba, yaja baya da sauri jin yadda yayan nasu ya jefo wani abu ta kofar. Ji kake gwararam gwam.

Ai kuwa sum-sum-sum Nasser ya sakko da sauri yana sosa keya.

"Yana zuwa wai."

"Ai ba kurma bace na jiyo sautin bugo kofar da yayi ai. Uban yan bak'ar zuciya kawai. Allah ya shirya"

"Aamin!" Nasser ya amsa ahankali hade da juyawa baya gudun kar yayan nasu ya taho ya jiyo shi...

××Shi kuwa Mukhtar yana zaune a gefen gado. Ya gama hada kayan sa a akwati. Bakin ciki ne fal cikin zuciar sa na komawa rayuwar cikin MASARAUTA da zeyi. Bayan tsananin tsanar da yayi mata.

Takanas mahaifin su yasa mahaifiyar tasu Haj zaynab taje tataho da Nasser din daga Newyork city. Da anan gabaki daya suke da zama. Bayan an masa kira kan yazo ya karbu mulki kuma gabaki daya iyalin sai suka koma kasar ta Nigeria. Mukhtar dinne kadai bai koma ba yace sai ya gama degree . Kuma yace ze dora da masters baban yace bai san zance ba. Sai ya fara zuwa MASARAUTA tukun ya zauna dasu na wani dan lokaci.

Ajiyar zuciya ya sauke, Ya rufe akwatin nasa ya bi dakin da kallo kafin ya fuce ya sauka kasa. Ransa a matukar b'ace...

Already sun shiga mota dama suna jiran sa, Sai daya mula ya sha iska tukun sannan ya wuce parking port. Ya shiga mota suka dauki hanyar airport don komawa kasar su ta gado wato Nigeria.....

--------------
Chapter 4 · 0% Book details