Sashe 1
Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[5/22, 9:58 PM] Miss Xoxo: *_MASARAUTA_*
_(A cindrella story) _
👑 💘
_*NA_*
_*NANA HAFSATU_*
_wattpad:missxoxo00_
_Arewabooks:mssxoxo_
_*ZAFAFA BIYAR 2002_*
_PAID NOVELS/LITTATTAFAN KUDI NE_
_*FREE PAGE: 1_*
_بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ _
_Wannan littafi kirkirarre ne, Sunaye, garuruwan ciki da sauran abubuwan daya kunsa idan sunyi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu. A gafarce ni. Sannan bloggers , YouTubers da sauran su, Dan Allah kada a daukar min littafi ayi amfani dashi ba tare da izini na ba. Duk wanda yayi hakan nabar shi da Allah. _
••••. <><>•••••
*YANKIN KINDAU*
*TSANGAYAR GWANI TSAYYABU*
×××Zaune gwani tsayyabu yake, Ya harde kafafuwansa. Sanye cikin babbar riga ba yar cikinta. Sai wandon rigar kalar sararin samaniya.
Hular kansa irin tashi ka fiya nacin nan ce. Hannunsa rike da sharbaceciyar bulala yana dagata sama da kasa .
Almajiran dake gabansa kowanne ya langabar da kai cike da fargabar kar dorinar sa ta ruguza akan su. Sai kururuwa murya suka sake yi dede lokacin da gwani tsayyabu ya mike yana maimaita.
"To kai, To kai..."
"minjaye , Nu'ara, Alu, hasabe, shimmeruwa, Ya, Mi, Ara. Aya. Alu, an, baki, waw, zal, baki, lallan, hakuri. .."
Suna fada yana kada kai. Dai dai lokacin da ya hango Gwani Dauda yana tahowa wajen sa. Sai zabga sauri yake yi
"A tsaya, Ina Rabilu?"
"Iya gida innani ta aiko an kiran sa. " Cewar Musaddiqu qani ga Rabilu.
"To kai masa jiranye kafin ya dawo. Ayi karatu dakyau. Idan 10 tacika atashi atafi gidajen aiki. Karfe 2 adawo anaji ko?"
"Eh!"
Da sauri ya fuce daga yar langalangar kwanon da yake koyar da almajiran nasa aciki. Dogon kwano ne da bai cika fadi ba . Don haka aka rabashi biyu. Rabin sa suke karatun aciki. Daya rabin kuma wajen kwanan su ne.
"Barka da safiya Dauda " ya karasa fada yana mai mikawa gwani Dauda hannu sukayi musabaha.
"Barka de . Baka shirya ba kenan. "
"Afuwan. Yar cikin kawai zan zuro yanzu agida mu wuce. Se mu hau achaba don muyi saurin samun daurin auren ko.?"
"Ai se 11:30 idan muka yanke ta cikin bingi nan da nan zamu isa.Ba sai mun batar kudi ba Insha Allahu "
"Hakanma yayi. Bari na zuro rigar. " Gwanni tsayabu na karasa magana ya haye dan dakalin dake kofar gidan sa ya shige.
**GIDAN KWANO**
Harira da Naja matansa kowacce na zaune daya na kallon gabas daya yamma.
Tunda suka amsa sallamarsa kowaccensu ta juyar da kanta gefe tacigaba da abunda take.
Daga labulen dakin harira yai ta mike da sauri tana janye hannun nasa.
"Malam ya haka kuma? Ko kayi ajiya ne bansani ba? Sarai de kasan ba kwana na bane bare kace kayi mantuwa."
"Karma ka soma budemun daki. Babu komai naka aciki " cewar Naja dake susar kunne da gashin kaza.
"Ah malam ka shigo? Sannu da dawowa. Kayi hakuri ina cikin bayi ne." Cewar amaryar sa zaituna Wadda tafito daga cikin bandaki. Tayi daurin zani. Sosonta na rataye a kafadarta. Hannunta daya Kuma yana rike da kwandon wanka da sabulu.
Naja dake can gefe taja dogon tsaki tana yatsina. Harira kuwa fuuu tashiga cikin kuryar dakinta tana mita.
"Shigowa ta kenan yar albarka. "
"To malam sannu da dawowa. Mu shiga ciki ko?" Ta karasa fada tana mai dage yamfadin dakinta.
Ya dan saci kallon Naja ta wutsiyar idanu ganin yadda tacika tayi fam tamkar zata fashe hakan yasa gwani tsayyabu hanzarin girgiza kai domin baya son tashin hankali.
"Yi sauri ki miko mun rigata yar ciki, Nan na barta ko?”
Zaituna ta shiga duddubawa, Can saman gadonta ta hango rigar a ninke. Ta dakko hade da turarenta na ruwa ta shafe rigar da shi.
Ta zura hijabi ta fito da rigar a hannunta,
“Gashi Malam….”
“Yauwa yar albarka. Sai kamshi take. Nagode miki.”
Nan da nan ya zura rigar, Hade da janyo nera dari biyu cikin aljihun sa.
“Gashi wannan a sayo kayan miya, Ai shine kadai babu ko?”
“Eh komai akwai Malam, Shinkafar ma Za’a dafa yau a dafa gobe da yardar Allah bata kare ba. “
“Toh Masha Allahu. Naja’atu yaran nan basu dawo bane.”
“Kawai dai kace yar gabon goshin naka bata dawo bane?”
Girgiza kai kawai yayi, Ya dan saki murmushi, Can kasan makoshi ya furta,
“Allah ya kyauta. Ni na tafi, Semun dawo.”
“Toh Malam Allah ya kai ku lapia ya dawo daku lapia. Mu ma idan rana tayi sanyi zamu leka wunin.”
“Aamin, Hakan nada kyau.”
Har kofar fita waje zaituna taiwa gwani tsayyabu rakiya. Sannan ta koma cikin gidah.
**INTEESAR*
**
Ina tafe ina tankadi da bokitin da yake kai na ina ‘digirgire da shi.
Wanki mukayi a kogin bagaja. Nagaji liqis, Allah Allah nake mu karasa gidah saboda gajiar da muka kwaso.
“Intee, Ni kuwa ya kukayi da Malam isubu? “
“Waye Malam isubu.?” Na kalli indo yayata ko nace kusan sa’ata. Ina gatsina fuska.
“Kutuma. Malamin naku yau kuma shine baki sani ba.”
“Au ho, Mugu zakice mun. Canta matse masa. Ni na manta da babun sa sai yanzu da kika budo shi.”
“Ai Intee yar renin hankali ce.” Fatsima kanwata tafada tana tafa hannuwa.
Daria muka kece na taune kasan lebe na, Hadi da gyara zaman zanin da ke daure ajiki na.
Muka cigaba da tafiya muna hira, Munzo dabdalar samarin yankin mu, Sai ga Adamcy wai shi bai yarda ba masoyi na. Se buda kafada yake yana takowa wajen mu. Na dube shi tamkar na feffella masa mari saboda bakin ciki.
Ya ajiye boko yace ba zeyi ba, Shi ba arabin ba, Bayan maza kadai ake bawa yancin yin boko a yankin mu. Ina matukar son karatun boko amman ba damar nayi. Inaji Ina gani dole na hakura. Duk kuwa da babu ranar da zatazo ban roki Allah bukata ta na sonyin karatun boko ba.
“Masoyi yahhhhhh…”Cewar adamcy yana wani kanne idanu.
Naja dogon tsakin dana tattaro tsawonsa tundaga ruwan cikina zuwa baki na. Hade da dankara masa harara.
“Au kwafsii.. Yayar mu ina kwana, Kanwata an wuni lapia.?” Ya rissina yana gaysar da Indo, Dake murmushi.
Suka amsa shi. Ni kuwa saboda takaici gaba nayi tamkar zan tashi saboda sauri. Sai jin iskar wucewar sa nayi ta kunne na. Ya karbi bokitin hannu na yana murmushi,
“Haba tagaban goshin Adamcy, Ki dena wahal mun da kan ki. Nafa gaya miki duk sanda zaki wanki, Na zama mawankin ki, Zan wanke miki kayan ki, Na durje su na sabe miki, Kana na kaiwa Buhari me guga ya goge miki su sab..”
Ai ban bari ya karasa ba nayi gaba abuna ina jan tsaki. Da naga yana kokarin cinmani a sauri, Na Kara kwasa aguje na shige gidan su Wasila kawata.
Haka yaita buga nacinsa a kofar gidan na hana wasila da kannenta zuwa wajen sa. Don kansa ya gaji ya aiko yaro da botikin nawa da kuma awarar dijama ta wazobia……
×ZAFAFA BIYAR×
pAGES 1K 1page kullum books biyar.
Pages 2: 3k vip group .
Vvip ta pc:3500.
Talla saman page:1k
Tsakiya 800
Karshe 500.
ZAFAFA BIYAR*
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
MSS XO WRITES❣️
[5/22, 9:58 PM] Miss Xoxo: _*MASARAUTA*_
_(A Cinderella story)_
👑💘
_FREE PAGE: 2_
_NA:_
®️ _NANA HAFSATU_
©️ _ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_wattpad:missxoxo00_
_Arewabooks:mssxoxo_
_BUSINESS:👇🏾_
_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_
_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_
_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_
_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_
_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_
_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_
_ARABIAN OIL PERFUMES_
_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_
_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_
_SKIN CARE PRODUCTs_
_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_
_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_
_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_
_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_
_instagram:yerwaincense_and_more_*
_WhatsApp: 08095215215_
__
×××Ina baje akan tabarmar gidan su Wasila mun gama cinye awarar da Adamcy ya aiko da ita. Na mike ina gantsare bayana. Saboda yadda hakarkari na ke ciwo tsabar durkushen wanki.
Yarkaccacciyar akuyar gidan su Wasila tayo kai na tamkar zata ciza. Nasa kafata na shureta ina had'e fuska.
"Idan talaka ne kai. Kowa da komai raina ka yake."
Innar su Wasila dake gefe tana tankade tayi daria.
"Ke Kuma da wa yar albarka?"
"Da akuyar nan mana Inna. Kamar mayya zata cinye mun kafa. Banda tsabar reni ta isa tayiwa masu kudi haka?" Na juya na gallawa akuyar harara hade da gatsine baki.
Inna tayi dariya kawai tana girgiza kai,
"Sabo ne kawai da tayi da ku. Kudi kuma da yardar Allah yar albarka wataran sai kin bawa wasu ma kyauta."
Sosai naji dadin adduar da innar su Wasila ta mun. Na dashare baki na saki murmushi kawai ina mai jujjuya zobena dake karamin yatsana na karshe.
Na zundumawa Wasila kira dake can kuryar daki tana neman hijabin da zata mun rakiya .
"Ke ni zan tafi. Bar rakiyar."
"Haba kawata"
"A'ah ba za'ai haka ba, Ke Wasila zo ga nawa jikin taga ki dauka ki mata rakiya har gidah." Cewar innar su.
Da sauri Wasila ta fito ta zura hijabin muka tafi , Bayan nawa innar su sallama.
Muna tafe a hanya muna hira. Ba wani tazara bace sosai tsakanin gidan su da gidan mu . Amma dake hirar bamason ta Kare ba kuma ma so mu rabu, Sai muke tafiyar ahankali. Bokitin kayan wanki na na dauke a hannun Wasila.