← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 5

Sashe 2

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har kofar gidah tamun rakiya. Muka tsaya a kofar gidan namu muna masu cigaba da hirar mu. Wanda rabin hirar dik zancen wulakancin da Fati kawar mu tayi mana ne. Babar su ta haihu, Fatin tahada pati ta gayyaci kawayen mu yan gayun yankin mu mu kuwa bata gaya mana ba , Su kaci biskit da su lemon kwalba ance har da cincin da kankarar lemon leda ta bakin kasuwa.

Naja kwafa hade da daga hannu sama na nanawa cinyata duka bayan na kwararo rantsuwa na dire.

"Ai Fati zataci kwal haka kaza na ubanta. Gidan ta tabo. Ko a islamiyya ta nuna ta sanni sena mata dukan kawo wuka, Shegiya da kai runtume-me uwa randa "

Wasila ta kece da dariya. Ta bani hannu muka sake tafawa.

Daga can lungu na hango baban mu yana tahowa da yar leda a hannun sa. Ai ban bari mun karasa hirar mu da Wasila kawata ba na tafi wajen sa aguje Ina murna.

"Baban mu sannu da zuwa"

"Yauwa yar albarka . Ba dai sai yanzu kuka dawo ba?"

Na sosa kai ina girgiza shi a tare.

"Na tsaya gidansu Wasila munyi wasa"

"Masha Allah. To Allah yayi albarka. "

Wasila ta karaso wajen mu ta durkusa ta gayar da baban mu. Ya amsa mata fuskar sa dauke da fara'a.

Nan yabar mu tsaye zai shige cikin gidah na figi bokitina dake hannun Wasila nayi cikin gidah da gudu ganin yar bakar ledar dake hannun baban mu.

Wasila dake tsaye ta girgiza Kai kawai tana daria kafin ta juya ta koma gidan su.

  ×××GIDAN KWANO×××

Ina shiga gidah na rafka sallama. Hade da zubewa akan kujerar Inna Harira. Da sauri tayo kai na tana makamun harara.

"Daga min kujerar uwar sarkin yan hankali. Daga tashi na kin dora wadannan kazaman duwaiwan naki akai. Bayan kashedin da nake rafka miki akan karki sake zama akan kujera ta. Tashi ina magana kin zubamun wannan idanuwan naki na mujiya."

Tunda ta fara magana na zuba idanu kawai ina kallonta, Duk rashin tsafta ta nafi Inna Harira . Domin haka kawai seta jera kwanaki bata wanka bare wanki.

"Kaii, Tashi dan kunzugurin buroaban ki. Ina magana kin zubamun idanu. "

Zumburo baki nayi gaba, Ta yo kai na zata dakeni nayi wajen Babanmu da sauri. Ya sha gabanta yana bata hakuri

"Aikin kawai. Yo ai dama kai ka bada dama ta rena mu. Tsintacciyar mage dai ba ta mage. Ka dinga fifita yarinyar da ba yar cikin ka ba akan 'yayan ka. "

Maganar Inna Harira ta doke ni kwarai matuka. Nayi hanyar dakin Umma ina mai danne hawayen da ke san kufce mun.

Umma zaituna dake shiryawa a daki tayi saurin riko ni ta rungumo ni jikinta. Kukan dana keson boyewa ya kufcemun. Duk kuwa da karancin shekaru na, Rashin sanin tushe na sam bayamun dadi. Gorin da akemun nagaji da shi Murya ta na rawa nace,

"Umma, Dan Allah waye mahaifi na ne? Menene tushe na, Taya akai aka same ni Umma? Wacece ni? Umma ki gayamun tushe na, Ko ni din she..."

"Kar ki karasa fada Inteesar, Kar na sake ji. Kema 'ya ce kamar kowa, Haifar ki akayi kamar yadda aka haifi kowa, Kina da tushe da usuli me kyau da yardar Allah. Bar kuka kinji diyar kwarai. Allah ya miki albarka."

Kuka na na share, Na shiga kada kai na alamar toh.

"Ga abincin ki can cikin kwanon ki. Maza wanko hannun ki kici kinji."

"Zo nan uwata." Babanmu ya kirawo sunana. Na share hawaye na na fita tsakar gidah wajen sa.

Takardar kifi ya mikomin daya kakkasawa kowa.

"Rike ke dana umman ku."

"To mungode Allah ya saka da alkhairi."

"Aamin"

Daki na koma bayan na wanke hannuna. Umma ta raba mana namu kifin. Na shiga yaga da fatar ina hadawa da abincin inaci. Kwan kifin kuma na dagargajewa mageta shi a takarda da abincin na ajiye mata taci idan tadawo daga yawon ta. Ina kaunar yar mageta, Jinta nake tamkar kanwa ta ta jini.

××× Ina daga kwance a daki na fara jiyo muryar Babanmu yana bawa su Inna labari kan makarantar maza da zaa gyara ta boko wadda zata zama za'a dauki har yara mata. Masarautar birni ce ta dauki nauyin komai. Ina karasa ji na fita da gudu ina haki.

"Babanmu me kace? Makaranta? Boko? Mata? Kowa kenan ze iyayi?"

Babanmu yayi murmushi hade da kada kansa.

"Shakka babu uwata. A dan guntun ilimin de da nake da shi. Makarantar ma sunanta yana nuna taci sunan marigayi sarkin birni na baya. Mai taken: SARKI ALIYU (ALKALI) MEMORIAL JUNIOR/SENIOR SECONDARY SCH. KINDAU)"

Ai ban bari ya karasa magana ba. Na figa nayi waje aguje, Ban tsaya ko ina ba se gangaren makarantar maza ta boko. Inda naga anata fashe fashe ana sauke kayayyakin gini. Bansan sanda na barke da hawayen da nake da tabbacin na farin cikin bane. Banda hamdala ba abunda nake maimaita wa cikin zuciya tah...

**ENGLAND**
LEICESTER CITY TOWN OF LEICESTERSHIRE (EAST MIDLANDS)

_
MASARAUTA (LABARIN SOYAYYAH) YANA AREWA BOOKS👇

https://arewabooks.com/book?id=6284e72eef85a63a21dbc5f5

SO DA ZUCIYA

SHIMA YANA AREWA BOOKS👇

https://arewabooks.com/book?id=623f824f9c4af77be0e96e3d

🥰😍
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

_MSS XOXO WRITES ❣️_
[5/22, 9:58 PM] Miss Xoxo: _*MASARAUTA*_
_(A Cinderella story)_
👑💘

_FREE PAGE: 4_

_NA:_

®️ _NANA HAFSATU_

©️ _ZAFAFA BIYAR WRITERS_

_wattpad:missxoxo00_
_Arewabooks:mssxoxo_

_BUSINESS:👇🏾_

_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_

_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_

_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_

_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_

_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_

_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_

_ARABIAN OIL PERFUMES_
_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_

_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_

_SKIN CARE PRODUCTs_
_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_

_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_

_instagram:yerwaincense_and_more_*

_WhatsApp: 08095215215_

__
**Ina gamawa na shige dakin Umma ina hawaye saboda abin inna Harira ya fara yi min yawa, bana san hantara na samu guri na kwanta. Umma ta shigo ta ganni sai faman turo baki nake, tayi murmushi kawai ta zauna kusa dani tana shafa kaina.

"Baki da lafiya ne?"

Ta tambayeni cike da kulawa. Nai narai-narai kamar zanyi kuka ina cewa.

"Umma bata sona."

"Waye baya sonki?"

"Inna Harira."

Cikin sauri ta kalli bakin kofa ganin babu kowa yasa ta kallona tana shafa gefen fuskata tace.

"Tana sanki karki sake cewa bata sanki idan taji sai tafi takura miki."

"Toh dagaske ne ni ba yar nan gidan bace?"

Ta kuma saurin rufe min baki alamar bata san ta dinga jin ina wannan maganar.

"Ki dena biyewa zancen ta so take taga kina kuka, bakiga yadda take yiwa su Fatsima ba? Suma ai ba kyalesu tayi ba ki dena damuwa kinji ko?"

Murmushi nayi sai naji dadi da kalamanta, Umma mutuniyar kirki ce, duk irin wulakanci da rashin mutunci da irin dibar albarkar da Inna Harira keyi mata tasan yadda zata zauna da ita, dan bata bari suyi rigima duk kankantar ta.

Nan da nan sai na tashi na fita da gudu muka hadu dasu Indo aka ci gaba da wasa. Ana gama abinci aka bamu mukaci sai muka sa hijabai muka tafi makarantar allo, kafin la'asar muka koma gida mukai shirin islamiya sai da muka yi sallah muka tafi.

Rayuwar mu haka take tafiya kullum tun tasowa ta a gidan duk munsan lokutan yin abubuwan mu.

Saboda Gwani Tsayyabu mutum ne jajirtacce akan duk wani al'amari nashi, baya san wasa akan sha'anin karatu musamman na addini, shi yasa duk muna haddar kur'ani a kan mu. Yana so yaga muna karatu sosai saboda yana yawan gaya mana cewa karatu shine mutum idan mutum bashi da ilimi wawa ne kuma dolo da bashi da alkibla.

Makaranta kuwa an kammala gina gabaki daya har an fitar da kalar uniform Kullum kunnuwan mu duk sun bude jira kawai muke a ce ga ranar da zamu fara zuwa makaranta.
Chapter 2 · 0% Book details