← Book details Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 5

Sashe 3

Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata rana an aikeni kai nika naje nakai sai mai injin yace dole sai na bari an tara da yawa sannan zai tada injin. Ni kuma dan karna koma gida inna Harira ta sani wani aikin yasa na koma karkashin bishiya ina yar carafke, akwai wani daga gefe zaune akan benci yana shan rake ya kirani.

"Ke zo nan."

Ina jinsa nai masa banza, ya sake kirana.

"Ke badake nake bane."

Na juya na kalleshi.

"Wai ni?"

"Eh ke, zoki karbi rake."

Na tashi da sauri na isa gurinshi, maimakon ya bani sai ya riko hannuna yana dariya tare da janyoni jikinsa nace.

"Sakarni."

"Bakya san raken? Ki tsaya baki zanyi."

Yana magana yana sake rikoni, ni kuma ina fizgewa, karshe dai dai ya matseni da kafa na fashe da kuka gashi babu mutane a wajan duk an tafi masallaci sallar la'asar.

"Ni ka sakeni, wallahi zan gayawa Umman mu, ka kyaleni bana san raken."

"Bazan sakeki ba, kuma idan baki min shiru ba sai na fasa miki baki yanzun nan."

Ganin ba zai kyaleni ba yasani cizansa a hannu amman be kyaleni ba sai ma kara matseni da yake yi. Sai da ya hango wasu mutane sun fara tahowa sannan ya sakeni ya tashi ya bar gurin da sauri. Suna karasowa suka gani ina kuka suka tambayeni nace musu wani ne ya gudu suka fara bani hakuri wani a gefe yana cewa.

"Be kamata dama a dinga barin yara mata suna yawan kai markade ko nika ba, gwara a samu ko almajiri ne ya dinga yin aiken."

Ina jin su nidai bance komai ba suka wuce ni kuma na koma inda nake naci gaba da wasana.

MASARAUTA (LABARIN SOYAYYAH) YANA AREWA BOOKS👇

https://arewabooks.com/book?id=6284e72eef85a63a21dbc5f5

SO DA ZUCIYA

SHIMA YANA AREWA BOOKS👇

https://arewabooks.com/book?id=623f824f9c4af77be0e96e3d

🥰😍
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

_MSS XOXO WRITES ❣️_
[5/22, 9:58 PM] Miss Xoxo: _*MASARAUTA*_
_(A Cinderella story)_
👑💘

_FREE PAGE: 3_

_NA:_

®️ _NANA HAFSATU_

©️ _ZAFAFA BIYAR WRITERS_

_wattpad:missxoxo00_
_Arewabooks:mssxoxo_

_BUSINESS:👇🏾_

_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_

_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_

_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_

_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_

_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_

_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_

_ARABIAN OIL PERFUMES_
_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_

_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_

_SKIN CARE PRODUCTs_
_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_

_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_

_instagram:yerwaincense_and_more_*

_WhatsApp: 08095215215_

*ENGLAND*
LEICESTER CITY TOWN OF LEICESTERSHIRE (EAST MIDLANDS)

**Zaune Haj Tasidi (Hafsat) take. Ta kifa kanta akan hannun kujera kirar royal. Kana kallon ta kasan ta lula duniyar tunani. Duba da yadda 'dan ta keta mata magana sam hankalinta baya jikinta.

"Maaa.. "Ya sake fada da dan karfi. Damuwa shima ta sake lallube shi ganin yadda mahaifiyar su take. Ga ba ba mai cikakkiyar lapia ba.

"Na'am.... " Ta amsa da sauri hade da juyawa .

Ganin Aliyu ne yasa ta danyi murmushi .

"Ka dawo?"

"Na dawo ba jimawa Maaa. Ya jikin na ki?"

"Jiki Alhamdulillah. Ga abinci can kan dinning. "

"Ban jima da ci ba a office, Sai dai ko anjima. Papaa ya tashi kuwa?"

"Maganin ne yana da dan karfi . Baccin har yanzu be sake shi ba sai ya sake komawa."

"Allah de ya kara muku lapia da nisan kwana mai amfani, Aamin"

"Aaamin"

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, Aliyu dake gefenta ya dan sake sunkuyar da kansa . Ahankali cikin tattausar murya yace.

"Kiyi hakuri Maa, In Sha Allah. Karshen damuwar mu ya kusa zuwa karshe. Tunda an tabbatar da h..."

Daga masa hannu tayi alamun yayi shiru. Hannunta daya na kan setin zuciyar ta. Ji take tamkar zuciar tata zata faso ta fado kasa. Saboda tsabar yadda gabanta ya tsananta bugawa.

"Hasbun Allahu wa ni'imal wakil. ." Ta furta ahankali tana mai dartse kasan lebenta

Ganin haka yasa Aliyu tashi ahankali yayi dakin mahafinsu dake kan gado ba lapia .....

**YANKIN KINDAU**

Murna taki barin cikin raina, zuciyata banda dadi da wani shauki babu abinda takeyi, ganin Allah yayi nima zanyi makaranta. A rayuwa ta ina so na ganni cikin uniform saboda ko a jikin wasu na gani sai naji wani farin ciki. Gashi muma yanzu za'a yi mana makaranta kamar yadda sauran yara masu galihu suke zuwa. Har wajan da ake tara kasa naje inda ire-irena suke wajan suna ta wasa akai, hauwa nayi nima ina ta tsalle tare da juyi.

Isowar Wasila wajan ya sake faranta min, na sauka da gudu naje muka rungume juna muna ihun dadi. Wasila ta sakeni tana kallona tace.

"Intee kema Babanku ya baki? Ni Kinga innar mu tace ko ana ha maza ha mata sai nayi saboda tana so nima na zama malama wata rana."

Nima na washe baki ina lumshe ido irin na firiritar nan na ce da ita.

"Tun yaushe ya yarda, Ai dama cewa yake inde Allah yasa muna da rabon yin boko, cewa yai ma sai nayi na samu aiki indai karatu ne."

Muka sake rungume juna cike da farin ciki kafin mu hau kan yashin muma.

Bamu bar gurin ba har sai da aka kira magariba, shi din ma sai da wani mutumi ya kore mu dukan mu yaran wajan. Muna zuwa wajan gidan su Wasila ta shige ni kuma na fara tafiya ina ta kallan yadda wani Dattijo ya sauke mai farantin tsire ana ta zuge masa a cikin takarda. Caraf naji an kamo min dan karamin hijab din jikina, nai saurin daga kai ina kallan ko wanene, ganin Adamcy yasa na turo baki cikin bacin rai nace dashi.

"Allah Adamcy idan kana cewa zaka aureni sai na gayawa malam, ni karka sake cewa dani zakai soyayya." Sai ya sakeni ya fara dariya yana cewa.

"Haba Intee, taya za'a ce kina kyakkyawar nan baki da masoya irina? Ni zan aureki na mallaka miki shanu uku kiyi ta kiyo kina samun kudin."

Na kuma turo baki.

"Allah idan ka sake cewa zaka aure ni Allah ya saka min." Sai ya sake kallo na yaga idanuna yana kan mai tsire, hakan yasa shi yin murmushi tare da cewa.

"Idan kika yarda zaki aureni yanzu muje na sai miki tsire tsinke biyu." Nayi shiru ina tunani gashi yawuna ya biya da tsiran, na kama kugu tare da kallanshi cikin ido nace.

"Banaci tunda ni ba mayya bace, aure kuma in ka sake cewa kana sona wallahi sai na gayawa Baban mu."

Adamcy ya toshe baki da hannunsa yana zaro ido cike da mamakin abinda nace.

Juyawa nai na tafi cike da jin haushi. Ina shiga na tarar an zuzzubawa su Fatsima tuwo nima naje gurin Umma na karbo nawa na samu guri a tsakar gida na zauna, ana ci ana surutu kuma duk akan ginin makarantar da za'ayi manane. Sai da mukaci muka koshi sannan kowa yaje ya dauki bjta yai alwala, nima nayo tawa naje nai sallah daga nan sai makarantar dare, a can muka yi isha'i sai karfe tara na dare muka dawo gida duk da cewa makarantar a kofar gida ce dan ta Babace.

Tsabar sanya makarantar a raina har mafarki nayi da ita, na ganni ina ta zuba kokari duk abinda akai nice nake fara iyawa. Sai da naji Umma na tashina sallar asubahi sannan ne na tabbatar da cewa mafarki nayi ba wai da gaske bane ba. Bayan munyi sallah makarantar asuba mukaje sai karfe takwas muka koma gida akayi karin kumallo daga nan sai debo ruwa, muna gamawa mukai wanka akai aiki wadanda suka yi da wuri ni da Fatsima da bamu gama da wuri ba aka samu dake-daken abubuwan da za'a dora girki.

Duk da irin karancin shekaru da nake dasu, dan a lokacin shekaruna tara a duniya, hakan be hanani gane irin yadda Inna Harira ke nuna banbanci tsakanina da sauran yaran gidan ba, ko abu indai itace zata raba sai nawa yafi na kowa kankanta, idan nai magana ta bubbuge min baki ko ta rankwashe ni tace na mata sharri ko tace haka taga damar bani idan ina da karfi nazo na kwata.
Chapter 3 · 0% Book details