← Book details Majanuni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 11

Sashe 7

Majanuni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce." Wannan mutumin ne da yake bina bashi zan bashi kyauta a madadin kudinsa, kin san yarinyar nakasashiya ce za'a sha wahala kafin a samu mai auranta shiyasa na yanke shawarar aura mata Saminu tunda dai shi din ma kansa d'aya da rabi ne.

Farin ciki ya cika zuciyar Talatu, babban burinta a duniya a ce Shahida ta wulakanta, a maimakon ta nuna masa kuskuran abinda yake shirin aikatawa sai ta cigaba da karfafa masa gwiwa cewa hakan da yayi daidai ne, domin shi yake da iko da 'yarsa.

Cikin wannan halin Shahida da Jamila su kayi sallama a gidan.

Talatu ta fito daga daki tana washe baki, abin mamaki cikin sakin fuska ta amsa gaisuwarta, ita kanta Shahidan abin ya bata mamaki mutuka.

Durkushe take a gabansa gabanta in banda faduwa babu abinda yake, tun kafin yayi mata magana ta karanci komai a fuskarsa, labarin gizo baya wuce na koki saura kwana uku wa'adin da ya bata ya cika, wasu zafafan hawaye suka shiga tsere a saman fuskarta.

Fuska a murtuke ya daka mata tsawa! da fadin.'' Ba kuka na ce kiyi min ba Shahida ki saurare ni da kyau! kina jina ko."? ya k'arashe maganar da karfin gaske wanda har sai da su Talatu su ka ji sautin muryarsa.

"Ina fatan baki mance magana ta dake ta karshe ba."?

Murya na rawa da yanayin maganarta ta ce." Ban man ce ba Baba."

Ya ce." Wa ki ka tsayar a matsayin wanda za ki aura."?

Kai tsaye ta ce." Babu kowa."

Ya jima yana kallonta kafin ya ce." To ba zaki mayar da ni mutumin banza ba, kina yawo godai-godai a gari ni ba shashashan uba bane, tunda kin kasa tsayar da mijin aure ni a matsayi na na wanda ya haife ki zan aurar dake ga wanda ya cancanta, saboda haka ki zauna cikin shiri ki kuma shedawa kakarki cewa nayi miki miji zan had'a ku tare da Hadiza na aurar daku a lokaci guda."

Wani irin kuka ne ya k'wace mata murya a sarke ta ke fadin." Baba ka da kayi min haka mana kayi min adalci ka sake bani dama a karo na biyu insha Allahu zan fito da wanda na keso."

Kafin ma yayi magana Talatu ta bankad'o dakin ta shigo domin duk abinda ke faruwa suna ji ita da yaranta, ta ce." Wa ne irin adalci ki ke so ayi miki ? ai ki godewa Allah tunda har ki ka samu wannan bawan Allah ya amince da cewar zai aure ki a matsayin ki na muskiniya, ki daina daukar kanki cikakkiyar mutum kamar kowa."

Maganganun Talatu sunyi mata zafi sosai! a shari'ance ma sunyi tsauri da yawa, jahili ne kadai ya ke bambamce jinsin mutum wanda Allah ya hallita mai lafiya ko mara lafiya, duk wata hallita da Allah yayi akwai manufa kuma ba don baya sonka ya hallicce ka hakan ba, shi ya fi so ya gan ka a hakan ne.

Da k'yar ta iya yunkurawa ta tashi. hanyar fita kawai ta nufa hannunta kunshe a bakinta kukan da take dannewa ya'ki dannuwa sai fita yake hawaye kuwa a saman fuskarta sai tsare suke.

A bakin titi adaidaita sahu ya sauke ta, yanayin tashin hankalin da take ciki ya sanya ba ta lura dashi ba, yana daga can tsallaken da jarkar ruwa a hannunsa zai je ya samu ruwan alwalwa a tuka-tuka! shi ya gan ta a firgice! hankalinsa kuma ya tashi ainun! ganin yanda take kuka! ya bi ta da kallo lokacin da take karya kwanar layin gidansu, sai da ta k'urewa ganinsa sa'an nan ya tsallaka titin cikin damuwa ya nufi in da tuka-tukar take yana tunanin abinda ya ke damunta.

Cikin matsanancin tashin hankali da damuwa ta shiga gidan, kai tsaye rugume kakar tayi tana rera wani irin kuka mai tsuma zuciya! duk da ta kasance nakasashiya ba zata so ayi mata irin wannan auran ba, gabadaya al'amarin bai kwanta mata a rai ba wannan shine dalilin da yake sanya ta zubda hawaye.

Baba Asabe ta rike ta suka shiga daki a tare, ita kuwa Saliha ko a jikinta ta'be bakinta ma tayi ta cigaba da aikin gabanta.

Da kyar Baban ta rarrasheta ta dora da fadin." Dama tun da naga wannan kiran na gaggawa na san akwai abinda zai faru, Jamilu ba shi da kirki ko kadan kiyi shuru ki fada min abunda sukayi miki."

Tasa hannu ta goge hawayen dake gudana a saman fuskarta, ido jawur! ta kalle ta da fadin." Wai aure zai yi min ."

Baban ta zuba mata ido cike da mamakin maganar

"Aure kamar yaya ."? ta sake tambayarta domin jin cikakken bayani.

Murya na rawa da yanayin maganarta ta fara sheda mata hukuncin da baban nata ya yanke a kanta cewa lallai zai had'a ta aure da wanda yayi ra'ayi.

Baba Asabe tayi tsalle ta dire! ta fara surfa bala'i ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce." Wato yanzu ne zai nuna iko a kanki saboda bashi da kunya an gama yi masa wahala kin girma kin zama mutum shine zai shigo da wannan maganar to wallahi bai isa ba mutukar ina raye ba za'ayi wannan auran ba."

Kawu Musa ya shigo gidan ya riski maganar ya zauna Baban tana sake jadadda masa cewa Jamilu bai isa ba yayi kadan sai dai duk in da za su shiga su shiga amma ba zata bari ba.

Ya ce." Baba musulunci ne ya bada damar hakan, ai budurwa ce mahaifinta na da ikon za'ba mata mijin aure bazawara ce kadai ke da 'yancin za'bar mijin da take ra'ayi, saboda haka babu ruwanki, ki cire kanki daga wannan maganar."

Ta ce." Ka san Allah ba zan lamunta ba, domin dai yarinyar nan ba ta da cikakkiyar lafiya to ba zan bari garin san zuciyarsa ya aura mata bara gurbi ba, a jikina nake jin akwai dalilinsa na aikata wannan abu."

Ya ce." To shikkenan yanzu abinda za'ayi shine zanyi binkice akan lamarin idan ya kasance shi wanda ake so ayi auran dashi mutumin kirki ne ya tara duk abubuwan da ake da bukata haka akeso, amma idan akwai mishkila a tare dashi nima ba zan bayar da goyon bayan tabbatuwar al'amarin ba."

Ta ce." Eh hakan yayi na baka wuka da nama kayi min binkice akan shi Jamilun da kuma dalilin da yasa yake so ya aura mata wanda ba ta so."

Ya mike da fadin." In sha Allahu zanyi kokarin gano yanda al'amarin yake.

A daran ranar Shahida ba ta iya rintsawa ba sallar dare ta kwana ta nayi tana kuka da rokon Allah yayi mata za'bi na alkairi a cikin ranta take jin za ta iya auran Baban-baba akan dai ta auri mutumin da mahaifinta yake kokarin aura mata, tun bata ganshi ba take masa wata irin tsana!

Da yamma tana daki a kwance tana tunanin rayuwarta ta tsinkayi muryar yaro." Wai ana sallama da Shahida in ji Saminu Abbatuwa."

Gabanta yayi mummunan faduwa! Baba Asabe ta harari yaron a fusace! ta ce." Ka je ka ce bata nan."

Yaron ya juya ya fita yana dariya! daman ya san za'a rina, tunda mutumin ya aiko shi gidan zuciyarsa ke raya masa cewa ba zai samu ganin budurwar da yake so ba duba da irin hallitarsa da tarin munin da Allah yayi masa.

A she bata hakura hijab ta zura a wuyanta ta kama hanyar fita tana surutai akan al'amarin, so take ta ga mutumin tayi masa cin mutunci!

Shirgegen mutum ta gani da katon ciki a tsaye a kofar gidan nata.

Ta kalli tafkekekiyar kafarsa da dunduniyar take waje sakamakon takalmin da yayi masa kad'an farce zako-zako kafafun sunyi wata irin daud'a da kaushi da faso abin babu kyawun gani!

Ta kalli sumulmulallan kansa da fuskarsa dake zuba uban kyalli 'kwayar idonsa jajawur gasu cike da kwantsa da alama dai yana da matsalar ido.

Hankalinta bai tashi ba sai da ya wangale bakinsa yana dariya babu ha'koran sama dana kasa sai turame a gefe da gefe! mummunan wawulo ne dashi! ya zube har kasa yana gaisheta.

Gefe ta matsa gabanta na dukan uku-uku! lallai Jamilu bashi da mutunci ina yarinya kankanuwa kamar Shahida za ta kai wannan katoton mutumin.

Ta gaza furta komai sai kallonsa take tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin.

''Baba Asabe Ina wuni." Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta.

Ta amsa "Lafiya lau kai ne kake sallama da Shahida."?

Ya ce." Eh ni ne sunana Saminu Abbatuwa ina sana'ar siyar da dabbobi a kasuwar Abbatuwa dake cikin wannan gari namu mai albarka."

Ta girgiza kai da mamaki a tattare da ita ta ce." Waye ya turo ka gurin Shahida? ko kuma kai ka ganta ka ga kana so."?

Yayi shuru yana nazarin maganar, fuskarsa ta sauya da bacin rai! ashe hujaj bai daidaita komai ba amma yasa shi zuwa domin a ci masa mutumci.

Ta sake maimaita masa tambayarta ta farko "Shin turo ka akayi ko kuma kai ka ga yarinyar kake so."?

Ya ce." Mahaifinta ne ya fansar min da ita a madadin kudin da nake bin sa."

Gabanta yayi wani irin fad'uwa! dama tasan ruwa baya tsami banza!

Ta kalle shi rai! a 'bace ta ce." To ka koma ka sheda masa cewa ni Asabe yayi 'karya bai isa ba ya sanya yarinya a caca na Shiriya zuwa kotun koli dashi a kan wannan al'amarin."

Ya sa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa ya kalle ta da mummunar fuska ya ce .'' Dama ba ni na nema ba shine yayi min kyautar ta a madadin kudin da nake bin sa kimanin dubu dari uku da hamsin saboda ya kasa biya na, don haka yanzu daga nan gidansa na nufa domin muyi wacce za muyi."

Ta ce." Wannan kuma ya rage naku." gida ta shige tana bambami da mamakin al'amarin.

Dawowarsa kenan daga kasuwa Saminu yayi masa dirar mikiya.

Tunda ya fito ya ga yanayin fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala ya bude baki kenan zai yi magana ya katse shi ta hanyar fadin......
Chapter 7 · 0% Book details