Sashe 6
Majanuni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ja dogon tsaki ta fita tana surutai, gabadaya Talatu ta raina shi, bashi da wata 'kima a idonta.
Kayan sa ya sanya ya fita yana cin kunu! sai dai yanayin yanda ya sami Saminun ya firgitashi, mutumin bai ta'ba bashi tsoro ba irin yau ba! amma sai ya jajurce yayi ta ma za! hannu ya mika masa da fadin." Malam Saminu barka da asubah."
Ba tare da ya amsa ba ya ce." Hujaj haka mu kayi da kai ."?
Yayi shuru bai ce masa komai ba.
Ya girgiza kansa yana hura katoton hancinsa ya ce." Lallai yau zan nuna maka asalin waye ni."!
Cike da burga da rashin gaskiya ya daga masa hannu da fadin." Ka ga Saminu ba fa za ka zo har k'ofar gidana ka fada min bakar magana ba, mai akayi akai dubu dari uku da hamsin da har za ka ishe ni da sallama wallahi na fi karfin haka."
Ya fusata! yana numfarfashi! fuskarsa na maiko ido cike da kwantsa ya ce." Kai har kana da bakin wata magana anan gurin wallahi i dan ba kayi wasa ba zan dau'ke ka na damfara ka da 'kasa! ni ba'a rai na min hankali."
Jin abinda ya ce yasa ya d'an tsorata amma bai nuna masa a zahiri ba, ya ce.'' Na so mu fahimci jun.......Ya katse shi da fadin." Jiya na zo da daddare ban same ka sai na barwa makocinka sallahu saboda haka bani da lokacin sauraran maganarka a yanzu." Wayarsa ya fito da ita "Eh gani a kofar gidansa ku 'karaso." Ya kashe wayar ya mayar da ita aljihu! Malam Habu ya fito da shirin tafiya kasuwa ya ga abinda ke shirin faruwa 'Yan sanda sun zagaye Hujaj daya na kokarin daura masa ankwa a hannu.
"Subahanallahi." Wannan kalmar ya furta yana kallonsa, kafin ya ce." Haba Saminu har an kai ga haka kuma? kayi hakuri ku fahimci juna mana.''
Ya ce." Malam Habu na dawo daga rakiyar wannan mara mutuncin bashi da gaskiya mugun makaryaci ne, saboda haka hukuma zata raba ni dashi."
Hujaj ransa idan yayi dubu ya 'baci sai gumi yake ya gaza furta komai bai ta'ba tsammanin mutumin zai masa haka ba.
Ya kalli yanda jama'a suka fara taruwa a gurin suna kallonsu abinda ya tsana kenan zubewar mutumci mutane na kallonsa da kima da mutunci amma Saminu ya ci masa mutunci a gari.
Hayaniya tasa Jamila fitowa kofar gidan, can ta hange su sun tasa k'eyarsa domin tafiya ofis dashi, da sauri ta koma gidan tana shedawa Talatu abinda ke faruwa, ko a jikinta ta cigaba da sabgoginta a fili ta ce.'' Shi ya janyo wa kansa cin mutumci saboda haka babu abinda ya shafe ni shi ya siya."
Yaran suka zauna jugum!-jugum! duk lalacewar sa, ba za su canza shi a matsayi a ubansu ba.
Wai a kace labarin duniya ba ya 'boya har gida labari ya same ta, da yake sana'arta ta jama'a ce, duk wanda ya zauna sai ya jajanta mata wasu kuwa munafurci ne ya ke sanya su maganar.
Shahida kam daki ta shiga ta ci kukanta ta koshi, ta rasa yanda za tayi da rayuwarta kunyar fitowa take saboda irin kallon da mutane ke mata dole sai sun nuna ta da tambayar Baba Asabe ita ce 'yar Hujaj wanda bai san ma shine mahaifinta ba to a ranar ya sani.
***
"Ranka ya dad'e iyakar hakuri nayi kawai abinda nakeso ku sanya shi ya biya ni kudi na domin akwai hidima a tare dani."
Officer ya ce." Saminu kaje kuyi sulhu a tsakaninku mu za mu shiga cikin al'amarin mutukar bai cika alkawarin da ya dauka ba, tunda dai ya ce yasa gidansa a kasuwa yana jira a bashi kudin a karshen wata to zamu zuba ido lokacin ya cika, idan ya sa'ba alkawari za mu shigar da 'kara kuto."
Fuskar nan a murtuke! ya ce." Ranka ya dad'e aure nakeso nayi a wannan lokacin nima ina da uzuri gaskiyar magana kenan wannan mutumin makaryaci ne na daina yarda da maganarsa."
Ya kalleshi da fadin." Saminu ni ne fa nayi alkawari cewa 'karshen wata ana bani kudin gidana zan biya ka kudin ka amma cin mutuncin da kake min ya isa haka muna gaban hukuma anyi komai a rubuce da kuma sharad'i ka kwantar da hankalinka zamu rabu lafiya insha Allahu."
Ya d'an sassauta amma bai saki fuskarsa ba tana tanan kamar hadarin dake dab da zubda ruwa, ya kalli Officer din da fadin." Na amince da hakan amma ayi komai a rubuce da sanya hannuku sannan kuma a fada min ranar da zai bani kudi na domin nima na shiryawa hidimar dake gabana."
Officer din ya kalleshi da fadin." Hujaj kaji bayanin Saminu yana bukatar sanin rana da kuma kwanan watan da zaka biya shi hakkinsa."
Yayi jim yana nazari wannan maganar ya shata ne kawai ya fad'a amma babu wani dilalli da sukayi cinikin gida dashi kawai ya fadi hakan ne saboda ya kubtar da kansa yana kuma hasashen kafin zuwan lokacin sa'a ta fado kansa a gurin sana'ar tasu.
Ya ce." ashirin da takwas ga watan uku ya kama ranar lalata kenan insha Allahu zan biya Saminu kud'insa."
Officer ya rubuta ya sanya hannu, ya mika masa shima ya sa hannu. Ya kalli Saminun dake tsaye ya sa katon ciki a gaba, ya ce."Kai ma kasa hannu akan wannan yarjejeniyar ni ne sheda."
Ya kar'bi zungureriyar takardar yayi jagwlgwalonsa a kai domin dai bai san me ake nufi da singing ba.
Bayan kwana biyu 'kura ta d'an lafa ya nufi can abbatuwan in da Saminu ke kasuwacinsa na siyar da nama ya same shi da wata sabuwar magana.
Bayan ya gama sauraransa sai ya hau shafa 'katoton cikinsa yana dan murmushi wargajejen wawulonsa ya bayyana ya ce." Eh to Hujaj ban k'i maganarka ba zan iya amincewa da manufarka mutu'kar yarinyar ta kwanta min a raina, saboda haka zan je na duba ta na gani idan ta cancanta sai mu fanshe kawai."
Ya sanya dariya da fadin." Ai wannan yarinyar tawa ba ta da makusa cikakkiyar macace san kowa kin wanda ya rasa, matsalar kunne kawai ke da ita amma bata da wani nakasu."
Shima yana dariyar ya ce." Ai ni babu ruwa na da matsalar rashi ji daga gare ta, idan tana da abubuwan da nake bukata daga jikin mace falillahil hamdu.''
Ya bashi hannu suka tafah! kafin ya ce." Kawai ka je ka same ta a can gidan kakarta dake bakin titin jakara 'yan gurasa ai gidan ba 'boyayye bane Baba Asabe kowa ya santa a kan sana'arta."
Ya ce." Babu damuwa insha Allahu gobe da daddare zan je na duba ta yanda ya kamata."
Su kayi sallama cikin barkwanci kamar ba su ta'ba samun matsala ba, Hujaj ya nufi kasuwa cike da farin cikin rabuwa da nauyin Saminu dake kansa, yana da tabbacin cewa yarinyar za tayi masa kamar yanda yake bukata, tunda duk in da ake bukatar cikakkiyar mace to ta kai gurin.
*Turkashi!*
*LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV*
[9/7, 10:43] bintaumarabbale: _MAJNUN!_
*'BOYAYYAN -ATTAJIRI*
_NA_
*_BINTA UMAR ABBALE🍒_*
_MANAZARTA WRITES ASSO_
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*29&30*
Da wuri ya dawo gidan, ya umarci Jamila cewa ta shirya da sauri kada magariba tayi ta je ta kira masa Shahida maza su zo tare yana nemanta.
Tunda Talatu ta ji haka ta san da wata a kasa. sai ta bishi dakin ta same shi a kishingide yana zan can zucci.
Gefan sa ta zauna da fadin." Na ga ka aika a kira maka wannan yarinyar a jikina na ji ruwa baya tsami banza."
Ya kalle ta na second biyu kafin ya ja tsaki da fadin." A nan ki ka fi kauri gulma da tsugudidi dube ki don Allah kamar ba mace ba, wannan tufafin na jikinki idan ban mance ba yau kwanansa hudu a jikinki."
Hannu ta daga masa da fadin." Ya isa kada ka ci min mutunci, shin da kake wannan maganar ka siya min sabulun wanka ko omon wanki ne."?
Shuru yayi mata banda hararar ta babu abinda yake.
Tace." Da fatan dai yarinyar nan ba gidan nan za ta dawo da zama ba domin wallahi ba zan iya rike ta ba nima naji da nawa."
Tsakaninta da Allah take maganar.
Ya gyara zamansa da fadin." Aure zanyi mata itama ta huta da wannan cin mutuncin naki."
Tabe baki tayi kafin ta ce." Au ashe ta samu mijin aure amma babu labari."