← Book details Majanuni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 11

Sashe 4

Majanuni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can gurin mai siyar da wainar geron ta nufa. A ka ci sa'a wainar bata k'are ba. to koda ta siyi wainar a maimakon ta nufi gida kai tsaye gurinsa ta koma domin ba ta tsammanin za ta iya sanya wani abu a cikinta mutukar ba tabbatar da cewa shi din yaci wani abu ba.

daf dashi ta tsuguna da ledar wainar a hannunta, cikin yanayin tsoro ta kirayi sunansa, ya bude ido yana kallonta, tace." Ga waina za ka ci ko.? ya bi hannunta da kallo lokacin da take mi'ka masa ledar wainar.

Ta fara kokarin kwance ledar tana fadin." Ga ta nan da zafi kaci bari na je gida na kawo maka kunu ka had'a."

Kallonta kawai yake bai sa hannu ya kar'bi wainar ba.

Ta marairaice fuska kamar za tayi kuka tace." Don Allah ka ci wallahi tausayi kake ba ni.''

Tsigar jikinsa ce ta tashi jin abinda tace. Ya tsira mata idanuwansa yana jin wani irin tausayinta, ya lura da yarinyar ta na sonshi sosai kuma duk abinda ta fad'a gaskiya ne.

Hannu yasa ya karbi wainar a takaice yace." Na gode."

A hankali yayi maganar shi yasa ba ji ba, amma ta fahimci godiya yake mata.

Ta mi'ke da fadin." Bari na je na dawo."

Bai ce mata komai ba, ta tsallaka titin ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a kanta.

Cikin farin ciki ta shiga gidan, lokacin har sun fara aikace-akaice abincin siyarwa Baban tana yanka kabewa ita kuma Saliha na gyara alayyahu.

Da farin ciki a tare da ita tace." Baba akwai kunun ko."?

Tace." Eh saura naki a kadai gashi can a jug."

Tace." Baba yau dai na ga Baban -Baba a bakin titi wallahi dadi ya rufe ni.'

Ta harareta da fadin." Matsalarki ce wannan Shahida ni abinda nakeso ki zo ki daka min gyadar miya domin yanzu zan hura wuta na dora miya."

Tace." Shikkenan yanzu zan zo nayi."

Ba ta sake magana ba, kawai sai gani su kayi ta shiga daki minti biyu ta fito da kwano a hannunta, ta dauki jug din kunun ta kama hanya ta fita.

Saliha tace." Wallahi Baba idan ta dawo da kwanukan kada kiyi amfani dasu domin ba kowa za ta kai wa sai wannan mahaukacin.'

Tace." Saliha ya zanyi da Shahida, na yi magana cibi ya zama 'kari, na zuba mata ido kawai amma ya zama dole idan mahaifinki yazo mu tattauna dashi domin ina wani tunani a kan yarinyar."

Tana 'yar dariya tace." Wallahi lafiyarta lau tsabar iskanci ne wai ita mai tausayi watarana sai taje ya buga mata dutse idan haukan nasa ya motsa."

Ta girgiza kai da fadin." Allah ya rufa asiri.

"Wannan naman sallah ne na kawo maka, wannan kuma kunu ne in sha Allahu da rana ma zan kawo maka abinci."

Ya kalleta kafin ya kalli abubuwan da ke gabansa, hannu yasa ya bude kwanon naman babu abinda yayi suyar tayi kyau sosai sai kamshi yake.

Rufe wa yayi kafin ya bude jug din kunun shima da zafinsa sai kamshin lemon tsami yake, sosai kunun ya bashi sha'awa, amma bai nuna a fuskarsa ba.

Sunkuyar da kansa yayi ba tare da yace mata komai ba.

A sanyaye tace." Sannu ko baka da lafiya ne?"

Ya daga mata kai alamun ."Eh." gabadaya jikinta ya mutu kamar za tayi kuka tace." Zazzabi ko ciwon kai.?

Ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ya sassauta fuskarsa yace." Babu ko daya jikina ne yake ciwo."

Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Sannu Allah ya sawwake amma ka daina kwanciya cikin lema dubi abin shimfidar ka a jike ga 'kazanta da kashin awakai dole lalura ta kama ka."

Shuru yayi bai ce komai ba.

Tace." Ka sha kunun sai na tafi na siyo maka magan........Ya buga mata tsawa a burkice yace."Ke! tashi ki bani guri bana so."

Ta tsorota ta mi'ke tsaye tana kallonsa, gabad'aya idanunsa sun jirkice! ya dauki robar ruwan paro ya jefa mata, wanda ya janyo hankalin yara gurin.

Aikuwa suka fara ihu! "Baban-baba mahaukaci! Baban Baba mai annakiya." wasu suka fara tsintar duwatsu suna jifansa tare da tofa masa yawu, sai su ruga a guje suna dariya.

'Karkashin motar ya shige ya takure jikinsa guri daya yana makyarkyata!

Ita kuwa zuciyarta a 'kuntacce ta bar gurin wani k'atoton abu ya tokare mata a wuya tana shiga gidan kai tsaye daki ta nufa ta kwanta saman gado tare da fashewa da wani irin kuka!
Kuka taci ta koshi ta fito idanunta jawur! babu wanda ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka aikin gabansu kawai suke, murya a dashe tace."Baba ina gyadar take.?

Da hannu ta nuna mata. ta cigaba da aikin gabanta zuciyarta cike da kunci da takaicin halin da yarinyar take 'kokarin jefa kanta.

****
"Wai ana sallama da maigidan." muryar wani yaro kenan, yayin da aka aiko shi yayi sallama da Hujaj.

Jamila ce ta fito da fadin." Ba ya nan.'' yaron ya juya ya fita, minti biyu ya dawo da fadin." Wai idan ya dawo a fada masa cewa Saminu abbatuwa yana nemansa."

Tace." To za'a fada masa.

Da ya dawo gidan Talatu ta sheda masa cewa wani yazo nemansa mai suna Saminu Abbatuwa, ko gezau bai yi ba ballanatana ya razana, cin bashi dai ba akansa aka fara ba, kuma sai yana dashi zai bayar.

Hankalinsa a kwance ya cire babbar rigar jikinsa ya rataye, ya kashingida yana tunanin yanda za'ayi kudi su shigo masa, kwana biyu kamar wanda a kayi wa baki gurin sana'ar tasu haka yake dawowa babu ko sisi a aljihunsa, hakan kuma baya ha nashi gobe ya koma da wani abun nashi domin samun nasara da nin ka abinda ya bayar.

*LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV*
[9/7, 10:42] bintaumarabbale: _MAJNUN!_
*'BOYAYYAN -ATTAJIRI*
_NA_
*_BINTA UMAR ABBALE🍒_*

_MANAZARTA WRITES ASSO_
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_

*25&26*
Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki yaji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai yace." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? tabe baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi musu, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu.

Babu ladabi a maganarta tace." sai ranar da akayi hankali nima zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo.

Tace." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi."

Yana kokarin tashi zaune yace."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan."

"Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya ne."?

Yana kokarin magana su kaji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana tsaye fa yana jiran Maigidan a waje."

Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana k'unk'uni.

Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, tace." Da alama dai wannan mutumin kudi yake bin ka."

Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa.

Tace." Kai har mai ka siya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bukatar auran 'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji."

Yace." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri."

Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta kama hanya ta fita daga dakin tana surutai.

Jallabiya yasa ya fita.

Wani shirgegen katon mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne.

Ya mika masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo."

Ba tare da ya rike hannun da ya mika masa ba yace." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba."

Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna kaji Uzuri na, ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka."
Chapter 4 · 0% Book details