← Book details Majanuni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 11

Sashe 2

Majanuni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta tashi ta fita gabanta na wani irin fad'uwa! akwai dalilin da yasa ta tambaye shi saboda sanin halinsa mugun dan rigima ne zai iya zuwa yaci bashin mutane duk domin yazo yayi bajinta burga! da neman suna a cikin unguwa babban burinsa ace masa ya isa shi mai kudi ne.

Hasashenta ya tabbata domin kuwa bayan fitar ta, ya zurfafa cikin tunanin hanyar da zai bi gurin ganin ya biya mahaucin da ya kar'bi *SAH!* da ragon a gurinsa.

Yayi nazari ya hanga ya hango a yanzu dai bashi da dubu dari uku da hamsin din da zai biya mutumin idan ba gidan da yake ciki a zaune zai daga ya siyar ba.

Dama yasa ran samun wasu kud'i ne sai kuma asara ta same shi, domin hak'ansa bai cimma ruwa ba, a gurin sana'ar tasu shine ya tashi fanko fayau!(ziro) hatta da motarsa bata tsira ba sai da aka kwamushe haka ya dawo gida a motar haya.

Kwabo yanzu babu a cikin account dinsa sai 'yan canjin dake hannunsa, gabadaya tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin hanyar da zai biya mahaucin kud'insa.

Ta shiga dakin tana gyara daurin zanin jikinta da yayi muguwar daud'a sai karni take fuskarta na maiko.

Kerere ta tsaya a kansa da fadin." Babu icce ya 'kare ga kuma uban 'kashi can da za'a soya yanzu dai abunda ake bukata icce da man gyada."

A sakarce ya kalleta yaji wani mugun takaici ya turnuke shi, ta tsaya masa aka kerere! ba ta san halin da yake ciki ba, girgiza kansa yayi yace." Je ki zan fito yanzu na bada kudin."

Ta juya ta fita bagazan-bagazan!

Ya fito tsakar gidan yana nazarinsu. babu Shahida a cikinsu ta tafi, wato da yace ta tsaya ta tafi da nata rabon shine ta kama hanya ta tafi, shikkenan ai tayi wa kanta, waje ya fita minti biyar ya dawo gidan tare da zaratan samari biyu, a yanzu dai bashi da kudin icce ballantana wani man gyada, saboda haka ya yanke shawarar bada sadakar naman da niyya biyu.

Ganin abinda yake shirin faruwa yasa ta fito afujajan! baki na rawa tace." A'a ya haka kuma." ?

Bai saurareta ba ya cigaba da loda tsoka da k'ashi cikin buhu yana fadin gidajan da za'a kai musu.

Talatu kamar ta dora hannu ta kurma ihu! jikinta sai rawa yake tana fadin." Ya haka ina za'a kai kuma."?

Yace." Na bayar sadaka dama haka Allah yace ayi saboda haka wannan na cikin kaskon ya ishe ku."

Idonta ya ciko da ruwan hawaye ta dinga zabga masa harara! wannan ai wulakanci ne! duka na cikin kaskon bai fi ya cika bokin fenti ba.

Su Hadiza ma jikinsu ne duk ya mutu saboda ganin yankan kaunar da mahaifin nasu yake musu.

Kaf ya kwashe naman ya bayar, ya bar musu kadan hatta da kawunan dabbobin da gandar dake shanye a buhu bai bari ba sai da ya bayar, dalili baya bukatar ta sake zuwar masa da wata bukata ta siyan icce ko man gyada da makamantansu.

*LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV*
[9/7, 10:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_
*'BOYAYYAN -ATTAJIRI*
_NA_
*_BINTA UMAR ABBALE🍒_*

_MANAZARTA WRITES ASSO_
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_

*21&22*
Talatu tare dasu Hadiza kamar su mutu saboda takaicin da Hujaj ya k'unsha musu, babu shakka ya cutar dasu, domin naman da ya bar musu bai taka kara ya karya ba, da 'kyar zai kai sati d'aya, gashi sun ci burin ajiyar nama saboda bayan sallah idan kwadayi ya tashi su fito dashi su gyara abinsu, Talatu dai kasa hakuri tayi ta shige daki tana matsar hawayen bakin ciki, tunanin hanyar da zata kuntata masa take.

'Bangaran sa kuwa har ya manta abunda ya aikata domin wanka yayi ya shirya cikin sabon yadi mai tsada anyi aikin kufta a wuyan rigar da hannuwa, ya dora hula zannar bukar a kansa ya fito yana kamshin tsadaddan turaransa.

Yaran ya samu sunyi jugum-jugum! kamar anyi mutuwa.

Ya kallesu na minti biyu kafin ya girgiza kansa ya kama hanyar fita ba tare da yayi musu magana ba, Jamila ce kawai ta iya yi masa a dawo lafiya Hadiza da Amina kuwa harara suka bi shi da ita yana fita Hadiza taja tsaki ta mike tsaye tana kunkuni! daki ta shiga, Jamila ta bita da kallon mamaki! ita kuwa Amina bakin kasko ta nufa ta juya naman dake kan wuta kafin ta tsamo katuwar tsoka tasa a bakinta tana taunawa tare da hure zafin dake barazanar 'kona mata dadashi.

***
Jiki a sabule ta koma gida. Abin duniya yayi mata katutu! matsalar Baban-Baba ita tafi damunta, sai kuma matsalar mahaifinta, sharadin daya gindaya mata na fito da mijin aure cikin wata uku yayi mata tsauri! ba ta da madogara sai Allah domin kuwa babu wani namiji da ya nuna yana sonta ballanatana har su kai ga maganar aure.

Sallah ta wuce da sati biyu da yawa daga cikin wa'inda sukayi layya sun cinye naman su, har sun fara siyan na miya, ita kanta Baba Asabe da ta yanka RAGO a yanzu bata da nama sai diddiga da kakide domin ba tayi son zuciya ba tayi sadaka da naman kamar yanda Ubangiji ya umarta Saliha ma tuntuni ta cinye nata, Shahida ce kawai mai nama a gidan ta kime shi a cikin kakide ta boye a karkashin gado ita bata ci ba, ba kuma ta bawa wani yaci ba yana ajiye.

Tana zaune a tsakar rumfa tana taimakawa Baban da daurin gishiri taji motsi a cikin uwar daki.

Haka kawai jikinta ya bata wani abu, da sauri ta ajiye gishirin dake hannunta ta shiga dakin wanda yayi dai-dai da lokacin da Saliha ta janyo kwanon naman da ta boye a karkashin gado.

Suka had'a ido Saliha ta diriri ce! sai ta wayance da fadin." Ke ni ba naman ki zan ci ba ina neman warin takalmi na ne."

Tsaki taja ta dauke kwanon naman da fadin." Saliha ko kinfi kud'a maita wannan naman yafi karfinki wallahi domin wanda na ajiye wa ya fiki daraja a guri na."

Saliha ta fusata! "Ni ce mayya."

Tace." Me yasa to zaki zo kina min binkice naman nan an raba an baki naki kin cinye, sai kuma ki dinga bibiyar nawa."

Tace." Don Uwarki sharri zakayi min naman banza naman wof.......! Shigowar Baban ya katse maganar tace." Menene wai ? tun daga soro nake jin hayaniyarku."

Cikin yanayin maganar ta tace." Nama na zata satar min shine don na ganta take borin kunya."

Cike da mamaki tace." A ina ki ka samu nama ke kuma."?

Tace." Wanda ki ka bani ne na boye abina."

Tace." Meye amfanin boye wa sai ya lalace yanzu lokacin zafi ne gwara ki fito dashi ki cinye ni bana san neman fitina."

Kai tsaye tace ." Baban-Baba na ajiye wa."

Gabadaya suka zuba mata ido.

Baban ta sake maimaita maganar." Ki kace Baban-Baba ki ka ajiye wa ."?

Ta gyada kai alamun "E."

Ba ta iya cewa komai ba kawai ta kama hanya ta fita daga dakin da tunanin wani abu a ranta, lallai dole ne idan Kawu Musu yazo ta sheda masa abinda ke faruwa domin ta fara zargin wani a cikin ranta.

*ABUJA*
Tun daga bakin Estate din zaka gane lallai mazauna gurin manya mutane ne, gida hudu ne kacal sai tarin sucurites wanda suke kai kawo a gurin, can gefe kuma wasu lafiyayyun karnunaka ne biyu a kwance da alama suna rama bashin baccin da suka ci.

Gida daya a cikin hud'un yafi tsaruwa da burgewa yanayin ginin zai baka sha'awa sosai babu shirman kyale-kyale irin na almubazzaranci.

Daga saman babban gate din da ya katange gidan anyi ado da suna Annabi Muhammad SAW da gold an rufe da wani irin glass mai mutukar daukar ido daga ciki wasu irin fitilu ne da suke bada haske kala-kala sai dare abin yake sake k'ayatuwa da jan hankali.

Ginin tsakiya ne wanda yake dauke da bangare uku sai filin ball dake can gefe da parking spece a in da yake dace, sai kuma gurin hutawa wanda akayi masa ado da wasu irin kujeru masu kyau da daukar hankali.

Suna tsaye sanye da bakaken kaya a bakin kofar suna dakwan fitowarsa, Adamu ne da Sule Escort dinshi.

Yana zaune a gabanta kafafunshi a tankwashe kamar karamin yaro da alama Umarninta yake jira."

Hajiya Saude ce kakarsa wacce ta haifi mahaifinsa ita kadai ce ta rage masa a duniya ita kuma yake gani yayi farin ciki duk mai son yaga walwalarsa ya mutunta ta, mai san ganin dariyarsa ya daraja ta.

"Hajiya lokaci na tafiya." Ya fada yana duba tsadaddan agogon dake daure a hannunsa.
Chapter 2 · 0% Book details